← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 116

Sashe 50

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

1:53 pm duk sun gama shirin komai,
takofar baya Dr Adnan yashiga yaturo gadon yafita takofar bayan,
Dr Arabi natsaye ajikin motar da zai kaisu airport da taimakon sa suka tura gadon cikin motar suka dai-dai zaman gadon sosai acikin motar,
Kana Dr Adnan yakoma indasu Ummi suke yace.
"To Ummi an gama shirya komai shirya komai ku akejira yanzu,
sanna kuma tafiyar zai kasance dole damutun biyune sanna kuma... da sauri Raihana tace.
"Ummi ku kutafi keda Hayatuddeen, mu zamu koma gida nida Raliya fatanmu samun saukin Hamma Saifuddeen zan kira Abban Farida yayi k'ok'arin dawowa,."
cikin gamsuwa Ummi tace. "to".
"kuyi maza kutafi nima zuwa gobe da yamma zan shigo Abujan."
Dr Adnan ya fad'i tare da juyawa yayi gaba,
da sauri suka bishi abaya.
koda suka'isa jikin motar, Ummi da Hayatuddeen suka shiga,driver yatada motar Raliya da Raihana nad'aga musu hannu dayimusu fatan samun nasara,yiyinda dukansu suke ta sharar kwalla,driver yaja sukabar harabar asibitin,
"Sukadau hanyar Airport, in da tuni ishaq na can su kawai yake jira.
suna isa bada jimawa ba jirginsu ya tashi.
3:00pm yamusu a cikin birnin taraiya Abuja direct National hospital suka nufa.
Kasancewar duk abinda yadace Dr Adnan yarigada ya'aiwatar dashi ta online , so ansan da zuwansu,basusha wani wahalaba,suna isa nurses suka taho jikin motar data d'aukosu daga airport nan suka fito dashi.
Kana Ummi
tamikawa d'aya dagacin nurse d'in takardar da Dr Adnan yabata,sanna suka turoshi sukashiga cikin asibitin, direct Emergence room aka shige dashi.
Nan Doctors suka dukufa akanshi basu yi wata-wata ba suka fara bincike akan laluransa kamar yanda yazo musu arubuce,
cikin k'ank'anin lokaci S.....!

By
*GARKUWAR MARUBUTA*
8/18/20, 7:52 PM - Ummi Tandama: [3/30, 10:50 AM]
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*NAKASA BA KASAWA BACE*

*PAGE 15*

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

~Free page~

Suka gano matsalar shi, kana suka dugufa kanshi dan samo numfashin sa ya dai-dai ta, domin babu wani aiki da zasuyi mishi har sai ya dawo haiyacinshi.
Hakan yasa suka meda hankali ganin komai ya dai-dai ta, cikin ikon Allah a daren ranar ya farfad'o yana kuma cikin haiyacin sa, kasan cewar dare yayi nisa, yasa aka bar batun dubashi zuwa safiya.

Bappa Ali da Warisu da Mudassir kuwa tunda Hayatuddeen ya sanar musu gaba d'aya hankalin su ya tashi sai dai sun meda hankali wurin yi mishi addu'ar samun lfy a cikin ka'aba.

Ishaq kuwa, tunda aka shaida musu bazasu dubash yau ba sai gobei, sai ya kira babban yayanshi dake nan Abuja da iyalanshi ya shaida mishi, ba jimawa kuwa Ya Rabi'u yazo tare da direbanshi, domin dukkan sashin zuriya biyun sun san abotar Ishaq da Saifeddeen domin abotace tun na yarinta, hakan yasa har iyaye su suke mutunci da zumunci mai k'arfi.
Kasan cewar babban doctor uban gidane ga Dr Adnan hakan yasa tun kafin suzo an shirya komai, hatta da masu kula dashi, ya tanadar cikin ma aikatan nasu,
ya kuwa kontarwa Ummi hankali ta tare da bata k'arfin guiwa.
Haka yasa Ya Rabi'u ya tafi da su gidanshi, cikin sa'a ma kuwa asibitin ba tazara sosai da diganshi.

