← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 116

Sashe 95

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tasowa Ahmad yayi tare da ƙarasowa har gaban keken Saifuddeen, cikin yanayi me ɗauke da tsananin tausayawa Ahmad ya rungume Saifuddeen, tare da sakin sabon kuka, tunda yake bai taɓajin zafi da ciwon Nakasar da ta samu Saifuddeen ɗinba sai yau.
Ummi datun shigowarsu ke tsaye abakin kitchine tana jinsu batare dasun kula ba, wani irin karyewa zuciyarta tayi, yayinda tsananin rauni ya bayyana akan fuskarta, idanunta ne suka cika tab da ƙwalla, cikin sanyin jiki ta tako ta ƙaraso cikin falon,   jin motsinta yasanya Ahmad sakin Saifuddeen ya juyo tare da kallonta, ganin yanda hawaye ke gudana akan idanun Ahmad ɗin yasanya hawayen dake cikin idanunta samun daman gangarowa, murya araunane tace.
"Kada ka ɓoyemin komai Ahmad, taƙisa ko? taƙisa saboda Nakasar dake tattare dashi ko?".
Wani murmushi mai ciwo Ummi tayi tare da duban Ahmad cikin rawar murya tace.
"Sanar dani gaskiya Ahmad kada ka ɓoyemin!".
Kuka Ahmad ya fashe dashi tare da zama akan kujera, ayanda yakejin zafi da tsanar Zaleeha acikin zuciyarsa bayajin zai iya rufe cin mutumcin da tayi musu, cikin muryar kuka yasanar da Ummi duk abun daya faru inda ya ƙarishe maganan  yana kuka sosai, don sosai abun keci masa rai.
Hawayene suka cigaba da fita daga cikin idanun Ummi.  Sosai hankalin Saifuddeen yakai ƙololuwa wajen tashi sakamakon ganin da yayi Umminsa na kuka, aduniya idan akwai abun da ya tsani gani to hawayen Umminsa ne, Yana matuƙar son mahaifiyarsa ta yanda bayason shiga damuwarta koda ta ƙwayar zarra ne, sam baiso ace sanadinsa Umminsa ke kuka ba, ahankali ya shiga murza kekansa har ya ƙaraso gareta, hannayensa yasanya yashiga share mata hawayen dake fuskarta, ɗago kai Ummi tayi tana kallonsa, Idanunsa wanda sukai ja ya lumshe tare da gigiza mata kansa,  wani irin sabon kukane ya zo mata, hakan yasa takawar da kanta gefe,  ji take kamar zuciyarta zata fashe saboda tsabar tsananin tausayin ɗan nata daya cika zuciyarta,  cikin dauriya haɗi da ƙoƙarin kauda rauninta ta juyo ta kallesa, hannunta tasanya ta shafi ƙuncinsa cikin son kwantar masa da hankali tace.
  "Kada  hakan yasanya rauni acikin zuciyarka Saifuddeen, idan ita taƙika balallai ne ace kowacce mace taƙi kaba, haƙiƙa nasan itama rashin sanin nagartan kace yasanyata ƙin amincewa, amma sam baƙinka take ba, babu macen da zata ƙin Saifuddeen, saidai taƙi aminta dakai abisa rashin sani nagartarka."
Lumshe kyawawan idanunsa yayi tare da ɗan sakin murmushi, haƙiƙa yaji daɗin ƙarfin guiwan da Ummin nasa ta basa, har acikin zuciyarsa yaɗanji sanyi.
Ahmad dake kallonsu tsananin tausayinsu ne yasake rufesa, hannayensa yasanya ya sharce hawayen dake kan fuskarsa. 
Ishaq kuwa kasa cewa komai yayi, raunin dake zuciyarsa yasanya gaba ɗaya jikinsa yayi weak, sosai kukan da Ummi tayi ya taɓa masa zuciya, sam baitaɓa tsammanin haka daga Zaleeha ba koda wasa, baitaɓa tunanin cewa ƙuruciyarta zai ruɗeta har takai gayi musu rashin mutumci ba, haƙiƙa zafafan kalaman da ta faɗamusu sun daki zuciyarsa sosai, sam bai damu da baƙaƙen maganganun da ƙawayenta suka faɗa musu ba, saboda koba komai sudama basaninsu sukayi ba, amma ita Zaleeha fa?."

