← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 116

Sashe 90

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin murmushin farin ciki ne ya bayyana akan fuskar Baffa Ali, cike da tsananin jin daɗi yace "Alhamdulillah masha Allah, Allah Abun godiya, haƙiƙa kun zomin da labari mai daɗi Ishaq, na kuma yi murna ƙwarai matuƙa, tabbas yanzu naƙara yarda dacewa NAKASA BA KASAWA BACE, haka kuma nakasar Saifuddeen bata tauye masa zamowa cikakken ɗa Namiji ba, Allah Abun godiya".
Duban Saifuddeen wanda kansa ke ƙasa Baffa Ali yayi cike dajin daɗi yace .
"To ita yarinyar a inane take sannan wanene mahaifinta?"

Ishaq ne yace.
"Anan Gombe take cikin G.R.A sannan mahaifinta babban Malami ne wanda ƙasa gaba ɗaya ke alfahari dashi Malam Bashir!"

Cikin jin daɗi Baffa Ali yace "Alhamdulillah mungodewa Allah, Insha Allahu yau yau ɗinnan zan sanar da aminin mahaifinka Malam Ashiru, don kuwa gobe zamu dira acikin garin Gombe, bazamuyi k'asa a guiwaba don ba'a wasa a lamarin aure".

Sosai daɗi ya cika zuciyar Saifuddeen wani irin farin ciki yakeji, yayinda zuciyarsa ta cika da annuri, kasancewar tanaji ajikinta cewa takusa samun muradin ta.
Anan cikin Dukku su Saifuddeen suka wuni inda suka zazzaga ƴan uwa da kuma abokan arziki a gidan Goggo Dada ma sun dad'e. har gidan Malam Ashiru sukaje da Baffa Ali, nan Baffa Ali yayi masa bayani, sosai yaji daɗi shima kuma yayi na'am tare da nuna farin cikinsa, inda suka tsayar akan cewa gobe insha Allah zasu sauƙa acikin garin na Gombe. Anan cikin Dukku su Saifuddeen sukayi sallan Magriba daganan suka kama hanyan dawowa cikin Gombe.

Zaleeha ce zaune acikin falon Mahaifiyarta yayinda ta tanƙwashe ƙafafunta washe guda, kayan ciye ciyene zube agabanta dangin su snacks da chocolates, sanye take da wata ƴar riga marar nauyi wanda taɗan kama jikinta, idanunta ta lumshe akaro na barkatai tare da jingina bayanta da jikin kujera, damuwane ke ƙoƙarin hallaka nutsuwarta, yayinda wutar ƙaunarsa ke tsananin ruruwa acikin zuciyarta, gaba ki ɗaya kwana biyunnan sam bata da nutsuwa, ko abinci bata wani ci sosai, sam batajin daɗin zaman gidan nasu ayanzu, don kuwa akowacce rana sake hura mata wuta ake akan fitarda gwaninta, sam idanunta sun rufe, bataji bata gani akan soyayyarsa, akullum akuma koda yaushe, duk bayan shuɗewar wasu mintuna soyayyarsa ƙara ninkuwa take azuciyarta, yayinda abun ke ƙara girmama akowacce rana, don yanzu hartakai ta kawo hatta numfashin da zata shaƙa da Soyayyarsa yake tafiya, zuciyarta tuni ta narke akan tsantsar ƙaunarsa, takanyi kuka sosai akan soyayyarsa amma babu me rarrashi,, ahankali take fitar da numfashi tana mejin tsananin kewa da begensa.
Zakariyya da tun ɗazu ke tsaye akanta batare da ta sani ba ya gyara tsayuwarsa, duk da cewa suna yawan faɗa atsakaninsu, amma duk da haka yana matuƙar son yayartasa, haka kuma yanajin duk wata damuwa tata shima damuwarsa ce, cikin tausayawa yace.
"Adda Zaleeha!"
Jin muryan Zakariyya acikin kunnuwanta yasanyata buɗe idanunta wanda sukayi ja.

Ganin yanda idanunta sukai ja, yasanya Zakariyya zama akusa da'ita cike da kulawa ya kamo hannunta, cikin ƙaunar ƴar uwartasa kuma yayarsa yace.
"Wace damuwace haka take neman rabaki da nutsuwarki? wace damuwace haka ta sauya gaba ɗaya yanayinki? Dan Allah Adda Zaleeha kidawo kamar yanda kike da, banason wannan damuwar taki, kiduba fa kiga yanzu ko ƴar faɗannan bamayi banajin daɗin hakan wlh nafi son muna fad'a abinmu a shiga tsakaninmu aji kunya!".

