← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 116

Sashe 33

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kusan tsawon mako uku kenan da farashin maggin yayi sama,
wanda yayi dai-dai da cikin tsakiyar damuna ne sama ruwa k'asa ruwa, kayan abinci yayi tsada,
tuni talaka ya fara shiga hau'ula'in rayuwa,
bappa Ali da Saifuddeen kuwa tuni sun fara shirye-shiryen bud'a kasuwancin nasu Yau jumma, kuma tun bayan sallan la'asar aketa zuga ruwa kamar da bakin gwarya,
dole cikin ruwan Salisu da Saifuddeen suka kamo hanyar dukku,
daga gombe har cikin Dukku ruwane yake dukansu tamkar zai jasu ya tafi dasu,
k'arfe shida dai-dai suka isa cikin dukkun sauri-sauri gudu-gudu Saifuddeen ya shiga cikin gida lokacin da Salisu ya sauk'eshi dan har lokacin ana d'an yayyafi irin na alamun ruwan ya d'auke sai yaf-yaf ruwan keyi.
Yana shiga kai tsaye d'akin Umminshi ya nufa dan wannan al'adarshi ce muddin ya dawo ko ruwa ko iska ko dare ko rana sai ya fara shiga inda take ya ganta ta ganshi kafin ya wuce d'akinshi,
yayinda ita kuwa Ummi duk nisan dare bata tab'a iya yin bacci har sai taga dawowanshi, duk ruwa kuma bata rumtsawa sai taga ya dawo.
Yana isa bakin k'ofarta yasa hannu ya bud'e labule,
murmushi yayi ganinta zaune ta zubawa k'ofar idanu yayinda Hayatuddeen ke konce yayi pillow da cinyarta Rahma kuwa na gefenta tana gugan kayan data wonke,
Raihana kuwa nayiwa Ummi kitso,
ajiyan zuciya Ummi tayi tare yin murmushi ganin gudan jininta,
cikin tausayawa Raihana tace.
"Sannu da hanya Hamma Saifuddeen."
kai ya jinjina mata alamun yauwa.
Rahma kuwa ajiye anyone d'in tayi tare da cewa.
"Saifuddeen jeka canza kaya kalli yadda ka jik'e jilik sanyi zai kamaka illah fa."
cikin body language yace da ita.
"To."
sai ya kuma yi musu alamun ina Raliya dasu Faruq."
gane abinda yake nufine yasa Ummi ce mishi.
"Suna wurin Aunty Nina."
kai ya jinjina dan yasan dama su Faruq suna son zuwa wurin Aunty Ninan wacce tuni ta haifi d'anta wanda akayiwa Abba mai suna shiyasa su Rahma ke kiranshi da Abban tuni yaron ya girma har yana rarrafe.

Juyawa yayi ya nufi d'akinshi daga bakin k'ofa ya mik'a hannunshi ya jawo towel inshi dake shanye a kan k'ofanshi, botiki ya d'auka ya cikashi da ruwa kana ya d'auki kondon soson wonkenshi,
ban d'akinshi ya juya ya nufa dan jin ruwan ya d'auke kit.

Wonka yayi fes sannan ya d'aura towel d'in ya fito,
buta ya d'auka yayi al'wala sannan ya shiga d'akinshi mai ya dauka kana ya zauna bakin katifarshi murze jikinshi yayi ciki da woje sannan ya mik'e tsaye ya zaro tattausan boxer inshi fari k'al ya fesheshi da turare sannan ya saka,
yana gama gyara zaman boxer d'in a k'ugunshi ya konce towel d'in ya d'anyi taku biyu zuwa uku sannan ya isa bakin k'ofar wore towel d'in yayi ya shanshi kan k'ofar,
sannan ya juya ya isa bakin 'yar durowar tashi ya zaro farin vest fara kal ya fesa mata turare yasa sannan ya kuma zaro bak'ar jallabiya ya zurata a jikinshi,
sai ya kuma feffesa turaren,
sannan ya matso gaban madubin shin hannu yasa ya gyara suman kanshi da yake konce lib sai shek'i yakeyi wayarshi ya zura a al'jihu sannan yasa takalmanshi dake bakin k'ofa ya fita.

