← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 116

Sashe 28

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Pillows inshi ya d'an d'ad'ad'aga alamun yana duba abu,
sabuwar woyarshi ya d'auka sannan ya fito ya nufi d'akin Ummi yana kunna woyar,
gefen Ummi ya zauna wacce take shan fura da nono mai sanyi.
da sauri ta mik'a mishi kofin kai ya jingina da gado kana ya amshi kofin,
kurb'a ya d'anyi sannan ya fara rubutu a woyar da tun randa ya dawo daya sata a caji ta cika ya cireta ya ajiye bai kuma bin ta kantaba sai yanzu,
rubutu yayi sannan ya nuna mata fuskar woyan.
"Ummi zanje in gaida su Baba Ashiru kuma zan isa gidan Baba Hamisu ma, kuma ya kamata inje dasu Faruq da Hayatuddeen,
gashi kuma suna gidan Goggo Dada."
bayan ta karanta ne ta d'an gyara zama kana tace.
"To kaje ka cewa Salisu ya d'aukosu mana."
kai ya gyada cikin gamsuwa daga nan yasha fura da nonon sannan ya fita yaje ya gayawa Salisu, cikin k'ank'anin lokacin Salisu ya d'aukosu.

Bayan sun dawo ne ya tasasu a gaba suka tafi Katafila inda nan gidan Baba Ashiru yake,
suna shiga matarshi ta tarbesu a mutunce bayan sun gaisane tace su isa yana k'ofanshi tare da abokanshi
nan ya tasa keyarsu Hayatuddeen suna isa suka samesu a harabar wurin yana tare da abokanshi a ciki harda Malamin isilamiyar su Saifuddeen,
yana ganin Saifuddeen ya saki murmushi tare da cewa.
"Masha Allah Saifuddeen d'alibina, yanzu kuwa nake mgnarka."
da sauri ya isa inda suke cikin girmamawa ya basu hannu duk ya gaidasu d'aya bayan d'aya,
Baba Ashiru kuwa rik'e hannun Hayatuddeen yayi yana shafa kanshi,
shi kuwa Malaminsu Saifuddeen cikin iya mgnar kurame yayi ta tambayar Saifuddeen bayan rabuwa nan yake sanarwa Saifuddeen shima ya k'aura ai yanzu baya Dukku jiya da yamma yazo dan ziyartan 'yan uwa da abokan arzik'i,
hira sukayi sosai dan Malamin nasu yana tsananin son Saifuddeen dan ya yarda da tarbiyarshi tun yana ji gashi yasan yaron yanada tsananin ilimi da fahimta.
koda suka tashi tafiya sai Saifuddeen ya d'an sunkuyo kud'i ya zaro a aljihunshi 'yan d'ari bibbiyu kimanin dubu bakwai dubu biyu ya ware ya ya ajiye a gaban Baba Ashiru sannan ya kuma zaro dubu biyu ya ajiye a gaban Malamin nashi ya kuma ajiye a gaban d'aya abokin nasu dubu biyu kana ya maida dubu d'aya cikin al'jihunshi,
kusan a tare suka had'a baki wurin cewa.
"A a haba dai Saifuddeen in bamu baka ba ai baza mu karb'a daga gareka ba."
kai ya rink'a jujjuya musu alamun dan Allah kada suk'i amsa su karb'a su samishi al'barka.
Cikin sanyi Baba Ashiru yace.
"Deen ai sai ka sani jin kunya ni ya cancanci in taimaka muku, amman na gaza sabida lamarin yau da gobe ya hana."
kanshi ya rinka jujjuyawa alamun kada yak'i karb'an kud'in,
sai ya kuma kalli Malamin nasu dake cewa.
"Kud'in sunyi yawa ai Deeen."
wayarshi ya d'an zaro yayi rubutu kana ya bawa melanin nashi wayar,
amsa yayi tare da fara karantawa yana karatun yana murmushi cikin dottaku yace.
"Bodd'i ta girma ai yanzu ta bar kukan zuwa makaranta ta daina genged'i in zata bada hadda,
to ta gode niko zan saya mata sweet dan har yanzu tana nan da son shan zak'i tunda ka koya mata."
murmushi Saifuddeen yayi tare da nuna Hayatuddeen yayi alamun tambaya ko ta kai Hayatuddeen d'in tsawo,
da sauri ya gyad'a mishi kai tare da cewa.
"wai ai tafi Hayatuddeen tsawo yanzu kusan shekaru biyar fa rabonka da ita tun randa ka bar zuwa Islamiya, nima tunda ka fara spacial education ban kuma ganinkaba saida ka gama daka gama d'inma sai rasuwar Abbanku na kuma ganinka."
murmushi yayi kana yayi alamun a gaidata daga nan ya sallamesu ya tafi.

