← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 116

Sashe 2

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saida akayi sallan asuba sannan suka dawo gida, nanma dan yaga Saifuddeen d'in yanata kuka.
Suna dawowa Ummi ta jawo d'anta ta ruggumeshi cikin kuka take tambayarshi ina sukaje,
baki ya bud'e da nufin ya kuma gwada yin mgna amman ina ya kasa, hakan ya sashi kife kanshi jikin gini yana wani irin gurnanin azabebben kukan da duk mai imani sai ya tausaya mishi babu mai sanin zafi da kun'an da yakeji a ranshi sai wanda ya tab'a shiga irin wannan halin ace an haifeka lfy ranatsaka nakasa ta sameka, so yake ya bud'i baki ya yiwa Umminshi bayanin yadda yakeji amman ina Allah bai bashi damar hakanba ganin ya kuma kife kanshi jikin ginin ya sake zazzafan shesshek'an kukane yasa Yayanshi mik'ewa ya nufi inda yake.

Da Sauri Nuruddeen ya kamoshi,
hannu yasa ya tallabe kanshi cikin tsananin kuka da tausayawa k'anin nashi murya na rawa yace.
"Saifuddeen...!!!

BY

*NAKASA BA KASAWA BACE*

*PAGE 2*

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

_Ga masu buƙatar biyan kuɗin karanta wannan littafi na Nakasa ba kasawa bace.ƙowa a buɗe take, turo katin mtn na 300 kacal ta wannan layin 09097853276. Ko kuma ka/kiyi transfer ta bank account na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ka/kiyi screenshot shaidar biyanki ki turo min, sabida kids samu damar karantawa koda na gama free page_

