← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 116

Sashe 93

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru sukayi baki ɗayansu a gaban mahaifin nasu,
yayinda Aminu ke gefe riƙe da wani littafi.
Ganin shirun yayi yawane murya na rawa tace.
"Baba malam gani."
tsareta yayi da ido kana yace.
"Na ganki ai, ke nake jira inji ko kin fidda tsayeyye kamar yanda na umurceki."
Kai ta jujjuya a hankali kana tace.
"A'a."
Murmushin girma yayi tare da cewa.
"To ba matsala, ni na zaɓa miki,
zai zo gobe ki ganshi, in ya miki shike nan, in kuma bai mikiba ba dole na baki kwana biyar daga goben sai ki kawo wanda kike so,
In kuma har kwana biyar ya cika baki kawoba to tabbas zaɓina ya zama naki."
Da ƙarfi ƙirjinta ya wani irin wawan bugawa, take tsoro mai tsanani ya rufeta,
da sauri ta rumtse ido jin Ya Aminu na cewa.
"Gobe da yamma zaizo kuga juna kada kije ko ina."
Kai ta ɗago da nufin zatayi magana kenan.
Baba Malam yace.
"Tashi kije sai da safe, Allah ya muku al'barka."
Da kyar ta iya cewa.
"Amin. " kana ta miƙe ta fita.

Kafinma ta isa falon tuni hawaye sun ɓata mata fuska.
kai tsaye ɗakinta ta nufa.
Da sauri Aunty Lubna tabi bayanta tsaye ta sameta ta kifa kai jikin gini tana rera kuka.
Kamota tayi suka zauna kan gado.
Cikin sassauta lafazi tace.
"Meyasa bazaki zama jaruma ba wurin tinkarar matsalarki abu kad'an ki fara kuka."
Cikin zubda ƙwalla ta gaya mata abinda Baban nata ya gaya mata.
Gyara zama tayi tare da share mata hawayenta kana tace.
"To ai da sauƙi tunda har yanzu dai an baki damarki,
ki kuma dage da addu'ar Allah ya kawoshi gareki kafin kwanakin da Baba malam ya faɗan su cika.
Kuka ba naki bane addu'ace ta kama ceki."
cikin jin ƙarfin guiwa ta gyaɗa kai.
Haka dai tayi ta rarrashinta har ta sake.

Sannan ta fita ta koma side ɗin Mamy, inda ta samu tuni Mamy ta tafi wurin Baba malam.
Ɗakin da take sauƙa idan sunzo ta shiga, nan ta samu Ahmad ɗin na yiwa yaransu addu'a.
yana gamawa suka dawo parlour'n Mamy nan yake bata labarin komai a kan Saifuddeen, shiru tayi a ranta tana cewa nakasasshe kuma? a fili kuwa lafewa tayi jikin mijinta.

A can wurin baba malam kuwa sosai yayiwa Mamy bayani sanin tanada nisuwa kuma Alhamdulillahi don ai ita tasan Saifuddeen farin sani.

Ita kuwa Mama Allah-Allah takeyi girkinta yazo, ta shigar da batun Abdussalam a wurin baba malam, akan zata ce mishi Zaleeha ta amince dashi.

Washe gari da yamma ƙawayen Zaliha Bilkisu da Rashida suka zo,
inda tuni itama ta shirya,
har zasu fita Ahmad yace
kada su fita su bari sai gobe in yaso suje,
ya fake da yasan Rashida ta iya zana lalle yace ta zanawa Lubna.
Sosai suke ganin daraja da girman Ya Ahmad ɗin, dan haka ba musu suka amince.
Nan Rashida ta fara zanawa Aunty Lubna lalle,
ita kuwa Zaleeha kamar ta mutu dan baƙin ciki, dan tasan abinda yasa Ya Ahmad ɗin nata yayi musu haka.
Bilkeesu kuwa gyara kwanciyarta tayi tana kallon film d'in Sanam Teri Kasam da ake haskawa a tashar MBC Bollywood.

Biyar dai-dai Ahmad ya shigo tare da ishaq.