Kai tsaye gidan Baba Hamisu ya wuce dasu Faruq,
bayan sun gaisa ne ya bashi sauran dubu d'ayan nan sannan ya bar Faruq da Adam anan dan suyi d'an kwana biyu.

daga nan ya tasa keyar Hayatuddeen suka nufi gidan su Aunty Nina dan yi musu gaisuwan salla,
suna fitowa yaji alamun saqo ya shiga woyarshi dake cikin aljihunshi,
yana dubawa kuwa yaga sak'on Ishaq ne yana ce mishi yazo Dukku fa gashi ga Ummi,
so jin haka yasa suka kama hanyan gida.
Yana shiga ya samu suna zaune a tsakar gida bisa taburma,
Ishaq sarkin surutu sai hira suketayi da Ummi da Adda Rahma,
suna shiga imran yayi sauri ya mik'e yaje ya ruggumi Saifuddeen tare da cewa.
"Oyoyo Hamma Saifuddeen yau kam nima nazo gidanku, Umminka ta bani fura da nono nasha."
kanshi ya shafa tare da jinjina mishi,
Hayatuddeen kuwa tuni ya isa jikin ishaq sunata surutu dan duk masurutane,
Ummi da Rahma kuwa sai murmushi sukeyi,
yayinda Ishaq yake cewa Hayatuddeen.
"Yauwa Autan Ummi kaga yau na kawo maka abokinka imran autan Mama."
da sauri Hayatuddeen ya juyo ya kalli Imran tare da cewa.
"Shima autane?."
cikin dariya ishaq yace.
"Eh shima autane kuma sakali irinka."
aifa daga nan Hayatuddeen da imran suka d'inke dan sakalcinsu iri d'aya ga tsawonsu dai-dai.
ranan Ummi da Ishaq da Saufuddeen da Adda Rahma da Aunty Nina tare suka wuni koda yamma tayi Ishaq yace dole Saifuddeen ya rakashi Shabewa dan zaije ya gaida Goggo Dada ya kuma ga Raihana da Raliya dan yayi missing d'insu,
aifa haka suka d'unguzuma da su Saminu da dama yake son bin bayan
Raihana nan sukaje suka gaida Goggo Dada,
daga bisani suka dawo dole Ummi tasa Ishaq da Imran suka kwana.

Washe gari suka tafi da Saifuddeen.
saida yayi kwana biyu a gombe sunje gidansu Jabeer da Hisham har gidansu Ibrahim duk sunje, kana Baban Ishaq ya tasasu gaba shida kanshi ya kaisu k'ungiyar (Jonapwd) nan take sukayi duk abinda ya kamata na shaidar suna cikin members d'in k'ungiyar.
Daga nan suka ziyarci abokan su da suka yi makaranta d'aya.
Sannan ranar da zai koman yaje ya wuni a kasuwa dan hutun salla ya k'are.
to a ranar ya tambayi Alhaji Aliyu gidan baba Bello ina yake,
to cikin sa'a ya samu Alhaji Aliyu da kanshi ya d'aukeshi sukaje gidan Baba Bello dake cikin jeka da fari,
nan suka samu ashe baida lfy shiyasa tunda akayi salla bai dawo kasuwa ba,
yayi farin cikin ganin Saifuddeen sosai bare da Alhaji Aliyu ya yaba mishi nagartan Saifuddeen d'in,
shi kuwa Saifuddeen wannan 10k d'in ya zaro ya bashi ya yace ya nemi mgni sannan ya d'anyi cefene,
yayi godiya sosai hakama matarshi Inno sunji dad'in sosai,
sannan yace ba matsala Saifudddeen yaci gaba da kasuwancin shi, sai in Allah yasa ya samu lfy, in ya dawo sai suci gaba da kasuwancin.

Da haka dai sukayi sallama suka tafi.

