← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 116

Sashe 15

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Washe gari kuwa kamar kullum da sassafe suka tafi gombe shida Salisu nan suka wuni kasuwancinsu,
bayan sallan isha suka koma Dukku.

washe gari wanda ana gobe za'a d'au Azumi sabida ana zaton ganin wata yau,
wanda ranar ne kuma Baba bello zai sallami kasuwa sai kuma bayan salla.

Ranar sammako sukayi sosai shida Salisunshi k'arfe bakwai dai-dai na safe suka isa birnin bubayero,
bayan Salisu ya sauk'eshi sai ya tsallaka bakin tashar gombe line,
ya fara d'aukan irin masu kai aike tasha da sanyin safiyan nan.

Shi kuwa Saifuddeen yazo dai-dai mashigar kenan yaga Jabeer ma,
da sauri Jabeer ya iso gabanshi tare da bashi hannu cikin fara'a yace.
"Tab Lallai wannan balaraben dukkun da himma kake wato in junin wani sammako kai a tafe ka kwanako?."
hannu yasa ya d'an bugi k'eyar Jabeer irin ya cika surutu nan.
shi kuwa Jabeer kama hannunshi yayi suka nufi cikin kasuwar da yanzu ake shirin bud'eta sai ya kuma kalli Saifuddeen tare da d'aga mishi gira kana yace.
"Ko dai kudin aure kake nema ne wannan iya sammako haka har ka rigamu mu yan cikin gari,
nima dana fito yanzu yaseen Ya Adamu ne ya matsa wai inzo in kimtsa shagon yau zuwa jibi kayanmu zasu iso zamu fara baza hajar cinikin salla ne."
murmushi ya d'anyi kana ya jinjina mishi hannu alamun mgninka ai.
suna isa shagon Jabeer ya bud'e sannan ya fara kikimtsa wurin,
yayinda Saifuddeen ke taiyashi,
tuni suka kimtsa shagon suka gyara komai yayi ras,
kafin su gama tuni kasuwa ta fara cika duk masu shaguna sun firfito da kayayya kinsu
cikin yin mik'a alamun gajiya.
Jabeer ya kalleshi tare da cewa.
"Yauwa Balarabe jirani bari inzo."
kai ya gyad'a mishi kana ya konta bisa tattausan sallayan daya shimfid'a cikin shagon ga iskan fanka na kad'ashi ido ya lumshe tare da gyara kinciyarshi.
Shi kuwa Jabeer yana fita bakin tashar ya nufa inda wasu masu saida abinci suke,
soyayyan dankali da kwai,
sai gasashiyar kaza ya sai musu kana ya shiga shagon gefen wurin ya saya musu Faro k'ananun roba guda biyu, sai molt,
kana ya juya rik'e da ledojin ya nufi cikin kasuwar.

Bayan ya isa ya tsallaka wani dandamali da akayi wanda yake shamaki tsakanin masu shago da masu sayan kaya,
kusa da Saifuddeen d'in ya zauna bubbud'e musu takardun abincin yayi kana ya kalli Saifuddeen dake konce yanata tab'e baki cikin tsuke fuska yace.
"Ka tashi muyi breakfast."
fuskar ya kuma ya mutsawa tare da jujjuya mishi alamun bazai ciba ya koshi,
ido Jabeer ya tsura mishi domin tabbas yasan wannan d'abi'ace ta fulani yin fulaku wa kowama.
shi kuma Saifuddeen tashi zaune yayi ganin kamar ran Jabeer ya sosu sai ya d'auki ruwa kana ya b'alle marfin sannan ya d'an sha ruwan har kusan rabin robar,
a hankali yayi gyatsa kana ya ajiye goran ruwan sannan ya d'auki na molt,
ya fara k'ok'arin mik'ewa da sauri Jabeer ya rik'o hannunshi kana yace.
"Meyasa ne kake min haka shin baka d'aukeni aboki bako bare in kai matsayin amini."
kai ya jujjuya mishi kana ya zaro bironshi tare da ballan takarda ya rubuta mishi.
"Am so sorry my friend, wlh a k'oshe nake Ummi ta cika min ciki da d'umame yau da kanta taimin dan Adda Rahma taje gidan Goggo Dada can ta kwana,
kana ni bana cin kaza,
shiyasa,
sannan dankalin kuma ba irin suyan da nake so bane akayi shiyasa bazanci ba,
ai dani da kai yanzu mun zarta abokai mun zamma aminai,
ka fahimceni."
yana karantawa yace.
"To gaya min me Kakeso in sayo maka?."
amsar takardar ya kumayi ya juya bayanta kana ya rubuta mishi.
"Am sorry Jabeer ba wai nak'i ci bane haka nan badan wani abu ba because inada wani banzai kyakk'yani wanda ni kaina yana damuna ba ko ina nake iya cin abinciba.
Kaga zansha molt baka tab'a lura daniba haka nake wuni bani cin komai wani lokacin sai dai in had'a molt da pic milk sai insha."
tabbas Jabeer yasan hakane so duk da haka baiji dad'in rashin cin nashiba,
amman dole ya hak'ura dan Saifuddeen da wuya yaci, shi kuwa Saifuddeen tsallaka madandalin yayi kana ya nufi shagonsu Hisham wanda yau cikansa ya zarta na kullum,
bayan sun gaisane yaje ya amshi botikinshi sabida lokacin wasu nata karya kumallonsu so zasu buk'aci ruwa da kayan zak'i.
cikin sa'a kuwa a safiyar yayi ciniki kusan na 3,500
sha d'aya dai-dai ya kuma komawa da nufin k'aro ruwan sai ya samu Baba Bello ya iso yazo wurin yana nemanshi,
haka yasa ya ajiye botikinshi anan shagon su Kabir kana suka juya suka nufi dilan ledodin.
Chapter 15 · 0% Book details