← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 116

Sashe 6

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Bayan wata uku
Ranar wata asabar bayan sallan magrib,
duk suna tsakiyar gida, Ummi ta tasa Rahma dasu Raihana da Raliyya suna d'an hira,
Saifuddeen kuwa da Hayatuddeen suna gaban Abba.
mik'ewa Abba yayi kana ya kalli Ummi da yaranta da suke shawarar a saida kayan d'akin Rahma a kaishi asibiti ai mishi aikin mak'ok'on .
murmushi ya d'anyi kana ya d'auki butar dake gefenshi tare da nufar hanyar ban d'aki yana mai ce musu.
"Uhumm Rahma kenan, kada ku yarda ku saida wani abunku a kaina fa, domin wannan ciwon nawa tabbas wata rana shine ajalina."
d'an tsayawa yayi jin Rahma na cewa.
"Dan Allah Abba kayi hak'uri mu kaika asibiti, bazamu iya ganinka hakaba."
murmushi ya kumayi kana yace.
"Rahma iyayena mafa haka sukayi ta nema min mgni k'arshe har suka rasu ban samu lfy ba, hakama k'annena gaba d'aya Ali ya saida gonakinmu da filayanmu na gado,
a kan nema min mgni yanzu du-du du gonaki ukune suka rage sai wannan filin da ke can bayanmu wanda shi kuma dama nine na sayeshi da sunanku.
dan haka ku dena wahal da kanku ai sauk'in yazo."
yana fad'in haka ya juya ya nufi bayan gidan,
a dai-dai bakin k'ofar ya fad'i.
Wanda kafinma a d'agashi ya cika.
Wannan rana anga tashin hankalin wannan ahlin,
dole Abba kwanan keso yayi,
washe gari da hantsi akayi mishi sutura, wanda tuni k'ofar gidansu ta cika da al'ummar annabi.
Bayan an mishi sutura an kimtsashi kamar yadda musulunci ya koyar damu
anzo za'a d'auki makar ne za'a fiddashi.
da sauri Bappa Ali ya kalli Saifuddeen daya rik'e makarar yanayin wani irin kukan da yasa dukkan bani adam dake wurin zubda zazzafan hawaye,
tuni shima Bappa Ali sai ya zame kana ya ruggumi Saifuddeen da Hayatuddeen dake ruggume dashi, kuka sukeyi wanda duk kan mai imani zai tausaya musu.
shi kam Saifuddeen duniya ta mishi zafi ji yakeyi tamkar bai tab'a farin cikiba, fata yake inama shima mutuwar tazo ta d'aukeshi.
tausayin kanshi da mahaifiyarsu da k'anneshi da yayarshi yakeji tamkar zai d'auke numfashi sa.
Man Liman ne suka janye bappa Ali kana Baba Hamisu yasa hannu ya janye hannun Saufuddeen daga rik'on da yayiwa makarar.
Baba Ashiru kuwa da wani abokinshi wanda kuma malamin islamiyarsu Saifuddeen ne sune suka kamashi ganin yanayin da yake ciki,
cikin sanyi Baba Ashiru ya cewa Hayatudden.
"Deen je ka kawo min ruwa.
cikin kuka ya mik'e kana ya kawo ruwan amsa yayi kana ya kalli Saifuddeen da idanunshi sukayi jazir tamkar zasuyi aman wuta, ganin bazai k'arb'a bane yasa Malaminshi amsar ruwan ya kai mishi har baki,
kana cikin sanyin murya yace.
"Saifuddeen kasha ruwa zakaji sanyi a ranka."
a hankali ya fara shan ruwan domin jin zuciyarshi yake tamkar ana soya mishi ita,
ajiyan zuciya ya rink'a sauk'ewa akai akai kana hawayenshi suka tsagaita,
Ya Nuruddeen d'inshi ne ya fad'o mishi a rai, tabbas da yana raye da bazai bari kukansu ya tsanantaba,
wani numfashi yaja kana ya kalli Malamin nashi da yake ce mishi.
"Tashi muje woje Saifuddeen muje ka tsaya a sallaci gawan mahaifinka,
kayi mishi addu'a a madadin kukannan da kake mishi, ka sani dukkan tsanani yana tare da sauk'i in sha Allah muna zatawa d'an uwanka da mahaifinka rahama, kada kayi musu kuka domin su mutanene na gari musu imani da tawakkali basu da abakan musu bare na fada ko gaba,
ka sani babu maraya sai rago, kuma nakasa ba kasawa bace.
Kada kayi ta kuka domin kukanka shi zaisa yan uwanka kuka, kuma kukanku shi zaisa mahaifiyarku kuka har ta kai ga ta kamu da wata cutar ka daure ka jumre ka zama Garkuwarsu."
Cikin tsanani rauni ya mik'e tare da yi mishi alama da yaji zai bari,
daga nan sukaje suka sallaci gawar kana aka kaita makwancinta.
Nan aka zauna zaman makoki.

