← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 116

Sashe 40

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bedroom guda biyu dake cikin parlour dake k'asan suka fara kimtsawa suka kafa gadajen tare da durowowin da mirrors d'in,
sannan suka sassaka katifun,
sai kuma suka dawo cikin parlour suka kimtsa lumtsuma-lumtsuman kujerun masu kama da kiran royal sai dinning table mai azabar kyau da suka shiryashi a dinning area,
sai da suka gama kimtsa parlour sannan suka shiga d'aya kofar da zata sadasu da d'an karamin parlour da bedroom nan gado durowar suka kafa,
parlour kuma suka barshi ba komai,
sai kuma suka haura sama can suna shiga parlour bedroom d'in dake hannun dama suka shiga nan suka kafa gado da durowa da duk sauran kayan gado sannan
suka dawo falon nan suka samu Ahmad ya firfito musu da sauran kayayyakin da suka saya suka tara a d'aya bedroom d'in kamarsu cainis carpet da labulaye sai zannuwan gadaye da TV, Firij da dai sauran kayan wuta.
daga parlour saman suka fara saka labulayen masu azabar kyau da shek'i kalarsu pink and white, hakama kujerun da carpet d'in.
bedroom d'in da suka kafa gado suka shiga nanma suka sa labulayen masu kalar ja da fari,
zanin gado ma red and white sai carpet shima red and white,
suka gama kimtsa komai sannan suka dawo parlour suka ajiye d'an madaidaicin firij a cikin dinning area wanda shi bai samu damar samun dinnin table ba,
sai katon TV da suka manna a parlour,
daga nan suka sauk'o k'asa suka gama shirya koma inda kalan labule da carpet suke white and people.
sai tv da firij da suka ajiye komai a mazauninshi,
sai kuma suka shiga d'an k'aramin parlour nan suka malale tattausan carpet a tsakiyar parlour sannan suka lik'a tv a jikin bongo,
daga nan suka ajiye d'an k'ank'anin firij a parlour.

Daga nan kuma suka shiga cikin kitchen d'in suka shirya durowowin kitchen d'in na sama da k'asa sannan suka ciccibo kwalin gas suka zo suka sashi a mazauninshi sannan suka had'a ma sank'alin sink da bakin pompo sosai kitchen din yayi kyau.

Sosai gidan yayi kyau komai yayi ras,
daga nan Saifuddeen ya biyasu kud'in aikinsu kana ya sallamesu,
sannan suka dawo parlour suka zauna shida Ahmad bisa kujerun suka zube suna shak'ar k'amshin sabon fenti da k'amshin sabbin kayan d'aki inda ya had'e ya zama daddad'an k'amshi, Ahmad ne yayi mik'a tare da cewa.
"Masha Allah gida yayi kyau sosai,
sai dai nasan Hayatuddeen zaiyi mitar an sa mishi k'aramin tv a d'an k'aramin parlour shi."
murmushi Saifudddeen yayi tare yin alamun.
"Ai zaiyi fushi kam dan zaice ban sa mishi kujeru a parlournba."
dariya Ahmad yayi tare da zaro wayarshi daketa ringing da sauri ya d'aga ganin Salisu ke kiranshi.
"Hello Salisu ya kake."

"Lfy lau Ahmad ya kasuwa?."

"Alhamdulillahi ya naka kasuwan?."

"Lfy lau wlh, ina kake ne nazo shagonku ban sameka ba."

gyara konciyarshi yayi tare da cewa.
"Muna gidan Saifuddeen d'azu nai ta kiranka baka picking call."
Numfashi Salisu ya fesar tare da cewa.
"To gani nan zuwa ku jirani."

"To sai ka zo." cewar Ahmad har zai katse kiran sai kuma yace.
"Kana inane yanzun?."

"Ina nan cikin shagonku."

"Yauwa to d'an taho mana da abin sanyi,
sannan ka d'an biya ta tashan dukku ka biya Abba bekery ka sama mana abinda zamuci dan wlh ni yunwa nakeji."