Idanunta ne sukayi rau rau, yayinda hawaye ya cika cikinsu, cikin sassanyar muryar dake bayyana zallan damuwan da take ciki tace "Yazanyi Zakariyya? Yazanyi da soyayyarsa? inajin zafi acikin ƙirji da zuciyata, inajin idan bansamesa ba bazan taɓa samun cikar farin ciki ba, Ina sonsa! Ina matuƙar son sa!!". Ta ƙare maganar hawaye suna me gangara akan ƙuncinta.

Ajiyar zuciya Zakariyya ya sauƙe, duk da cewa shi yarone sannan baisan komai agame da soyayyaba, amma tabbas yaji ajikinsa cewa ƴar uwar tasa tana cikin wani hali, cikin son kwantar mata da hankali yace.
"Kiyi haƙuri Adda Zaleeha Insha Allah Zaki gansa, kuma shida kansa zai zo ya furta miki kalman Soyayya, nasan shima yanacan yanata tunaninki, yana kuma taso ya ganki, nasan shima yana can yana kuka akanki, yana cewa wayyo Zaleeha na, idan bake ba zan faɗa rijiya!".
Duk da cewa tana cikin halin damuwa sosai maganan Zakariyya ya bata dariya wanda har batasan sanda tayi ɗan murmushi ba, wani irin sanyi kalaman ƙanin nata suka sanya mata azuciya, cikin jin daɗin ganin murmushin Yayartasa yace . "Yauwa ko kefa Adda Zaleeha kinsan idan kina dariya ƙara kyau kike, sannan kuma idan kina dariya maza suna ganinki kamar tauraruwa ne, to waima wayeshi da zaice tunanin ƴar uwata bai kama masa zuciya ba? dagaske nake kiyarda dani shima yanacan yanata tunaninki, harma da inda zai sake ganinki, wataƙila ma yanacan soyayyarki ta kwantar dashi jinya, wata ƙilama baya iya bacci saboda ke, burinsa kawai shine ganinki, tabbas zaki ganshi zakuma ku haɗu nan bada jimawa ba, sannan har ƙasa zai tsugunna miki yace, wayyo Zaleeha na kibani soyayyarki dan Allah!!".
Yanzu kam dariya sosai Zaliha keyi inda har fararen haƙwaranta saida suka bayyana, wani irin farin cikine ya lulluɓeta, jin kalaman ƙanin nata takeyi tamkar dagaske, ganin tana dariya ne yasanya Zakariyya ɓare chocolate ɗaya yakai bakinta cikin kulawa yace.
"Yauwa to kici chocolate ɗinki, kuma kiyi farin ciki yananan yana zuwa Insha Allah!".
Babu musu ta amshi chocolate ɗin taci, wani irin sanyin daɗi takeji azuciyarta.

Wani dogon tsuka sukaji yafito daga bayansu hakan yasasu waiwayawa da sauri, Mama dake tsaye tun ɗazu gaba ɗaya taji kome suka tattauna, harara ta watso musu su duka biyun cikin takaici tace.
"Ae dama batun yauba nasan cewa daga ke har Zakariyyan baƙananan shashashai bane, kina kuka harkina cewa bazakiyi farin ciki ba idan babu wani wanda baimasan kinayi ba, wataƙila ma yanacan duniyarsu ta aljanu, waya sani ma ko yashiga jikin wata anƙonesa da ayar Allah zuwa yanzu babuma labarinsa, Wallahi Zaleeha kidawo cikin hankali da nutsuwarki, nagama fahimtar cewa tunaninki ne ke neman gushewa, saboda haka ko kinaso ko bakyaso Abdussalam shine wanda zai zamo miji agareki, kai kuma kada ka sake nasake dawowa cikin falonnan na iske ka azaune, baka da aiki sai hauka, har wai kana kwaɗaita mata cewa zaizo gareta".
Ƙwafa tayi tare da juyawa ta koma ɗaki.

Fuska Zaliha ta kwaɓe tare da duban Zakariyya, murmushi Zakariyya yayi mata tare da yin ƙasa da murya cikin kulawa yace.
"Kar maganan Mama ya dameki, ae dai bakyason Abdussalam ko?".