Yau akayi sadakan Uku, duk da haka Bappa Ali dasu Malam Ashiru da Baba Hamisu dasu Saifuddeen d'in suna zama dan akwai masu zuwa gaisuwa.
Bayan sallan azahar ne duk suna zaune a gindin bishiyar limis dake harabar massalacin k'ofar gidan nasu,
wasu maza su uku sukazo wanda kusan abokan Abban ne bayan sun gaisa ne d'aya daga cikinsu ya zurawa Saifuddeen idanu yana kallonshi ido cikin ido,
shi kuwa Saifuddeen bai kauda idanshi bane dan ganin mutumin yana jujjuya kai alamun zaiyi mgn to sanin in ba kallon bakinshi yakeyi ba bazai gane abinda yake fad'anba shiyasa ya tsurawa mutumin ido,
shi kuwa mutumin cikin jujjuya kai yace.
"Allah sarki duniya mutuwa bata zabi,
Allah bai barin wani dan wani yaji dad'i."
sai ya kuma kalli su Bappa da Malam Ashiru da suke jinjina kai sannan ya meda hankalin shi ga Saifuddeen tare da cewa.
"Da ana bawa mutuwa zab'i ai da an bata zab'i ta d'auke wannan nakasasshen ta bar Nuruddeen da shike kula da rayuwar k'annenshi."
da sauri su Bappa Ali suka zaro ido tare da cewa.
"Subahanallahi Mala Bala wannan wanne irin mugun furuci ne?."
kai jinjina musu tare da jaddada musu cikin rashin iya mgna yace.
"A ai gsky ne Malam Ashiru shi wannan dame zai amfani kanshi ma bare ya amfami wasu,
yaron dashi da dutse bashi da banbanci ai su Rahma sun tagaira da mutuwa ta d'auke Nuruddeen ya bar musu mara amfani,
ko su da kansu ai zasuce da mutuwar ta had'a uban nasu dashi wannan kurman ta yashe su ta bar musu Nuruddeen."
cikin tsananin b'acin rai Malam Ashiru yace.
"Kai tafi daga nan gaisuwa kazo ko cin zarafi?."
Bappa Ali kuwa ya gaza cewa komai sai idanu ya zubawa Saifuddeen wanda ya rumtse idanunshi da tsananin k'arfi dan azabar b'acin ran kalaman da Mala Bala ya mishi gashi abokin mahaifinshi ne ba daman ya mishi wani abun.
Sauran abokansu biyun da suka zo tare da Mala balanne suka mik'e cikin jin haushin kalamanshi suka sallami su bappa Ali tare da basu hak'uri sannan suka tafi.

A daran wannan ranar Saifuddeen yayi kukanda bai tab'a yiba,
inda yake ganin inama shi mutuwar ta d'auke ta bar Ya Nuruddeen d'inshi a ranar mutuwar ta dawo mishi sabuwa a ranshi,
tausayinsu Rahma da Ummi ya hanashi sukuni ya zaiyi ya kula da rayuwarsu? haka dai kwanaki sukayi ta tafiya

Randa akayi sadakan bakyai duk yan uwa suka watse gida ya rage su kadai.
Hakan yasa suka zauna sukayi ta kuka.
Chapter 6 · 0% Book details