← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 116

Sashe 73

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina son kabar sajennan afuskar ka, saboda ya matuƙar yi maka kyau sosai. irin kyan da ban tab'a ganin saje yayiwa fuskar wani d'a namiji kyau ba. Lumshe ido tayi tare yin k'asa da murya tace.
"Kayi kyau fuskarka ta zama mai cikekkiyar kyau da haiba."
Yanayin yanda ta faɗi maganar cikin  shauƙi shiya sanya Hayatuddeen dake gefe sakin dariya tare da cewa.
"Dagaske ashe sajennan yayi masa kyau? karki damu bazamu bari ya aske ba! tunda kin yaba, dan da alamu dai kin ƙyatsa ko".
Wani irin tsananin kunyane ya rufe Amina don sam bata taɓa kawowa aranta cewa Hayatuddeen na nan ba duk zatonta ya fita ne.  Hannayenta tasanya ta rufe fuskarta da sauri tare da datse ƙiran tana murmushi mai cike da tsantsar nishadi da farin cikin gani Saifuddeen.
Shima Hayatuddeen dariya yakeyi sosai musamman yanda yaga Hamman nashi yayi jigum yana kallon bakinta tamkar wani me ɗaukan karatu ko k'ibta idon bayayi, saidai ya rage girman idanun nashi,
tabbas yayi imani cewa Amina batasan da cewa Hammanshi na fahimtar maganar mutunba idan yana kallon bakin me maganar ba, tabbas da batayi wannan katoɓarar ba.
Shikuwa Saifuddeen idanunsa ya mayar ya rufe yana mejin yanda heart ɗinsa ke beating, sam yarasa ma tunanin me zaiyi hakan yasa yanemi ƙaƙalowa kansa bacci.

***
A nan Nigeria kuwa Zaliha jiki asaluɓe haka kuma zuciyarta ɗauke da mamakin ganin Abdussalam da iyayensa acikin gidansu ta tura hancin motar tata cikin gidan.
Tana gama dai-dai-ta parking ta ɗauki ƴar jakanta me kyau tare da buɗe murfin motar ta fito. 
Kaitsaye ɓangaren Mamy Hajiyar Ya Ahmad ta nufa, da sallama ɗauke abakinta ta kutsa kanta cikin falon, Mamy dake zaune akan kujera ta amsa mata sallaman nata fuska ɗauke da murmushi.
"Mamy sannu da gida". tafaɗa tana me nufar inda makeken fridge ɗin dake cikin falon yake.
"Yauwa Zaliha ya wajen aikin naku?".
cewar Mamy data maida hankalinta ga tv.
"Alhamdulillah". tabawa Mamy amsa tana me ƙoƙarin kafa bakinta ajikin goran ruwan data ɗauka acikin fridge, dawowa cikin falon tayi tare da kwantawa akan kujera kana ta lumshe gajiyayyun idanunta wandanda suke cike da zallar zazzafar soyayyan Saifuddeen, wanda kullum take k'ara narkar da zuciyarta.
Zahira ce tashigo cikin falon daɗan sauri, ganin Zaliha kwance yasanya taɗan tsaya tare da cewa
"Laaa Adda Zalee dama kina nan?".
Harara Zaliha ta wurga mata tare dacewa.
"Da bananan ai bazaki ganni ba!".
  dariya Zahira tayi tare da cewa.
"Dama kina da baƙo a BQ yanajiran dawowarki".
Idanu Zaliha ta ɗan zaro cike da mamaki tace.
"Baƙo kuma wajena yazo?". 
Mamy dake jinsu ne tayi murmushi tare da cewa "Bak'ofa akace miki ba dodoba, kike wani zaro ido Abdussalam ne yazo".
Jitayi gabanta ya faɗi don sai yanzune ma tatuno ganin da tayi musu shida iyayensa a lokacin da zata shigo cikin gidan, fuska ta kwaɓe tare da langwaɓar da kanta gefe, murya asanyaye tace.
"Ayya Mamy mekuma yazoyi?".

