← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 116

Sashe 17

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salisu ya samu da Mudasir sai Warisu ganin Saminu baya nanne yasa suka raja'a gidan sarki gidansu Saminun kenan,
a d'akin saminu suka yada zongo sunata hira,
har dai dare ya fara nisa kafin suka fito,
Warisu ya shiga gidansu shima Mudassir yayi hanyar gidansu.
Saifuddeen kuma da Salisu tare suke tafiya dan kusan katangar gidansu d'aya ne.
suna isa bakin masallaci Saifuddeen ya zaro biro kana yayi rubutu a jikin takardar daya b'alla.
"Yauwa Salisu dama inaso in gaya maka an rage balance enka ka rink'a bada dubu biyu duk sati,
sai mu rink'a tasowa biyar dai-dai na yamma kafin a kira magrib kuma mun iso dukku kaga zamuyi bud'a baki a gida kuma zamu dena tafiyan dare,
in kuma gari ya waye in yaso ana fitowa masallaci mu tafi tunda ba batun jiran karyawa."
cikin tsananin jin dad'i Salisu ya ruggumeshi tare da cewa.
"Kai Alhamdulillahi wlh ka kawo shawara mai kyau, amman dubu biyu yayi kad'an gsky zan dai bada 4k tunda du-du du dai awa d'aya da rabine aka rage.
Ngd matuk'a Allah bar zumunci da k'auna my friend."
cikin sanin mutuncin juna ya kuma ce mishi.
"No kai dai kabar 2k d'in ai kaima kanada buk'atun kanka dana iyayenmu."
cikin sanin ya kamata Salisu yace.
"To naji na kuma gode, amman gsky 3k zanke badawa kada ka cemin komai."
jin haka yasa Saifuddeen rubuta.
"To Allah ya musu al'barka."
da haka sukayi sallama,

Koda ya shiga gida tuni su Ummi sunyi bacci acewarsu kada suyi dogon hira su zo su makara.

Shima hakance a wurinshi shiyasa yanayin wonka yayi al'wala yazo yayi konciyarshi.

2:00 Am Ummi ta farka kamar yadda Ummi takeyi ko wanne lokaci in dai cikin Ramadan ne,
kana ta bud'e k'ofa ta fito tsakar gida yayinda iska mai sanyi ke kad'awa, babbar taburma ta shimfid'a kana ta fito da wani d'an madaidaicin cainis carpet amman irin na da fa,
ta shimfid'a bisa taburmar kana ta ajiye hijabinta da carbinta da Qur'an sai lantanta mai wadaceccen haske.
al'wala tayi kana kana taje baki k'ofar d'akinsu Rahma kira d'aya ana biyu Rahma ta amsa.
Itako Ummi tana jin Rahma ta amsa ta koma bisa taburmar ta fara nafila,
Rahma kuwa tana tashi ta tada Raihana Raliyya.
sun jima kafin suka tashi,
suna fitowa duk sukayi al'wala kamar yadda aka sabar musu tun basu kai hakaba,
kana sukazo ko wacce tayi iya nafilar da zata iya daga bisani suka fara karatun Qur'an.
Yayinda tuni Saifuddeen ma ya tashi yazo ya tashi Hayatuddeen sun je bakin k'ofar d'akinshi bisa k'aramar taburma ya shimfid'a musu sallaya,
suka fara nafila bayan sun zauna sun fara tilawa ne ba jimawa Hayatuddeen ya fara gyangyad'i yana rab'awa jikin Hamma Saifuddeen d'in nashi tuni bacci ya sureshi shiko Saifuddeen gyara mishi jinginar yayi kana yaci gaba da tilawarshi.