Kai tsaye parlour'n Saifuddeen suka nufa.
zaune suka sameshi bisa wellchair ɗinshi, mai kalan golding ash.
Wani irin murmushi Ahmad yayi tare da cewa.
"Fatabarakallahu fi hasanil Kaliƙin, tsarki ya tabbata ga ubangijin sammai da ƙassai da yayi wannam kyakyawar halitta."
Ishaq ne ya amshi zancen da cewa.
"Masha Allah!."
Murmushi Saifuddeen yayi wanda yake sanye da wata ɗanyen yadin getzner mai azabar kyau kalar dark green mai turuwa, irin dark mai shinng ɗinnan, yayinda aka zubawa kayan wani fitinennen ɗinkin half jumper and pencil trouser, daga wuyan rigar kuwa aka watsa mishi wani tattausan zaren surfani.
yayinda ya murza wata kyakyawar hular damanga mai ratsin dark green akansa,
daga ƙafansa kuwa wasu irin fitinannun toms mai kalan shaddarsa yasa, ƙiran company'n Gucci, me matuƙar tsada,
still kuma zazzafan agogon company'n Gucci ne ke ɗaure atsintsiyar hannunsa wanda kuɗinsa kaɗai ya haurawa 80k,
sai wayarshi ƙiran iphone 11 pro max daya zura cikin al'jihun gaban rigarshi, wanda abayyane ta saman al'jihun rigartasa, kake iya hango kyawawan camera's ɗinta guda uku dake jere reras, biyu asama ɗaya aƙasa.
Yanayin shigar tasa ta matuƙar ƙara fito da farar fatarshi kai ka rantse da Allah cewa balarabe ne.
Sajen nan nashi yayi wani lub-lub yayiwa fuskarsa ƙawanya sai sheƙi da ƙamshi yake,
red colour lips ɗinshi sai shinning skeyi tamkar an shafa mishi mai a kansu.

Shida kanshi ya sarrafa whellchair ɗinshi suka fito zuwa parlour.
Ummi suka samu ita da Hayatuddeen azaune.
gabanta suka tsaya
cikin shirinsu na fita, murmushi tayi tare da godewa Allah daya bata wannan kyakkyawan ɗan, cikin gane batun da ya mata tace.
"Allah ya kaiku lafiya, ya dawo daku lafiya, Allah ya baku nasara da sa'a kan abinda zakuje nema.
Allah ya sadaku da al'khairin dake cikin tafiyar ya rabaku da sharrin dake tare da tafiyar."

Da "Amin." Suka amsa baki ɗaya.

Shi kam Saifuddeen wani sanyi da farinciki ne suka rufeshi sabida addu'o'inta gareshi.
Shiko Hayatuddeen sai hotuna yaketa musu.

Daga nan suka fita,
har bakin gate Hayatuddeen ya rakasu, saida yaga sun fita sannan shima ya ɗauki machine ɗinsa ƙirar UD, ya nufi gidan Inna dan zaije wurin Zakariyya.

Su Saifuddeen kuwa suna isa G.R.A.
Ahmad ya rinƙa bin ƙwatancen da Baffa Ali yayi musu,
suna isa bakin gate ɗin suka danna horn, sunyi biyu ana uku aka wangale musu makekem gate ɗin.
Cikin nitsuwa Ahmad ya dai-daita parking ɗin motar,
a hankali ya buɗe marfin motar ya fito cikin shigarsa ta al'farma,
both ɗin motar ya buɗe tare da fiddo whellchair ɗin Saifuddeen,
ta inda yake yazo, buɗe mishi murfin motar yayi kana ya gyara mishi keken.
Yayinda tuni Ishaq kam ya fito.

Yana gama gyara zamanshi kan whellchair ɗin sai ga Ahmad ya fito daga cikin gidan hannunshi riƙe da Unaisa
ganinsu yasa cikin sauri ya nufi inda suke,
ganin haka Ahmad Abban farida ma ya saki fuska kana ya nufi inda suke hannu suka bawa juna,
Abban Farida ne ya fara magana, inda yace.
"Assalamu alaikum."
"Ameen wa alaikassalam, barkanku da zuwa."
"Yauwa barka dai."
Murmushi yayi tare cewa.
"Ahmad yayan Zaleeha."
cikin sakin fuska Abban Farida yace..
"Ni kuma Ahmad yayan Saifuddeeen."
Murmushi sukayi baki d'aya,
sannan suka taho inda su Ishaq ke tsaye,
cikin tsananin son Saifuddeen ya sunkuyo ya bashi hannu sukayi musabaha,
sannan suka gaisa da ishaq wanda shi sam bai gane cewa Ishaq makaho bane.
Jagora yayi musu zuwa BQ inda dama yasa Lubna ta gyarashi fes tunda safe.