"Me kuwa zaizo yi idan ba abun da bakyaso ba, kullum muna miki faɗa akan kifitar da tsayayye guda ɗaya amma kinƙi, to dai Abdussalam kam yagaji da wainasa da kikeyi yaturo iyayensa sun nema masa izinin zuwa zance awajen mahaifinki, ko tantama banayi kuma nasan ya amince musu!"
Wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya tsaya amaƙoshin Zaliha, take haushin Abdussalam ya cika ranta, meyasa zaiyi mata haka batare da ya tsaya yaji ta bakinta ba? ɗan ƙaramin bakinta ta turo gaba tare da komawa ta kwanta.
"Tashi kije ko bakiji Zahira tace nemanki akeyi ba,
Kije ki sameshi ku fuskanci juna, inafa gaya miki Zaleeha kada ki bari ki k'ure Malam kinfa sanshi kaifi d'aya ne zafa kiyi kuka a sanda babu mai lallashinki".
Mamy tafaɗa cike da kulawa,
cikin turo baki gaba Zaliha ta-tashi daga kwancen da take tare da ɗaukan hand bag ɗinta tafice, sashinsu ta nufa fuskarnan tata babu fara'a ko kaɗan,  harta kusa kaiwa ɗakinta taji muryar mahaifiyarta inda take cewa.
"Da kika dawo tun ɗazu kika tsaya shashancinki bakisan cewa kina da baƙo bane?".    bakinta taƙara turowa gaba tare da cewa.
"Ni agajiye nake yaje sai wani lokaci kawai".
  kallon bata da hankali Mahaifiyarta ta tayi mata tare da cewa
"Zaki shirya kije ki samesa ne ko ko sai na ɓata miki rai yaro yazo yana son ganinki kice yaje sai wata rana shi bawan gidanku ne, ko kin mance shi d'an wanene?".  
ganin yanda mahaifiyarta ta ta haɗe fuska ne yasanya ta buɗe ɗakinta ta shige tana me guna-guni acikin ranta, kayan jikinta ta rage tare da faɗawa bathroom, haka tayi wanka ranta duk acushe, koda ta fito sama sama ta shafa lotion ajikinta, riga da sket na wani purpule ɗin material tasanya, sosai kayan suka amshi jikinta sukayi ɗas. kallon kanta tayi amadubi, tabbas ita kanta tasan cewa kyawunta ya zarce misali, sannan tanada diri irin wanda ke ɗaukan hankalin maza,  yanda takeji aranta yasanya bata jin zama ta iyayin kwalliya akan fuskarta, saidai kuma abun da batasani ba shine ko babu kwalliya akan fuskarta tauraron kyawunta haskawa yake, farfumed ta fesa ajikinta me daɗin ƙamshi kana ta ɗauki wani purpule ɗin mayafi tayafa ajikinta, normal flat shoe ta zura aƙafanta kana ta murɗa handle ɗin ƙofar tafice, BQ ta nufa inda tuni tasake sanja yanayin fuskarta.

