← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 116

Sashe 72

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A hankali take jin sautin wak'ar da tasa yana ratsa mata jiki da jini har zuwa cikin zuciyarta a hankali ta bud'e bakinta ta fara bin wak'ar.
Yayinda akejin muryarta na gaurayewa da muryar mawak'an dan ta rage sautin hakan yasa abin ya had'e yake bada wani sok'o mai armashi wanda da zaran kajita kasan wani takewa baitukan,
lumshe ido tayi tare da bin sautin waƙar a hankali take cewa.
"Soyayyar dake raina bazan sauya ra'ayi ba."
sai kuma ta bud'esu tare daci gaba da cewa.
"Nayi lullubi kamar na ango da amarya."
sai kuma ta d'an d'aga sautinta kad'an taci gaba da rere wak'ar.
"So yanada dad'eeeee maso dashen wani ya shiga haushi."
sai ta kuma d'an k'ara volume na radio kana taci gaba bin waƙar.
"Soyayya ta zahiri ba'ayi mata gudun barewa."
sai kuma wani sassanyan shesshek'a ya danne mata harshenta wanda kowa yaji salon yadda muryarta ke fita zai iya gane tana kuka da zubda hawaye take bin wak'ar cikin tsananin tausasa lafazi take cewa.
"In nayi rashin sautinka zan fad'a k'inshi ruwa.
Idan har na barka aban sona bani da kowa.
Dana ganka sai na wadatu da k'oshi bani yunwa.
Duba ka gani tsuntsun k'auna ya zana barewa.
Girgije samani tai lub-lub, lif tana zubar ruwa.
Ga itatuwa koraye d'orowa da sanwa."
sai kuma ta lumshe idanunta hayenta suka samu daman zubowa sannan taci gaba cewa.
"Munshiga ginin sha'awa ga iska tana kad'awa.
Da k'auna tabi jiki an komawa wa da k'anwa.
a hankali ta lumshe idanunta yayinda hawayenta sukaci gaba da kwaranyowa,
tana ganin wayarta nata kawo haske alamun ana kiranta amman bata da tunanin d'agawa,
murya na rawa taci gaba da bin baitukan wak'ar a hankali take cewa.
"Jikina yana jurar rab'ar wata soyayya.
sai kuma ta d'an d'aga murya da ɗan ƙarfi kana tace.
*"Nayi adanin soyayyata bani baiwa kowa!*
Barewa batayi gudu d'anta ya rarrafaba,
*Soyayyar dake raina bazan mata kishiya ba.*
sai kuma ta lumshe ida nunta kana ta buɗi baki a hankali ta taci gaba da raira wasu baitukan da yafi kama da amsa take bawa ƴan Nakasa ba kasawa bace fans 2, murya a tausashe take cewa.
*Mai sukar masoya bai san sirrin zuciya ba.*
_Idan na rasata jiki bazai daina bariba_
*baniwa masoyi rowar tattausan lafaziba.*
_K'auna ke gushe haushi so bazai canja wuriba
So in yayi kewar gani aso bazai tsayaba."_
Tana ganin ana danna mata danja alamun akwai matsala amman bata kulaba,
saima ta k'ara d'aga muryarta ta gaurayeta da muryar mawak'a har nata yana d'an d'ara na radio take cewa.
*"Bani bada rancen k'auna bazanyi aroba!.*
*Na dad'e ina rarrafe cikin masu soyayya!.*
*Gashi nayi fincinkawau misalin gudun barewa!.*

Hakafa tayi ta sakin wak'ok'i masu jijjiga zuk'atan masoya wanda duk yaji yasan abin daga cikin zuciyarta ne.
Koda akazo dan a shiga a ankarar da ita sai aka samu ta kulle k'ofar, a k'arshe dai saida tayi 35 minutes tana caccanza wak'ok'i wanda a zahiri ma program nata 30 minutes ne.
Saida taga kuka zaici k'arfinta ne ta mik'e da sauri ta fita.
A bakin k'ofar ta samu Raveel da manager da Aminiyarta Bilkisu maigado dama wasu maikatan nasu.
ido suka zuba mata ganin hawaye har kan habarta,
sannan kuma ta wucesu da sassarfa,
kai tsaye parking lot nasu ta nufa tana shiga motar a guje ta bar aharabar ma'aikan nasu.

