← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 116

Sashe 23

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ya gama irgasune ya d'ago kai ya kallesu ganin kowa harkar gabanshi keyi ya sashi yin gyaran murya wanda yasa suka d'an kalleshi,
cikin d'an bud'a kafad'u ya bugi cinyar Saifuddeen haka yasa ya zuba mishi ido shi kuwa Ahmad murmushi yayi tare da cewa.
"Alhamdulillahi Ummi munyi kud'ifa wlh dole a fara ce damu alhazai."
cikin dariya Rahma tace.
"Toh al'hazai nawane asusun naku?."
gyara zama yayi tare da cewa.
"Kud'infa da yawa har dubu hamsin da takwas ne da d'ari biyu ne."
cikin jin dad'i Ummi tace.
"Alhamdulillahi Allah ya musu Al'barka."
Amin Amin sukace baki d'aya,
shi kuwa Saifuddeen gyara zamanshi yayi kana yayiwa Ahmad alamun ya cire dubu takwas da d'ari biyun saman ya bawa Ummi su,
haka kuwa yayi dan yana gane maganar abokinshi kuma d'an uwanshi, cikin lumshe ido Ummi tace to ni me zanyi dasu?."
kanshi ya tonk'oshe hagu da damanshi sannan cikin mgnar kurame ya mata bayanin,
"Ta karb'esu in akwai wad'anda take son yiwa wani ihsani tayi amfani da kud'in."
gane abinda yake nufi yasa tayi murmushi tare da cewa.
"To Allah ya saka maka da mafi kyawun sakamako Allah ya bud'a muku k'ofofin samu,
wannan zan sayi kayan yara koda kala uku ne a bawa ungiyar marayu."
kai ya jinjina mata alamar hakan yayi,
sai ya kuma yiwa Ahmad alamun ya cire dubu goma ya ajiye mishi,
bayan ya cire goman ne sai ya amshi sauran 50k d'in sannan ya zare dubu biyar ya bawa Adda Rahma yace ta d'auki dubu biyu ta bawa Raihana da Raliya 1-1,500 godiya tayi mishi sosai kana yasa 45k d'in a aljihunshi tare da musu bayanin dasu zai musu kayan salla.

Daga nan sukaci gaba da hira har zuwa 12:15 Am na dare jin masallatai sun fara tahajjudi yasa basuyi batun wani bacciba kawai sukayi al'wala suka nufi masallacin fada dan ba'ayi a masallacin k'ofar gidansu.
3:12 Am aka idar da tuhajjdin,
daga nan kowa ya nufi gidansu,
suna dawowa suka samu Rahma tana kitchen tana d'umama musu zabin, Ahmad ne ya nufi kitchen d'in tare da cewa.
"Adda Rahma nifa ferfesun nan ya ishen, me zaki dafa mana a sauk'ak'e?."
mik'a tayi tare da yin hamma kana tace.
"Dama nayi miya tun da dare dan nasan Ummi tafi son tuwo to nayi miyar bisasshiyar kub'ewa yanzu kuma na tuk'a tuwon semo."
"Yauwa to yafi kam."
cewan Ahmad yana juyawa yayi tsakar gidan inda ya samu Saifuddeen konce yayi pillow da cinyar Ummi,
suna zaune a nan dasu Raihana da Raliya har Rahma ta gama komai, kamar kullum Saifuddeen ne ya karb'i na gidan Babba Ali ya kai musu sannan ya dawo,
yau ya d'anci abinci sosai al'barkacin Ahmad,
bayan sun gama yin sahur d'insune ya mik'e sauri-sauri ya shiga wonka dan ganin an kusa kiran salla,
yana fitowa Ahmad ya shiga kafin ya fito tuni anyi assalatu,
yana fita ya kimtsa yasa wasu kayan Saifuddeen wanda shi kuma tuni ya kimtsa cikin k'ananun kaya wanda sukayi matuk'ar mishi kyau,
tare suka fita zuwa masallaci inda Hayatuddeen ke gabansu.