Cikin son kwantar musu da hankali shida Ishaq Ummi tashiga basu baki, tare da yi musu nuni da cewa, ɗan Adam baya taɓa iya tsallake ƙaddaransa, ko ba gasu bama, mutanen da suke da cikakkiyar lafiya ma suna iya fuskantar irin haka, sannan taƙara da tausasa musu zuciya,  sam Ummi bata barsuba saida taga zuciyar kowannensu yayi sanyi, amatsayinta na Uwa ta gari, haka ta shanye gaba ɗaya damuwarta ta kwantar musu da ɓacin ransu, cikin ɗan nutsuwa da Ishaq ya samu, ya tashi tare dayiwa Ummi da Saifuddeen Sallama, Ahmad ne ya rakashi har waje, inda driver'n sa ke tsaye yana jiransa.  Koda Ahmad ya dawo daga rakiyan Ishaq kai tsaye ɓangarensu ya nufa.

lura da Raliya tayi cewa mijin nata yana cikin yanayi marar daɗi, yasanyata kwantar da murya tare da lafewa ajikinsa, cikin salo irin nata na ƴa mace ta shiga kwantar masa da hankali tare da neman sama nutsuwa, lokaci guda ta fitar dashi acikin hayyacinsa, inda ya rungumi matar tasa tare da kawar da duk wata damuwa dake cikin ransa.

Cikin son samawa zuciyarsa nutsuwa ya sarrafa kekensa, inda ya nufi hanyar ɗakinsa,  yana shiga ya turo ƙofar ɗakin ya rufe,  ahankali ya tuƙa keken nasa tare da ƙarasowa cikin tsakiyan ɗaki, cikin hikima ya cire kayan jikinsa, inda ya rage dagashi sai boxer,  kaitsaye bathroom ya wuce, nan ya haɗawa kansa ruwan wanka, kamar yanda ya saba, cikin hikima yayi wankansa,, bai wani jima acikin banɗakin ba yafito sanye da bathrobe ajikinsa,   sama-sama yashafa body lotion ɗinsa, tare da feshe gaba ɗaya jikinsa da daddaɗan turarensa, sif ɗinsa ya buɗe tare da ciro wata farar short sleeve da kuma wani combat 3 guater jeans ya sanya, sosai kayan suka amshi jikinsa,   kasancewar akwai alwala ajikinsa, yasanya ya shumfuɗa sallaya tare da sauƙa daga kan kekensa, kamar kullum kuma koda yaushe azaune ya gabatar da sallan Magrib ɗinsa, bai tashi akan sallayan ba harsaida yayi sallan Isha, koda ya gabatar da addu'o'insa kamar yanda ya saba, yunƙurawa yayi ya hau kan kekensa, cikin nutsuwa ya shiga tura keken nasa har izuwa bakin haɗaɗɗen gadonsa wanda aka lailaye samansa da tattausan bedshet mai kyau,  cikin hikima ya sauƙo daga kan keken nasa tare da kama jikin gadon nasa ya hau,    kwanciya yayi luf akan gadon tare dakai hannunsa gefen gadon inda anan makunnin wutan ɗakin yake ya kashe,  bedsite lamb ya kunna, sai yanayin ɗakin yayi daɗi shiba duhu ba shikuma ba wadataccen haske ba.

Ɓangaren Zaleeha kuwa, ranta amatuƙar ɓace haka suka koma falon Mama, cikin rufewar ido Zaleeha na shiga cikin falon ta yaye mayafin kanta, saboda tsaban ɓacin rai da takeji, idanunta har rufewa suke, cikin ƙunan zuciya tace.
"Ni! wai ni! Zaleeha Kurma kuma Gurgu zaizo yace yanaso,
lallai mutanen nan sunfara ganin damata da yawa, chab lallaima nakasassunnan, wato shiga cikinsu da nakeyi ina murmushi shine abun dayasa harsuka rainani ko, waima wannan ɗan ruwan ni zaice yanaso na, ko nayi masa kama da kalan matar aurensa ne?, da sauri taƙarasa gaban ƙaton madubin dake jin k'ofar falon, tsayawa tayi tana me ƙarewa kekyawar surar jikinta kallo, wani irin kuka ta fashe dashi tare da kai dubanta ga su Balkisu waƴanda sukayi saƙare suna kallonta, cikin ƙunan rai da sheshsheƙan kuka tace.
"Shin nima akwai wata nakasa ajikina ne dahar wani banzan nakasashshe zaizo yace yana sona?".
Dariya Bilkisu ta kwashe dashi cikin tsananin shaƙiyaci tace.
"Kawai ganin dama ne irin nasa, hmmm amma wallahi wannan mutumin ya raina miki hankali, tayaya ma in ban da rashin tunani irin nasa da tsaurin ido zai dubi ajibon yarinya kamarki yace wai yanaso".
  Dariya ta ƙara kwashewa dashi tare da tafa hannunta, cikin son ƙara cusawa Zaleeha tsanan Saifuddeen tace.
"Kurma fa, kuma bayan haka ma wai gurgu, lallai kam aikuwa daki auri wannan gwara kin auri dutsi, donshi dama dutsi-dutsi ne bayako motsi, sai inke kika motsa shi, amma wannan kam banga dame zai amfaneki ba, saidai in kuma ko zaman jinyarsa zakiyi ba zaman aure ba!".