Maigadoce tayi sauri ta shiga cikin d'akin dan gabatar da shirinta.
Raveel kuwa da sauri yabi bayanta,
shi kuwa manager ko motsi ya gazayi.

Shida saura minti goma ta isa bakin gate d'in gidansu,
tana k'ok'arin danna hancin motarta cikin gidan taga wasu tsala-tsalan motoci guda uku suna fitowa a jere, bisa dukkan alamu manyan mutanene masu kamala,
dan haka ta d'an tsagaita,
Suka fita ido ta d'an zaro dai-dai lokacin da mota ta ukun ta iso inda take murya na rawa tace.
"Abdussalam, kuma da iyayenshi a gidanmu." da sauri ta zaro ido...!

A can Mumbai babban birnin k'asar India kuwa.
Hayatuddeen ke zaune gefen Saifuddeen,
yana yanke mishi farcen kafafunshi ne ya d'an d'ago kanshi sannan ya zaro wayarshi daketa ringing a cikin al'jihunshi da sauri yayi picking call d'in sabida ganin number k'asarshi Nigeria kuma video call ne,
yana d'aga yayi murmushi tare da zazzaro ido ganin Amina ce nurse d'innan da take kula da Saifuddeen lokacin da suke Abuja,
fuska a sake yace.
"Amina kece?." hararanshi ta d'anyi tare tsuke fuska sannan tace.
"Amina gatsal babu karanta min Aunty."
Dariya ya d'anyi tare da cewa.
"Ke nafa fiki tsawo."
"To dai ai tsawon ka fini ba shekaru ba. "
ta bashi amsa cikin wasa.
murmushi yayi sannan yace.
"To idan dai kina son in ce miki Aunty to ki dage ki k'ara tsawo."
ido ta lumshe tare da fidda sassanyan nufashi kana tace.
"Ina Hamma Saifuddeen? Ya jikinshi? Da sauk'i sosai ko? yana tashi zaune da kanshi?."
kai ya liggob'ar tare da cewa.
"Wayyo Allah na to wacce tambaya d'aya nasan zan amsa miki?."
cikin zak'uwa tace.
'"Duka zaka amsa min."
murmushi yayi kana yace.
"A ina kika samu wannan number tawa?."
"Kai dai me ruwanka da inda na samu number kawai gaya min ya jikin Hamma."
cikin halinshi na tsokana yace.
"In baki gaya min inda kika samu number taba yasee bazan baki amsoshinkiba."
Da sauri tace.
"Dr Aliyu na tambaya shi ya bani dan Allah nuna min shi."
murmushi yayi tare da kallon Saifuddeen dake konce amman a jingine in ka ganshi kamar a zaune.
Da sauri ya dawo saitin Saifuddeen d'in dan ganin yana tambayarshi da waye yake mgn.
Dai-daita fuskokinsu yayi da fuskantar wayar yadda zasuga juna da kyau,
kana yace.
"To gashi ina shine amsar tambayoyinki."
yana fad'in haka ya mik'e ya koma wurin kafafun Saifuddeen yaci gaba da yanke mishi k'ummarshi.