Suma su Ummi tuni sunyi haraman salla.
Ana idar da sallan Ahmad da sai hamma yakeyi ya yunk'ura zai tashi da sauri Saifuddeen ya kamo hannunshi tare da mishi alamun yayi azkar tukun,
tsaki ya d'an ja tare da cewa.
"Kai ni bacci nakeji."
bai kulashiba kuma bai sake mishi hannuba dole dai ya zauna sukayi azkar d'in a tare.

Suna shiga gida sauri-sauri Ahmad ya gaida Ummi sannan ya nufi d'akin Saifuddeen k'ure iskar fankar yayi sannan ya tura k'ofan d'akin kana ya hau bisa katifar yayi lub tuni bacci yayi awon gaba dashi.

Shi kuwa Saifuddeen bayan ya gaisa da Ummi da Rahma su Raliya suka gaidashi sannan ya tambayesu me sukeso ya saya musu kayan salla,
kab d'insu zabi suka bashi so da haka ya fita ya nufi k'ofar gida inda Salisu ke jiranshi,
yana zuwa suka gaisa kana ya hau yaja machine suka tafi.

Bakwai dai-dai suka isa, Saifuddeen na sauk'a Salisu yaja machine ya tafi,
shi kuma Saifuddeen kamar kullum cikin masallacin nan ya wuce dan baccin da yakeji yau yafi na kullum,
yana shiga ya koma gefe ya konta yana tasbihi a ranshi tuni bacci mai dad'i ya figeshi,
sai k'arfe tara da kwata ya tashi al'wala yayi sannan yayi walaha bayan ya idar ya fita ya tsallaka titi ya shiga cikin kasuwar da tuni ta cika tayi mak'il da bani adam.

Kai tsaye layin kantin kwari ya nufa inda nanne layin da dilansu yake,
yana zuwa ya samu ba kowa a gabanshi nan aka ware mishi aka bashi, daga nan ya cika k'aton kwalin nan ya azashi a kanshi ya fara bin layi-layi lungu da sak'o yana raba musu suna bashi kud'in na jiya.
Cikin awa hud'u ya gama, to yau sai bai nufi karb'o omonba sai ya wuce shagon Alhaji ishaq mai atampopi dasu laces materials shadda da dai sauransu.

Yana isa Alhaji ishaq d'in da kanshi ya tarbeshi fuska a d'an sake yace.
"A Balarabe yau babu omone?."
numfashi ya d'an fidda kana cikin yanayin zafin rana ya mishi nuni da kaya yakeso zai saya,
gane abinda yake nufi yasa Alhaji ishaq d'in nuna mishi ya tsallako ya shigo daga ciki dan ganin mata sun cika bakin shagon nashi mak'il ,
yana tsalla kowa ya shiga Ibrahim ya bashi hannu suka gaisa irin gaisuwar nan ta abokai,
cikin bada umarni Alhaji Ishaq d'in ya cewa.
"Yauwa Ibrahim kama fini gane mgnarshi maza kula da lamarinshi ka bashi duk abinda yake so a farashin sari."
cikin jin dad'i Ibrahim yace.
"Toh ba matsala."
sai ya kuma maida hankalin shi kan paper da Saifuddeen ya bashi inda ya rubuta mishi.
"Ina son atampa masu kyau da taushi guda biyu ka bani masu kyau na Ummi nane,
sai ka bani laces guda uku masu kyau Adda Rahma orange color takeso Raihana kuma lemon green da ratsin white take so,
Raliya kuwa red mai ratsin yellow color,
sai ka had'a musu da atampa d'ad'd'aya masu kyau fa."
cikin kula Ibrahim yace.
"Ba matsala."
sai ya kuma juyo ya fara zabo atampopi da laces masu kyau yan ma dai-dai tan kud'i,
duk wanda ya zaro in ka ganshi saikayi sha'awarshi.
nan ya gama zaro kusan laces kala goma atampa goma,
duk ya jibgesu gaban Saifuddeen,
nan shi kuma Saifuddeen ya fara zab'o wad'anda zai saya laces uku ya zaro sai atampopi biyar biyu na Ummi ne,
sosai ya zabo masu d'an karen kyau.
Wata mata dake cikin taron matan da suka cika bakin shagon ne ta zuba sshi ido tace.
"Kai wannan kekyawan yaro ya iya zab'an abu mai kyau gsky nima to shi zan bawa zab'i."
murmushi mutanen wurin sukayi dan gsky ta fad'i.
shi kuwa Ibrahim kud'insu ya rurrubuta mishi,
bayan ya amshi takardar ya karanta rubutun Ibrahim sai ya rubuta mishi amsa da cewa.
"Nima in nazo nan ba a farashin sari nake baku ledodina ba so nima kada kuce bazakuci riba a kainaba ai ita kasuwa ba k'arya bace kuma dan riba akeyinta sai ni kuma ba sarin zanyiba so naji duk yadda kuka saidawa saura laces in nan nima haka zan biya,
dan haka samin su a leda."
dole a dai yadda suke saidawa kowa a haka ya biyasu.