"Saifuddeen magana kake son kayi ne?."
cikin tsananin kukan ya rink'a gyad'awa Nuruddeen kai.
Duk da k'arfin hali irin na Ummi tuni kuka takeyi dan tausayin d'an nata wanda yaci sunan babanta.
shi kuwa Nuruddeen cikin mamaki ya kalli k'anin nashi cikin kad'uwa yace.
"Kana ji nane idan nayi Mgna kana gane me nake cewa ne?."
kanshi ya jujjuya kana ya zame hannunwan Nuruddeen daga rik'on da ya mishi sannan ya tsuguna a gaban Nuruddeen d'in tafin hannunshi yasa ya lailaiye yashin tsakiyar gidan nasu kana yasa yatsarshi ma nuniya ya fara rubutu da harshen fullanci yace.
"Ya Nuruddeen bana jin kuma naji na kasa yin mgna, cikin mak'ok'orona kamar an cusheshi kunnuwana sunyi dim bana jin komai,
Amman da ina ganin bakinku ina gane abunda kuke fad'a."
sai ya kuma d'ago kanshi ya kalli Nuruddeen daya rusuna yana karantar rubutun yana kuka tamkar an musu mutuwa,
hannu yasa ya share hawayen fuskar Nuruddeen d'in kana yaci gaba da rubutu da harshen hausa yace.
"Ya Nuruddeen ku nema min mgni mana, insamu irink'a Magna kamar kowa, ku kaini a bud'e min kunnena mana in rink'a jin muryar Ummi na da naku ku rink'a hira dani."
Ruggumoshi Nuruddeen yayi tare da sakin kuka murya na rawa yace.
"In sha Allah zan nema maka mgni Saifuddeen zan tattare dukkan buk'atun rayuwata zan jinginesu zan gina taka rayuwar, don gobenka tayi kyau."
Sai ya kuma tsaidashi tare da matsawa baya suna fuskatar juna yace.
"Saifuddeen kana gane abinda nike fad'i maka?."
kai ya gyad'a mishi, da sauri alamun eh yana ganewa, ganin haka Nuruddeen yayi wani murmushi da yafi kuka ciwo a zuciya tare da cewa.
"Saifuddeen kayi murmushi kamar yadda nayi."
ba musu yayi murmushin da har saida dimples enshi duka uku suka lotsa biyu na kumatun gefe dama da gefe hagu d'aya kuma na tsakiyar d'an gemunshi,
murmushin ya kuma fad'ad'awa ganin itama Ummi tana murmushi still su duka hawaye na kwaranya a idanunsu,
Abba kuwa tuni ya mik'e bisa taburmar dake tsakiyar gidan da yake konciyan zafine, kwanan woje akeyi,
kuma har yayi baccin da ya kwana bayiba.
Shi kuwa Nuruddeen hannunshi ya d'aura kan k'ahon zuciyarshi kana ya fara mgna yana murmushi still hawaye na zuba yake cewa.
"Saifuddeen *Babu nakasasshe sai rago*, kasa a ranka ita. Nakasa ba kasawa bace,
in sha Allah ni d'an uwanka Nuruddeen zan baka dukkan kulawa zaka rayu kamar ko wanne mai ji da gani da mgna, kada ka kareya shi nakasa baiwace ta Allah wonda yakewa wanda yakeso,
lokuta da dama bahaushe na karin mgnar da kan zama izina misali inda suke cewa, wani hanin ga Allah baiwane."
sai ya kuma sharte hawayenshi kana yaci gaba da cewa.
"Zan nema maka mgni iya raina da mutuwa, amman kasa a ranka mgni baya canza k'addarar mutun,
kasa aranka wani hanin ga Allah baiwace.
Kasa a ranka Allah yayi maka rahamar tsare maka harshenka daga sobon Allah ne kasa aranka Allah ya tsare maka kunnenka daga jin zantuka na haram ne da aikata sabon Allah, kamar yadda haka abin yake ga makaho Allah ya tsare mishi idanunshi daga ganin Haram,
Saifuddeen zan yi iya iyiwana kan ciwonka dana mahaifinmu har sai dai in yafi k'arfina."
tuni Rahma da Raihana suketa kuka, Hayatuddeen ma dake gefen Ummi kuka yakeyi ganin yayunshi na kukan.
Kuka sosai Ummi takeyi dan tausayin Nuruddeen yaro k'arami Allah ya jarab ceshi ya d'ora mishi nauyin jinyar uba da k'ani bugu da k'ari shike ciyar dasu,
domin sam Abba baya iya noma makaranshi sai su murdeshi haka yasa shima Nuruddeen baima iya nomanba,
kasan cewar su Abba sun gaji tarin filaye a wurin babansu wanda shima babansu a wurin babanshi ya gada,
to nauyin rayuwarsu ya ta'allaqa da su bada jinginan filayen ana noma ana basu yan wasu kud'ad'e da zasu iya ciyar dasu.
To amman da yake larurar jinya ta shiga sai ya zama kud'in basu isarsu,
wasuma in sun karb'i gonakin basa basu kud'in jinginar wasu kuma suyi ta bayarwa har kud'in yafi k'arfin yadda zasu iya maida musu su bare su amshi gonarsu dole sunaji suna gani gonakinsu suke fin k'arfinsu,
uwa uba ga Bappa Ali k'anin Abba irin mutanennan masu saude-saide.
Shiyasa tun bayan rasuwan iyayensu motsi kadan sai ya saida gona.
Yaje yayi tabin masu magani wai zai nemawa Abba mgnin jikinshi wai ko Allah zaisa ya rabu da makaranshi,
kwana kad'an abu yayi sanyi in ya sake tashi sai yafi na baya.
bud'e ido Ummi tayi jin abinda Nuruddeen yake fad'i, rubutun gaban Saifuddeen ta zubawa ido inda yake cewa.
"Ya Nurudeen makaranta nafa ya zanyi inyi karatu? banaji bana iya Magna, gashi next week zamu fara exams, isilamiya ma an kusa ayi musabak'a Ya Nuruddeen ta ina zanyi karatu ta yaya zan bada hadda?."
wannan tambayar tashi itace tasa kukan Nuruddeen k'aruwa yana kuka yake cewa.
"Zakayi karatu Saifuddeen, in sha Allah zakayi karatu boko da Arabic, in Allah ya yarda nakasarka bazata zama tawaya ba."
kai ya gyad'a alamun gamsuwa kana ya koma bayan Abbanshi ya konta time to time hawaye na zubo mishi yana sharewa, a haka yayi bacci kasan cewar basuyi bacci ba daren jiya yawo suka kwana sunayi.

Allah sarki Nuruddeen daga wannan ranar,
ya fara fafutukar nemawa Saifudddeen mgni amman ina,
k'addara ta rigayi fata, domin wannan abune da muka sani a k'asar hausa, some times k'enda tana sanadin makanta, kuramta gurguntaka, koma tab'uwar hankali gaba d'aya wa Al'ummarmu musamman in lokacin zafi akayishi. Kamar dai yadda ta kasance akan Saifuddeen.