Ummi kuwa da Hayatuddeen dugufa sukayi da Addu'a jigon nasu.
Deren ranar sam basu rumtsaba, shima Ishaqa bayi bacciba.

A can gida Gombe kuwa, bayan su Raihana sun koma gida, kai tsaye falon Ummi suka wuce,
cikin sanyin jiki Raihana ta zauna bisa kujera,
idonta ta rumtse da k'arfi, a jere wasu zafafan hawaye suka zubo mata,
ita kuwa Raliya wayarta ta d'auka, ta fara 'yan dube-dube bayan yan wasu dak'ik'u ta kara wayar a kunne,
a hankali ta bud'e labbanta tare da cewa.
"Wa'alaikassalam, Abban Farida, yaushe zaka dawo?."
a can d'aya sashin Abban Farida yace.
"Lafiya dai ko?."
murya a sanyaya tace.
"Alhamdulillahi ala kulli halin."
jin haka yasan to tabbas akwai matsala sai dai iya sarrafa harshe na matar kwarai wacce tasan yadda zata isar da sak'o wa mijinta ba tare data firgitashi ba,
cikin dakiya yace.
"Meke faruwa?."
tallabe hab'arta tayi tare da cewa.
"Abban Farida ka dawo gobe, please inda hali in zaka samu jirgin yau dan Allah ka taho gida."
cikin kad'uwa yace.
"Raliya meke faruwa ki gaya min mana, zuciyata ta cika da zulumi."
"Hamma Saufudddeeen! Saifuddeeen!! Saifuddeen..!!!."
tai ta maimaita mishi murya na rawa.
mik'ewa yayi tsaye cikin fargaba yace.
"Innalillahi wa Inna'illaihi rajiun. Meya sameshi? ina Hayatuddeen? Ina Ummi?."
Cikin kuka tace.
"Suna Abuja an tafi dashi asibiti."
daga nan ta sanar dashi dukkan abinda yake faruwa,
ta k'ara da cewa.
"Ya Adnan ya turasu Abuja. Abban Farida ka dawo wlh Hamma Saifuddeen ko motsi baya yi sanda suka tafi dashi."
ta karishe maganar tana zubda hawaye.
Shi kuwa Abban Farida datse kiran yayi kana ya fara harhad'a yan abin buk'atunshi, kai tsaye Airport ya nufa cikin sa'a ya samu jirgin Abuja, dama shi bai niyar zuwa Gombe ba.

Kafin su isa abuja dare ya d'an fara nisa kuma yayi ta kiran number Hayatuddeen da Ummi duk basu d'agawa, haka yasa ya nemi masauk'i inda ya kwana da nufin da safe zai nemesu.