Dariya Salisu yayi sannan yace.
"To ba matsala a cici,
ci ba k'iba asaran gaya kawai."
yana fad'in haka ya katse kiran,
sannan ya juya ya kalli Mudassir dake dariya dan yana jiyo mgnar Ahmad kad'an-kad'an ,
sai ya kuma nuna Warisu da idanu yace.
"Nida Ahmad ci kamar gara, amman bama k'iba, ga oga Warisu kuwa yanata yiwa kanshi k'aidar ci amman a banza sai zuba k'iba yakeyi."
hararanshi Warisu yayi tare da cewa.
"Kada ka damu yaro nima zan sace."
dariya sukayi baki d'aya,
sannan Salisu yace.
"Yauwa ina son shinkafa buhu biyu d'anya da gumi sai buhun semo, da katon d'in spaghetti and macaroni indomi. d'ad'd'aya
Sai kuma mai manja magi sugar fulawa.
Bello ne dake tsaye ta woje yace.
"To an gama Warisu had'a mishi lissafin kud'in da zai bada."
to Warisu yace kana ya jawo Calculator dake gabanshi ya fara had'a lissafin,
yayinda tuni shi kuwa Bello ya had'a kayan duka,
sannan Warisu ya fad'i lissafin nan take ya biya kud'in sannan ya kira 'yan baro guda biyu suka kwashi kayan suka fita Salisu na biye dasu a baya.

Suna zuwa inda yayi parking motarshi ya bud'e but d'in motar kana ya loda kayan daga nan ya sallami yaran suka tafi shi kuma ya shiga mota yaja ya tafi direct Abba Bakery ya nufa ya sai musu abinda zasuci kana ya shiga cikin federal law cos,

Yana isa ya kira Ahmad yazo ya bud'e mishi gate sanan ya shiga da motar,
daga nan ya bud'e but d'in motar suka fara jidan kayayyakin sukayi ta shigarwa cikin sito d'in parlour da aka gyara.

Sosai Ahmad yaji dad'in kawaicin da Salisu yayiwa Saifuddeen,
shima kanshi Saifuddeen mutuncin Salisu ya k'aru a ida nunshi duk da bashi da matsalar kayan abinci amman yaji dad'in kyautar.

Nan sukaci suka sha sai bayan sallan la'asar suka fito,
suna fitowa gidan Alhaji Kabiru suka shiga nan sukayi sa'an samunshi a harabar gidanshi yana shirin fita,
bayan sun gaisane yacewa Saifuddeen.
"Ya kamata ka samu mai gad'in da zai zauna a gidan dan barin gidan haka ba mai gadi baiyiba."
kai Saifuddeen ya gyad'a mishi alamun za'ayi hakan.
shi kuwa Alhaji Kabiru buzayen dake zaune can harabar gidanshi ya nuna musu wani d'an ma daidaicin dottijo dake tsakaninsu kana yace.
"Ga wannan dottijon yanada kirki dama shine a gidan kauran masu gidan ne yasa nace ya dawo nan kafin a samu mai d'aukanshi aiki."
cikin gamsuwa Ahmad yace.
"To shike nan ba matsala kawai ya koma can yaci gaba da aikinshi."
cikin jin dad'in nitsuwar yaran Alhaji Kabiru yayi musu bayanin kud'in da ake biyanshi sun amince da za'a biyashi hakan,
nan take ya kwashi kayanshi ya koma gidan akan za'a rink'a bashi abinci daga gidan Alhaji Kabiru kafin su Ummi su k'auro.

Shirye-shiryen k'aurafa ya kankama Bappa Ali ya kwashi d'alibanshi sukaje sukayi kwana uku a gidan suna sauk'an karatun Qur'an da sadaka maganin masifa,
bayan sun gama suka dawo gida,
sannan Adda Rahma kuwa ta fara shirya musu waliman k'aura.
Raihana ma da Saminunta sun baro Kd zuwa gombe dan ayi k'auran a idansu,

Imran kuwa shida kanshi yaje gidajen abokanshi ya gaggayacesu suzo tarban abokinsu ba dukke,
Saifuddeen kuwa ya sanarwa abokanshi Jabeer, Hisham, Ibrahim da dai sauransu.

