← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 116

Sashe 51

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

A can Abuja kuwa, tunda asuba matar ya Rabi'u Aunty Mami ta tasa yar aikinta gaba suka shiga kitchen, dan Ishaq ya gaya mata da sanyin safiya zasu koma asibitin.
bayan ta gama komai ne ta d'auki na su Ishaq da yayanshi da Hayatudddeen ta kai musu bisa dinning table dake nan men parlour nasu,
inda tunda suka dawo masallaci suna nan zaune suna tattauna matsalar inda shi Hayatuddeen yake cewa shi yafi son a fita woje da Hamma Saifuddeen nashi yaci gaba da cewa.
"Ance Jermaine itace k'asar da tafi shahara da kwarewa ta fannin wannan ciwon, ni kam da zan samu mu fita dashi."
ya k'arishe mgnar yana mai kallon Ishaq da yanayin neman izini.
Cikin tausayawa Ya Rabi'u yace.
"Ba matsala ! Hayatuddeen in sha Allah tun da Dr Aliyu yasa hannu kan lamarin so ko can Jermaine aka kaishi iya abinda yace zasu ce, kana nasan zaiyi duk abinda ya dace in kuma yaga fitar da shid'in nema maslaha to tabbas, nasan zai bada dama a fitar dashi, kuma zai shige mana gaba yadda komai zaizo da sauk'i.
Yanzu ku matso muyi breakfast saimu hanzarta zuwa, tunda ya shaida mana kwana zai a asibitin kana da safe zai dubashi kafin ya tafi gida."
cikin lumshe ido irin na marasa gani Ishaq ya d'an shafa kan Hayatuddeen tare da cewa.
"Zo muje kaci abinci in sha Allah Saifuddeen zai samu lfy."
haka dai sukayi ta bawa juna k'arfin guiwa.

Ummi kuwa sam ta gaza samun sukuni, abinda ta sanine bazata iya cin abinciba, amman ganin yadda Mami ta matsa akan dole taci abinci yasa tace.
"Bani tea kawai in sha."
cikin jin dad'i Mami tace.
"Yauwa Ummi gwara kici wani abu kafin ku tafi domin, bamu san yaushe zaku dawoba, kuma shima zama da yunwa cutane."
amsar cup d'in tayi tare da cewa.
"Sannu Mami Allah ya saka."
Amin tace tare da mik'ewa ta fida dan ta bata wuri, tasan in tana nan ba sha zatayi zabida sabida poolaku irin na al'ummar Dukku.
ita kam Ummi ji take tea d'in tamkar da mad'aci aka tafashi ba sugar ba.
Haka dai ta d'an sha rabi nai, kana ta kimtsa ta fito dan Hayatuddeen ya kirata akan tazo su tafi, tare da Ya Rabi'u da Aunty Mamin suka tafi, ita Ummi da Aunty Mami suna motar ya Rabi'u shiko Hayatuddeen key d'in mota ya Rabi'u ya bashi kana suka taho shida Ishaq.

Shi kuwa Ahmad Abban Farida kenan,
yana gama kimtsawa ya kira Hayatuddeen cikin sa'a ya d'aga bayan sun gaisa ne yake cewa.
"Hayatuddeen wanne asibiti kuke ne?."
cikin sanyi yace.
"Ya Ahmad kazo ne?."
da sauri yace.
"Eh nazo kuma ban san inda kukeba."
meda hankalinshi yayi bisa tuk'in da yake kana yace.
"Kana ina yanzu inzo in d'aukeka?."

masauk'in da yake ya gaya mishi hakan yasa ya juya akalar motarshi ya nufi Royal Hotel,
a harabar hotel d'in suka sameshi,
ba tare da b'ata lokaci ba ya shiga kana suka juya suka tafi.

Su Ummi kuwa suna isaya Ya Rabi'u ya nemi ganin Dr Aliyu nurses en suka ce mishi ya d'an jira nanda 20 minutes.
dan yanzu yana woyane,
haka yasa suka zauna a yar farfajiyar gaban office enshi,
bayan kamar 15 minutes su Hayatuddeen ma suka iso tare da Ahmad nan aka gaggaisa, kana suka zauna zaman jiran lokacin.