Rashida ce ta sauƙe ajiyar zuciya tare da duban Bilkisu dake ta dariyan mugunta, cikin ƙasa da murya tace "Haba Bilkisu dan Allah kibari hakanan, nifa Allah gayen yabani tausayi, sannan tsantsar kyawunsa ya tsoratani, koda farko Allah banso yin dariya ba kedaice kika sani, amma gaskia gayen sam bashida wata makusa, kunfasan wata nakasar bata zama kasawa, idan kikaga nakasashshe ya kasa, to tabbas ya kashe zuciyarsa ne, kuma kunsan nakasar zuciya tafi kowacce nakasa ciwo, sannan ayanda na fuskanci mutanen nan sam su awajensu.
Nakasarsu ba kasawa bace, don tabbas baƙaramin jahadi sukayi ba da sukazo miki da maganar Soyayya kuma ai komin yaya masoyi yafi mak'iyi".

Wata uwar harara Bilkisu ta aunawa Rashida cike da baƙin ciki tace.
"Tab amma dai Rashida baki da kai, me za'ayi da waƴannan nakasassun, kyawunsa na banza na wofi, idan kece suka zo gunki da batun soyayya na tabbata bazaki amince ba."   Tsagaitawa da maganan tayi tare da dafa duka kafaɗun Zaleeha cikin zugan hasada tace.
"Wallahi kada kiyarda ki kashe rayuwarki wajen zama da nakasasshe, me wannan zai yi miki wanna ai dashi da mace duk d'aya, saidai baƙin cikinsa yayi ajalinki,  da kyaunki da ƙuruciyarki da komai ki cuci kanki ki auri nakasasshen da bazai iya kauda miki budurcinki bama, ae wallahi Zaleeha kinci baya!".

Wani irin kuka Zaleeha ta sake tare da faɗawa jikin Bilkisu cikin aminta da kalaman nata tace.
"Bazan taɓa sauraransa ba Wallahi, koda ace duk duniya zasu taru akaina don na soshi, na kuma zauna dashi, bazan taɓa aminta ba, Wallahi na tsaneshi tsana me tsanani, danayi rayuwar aure dashi gwara na mutu, don bazan iya ɗaukar baƙin cikinsa ba!!".
Cikin kukan dayaci ƙarfinta ta juya da gudu ta wuce ɗakinta.
Wani irin munafukin killer smile Bilkisu tayi tare da bin Zaleehan da kallo.
Rashida kuwa ajiyar zuciya ta sauƙe tare da kwantar da kanta gefe, cikin sanyi tace "Amma Bilkisu dakin tausasa harshenki akan sa, saboda ƙaddara nakan kowa.....".

"Dakata Rashida ai nima nasan ƙaddara nakan kowa, amma wannan nakasashshen gurgunne dai Insha Allah Zaleeha bazata aureshi ba".

Ajiyar zucia Rashida ta sauƙe tare da ɗaukan jakarta, duban Bilkisu tayi tare da cewa. "Natafi sai gobe saduwar al'khairi".

Da sauri itama Bilkisu ta ɗauki jakanta tabi bayan Rashidan, don sam bataso kowa yagane ainihin nufi dakuma abun dake ranta da zuciyarta, saboda ita tamkar mage take me kwanciyar ɗaukan rai...

SAIFUDDEEN.
Chapter 95 · 0% Book details