Dr Adnan kuwa, saida yaga tashin su Ummi sai da ya koma asibitin kafin ya koma gida.
Shiru parlour nasu ba kowa haka yasa ya zauna bisa 1 str zuciyarshi da jikinshi na cike da fargaba da tsoron halinda martashi Rahma zata shiga in taji abinda ya samu d'an uwanta,
ya rasa tudun dafawa, a fili yace.
"Ya ilahi ya mujubbat da'awati ko taya zan sanarwa Rahma."
sai kuma yayi sauri zaro woyarshi Ishaq ya kira,
bayan sun gaisa yace.
"Kun isa lfy,?."
"Lafiya lau Alhamdulillahi."
gyara zamanshi yayi tare da kallon k'ofar corridor d'in part d'in Raihana sannan yace.
"Kun samu Dr Aliyu ko?."
"Eh to gsky mun samu tarba daga wurin Doctors har uku to gsky ban sanan wanne ne Dr Aliyun ba a cikinsu."
cikin sanyi yace.
"Zakaga Dr Aliyu shima nakasasshene ai domin shima yanada matsalar spanal cord kuma shine big doctor a k'asarnan in dai a wannan fannin ne, uban gida nane kuma wa nane d'an kawuna."
cikin jin dad'i Ishaqa yace.
"Alhamdulillahi, hakan yayi kyau domin dama shi nakasa ai ba kasawa bace, kuma ya yi mana k'arin bayani kan mu kontar da hankalin mu, Alhamdulillahi kuwa tuni ya farfad'o kuma yana cikin haiyacin sa, so zuwa gobe da safe zasu fara bincikan adadin zurfin ciwon."
lumshe ido Dr Adnan yayi kana yace.
"To Allah ya kaimu, in sha Allah nima gobe zan taho please kuke kontarwa Ummi hankalinta."
"In sha Allah ba matsala." cewar Ishaq.
Kana daga nan sukayi sallama,
shi kuwa Dr Adnan Dr Aliyu ya kira bayan sun gaisa yake mishi godiya tare da tambayar ya mai jikin, so shima Adnan ya samu d'an nitsuwa duk da cewa Dr Aliyu ya tabbatar mishi cewa Saifuddeen ya samu nakasar lakkar bayanshi.
bayan sun gama woyar ne yana d'ago kanshi ya hangi Rahma tsaye bakin k'ofar kitchen ta kafeshi da ido gaba d'aya jikinta tsuma yakeyi tuni hawaye sun jik'a fuskarta,
mutuwar zaune yayi domin tabbas yasan taji duk wayar da yayi dasu, dan sam hankalinshi bai bashi ko tana kitchen ba.
Ita kuwa matsowa ta farayi a hankali take taku still jikinta na rawa,
gabanshi ta tsaya tare da tirtsetsen cikinta,
da sauri yasa hannu ya jawota jikinshi kan cinyarshi ya ajiyeta, suna fuskantar juna, murya na rawa tace.
"Me kuma zaka boye min Ya Adnan me zaka boye min? gaya min me zaka boye min. wani abune kuma ke tinkarar rayuwarmu? meya samu d'an uwana? ina yake, waye zai nak'asa Saifuddeen ne ko Hayatuddeen gaya min wani hali Ummi ke ciki?."
gaba d'aya ta birkice ta gigitashi da tambayoyinta yama rasa wanne d'aya zai amsa mata kuma tana k'ara tuno mishi fargabar da Ummi ke ciki.
Kawai sai ya had'eta da k'irjinshi ya ruggumeta da k'arfi kana ya fara magna cikin dakiya yace.
"Madadin kiyi mishi addu'a sai kiyi mishi kuka? kin san halin da yake shiga duk sanda yaga hawaye a kwaranya a idanunki, meyasa rauninki yake yawaita, da can baya da juri na sanki to meyasa bazaki ruggumi k'addaraba, ki godewa Allah a cikin dukkan lamarinki."
tunda yace mata kin san baya son kukanki ta gane Saifuddeen ne, to wani zafin ya wuce inda hawaye yake fargabarta da nitsuwarta duk sun had'u sun hargitse sun danne hawayenta,
sai tayi wani azabebben murmushi da yafi kuka zafi cikin sanyi tace.
"Alhamdulillahi ala kulli halin, ya Allah ka fini sanin waye Saifuddeen ya Allah ka fini sani adadin mutanen da ya zame musu uwa uba yaya k'ana, ya Allah ka fini sanin rauninshi dana mahaifiyarmu ya haiyyu ya k'aiyyum ya zirjalali wal ikram ya Allah ka bashi lfy ka d'aga kafad'un shi."
da sauri Dr Adnan yace. "Amin Amin, Ameeen ya rabbil izzati."
daga nan yayi ta bata baki da nuna mata ciwon baiyi tsanani ba.
Amman duk da haka daren wannan ranar itama sam bata rumtsaba.

Raihana kuwa har dare Allah baisa ta tuno da Affan ba domin tunda suka dawo data haura sama d'akin Saifuddeen kuka tayi tayi,
sai bayan sallan isha da Amira 'yar Alhaji Kabiru ta dawo mata da shi itama haka ta kwana yiwa d'an uwanta addu'a.
Chapter 50 · 0% Book details