3:20 Am Rahma tayi addu'a tare da shafawa kana ta mik'e ta cire hijabinta ta ninke ta ajiye gefe sannan ta shiga kitchen ruwan zafi ta d'ora bayan ya tafasa ne ta d'an zuba man gyad'a cikinshi kana ta d'ebo couscous dai-dai misali tazo ta zuba kana ta meda marfin ta rufe,
sanan ta harhad'a kofuna tare da pilet da cokula,
ta fitar taje ta jera bisa babbar taburmar,
kana ta dawo ta d'auki filas d'in duka biyu babban da k'aramin,
sannan ta koma kitchen d'in,
bud'e tukunyar tayi tare da duba couscous d'in yayi lugub yadda akeso kuma yayi wasar-wasar bai kwab'e ba amfanin zuba man gyad'an kenan,
sauk'e tukunyar tayi ta ajeshi gefe sannan ta mik'e ta sauk'o dana miyar ta d'orashi kan rushin.
sai ta kuma sauk'o da kuloli guda biyu d'an madaidaci shi ta fara zubawa saida ta cikashi yadda zai iya isar mutun ukuma,
kana ta kwashe sauran duka a babbar kulan,
sannan ta kwashi kulolin ta kaisu bisa taburmar,
tana dawowa ta bud'e tukunyar miyar da sai bol-bol yakeyi sai mai da tsokokin da suka yiwa miyar k'awanya,
tukunyar ta d'auka baki d'aya kana ta d'auki d'an k'aramin kulan miyar,
tana fitowa ta zauna gefen taburmar kana ta kalli Raihana tare da cewa.
"Na mance ban d'auko biredin nan ba,
tashi ki kawoshi yana d'akin Ummi."
to tace tare da mik'ewa ta nufi d'akin.
Ita kuwa Rahma miyar ta saka a k'aramar kulan tare da tsokoki kusan shida kana tasa k'ashi biyu,
sannan ta d'auki k'aramin filas d'in nan ta had'a da kulolin kana ta amshi biredi d'aya a hannun Raihana da ta iso da su a hannunta,
cikin nitsuwarta tace.
"Yauwa Raihana bari in kaiwa su Bappa Ali nasu ke kuma ki sa mana ki sawa d'an uwana." da yake haka take kiran Saifuddeen wasu lokutan
ba musu Raihana ta tsuguna tare da fara zuba musu,
shi kuwa Saifuddeen da sauri ya mik'e yaje ya amshi abincinsu bappa Alin kana yayi mata nunin da ta koma taci abinci bari shi ya kai musu.
To tace mishi kana ta bashi kulolin,
sannan ita kuma ta koma ta zauna kofi ta d'auka tea ta had'a mishi mai kauri ta san ba wani abinci mai yawa zai iya ciba,
bayan ta had'a mishi ne sai ta kuma d'iba mishi couscous d'in tare da sa mushi miyar hantar a d'an k'aramin side soup tuni Raihana kuma ta gama had'a musu nasu a tire,
ta ajewa kowa kofin tea a gabanshi.
bisimillah sukayi tare da addu'a sannan suka fara sahur d'in.
Shi kuwa Saifuddeen koda ya dawo tuni k'arfe hud'u ta kusa gefen Umminshi ya zauna tare da d'aukan kofin tea d'in da Rahma ta had'a mishi ya fara sha,
ido ya lumshe jin k'amshin citta da kananfari da masoro da ganyen na'a-na'a, yana sha yana lumshe ido ko dan dama shi yana son tea yana nan kamar buzu,
ita kuwa Ummi cikin kula tace.
"Babana kaci abincin mana kanata shan ruwan zafi."
ido ya zuba musu yadda suka had'u su duka sunaci a kwano d'aya sai ya tuna mishi da baya, wanda baushe ke cewa kowa ya tuna bara baiji dad'in banaba,
idon ya kuma bud'ewa yana mai tunanin dah
ita Ummi taci da yaranta mata shida Nuruddeen kuma tare sukeci da Abbansu da bappa Ali koda last year haka sukeyi,
sai gashi bana kuna ba Abba ba Nuruddeen bappa Alinma da yake raye baizoba sabida rashin d'an uwanshi,
oh mutuwa wato dama haka abin yake ta rabaka da macecce ta rabaka da rayeyye,
gashi Hayatuddeen yanata baccinsa.
itako Ummi kamar ta gane me yake tunawa sai ta d'an gyara zama sannan ta zare cokalin cikin abincinshi ta saka cikin tiren da sukeci tace.
"To muci tare, kada kayi zurfin nazari gamu Allah ya barmaka mu gashi nanda bad'i kuma zakuyi taci da autana."
ganin ta tsareshi da ido ne kuma in baiciba bazata ji dad'iba yasa ya d'anci kad'an kana ya kuma amsar kofin tea d'in da Rahma take rik'e dashi tana sha kurb'a biyu yayi kana mik'a mata sannan ya mik'e da sauri.
ruwan wonka ya d'iba sannan ya shiga d'akinshi ruwan randar sanyinshi ya d'ansha kana ya d'auko soson shi da makilin da burosh.
a nitse yayi wonkanshi yana fitowa ana kiran assalatu.