  Sallama tayi can aƙasan maƙoshinta haka ta tura kofar katafaren falon tashiga. 
duk da cewa sautin sallaman nata baifito sosai ba amma yaji sautin acikin kunnuwansa, lumshe idanunsa yayi sakamakon wani daddaɗan ƙamshi daya kawowa hancinsa ziyara, ahankali ya amsa mata da "Wa'alaikissalam!"    Cikin takunta me ɗauke da nutsuwa taƙaraso cikin falon tare da zama akan wata kujera dake nesa da wanda yake kai. 
Murmushi Abdussalam yayi tare da cewa
"Barka da dawowa gimbiyar mata, kiyi haƙuri kindawo kuma na hanaki hutawa".   ɗan satan kallon inda yake tayi tare da ɗauke kanta gefe, sanin cewa ba lallai tayi magana ba yasanyashi cigaba da cewa
"Kiyi hakuri nima zazzafar soyayyarki ce take hanani hutawa, ita ke ingizani wurin kafa naci.
Haƙiƙa yau ina cikin farinciki kasancewar nasamu izinin zuwa wajenki daga wajen Malam.
Ina sonki Zaliha ina miki so me tsanani, tabbas kina da wata irin baiwa ta musamman wanda duk wani ɗa namiji idan yaganki dole zaiji wani abu dangane dake, burina bazai wuce naga na sameki amatsayin mata ta ba, dan Allah Zaliha ki amincemin ki duba girman soyayyar danake miki!". yaƙare maganar cikin yanayi na kwantar da murya.
wani murmushi Zaliha tayi wanda ya sake bayyana asalin kyawunta, bakomai yasata murmushin ba kuwa face jin ta tsuniyar da Abdussalam keyi mata akan wai yana fatan tazamowarta mata agaresa,  lumshe kyawawan idanunta wanda ke masifar jan hankalin maza tayi tare da jingina bayanta da jikin kujera,  hoton kyakkyawar fuskarsa ne ke yawo acikin idanunta koda yaushe, wani irin azababben so da shauƙin ganinsa ne suka dirar mata alokaci guda, take yanayinta ya sauya wani irin sanyi taji na shiga jikinta,  ƙwaƙwalwarta ne ta tuna no mata lokacin data kalli cikin idanunsa, tsikar jikinta ne taji yatashi yayinda taji zuciyarta na bugawa da sauri-sauri ji take kamar tayi ta shelanta duniya tana sonshi tana kuma nemanshi da buƙatar ganinshi. 
Abdussalam kuwa ganin tayi shiru kamar ma bata cikin hayyacinta yasanyashi ƙiran sunanta murya asanyaye yace.
"Zaliha!".
Ƙiran sunanta dayayi shiyayi sanadiyar dawowarta cikin sense ɗinta, ahankali ta buɗe idanunta da suke  cike da shauƙin ganinsa, sam bataso Abdussalam ya katse mata tunaninta ba, kasancewar ayanzu tunaninsa shiya zame mata abincin ruhinta, miƙewa tsaye tayi tare da duban Abdussalam daya ƙafeta da ido.
"Zanshiga gida!". ta faɗa ataƙaice.
Murmushi yayi tare da cewa. "Idan muna tare banaso kiyi nesa dani".
Bakinta taɗan taɓe tare da cewa.
"Saida safe".
Bata tsaya jin wani abu daga bakinsa ba tasakai tafice daga cikin falon, shiru Abdussalam yayi tare da bin bayanta da ido, jin soyayyarta yake tana ratsa ko ina na jikinsa, jiki asanyaye haka ya ɗauki makullin motarsa shima ya fice daga cikin falon.
  Itakuwa Zaliha tana kaiwa part ɗinsu kai tsaye ɗakinta ta wuce, kwanciya tayi luf akan gado tare da hugging pillow, idan da ace za a fasa zuciyarta to tabbas za'atarar da tarin begensa acikinta, wani irin abu takeji dangane dashi na musamman, sake rungume pillow'n tayi tare da sakin wata sassanyar ajiyar zuciya, a hankali take cewa.
"Ina kake? Me sunanka? Meyasa ka taimakane duk da ban sankaba baka sanniba? wani hali kake ciki? Me sukayi maka? Kana ina?." sai kuma ta kife kanta tare da sa kuka mai cike da rauni.

*Mumbai*
Yau tun safe su Hayatuddeen suke asibitin kasancewar yaune ranar da zasu gana da manya manyan likitotin guda hud'u da sukazo musamman dominsu.
Alhamdulillah ƙarfe biyu dai- dai suka samu ganawa da Saifuddeen, sunyi masa duk wani abun daya dace, sosai suka bincikesa suka kuma bashi duk wani iya taimakon da zasu iya, wanda kuma suke sa ran In sha Allah watara komai zai dai-dai-ta.

Bayan wata ɗaya.
Alhamdulillah acikin waƴannan kwanakin da suka gabata abubuwa da yawa sun faru ciki harda zuwan Mudassir, wanda ya shaidawa Ahmad kasuwarsu na buk'atarshi dan haka in jikin Saifuddeen da sauk'i to yayi k'ok'arin dawowa 9j.
kana sosai Saifuddeen ke samun sauƙin.
Zuwa yanzu yakan iya juyawa da kansa ya kwanta ta ɓangaren damansa, in yana rigingine kuma yana iya juyawa hagunshi, sannan yana ɗan iya motsa wasu gaɓɓai dake jikinsa, kuma acikin kwanakin da suka gabata ne.
Dr Akash prasat da Dr Malik khan sukazo har Mumbai ɗin suka duba jikinsa,yayinda agefe kuwa yake samun kyakkyawar kulawa daga wajen Dr Anan mehta da kuma Dr Mahesh khurana da kuma sauran nurses ɗin, sosai yakejin dadin zamansa a asbitin don suna ba sa kulawa ta musamman sosai yake jin canji a jikinshi,  duk da cewa jinya yake amma hakan baisanya kyawunsa gushewa ba, saima wani hasken fata da ya ƙara sabida tsananin hutu da kula da zama wuri mai kyau da ya samu, yayinda wani irin kekyawan saje yasamu mazauni akan kyakkyawar fuskarsa, zaman sajen akan fuskarsa ba ƙaramin ƙarawa fuskarsa kyau yayi ba, domin duk kyan namiji in dai fuskarsa ba saje tofa tsirara take bata da sutura.
    Ganin jikin nasa da sauƙi yasanya Dr Adnan da Ahmad suka shirya akan zasu dawo gida Nigeria. 
Chapter 73 · 0% Book details