A tsakar gida ya samu su Ummi dasu Raihana da Hayatuddeen suna al'wala,
kitchen ya lek'a ganin Rahma na kwasar abinci,
ganinshi a bakin k'ofa yasa tayi murmushi tare da cewa.
"Yauwa je kayi salla ana idarwa ka dawo yau miyarka nayi tunda naga hadari nasan zaka dawo da yunwa."
murmushi yayi tare da mata alamun tayi sauri ta gama lokacin salla yayi,
sai ya kuma kalli fuskarta ganin alamun saida tayi al'wala kafin tazo ta fara kwasan tuwon shiyasa ya juya ,
ya kamo hannun Hayatuddeen da Faruq da yanzu ya shigo suka nufi masallaci.

Koda aka idar da salla, basu dawo gidaba nan ya zauna da Hayayuddeen da Faruq saida akayi sallan isha sannan suka fito.
a bakin masallacin Saifuddeen ya kamo hannun Warisu sai ya kuma yafito Salisu tare da musu alamun su zo suci abinci,
kasan cewar yanzu su ukune rak suka rage a dukkun dan Ahmad, Samuni, Mudassir, duk suna cikin gombe,

Cikin yamutsa fuska Warisu yace.
"Tab aini bani cin abinci da dare dan wlh kun sani bani son k'iba,
gwara kai Saifuddeen jikinka ba irin nau bane."
Salisu ne ya d'an harareshi tare da cewa.
"Kuma in sha Allah wata rana sai kayi k'iba."
sai ya kuma juyo ya kalli Saifuddeen tare da cewa.
"Ni kam a koshe nake muna dawowa na samu iya shatu tana kwasar tuwo tayi wannan hegiyar koriyar miyar nan tata kad'a kwarya yunwace ta sani cinta dole."
dariyar mugunta Warisu ya mishi tare da cewa.
"Hege ka dai biyewa wannan tsohuwar yaseen sai ta toshe maka kwanyarka da koriyar miyar nan ka zama huhulahu."
yana fad'in haka ya juya da sassarfa ya gudu ganin Salisu zai kai mishi duka,
shi kuwa Salisu hamma yayi tare da cewa.
"Kaga mai jajayen kunnuwa ni zanje inyi bacci saida safe."
daga nan sukayi saida safe, shi kuwa yasa Hayatuddeen da Faruq a gaba suka shiga cikin gida yayinda Bappa Ali ke binsu a baya.

Suna shiga tsakiyar gidan ana dawo da wutar nepa,
kai tsaye d'akin Ummi suka shiga suna shiga ya mik'awa Raihana woyarshi tare da mata alamun taje ta sa mishi caji a d'akinshi,
da sauri ta karb'i wayar kana taje ta jona wayar sannan ta dawo.
tana shiga kuma Rahma ta kalleta tare da cewa.
"Je kitchen ki kawo musu abincinsu."
to tace tare da juyawa ta nufi kitchen d'in,
Ummi kuwa gyara zamanta tayi tare gyara sallayan da take zaune a kai sannan tayiwa Saifuddeen d'in alamun yazo ya zauna,
kai ya gyad'a mata kana yaje ya zauna a gefen damanta Hayatuddeen kuma ya zauna gefen hagunta yayinda Faruq ya zauna gabanta,
Adda Rahma kuma kan gadon ta hau ta kwanta tare yin mik'a sannan ta bugi k'afad'an Raliya da tuni ta fara bacci yayinda Adam ke bisa ruwan cikinta,
a hankali ta bud'e ido,
sai ta kuma yunk'ura ta zauna jin Rahma na cemata.
"Ke tashi kije ki shiga kada kiyi bacci anan ki d'auki Adam ku tafi tare."
Kai ta gyad'a kana ta mik'e ruggume da Adam ta fita ta nufi d'akinsu, tana fita Raihana na shigo musu da abincin.