Daga nan sai ya nufi shagon Alhaji Yawale nan ya sayi wasu datsastsun yaduka masu hegen kyau yad'i ashirin ya saya dan sun bashi tabbacin yadi uku zai isha kamanshi d'inkawa dan haka ya sai yadi ashirin, yayi lissafi yadi tara shida Salisu da Ahmad yadi tara kuma Warisu da Mudassir da Saminu yadi biyun sama kuma Hayatuddeen.
sai ya kuma sayan wani yad'i mai kyau yadi shida uku nashi uku kuma Faruq da Adam,
bayan ya gama biyan kud'in sai ya kuma fito ya nufi shagon su Jabeer nan ya sayawa su Rahma gyale daddaya wanda zai shiga da kayansun duka bibbiyun,
kana yaje shagon masu d'inka hijabai ya d'inkawa Umminshi hijabai guda biyu,

sannan daga nan ya fito da ribanshi na yau ya sayawa Faruq da Adam kayan kanti kala daddaya.
Bayan ya gama had'a kayayyakin da ya sayan sai ya samu kowa ya samu kala bibbiyu sai Hayatuddeen ne ya samu kala d'aya,
so shiyasa ya ciro sauran kud'in nashi ya saya mishi wani yad'i kalanshi mai kyau,
daga nan ya had'a kayanshi kab wuri d'aya cikin irin k'attin ledodin nan,
sannan yaje ya ajiyeshi a shagonsu Hisham daga nan yaje ya d'auko omonshi yayi ta zaga yawa,
Alhamdulillahi yau garin akwai lumshi alamun hadarin forkon damuna sai manyan gajumare masu yiwa sararin samaniya rumfa.

Ya saida omon sosai inda ya samu riban 2,700.
Ganin yamma tayi sai ya saya musu fruits na 700 d'in.
ganin biyar tayi sai ya fito inda Salisu zai sameshi ba tare da ya d'auki kayan daya saya ba,
ya barsu a shagonsu Hisham sabida yana son sai gobe in yazo ya sayawa Goggo Dada da Aunty Nina da Bappa Ali kafin ya meda kayan,
sabida yanaga in ya medasu yau tamkar ya waresu ne.

Koda ya koma yayiwa Ummi bayani,
Ahmad kuma yau bai zoba a zatonshi Saifuddeen zaizo ne.

Washe gari kuwa kamar yadda yayi niya haka yayi,
daya gama hada ribarsa na jiya sai ya sayawa Goggo Dada turmin zani hakama Aunty Nina sannan ya sayawa Bappa Ali shadda mai kyau.
daga nan ya hada kayan sannan ya tafi tallan omonshi.
Chapter 23 · 0% Book details