Bayan sun zauna ne yace.
"Bari naje na turo muku ita ko."
cikin fara'a Abban Farida yace.
"Ayi haka babban yaya."
"Ai anyima." ya bashi amsa yana ɗan murmushi, kana yafice daga cikin babban falon BQ ɗin.

Shiru sukayi kowa da abinda ke ransa,
shi kuwa Saifuddeeen azkar yakeyi azuciyarsa cikin nutsuwa.

Zahira yasa ta kai musu abin sha, kana ya nufi side ɗin Mama.
A Parlour Mama ya samesu suna hira sama-sama dan kowacce da abinda takeyi.
cikin tsare girar sama data ƙasa yace.
"Ke Zaleeha tashi kije BQ kinyi baƙi."
wani irin tsuke fuska tayi tare da yamutsa fuskar kana tace.
"Baƙi kuma ya Ahmad."
Ya Habune da yanzu ya fito ɗakin Mamansu yace.
"Ke shi sa'anki ne yana miki Magana kina zaune,
Zaleeha kifa kiyayeni nagafa baki da kunya ji kike kamar kin kamomu ko?."
Da sauri ta jujjuya mishi kai tare da miƙewa jiki na tsuma domin ita dai Allah ya sani tana tsoron ya Habu da Ya Aminu mugayene na bugawa a mujalla yazu zasuce zasu kai mutun mari.
"Maza ɗauko mayafinki ki ɓace mana daga nan."
Da sauri ta nufi ɗakinta,
shi kuwa ya fice daga falon.
A zatonta yana nan shiyasa tayi maza ta fito tana mai yin rolling kanta da ɗan kwalin lafiyayyar Arabian gawn ɗin dake jikinta,
ganin baya nanne ta zumbura baki tare da cewa.
"Bilkisu muje ki rakani."
Kai bilkisu ta jujjuya tare da cewa.
"Tab ina cikin kallon wannan film ɗin ai babu inda zani,
Rashida ta rakaki mana tunda ta gama zanen da takewa Aunty Lubna."
Ahmad ɗinne ya kalli Rashida cikin bada umarni yace.
"Rashida rakata ko."
"To" tace tare da miƙewa ta ɗauki mayafinta.
Suna gab da fita aka tafi talla,
ganin haka Bilkeesu ta miƙe tare da cewa.
"MBC Bollywood iyayen talla sun tafi,
muje inga sahibin namu kafin in dawo sun gama tallarsu na tsiya."
dariyan mugunta Rashida tayi, kana suka nufi BQ.

Shi kuwa Ya Ahmad parlour'n Baba Malam ya nufa.
Yana shiga ya samesu da Mamy da Mama da kuma Baba Malam ɗin.
Gefen da littatafan addini wanda suke jere ya nufa yana mai cewa.
"Baba Malam su Saifuddeen sun zofa."
kai ya gyaɗa alamun to kana yace.
"Ka tura mishi Zaleehan"
"ai tama tafi."
ya bashi amsa yana me zama kusa dashi,
kai ya ɗan kwantar cikin sanyin sauti yace.
"Naji tausayin Saifuddeen baba ya bani tausayi, mutun kyakkyawa matashi Allah ya jarabceshi da nakasa mai zafi,
wlh Baba sai ka ganshi yama fi kyau a zahiri akan a hoto,
in dai Zaleeha ta yarda dashi to haƙiƙa tayi dace da miji managarci,
domin sam nakasarsa bata zame mishi kasawa ba, in ka ganshi kamar ba kurmaba, haka inba dan wellchair ɗin da yake zaune a kaiba bazaka taɓa cewa gurgu bane."
Cikin mamaki Mama ta ƙara haɗe fuska tare da cewa.
"Wai maganar me kukeyi hakane ban gane inda kuka dosaba,
Gurgu kurma wurin waye yazo!?."
Cikin isa da tsare fuska Baba Malam ya mata bayanin komai akan Saifuddeen ya ƙara da cewa.
"Kuma ni yamin na yaba dashi muddin bata fidda waniba to niko zan aurawa Saifuddeen ita!."
Chapter 93 · 0% Book details