By

*NAKASA BA KASAWA BACE*

*PAGE 10*

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Free page

_Ga masu buƙatar sayan littafin turo katin mtn na 300 kacal ta wannan Number 09097853276. Ko ka/yi transfer ta bank ac na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa_

A gaban shi ta ajiye tiren, sannan ta d'an zauna gabanshi kular miyar ta bud'e sannan ta zuba mishi miyar a pilit mai d'an zurfi sai ta kuma bud'e na kulan ta sako mishi malmala biyu duk da tasan da wuya ya cinye d'aya ma,
kolban man shanun da Ummi ke mik'a mata ta karb'a bud'e marfin tayi ta tsulala man shanun mai d'an yawa, sannan ta jawo gongonin dakekken yajin borkonsu wanda yakeda ta k'amshi kanamfari da tafarnuwa d'an kad'an,
spoon tasa ta d'an motso miyar da yake wadace da kifi banda da busasheshen nama dariko kana ga wadacecciyar gyad'a da saida ya bulbulo mai,
robar da ta zubo ruwan wonke hannu ta mik'a mishi,
jawo robar yayi ya fara wonke hannunshi.
Ita kuwa Raihana wani pilet d'in ta kuma d'auka tasa malmala d'aya kana ta zuba miyar a kan tuwon sannan tasa man shanun tare da tarfa yajin borkonon a kai,
sai ta kuma kalli Hayatuddeen daketa yamutsa fuska shida Faruq cikin had'e fuska tace.
"Ku tashi kuci abinci."
Hayatuddeen ne ya zame ya konta tare da cewa.
"Ni wlh bazanci tuwoba na k'oshi."
shima Faruq had'e fuska yayi tare da cewa.
"Shima bazai ci tuwoba."
tura musu pilet d'in tayi tare da cewa.
"Kada Allah yasa kuci, cikina ko cikinku hegun yara sai iyayi da son k'arya talaka yace bazaici tuwoba."
Ummi dai sai ido ta zuba musu,
Rahma kuwa murmushi tayi sanin halin Raihana da gajin hak'uri bata jurar rainin wayo hak'urinta kuma ragaggene,
shi kuwa Saifuddeen gyara zamanshi yayi sannan ya jawo hannun Hayatuddeen da Faruq ya gyara musu zama sannan yasa hannu ya gutsuri d'an k'aramin loma tare da dandalo miyar sannan ya mik'awa Faruq wanda shi biyewa Hayatuddeen yake bawai baison tuwon har haka bane, bud'e baki yayi da sauri dan yana matuk'ar jin dad'in yaga Uncle inshi na bashi abinci a baki,
murmushi Saifuddeen yayi sannan ya kuma gutsuro loma ya dandali miya ya mik'awa Hayatuddeen dake zuzzumbura baki,
a hankali ya bud'e baki ya amsa dan dama muddin Hayatuddeen yaci tuwo tofa sai dai in Saifuddeen ne ya bashi da kanshi,
cikin lashe baki Hayatuddeen d'in yace.
"Adda Rahma miyar tayi dad'i yaseen kinfi Adda Raihana iya girki."
dariya sukayi baki d'aya yayinda tuni Raihana ta hatsala ta kai mishi bugu wanda ya kauce ya rab'a jikin Umminshi,
ita kuwa Raihana mik'ewa tayi ta fita ganin Saifuddeen ya sauya fuska,
shiko Saifuddeen loma ya kuma gutsura ya d'an dandali miyar da taketa nason man shanu da man kuli yasa a bakinshi,
idanu ya lumshe dan jin d'and'anon miyar nasa yawun bakinshi tsinkewa,
tabbas yasan yan uwanshi sun iya girki ko dan gada sukayi wurin Umminsu.
daga nan yaci gaba da basu abinci, yana basu yanaci, saida sukaci sukayi hanik'an sannan Adda Rahma ta tattare filin,
ganin Faruq ya fara hamma yasa Ummi ce musu.
"Maza ku hau gado ku kwanta saida safe."
da sauri suka hau suka konta tare da yin addu'a,
shi kuwa Saifuddeen alama yayiwa Adda Rahma da taje ta kira Bappa Ali,
kasan cewar tana ganewa yasa ta juya ta nufi side d'in Bappa Alin.

ita kuwa Ummi ta fito da asusun Saifuddeen duka uku dan ya mata alamun ta fitar dasu.
Chapter 33 · 0% Book details