Ita kuwa Amina cikin wani irin yanayi mai cike da farin cikin ganinshi tayi mishi wani tattausan murmushi murya can k'asan mak'oshi tace.
"Fatabarakallahu hasanil Kalil'in."
sai kuma ta lumshe ido tare sake bud'esu fuskarshi ta zubawa ido na tsawon 37 second a hankali tace.
"Wallahi a duk iya tsawon rayuwata ban tab'a ganin wani mahluk'in da *Saje* yayi mishi kyau koda kwatankwacin rabin yadda Saje yayi maka kyauba."
sai ta kuma tonkoshe kanta bisa kafad'anta na dama tare da cewa.
"Darajar sajen wannan kekyawar fuskartaka yasa idanuna gaza barin kallonka,
Hamma Saifuddeen kana kallon kanka a madubi kuwa, ? antaba ce maka kai kekyawa ne kuwa?. "
Shiru yayi ko numfashi a hankali yake fiddawa yayinda ya zubawa motsin bakinta ido yadda yana gane duk abinda take cewa,
kana yayi dib ya nuna mata sam baya gane komai.
ita kuwa a zatonta Hayatuddeen ya fitane gashi shi kuma kurmane hakan yasa taci gaba da fadin sirrin zuciyarta .
"Saje ya maka kyau in nace maka kyau ina nufin zazzafan kyawun da in dai mutun ba farin sani yayi makaba, in dai irin gani ɗaya zuwa biyu ne to wlh-wllhi bazai taɓa ganekaba duk yadda ya kai da rik'e kamanni!. in dai ba'ance mishi kai bane
Da kana jina da sai in ce maka.
Dan Allah da darajar iyayenmu dan alfarman anabi da Qur'an kada ka sake aske sajen fuskarka ka barshi dan soyayyarka da manzonmu saje da gemu alamace ta nagarta, kaikuwa managarci ne please kada ka aske min sajen nan."
Cikin wani irin yanayi ya rumtse idanunshi da k'arfi jin tana cewa.
"Ina sonk...!

Hahahaha wasa farin girki

BY
*GARKUWAR FULANI*
8/18/20, 7:53 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

        *NAKASA BA KASAWA BACE*

*Page 22*

*NA*

*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

_FREEE PAGE SUN ƘARE DAGA PAGE 22 IN KA/KIN SAKE GANI PAGE ƊIN A WASU GROUPS ƊIN SUNA YAWO DAI TO BABU SHAKKA NA SATANE, ƁARAYI ZASU FITAR BANI BA_

*FREE PAGES DAI SUN ƘARE KAT DAGA YAU SHINE ƘARSHEN FREE PAGE DAGA WANNAN FAPE 22 ƊIN AN ƘARE FREE PAGE, BIYA ƊARINKI UKU KACAL DAN CI GABA DA KARANCE LITTAFIN DAGA FORKO HAR ƘARSHE, TURO KATIN MTN NA 300 KACAL TA WANNAN NUMBER 09097853276 KO KUMA KA/KIYI MIN TRANSFER TA ASUSUNA NA JAIZ 0005388578 JAIZ BANK AISHA ALIYU GARKUWA, SAI KA/KI TURO SHAIDAR BIYANKI TA WANNAN NO DAI 09097853276. IN KA/KINSAN BAKI BIYA ƘUƊIN KARANTA LITTAFINBA NA ROƘEKI DA ALLAH KADAMA KI NEMA BARE KI KARANTA*

_AKWAI KAYAN GYARA NA MUSAMMAN GA MASU BUƘATA AMARE DA UWAR GIDAYE, INA BADA SAYAN ƊAƊƊAYA KO SARI, akwai abubuwa masu zafi da inƙanci kamarsu. Sumin, tartai na ƙasar chadi, akwai tsumi mai riɗi na sokotawa, akwai zumar gembu membila, akwai garin daka na mallaka da garin maɗi mai haɗe mace daga ciki akwai sa buzu kuwa, akwai garin sakayawa da garin da ba'a baiwa mai kishiya akwai ɗan batta akwai gimbiyar mata da kwanon ƙasaitacciyar mace akwai garin carmazaƙwoi akwai na gyara nono da mgnin narkanwa akwai butar sirri, akwai garin yaji na maza da kuma sabulan gyara jiki da mayuka akwai jigidar sirri kana akwai magungunan sanyi masu inƙanci, da dai sauransu.... sayan na gari maida kuɗi gida, duk inda kike ina aika kaya, inada reshena a Gombe Yola da kuma Sokoto da mai buƙata ka/ki tuntuɓeni ta wannan numɓer 09097853276,_
Chapter 72 · 0% Book details