Haka dai rayuwa tai ta tafiya yau fari gobe summa,
a cikin wannan yanayin aka aura da Rahma tunda ta gama Secondary school inta,
inda aka aura mata Sadik dan abokin abbansu Hamisu.

Shi kuwa Saifuddeen, ya bar zuwa makaranta dan ko yaje malaman basu wani meda hankali kanshi,
kuma gashi babu makarantar nakasassu a Dukkun,
sai dai yana zuwa islamiya,
kuma Alhamdulillahi malam suna matuk'ar kula dashi,
a wannan lokacin akwai wani babban malami su abokin Malam Ashiru ne wanda shida kanshi yake ware Saifuddeen ya koyar dashi, yakan bashi hadda ya kuma, iya in yazo sai ya zauna dashi ya bashi takardu ya rubuta mishi abinda ya koyar dashi kuma Alhamdulillahi da kai yake kawo komai yadda ya kamata,
wasu lokutanma har shike karb'ar haddan na k'asa dashi kuma duk k'ank'antar batan da akayi Saifuddeen zai gane har yayiwa yaran gyara ta hanyar rubuta musu komai.

kusan shekara biyu da faruwar abun kenan wanda tuni Saifuddeen yana da haddan izu 37 a kanshi yana kuma karanta littatafai na addini sosai kamar Hadisai, tauhit, Nahawa, kulasatul nurul yak'in, da kuma tajweed dan yama fi maida hankali kan tajwweed a cewar shine zai taimakawa karatunshi ya gane kurenshi da kanshi ya gyarawa kanshi, kana sosai yake bibiyar littafan koyan larabci.
Zuwa wanna lokacin ya saba da kuramtarshi, Nuruddeen kuwa har yau yana nema mishi mgnin.

Ranar wata Jummu'a da dare Nuruddeen shida Abba da Bappa Ali suna zaune suna hira kamar yadda suka saba
gyara zama Nuruddeen yayi kana ya sunkuyar da kanshi sannan ya kuma d'agowa ya kallesu, cikin sanyin murya yace.
"Bappa Ali, ya batun karatun Saifuddeen ne? kunyi shiru bakuce komai ba, kuma tun kwanaki naketa binku a saida gona d'aya, a saya min machine, tunda na iya na koya a mashidin abokina Adnan,
tunda akwai makarantar kurame a cikin Gombe, kullum da safe sai in tafi dashi in kaishi makaranta ni kuma na wuni yin acabana,
in zan dawo da yamma in d'aukoshi mu dawo tare, kunga baiyi nesa damuba kuma zai samu ilimi, kana mun sauk'e hakkinshi daya rataya kanmu, kuma mun cire mishi nakasar zuciya, kana mun ink'anta rayuwarshi, sannan zai samu k'arin fasaha da basira ta yadda zai k'ara samun experience,
sannan mu rabashi da barace."
shiru yayi ganin duk sun zuba mishi ido,
su kuwa yabawa sukeyi da shawararshi domin sun san gsky ya fad'i.
hakan yasa Bappa Ali gyara zama tare da cewa.
"In sha Allah hakan za'ayi Allah yayi maka al'barka Seyo da yake haka suke kiranshi *Seyoji ko Seyo duk d'aya ne* kakmar fillancine da take nufin FARIN CIKI a hausave.
murmushin jin dad'i Nuruddeen yayi kana ya kalli Abbansu da yake zubda hawayen tausayinsu yace.
"Abba kada kayi kuka, in sha Allah watarana muma zamuyi farin ciki, Allah zai sauqaqa mana zafafan k'addarorinmu ih zuwa dad'ad'aan k'adarori domin dukkan tsanani yana tare da sauk'i,
ku dai kuyita mana addu'a."
cikin sanyin murya Abba yace.
"Allah yasa haka Seyo na Allah ya al'barkaci rayuwarka ya baka damar rik'e k'annenka."
Amin Amin ya rabbil izzati. Suka amsa a tare.

Tofa daga wannan ranar akasa wata yar madaidaiciyar gonarsu a kasuwa cikin ikon Allah a wata d'aya akayi cinikinta aka basu kudin.
Chapter 2 · 0% Book details