Dama tuni su Ummi sun gama sahur d'insu har Raliyya ta tattare wurin.
D'akinshi ya shiga kasan cewar yau jumma'a ace kuma azumine,
shiyasa ya zaro wani tattausan yadi mai sauk'in kud'i fari k'al rigar anyi mata d'inkin zamani anyi d'an aiki da yellow zare, bayan ya gama sa kayan sunyi d'as a jikinshi sai yasa hular zannabukar mai d'an surkin yellown zare sai takalma suma farare masu d'an ratsin yellow.
Sosai yayi wani irin baiyanennen kyau,
wanda gani d'aya zakayi mishi kasan Allah ya masa cikar halitta da haiba, gaba d'aya alamun zarra da tsurar cikekken d'a namiji sunata baiyana a jikinshi tuni muryarshi tayi kauri alamun cikar balaga da d'an dad'ewa,
gwarabanshi suna ta hab'aka yayinda duk wani sashi na jin d'an adam dake iya fidda gashi,
nashi sunata yabanya,
hatta gefen kunnenshi yana ta nuna alamun tsirowar saje,
hakan sharabanshi da singalalin hannunshi da k'irjinshi,
tuni gashin girarshi ta zama d'aya daga cikin abinda ke Jan hankalin mutane ih zuwa ga kallonshi dan gashin girarshi har had'ewa suka bisa karan hancinsa,
hakama gashin idanunshi zar-zar dasu lips enshi kuwa jazir dasu ko yaushe kamar an shafa musu man baki zakaga suna shek'i sirarane sai dai sunada d'an fad'i da taushi dan ko d'an dannesu yayi da harshenshi sai kaga wani wurin ya lotso ya kuma yi fari,
yana kuma janye harshenshi zakaga ya koma janshi,
yatsun hannunshi da sawunshi kuwa suma kansu abin ganine.

Tsayuwa yayi gaban wannan dogon madubin hannunshi rik'e da turare,
feffesawa yayi a jikinshi yadda bazaiji gafinshi a mak'oshinsa ba.
carbi ya d'auka kana ya fita nan ya samu Raihana ta tada Hayatuddeen da Faruq sunyi al'wala,
shiyasa ya tasasu a gaba suka nufi masallacin k'ofar gidan nasu.

Bayan an idar da salla su Hayatuddeen suka tafi gida shi kuma sai ya d'an zauna yayi azkar saida ya gama sannan ya mik'e ya fita a harabar tsank'ayarsu ya samu Salisu na jiranshi.
Dan haka sai yayi sauri-sauri ya shiga gida a tsakar gida ya samesu duk suna ninnike hijaban da sukayi salla dasu,
Ummi kuwa har yanzu carbine a hannunta gefenta ya d'an rusuna kana ya motsa lips enshi a hankali alamun. "Ina kwana?."
"lfy lau Babana har zuku tafi ko?."
tace dashi cikin kula kai ya gyad'a mata alamun eh,
sai ya kuma gaida Adda Rahma kana su Raihana suka gaidashi,
Raliyya kuwa tuni ta har-had'a kwanun wonke-wonke tana wonkewa.
da sauri Ummi tace.
"To Allah ya kiyaye hanya ya kaiku lfy ya dawo daku lfy." sabida jin Salisu nata danna mishi hon
Amin Amin suka amsa baki d'aya kana ya mik'e ya fita.

Suna isa gombe kamar kullum Salisu ya ajiyeshi kana yaja ya tafi ya fara aikinshi.
Shi kuma cikin masallaci ya shiga,
baccin da baibane ya dan fara fizgarshi haka yasa ya konta,
cikin k'ank'anin lokaci yayi bacci.
8:00 Am ya farka da sauri ya mik'e,
ya fita harabar wurin ruwa ya saya yayi al'wala sannan yazo yayi walaha,
daga nan ya nufi cikin kasuwa.
Chapter 17 · 0% Book details