Shi kuwa Dr Aliyu da Dr Adnan yake waya inda suka tattauna matsakar.

Bayan ya gamane ya kira nurses guda biyu.
bayan sun shigone ya d'an kallesu tare da kallon ta gefen damanshi yace.
"Amina kin shirya mana komai ko?."
cikin girmamawa da nitsuwa wacce a k'ira da Amina tace.
"Yes sir an gama komai ku ake jira."
sai ya kuma juya ya kalli ta gefen hagunshi tare da cewa.
"Rebeka jeki kira min doctor Ayman."
"OK sir." tace tare da juyawa, wani office nan kusa da nashi ta nufa bayan an bata damar shiga, ta tsaya gaban Dr Ayman tare da cewa.
"Good morning sir."
ba tare daya kalleta ba yace.
"Morning."
gyara nitsuwarta tayi tare da cewa.
"Sir, Dr Aliyu na kiranka ."
kanshi ya d'an d'ago tare da kallonta kana yace.
"OK ."
tana jin haka ta juya ta tafi, shi kuwa Dr Ayman ya fara tattara takardun gabanshi kana ya mik'e yabi bayanta.

Yana shiga ya samu Dr Aliyu tare da Dr Batul, sai nurse guda biyun,
bayan sun d'an tattauna ne,
suka fito cikin shirinsu na aiki.
Cikin mamaki Hayatuddeen ya zubawa Dr Aliyu ido wanda yake cikin welchair bisa dukkam alamu bashi iya mik'ewa cikin sauri yace.
"Ya Ishaq shima wannan gurgun likitane?."
A hankali Ya Rabi'u yace.
"Babba ma kuwa."
ganin sun isone yasa suka d'an matsosu kana suka gaisa ,
cikin kula Dr Aliyu ya kalli Ummi dake rik'e da carbi cikin fullanci yace.
"Ummi kiyi mana addu'ar samun nasara yanzu zamu shiga aiki."
ajiyan zuciya tayi tare da cewa.
"Allah ya baku sa'an aiki yasa ku fara lfy ku gama lfy, Allah ya bashi lfy dama dukkan Al'ummar annabi."
Amin Amin suka amsa baki d'aya,
yayinda Dr Ayman ya kalli Amina tare da cewa.
"Jeki shirya shi kafin mu shigo."
da sauri tace to kana ta nufi room d'in da aka kontar da Saifuddeen.

Suma har sun juya zasu bi bayanta Ummi ta d'anyi gyaran murya sabida muryarta data disashe sabida yawan kuka a hankali tace.
"Doctor Saifuddeen Nakasasshene, baya ji baya mgna, bazai iya ce muku ga abinda ke damunshi sabida shi kurmane."
sai kuma tayi shiru hawaye na zubomata,
Ishaq kuwa cikin karsashi ya amshi mgnar da cewa,
"Ummi kin mance nakasarshi ba kasawa bace,
Allah da yayishi a nakasashe ya kuma bashi basira da hikimar da mai ido baida shi."
sai ya kuma juyawa ya kalli Doctors d'in da suka zuba mishi ido, especially Dr Aliyu da dama burinshi kenan kada nakasa ta zama kasawa ga masu ita.
Shi kuwa Ishaq gyara tsayuwarshi yayi tare da yin taku biyu zuwa uku tamkar ba makaho ba domin babu sanda a hannunshi bare d'an jagora, yana tafiya kamar ko wanne mai ji da gani cikin kula yace.
"Kuna ji ko Doctor's Saifuddeen kurmane, amman yanada hikimar da yake gane duk abinda mutane ke cewa matuk'ar yana ganin yadda bakin mutun ke motsawa, kana shi mai tarin ilimine fasihine ta yadda zakayi mgna dashi kamar kowa sai dai shi a rubuce zai baka amsar da duk kake buk'ata a gareshi yakan iya rubutama a phone ko laptop ko a fefa."
cikin Jin dadi Dr Aliyu yace.
"Masha Allah. Alhamdulillahi komai yayi tsanani iya tare da sauk'i,
yanzu bari muje muyi abinda ya dace."
fatan nasara sukayi musu kana, suka koma suka zauna a kujerun dake jere can gefe,
sannan su kuma suka shige cikin d'akin.
Chapter 51 · 0% Book details