Tun daga ranar Saifuddeen yaci gaba da kasuwancin sa ba kama hannun yaro, sosai fa harkan leda ta amsheshi harkalla taci gaba, ya k'ara sabawa da mutane sosai,
duk sati yakan ware ribar kwana biyu ya yiwa baba bello sayayyan kayan abinci,
na dubu goma sannan ya bashi dubu biyu ya rik'e wannan abu yasa sam Baba Bello bai kuma sha'awan komawa kasuwancinsa ba tunda yanaga ya huta da wahala kuma ya lura hannun Saifuddeen yanada al'barka duk abinda ya kama yana cin gaba.

Shi kuwa Saifuddeen ribar kwana biyar d'in yake had'awa yayi sayayyan abincin gidansu to zai yi mako biyu kuma yana saka ribanshi a asusu,
riban omonshi kuwa da pure water daya ya koma sai yake ajiyesu dan hidiman yau da kullum.

Ya Adnan kuwa tuni ya fara aikinshi gadan-gadan shida Dukku sai dai ziyara.
Tuni Mudassir ma yaci gaba da karatunshi a G.S.U inda a gidan Adnan d'in yake zama,
Ishaq ma tuni yaci gaba da karatunshi.
Hakama Saminu shima yayi nisa a karatunshi.

Salisu ma yanzu ya ci gaba da kanshi sabida Saifuddeen ya rege mishi kud'in balance sosai to sai in bashida darasi yake fita aiki dan ya samu damar yin hidimomin karatunshi da kula da kakarshi.

Hayatuddeen kuwa tuni ya fara koyan d'inki a wurin Ahmad da shima yanzu yanata cuku-cukun ci gaba da karatunshi inda yake son kafin ya koma cikin gombe Hayatuddeen ya gware a d'inkin,
shi kuma sai ya tafi da kekenshi zaije yaci gaba da karatu,
duk cikinsu Saifudddeen ne da Warisu sune basu samu daman ci gaba da karatun suba.

Sai dai shi Saifuddeen tuni ya samu ya gamawa Raihana da Raliya cuku-cukun karatunsu tuni ma Raihana kam ta k'are secondary school.

Yanzu hankalin Ummi ya fara konciya,

Tuni Ya Adnan kuma ya baiyana soyayyarshi da Rahma amman biki yace sai next year kowa yayi farin ciki da haka.

Koda Ahmad ya koma gombe gidan ya Adnan d'in shima ya zauna.

Kasuwa tayi al'barka kullum Saifuddeen baya fashin zuwa shida Salisunshi,
yana zuwa zai rarraba leda sai ya d'auko omonshi bisa kai sannan ya rik'o botikin pure waternshi dasu Coca-Cola yayi ta yawatawa kuma Alhamdulillahi sosai yake ciniki Allah ya sawa kasuwancin nashi al'barka.

Kota ina yanzu an sanshi a kasuwar gombe.

Yanzu duk kostomominshi suna da number shi yanada number su,
duk mai buk'atan kaya zai kirashi ya kai mishi misali in ledodin su ya kare suna son k'ari ko in suna son abin sha mai sanyi ko omo to kawai sai su mishi text.
Zuwa yanzu duk abo kanshi suna da woyoyinsu.

Yau jumma'a tunda sanyin safiya da suka shigo ya gama reba lododinshi har ya d'auko omonshi da da kayan sanyinshi yanata zagayawa.

K'arfe d'aya dai-dai na rana ya shiga bakin shagonsu Jabeer ya d'an zauna dan abin sanyinshi ya k'are kuma ya gaji shiyasa ya zauna dan ya d'an huta kafin ya d'auko wani,
sunata d'an tab'a hira da Jabeer
bai jima da zamanshi yaji wayarshi na babureshin cikin al'jihunshi na k'irjinshi alamun sak'o ya shiga, a hankali yasa hannunshi ya zaro wayar,
yana dubawa yaga Alhaji Kabiru ne mai shagonsu Mai, Manja, Maggi, kafi, da dai sauranshi.
Bud'e sak'on kana ya karanta sak'on.
"Saifuddeen kawo mana ruwa mai sanyi da molt guda hud'u sai fanta d'aya."
amsa ya maida mishi cewa.
"To gani nan zuwa."
daga nan ya mik'e tare da zaran botikin,
cikin sabo Jabeer yace.
"Allah ko Balarabe wlh ka rink'a hutawa fa."
kai ya jinjina mishi tare da mishi alamun ai.
"Me nema baya gajiya in dai yana samun d'an na kashewa a sama."
daga nan ya juya ya tafi.
Chapter 28 · 0% Book details