A dukku kuwa Aunty Nina sai kuka takeyi dan tasan zatayi kad'aici dan rabuwa da Ummi da yaranta zai shiga jikinta,
hakama goggo Dada maman Ahmad sai kukan k'auran sukeyi.

Ranar k'auransu ya kama jumma'a ,
'yan uwa da abokan arzik'i da mak'ota duk sunyiwa Ummi da ahlinta rakiya suna masu kewar rabuwa da juna.

A nan Gombe kuwa sun samu taron iyayen abokan Saifuddeen da Hayatuddeen sai Adda Rahma da mak'otanta da 'yan sirarun k'awayen da ta saba dasu. iyayen Jabeer, Hisham, Ibrahim, Sulaiman, Kakar Zakariyya, da matan Alhaji Kabiru duk sun zo,
anyi walima lfy, Ummi ta shiga ran matan dan tanada sakin fuska da mutunta mutane.

Bayan kwana ashirin da biyu da k'auransu duk bak'i sun tafi sai Ummi da yaranta da sabon gida da sabuwar Rayuwa.

Sauri-sauri Hayatuddeen ya fito daga cikin d'an k'aramin falonshi gaban Ummi ya zauna wacce Raliyya ke yanke mata farce.
fuska ya d'an tsuke tare da cewa.
"Ni wlh a matse nake a gidannan an wani lik'ani a wannan kurkukun side d'in kamar yaro,
kuma ko share min d'akinma Raliya batayi sai a barmin komai a hargitse."
tsaki Raliya taja tare da cewa.
"Ai ni ba baiwarka bace da zaka hargitsa komai kace ni in gyara maka."
harara ya watsa mata tare da cewa.
"To ni macece ni da zanyi shara?."
ita dai Ummi idanu ta zuba musu inda sabo ai ta saba da tsamar Raliya da Hayatuddeen da d'an korensu Faruq,
murmushi tayi jin Raliya na cewa.
"Eh baka iya kimtsa kanka da kayanka ba amman ka iya sabule wondo ka tsallake ka barshi a tsakiyar falo dan gaka isshashe kai kanada Raliya baiwa mai yi maka tattara."
Faruq ne ya mik'e tare da cewa.
"To ai yana jin bacci ne lokacin shiyasa."
tura baki tayi kana ta sharesu,
shi kuwa Hayatuddeen meda hankalin shi yayi kan Ummi cikin lallab'ata yace.
"Ummi kin yiwa Hamma Saifuddeen batun sauyin makarantar da zai mana ne?."
kai ta gyad'a mishi kana tace.
"Eh na gaya mishi yace zai bincika makarantar data dace daku."
ido ya kashewa Faruq sannan ya k'ara motso Ummi cikin sanyin lafazi yace.
"Ba na gaya miki cewar akwai wata sabuwar makaranta MATRIX nan bayanmu kadan a kan hanya gab da kuros mai k'ollo nan hanyar F, C, E , makarantar tanada kyau kice masa ya samu nan kinga kusa da gidane koda k'afama zamuje ko Faruq."
da sauri Faruq yace.
"Eh mana kinga kun huta bamu kud'in machine."
da sauri Raliya ta mik'e kalon tara saura kwata tayi musu tare da cewa.
"Kan bala'i wannan makarantar da sai yaran manya makarantar da sai dai d'an talaka ya gani da ido shine zakuce shi kukeson Hamma Saifuddeen ya saku ko tausayin shima ku bakwaji kaji hegun yara da girman kai da son k'arya da papa, tab lallai aiki ya sameku yaseen Ummi karki yarda zasu talauta miki d'a dan sunga yana musu duk abinda suke so."
da sauri ta kauce ganin Hayatuddeen ya kai mata duka,
d'akinta dake fuskantar d'akin Ummi ta shige da gudu tana musu dariyar mugunta.
shiko Hayatuddeen wayarshi ya zaro ya amsa kiran Imran wanda yazo dan d'aukan Hayatuddeen suje gidansu Zakariyya dan gaida kakarshi ta fad'i ta gurd'e a hannu.
bayan Imran ya shigo sun gaisa da Ummi,
sai suka sallameta suka fito.
Chapter 40 · 0% Book details