Kamar ƙaramar yarinya haka ta kaɗa masa kai alamar "Eh".
Murmushi yayi tare da cewa "Insha Allah Bazaki auresa ba, wanda kikeso shi zaki aura, kuma zaizo kamar yanda na faɗa miki, sannan baki dace da kowa ba saishi shi kaɗai!"
Murmushi tayi tare da lumshe idanunta, sosai tasamu gamsuwa acikin kalaman ƙanin nata, hannunta yakama tare da cewa takoma ɗakinta, anjima zaizo su buga game a laptop ɗinta, bata musa shiba ta tattare kayan snacks ɗinta inda Zakariyya ya ɗauki cake guda ɗaya, haka ya fita yanaci itakuwa ɗakinta ta wuce tana mejin sauƙin damuwarta, don acikin kashi ɗari yanzu babu kashi 80..

Su Saifuddeen kuwa ƙarfe 7:30 pm dai-dai suka shigo cikin garin Gombe, kamar yanda Ummi ta buƙaci da Ishaq yadawo, baiyi ƙasa aguiwaba wajen biyo Saifuddeen suka dawo gidan, Raliya ce ta cika musu gaba da kayan ciye ciye inda Ummi da kanta ta dafa musu fried rice mai rai da lafiya wanda yaji haɗin kayan lambu da hanta, gefe guda kuwa hadda haɗaɗɗen coslow wanda yaji madara da bama tayi musu, dayake Saifuddeen bawani maicin abinci sosai bane hakan yasa baiwani ci da yawa ba, Ishaq ne kam yaci sosai, don dama yana matuƙar son fried rice sosai, koda suka kammala hira ne ta ɓarke tsakanin Ishaq da Ummi inda sukayi hira sosai, har dare yayi sosai batare da sun ankara ba, ƙarfe 11 Ishaq yatashi daniyar tafiya, nan Saifuddeen yakafe kai da fata akan cewa dole lallai saidai ya kwana idan yaso gobe sai ya koma gida, Ummi ce tasa baki anan cewa Ishaq ɗin ya kwana kawai tunda dare yayi, hakan kuwa akayi ranan agidan Ishaq ya kwana tare da Saifuddeen, haka yasha baccinsa yayinda yabar Saifuddeen nata faman juyi, sam yakasa bacci sakamakon wata irin fitinannennen tunaninta da ta addabesa, haka yayita faman juyi akan gadon da ƙyar bacci ɓarawo ya iya ɗaukarsa, ko acikin baccin haka yadinga mafarkai kala kala da Zaleeha, wacce gaba ɗaya ta riƙe masa zuciya.

Washe gari.

Kamar yanda su Baffa Ali suka alƙawarta masa hakance takasance don ƙarfe takwas dai-dai sai gasu acikin garin Gombe, tarba ta mutumci Ummi tayi musu, inda aranta take me mamakin ganinsu, bayan sun gama gaisawa ne Baffa Ali ya gyara zama tare da sanar da'ita abun al'khairin dake shirin tunkararsu.
Wani irin tsananin farin ciki ne yakama Ummi har batasan sanda wasu ƙwalla suka gangaro daga cikin idanunta ba, cikin jin daɗi tace.
"Alhamdulillah! Allah Abun godiya, naji daɗin wannan labarin matuƙa Allah kuma yasa matarsace!".
Da "Ameen ya Allah ". Su Baffa Ali suka amsa, nan suka ɗan tattauna akan batun daga bisani Ishaq yazo tare da mahaifinsa, saboda tare zasuje, dan sosai mahaifin Ishaq ɗin yasan Baba Malam, mahaifin Zaleeha kenan, dan harma yaƙirasa yasanar dashi batun zuwansu, kai tsaye suka wuce G.R.A.

Atare Raliya da Hayatuddeen sukayi Wani irin Tsalle, cikin tsananin farin cikin jin kalaman Ummin nasu suka rungume juna, cike da zumuɗi Hayatuddeen yace "Yesss! Allah Nagode maka Hammana zaiyi aure zan samu Aunty!!"

Itama Raliya wani irin farin cikine ya lulluɓe mata zuciya cikin jin daɗi tace.
"Insha Allah auren Hamman mu sai yazama abun kwatance aduk Nigeria, zamusha shagali irin wanda wasu basu taɓa yi ba!".
Hannu Hayatuddeen ya bata suka tafa cike da murna yace "Dan Allah Ummina asa lokacin bikin nan kusa!"
Dariya Ummi tayi tare da cewa.
"Amma kai dai Hayatuddeen Allah ya shiryeka, bafa sadaki nace maka ankai masa ba, neman izinin hirafa akaje nema masa!"
Chapter 90 · 0% Book details