← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 116

Sashe 49

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari damisalin karfe 6:00 Am, Dr Adnan yafito daga room d'inda Saifuddeen yake,dukda sanyin asuba irinta hunturu dakuma sanyin AC dake zagaye awurin saida Dr Adnan yahad'a zufa sharkaf sabida tashin hankali da fargabar dake tare dashi,
kallo d'aya zaka yimasa kagane tsantsar tashin hankalin da ke shinfide akan fuskarsa cikin mutuwan jiki yayi isa office d'inshi,
Cikin hanzari Ummi dake zaune akan sallaya tana jan jarbi,
tamik'e tsaye tana mai zuba mishi ido tare da fad'in.
"Baban Adnan yafarka kuwa?."
saurin sai-sai ta nutsuwarsa yayi dan son boye tashin hankalin da yake ciki kana yace.
"Ehm Uhmm ba..ba..bakomai fa Ummi in sha Allah zai farka in Allah ya yarda ba wata matsala."
ita kam Ummi cikin rashin gamsuwa da maganarsa tafara magana cikin zubda kwalla tanafadin,
"Ka fad'amin halin da yake ciki in yamutune ma kada ka boye min dole inyi imani da k'addarata."
da sauri su Raliya dasuke zaune agefe suma bayan sun idar da sallah suka taso.
Hayatuddeen dayanzu dawowarsa daga masallacin dake cikin asibitin,shima ya'iso da sauri,
ganin haka yasa Dr Adnan cewa.
"Ummi baifa mutuba zo kuganshi ma."
kana ya juya yayi cikin room d'in dasauri suka rufamasa baya,can suka hangosa kwance ga na'urori sakale ajikinsa
da sauri suka nufi jikin gadon,idanunsa arufe ruf bayako motsi, abinda zainuna maka cewa yanada rai shine numfashin shi da yake ja tacikin na'uwar jan numfashi.
cikin rauni da fargaba jiki na rawa Ummi tariko hannunsa yayinda hawaye ke kwaranya a idanunta murya na rawa
tace.
"Saifuddeen wanene yayimaka wanna illa haka? waya zalincemu zalumci mafi muni arayuwar mu? memuka tare masa?."
a tare tajero tanbayar tareda kife kanta ajikin gadon ta saki sassanyan kuka.
Hayatuddeen,da shima kukan yake ganin dan'uwansa acikin mawuyacin hali,
Raliya Raihana duk kuku suke,
Dr Adnan ma shima kukan yake babu mai rarrashin wani a cikin su zuwa can Dr Adnan yashare hawayen sa cikin hanzari yamaso kusa da Ummi muryarsa narawa ya kwakulo murmushi dole yace.
"Ummi bawata masalafa ku kwantar da hankalin ku in sha Allahu zamuyi duk abinda yadace."
cikin muryar kuka Ummi tace.
"Adnan duba kaga halinda Saifuddeen yake cikifa sannan kace wai babu wata damuwa,
ka duba ka gani nice yau a gaban Saifuddeen amma yagaza d'aga ido yadubeni bare harya shiga farin ciki kamar kullum saboda ganina akusa dashi,
lallai Saifuddeen d'ina yana cikin mawuyacin hali."
sai ta kuma rik'e hannunsa tamatse acikin nata tanamai cigaba da kukan,
da sauri Dr Arabi yaturo k'ofar da sauri dan duk abinda suke yanajinsu daga cikin offece insa,ya'isa ciki tareda d'aura wata na'urar dake rike a hannunsa asaman kirjin Saifuddeen dan da alamun bugun zuciyarshi ta tsananta da sauri
yace.
"Ummi ku d'an je waje zamuyi aiki yanzu."
dakyar Ummi tasaki hannun Saifuddeen ta fita tana cigaba da sharar kwalla,
su Raliya ne sukabi bayanta.
Hayatuddeen ko wayar Saifuddeed ya d'auka wanda yagani agefensa sanna yafita, sunafita Dr Arabi yahad'a na'urar daya d'aura kan kirjin Saifuddeen,
kana ya juyo yana fuskantar Dr Adnan tare da cewa.
"Haba Dr Adnan a matsayin ka na Dr bai kamata karika kashewa majin yatanka guiwaba,
kamata yayi karika karfafa musu goiwa surika sawa aransu majinyacinsu zaisami lfy,
amma kaima kazauna agabansu kana zubda hawaye ai sai ka saka musu kokwanto azukatansu,
tabbas nasan shakuwar dake tsakanin ka da Saifuddeen,
so hakuri zakayi kabasu kwarin goiwa akan samun saukinsa sai kaga komai yatafi dai-dai."
a hankali Dr Adnan yashare hawaye kana yace.
"Hakane amman kaima kasan dai akwai babbar masala,
bazan tab'a iya mik'ewa ya tsaya da kansa ba,bazai iya morar kansa ba,
saboda illar da suka yimasa agadon bayansa zuwa kugunsa,bansan tayanda zansanarwa Ummi wanna mummunar labarin ba"
a hankali Dr Arabi yace. "Nasani,to amma ya zamuyi da ikon Allah, shi ya halicci Saifuddeen kuma ya fimu sonshi kuma insha Allah shi zai zama gatanshi,
yanzu dai ya kamata musan menene mafita."
shiru Dr Adnan yayi saboda tunanin hanyar data fi dacewa don dole a wuce da Saifuddeen Abuja.

Koda Hayatudden yafita Gefe yakoma yazaro wayarsa a'al'juhu dan tun jiya yake akashe yakunna sanna yasaka wayar Saifuddeen acikin aljuhun,
bayan yakunna wayarsa saiya lalub'o number Ishaq wato babban abokin Saifuddeen,
yana d'agawa yace.
"Hello Hatuddeen yau kuma gaisuwar sassafene za'ayiwa Hamma Ishaq."
cikin raunin murya yace.
"Ina kwana Hamma Ishaq."
da sauri yace.
"Lafiya lau, Hayatuddeen."
bayan sungaisanne Hayatuddeen yake ce masa. "Hamma ishaq muna asibiti Hamma Saifuddeen bashida lfy."
ba k'aramin tashin hankali Is'haq yashiga ba dajin cewa abokin sa na'asibiti wanda jiya da yamma suka rabu lafiya-lafiya sannan kuma yanada tabbacin cewa bakaramin ciwo bane zaisa Saifuddeen yakwanta a asibiti.
shiko Hayatuddeen katse wayar yayi yakoma inda su Ummi suke,
jugum-jugum sukayi kowa da abinda yake sakawa azuciyarsa.
sunan zaune har gari yayi haske.

Karan ababen hawane yacika cikin harabar asibitin motoci da mashunan guragu irin masu tsada da kyau wanda zasu iya kaiwa 23 kana sai wasu motoci kusan guda 6 wanda sukeda tambarin (Jonapwd) Gombe state chapter all the best! bi ma'ana tambarin k'ungiyar nakassasu ta jihar wato Joint national association of persons with disabilities.
kuma kowani mashin guda mutane biyu ne ke kansa,haka sukarika faka mashin d'in suna sauka akansa,abin mamaki mutanen duk nakasassune,
sai dai bazaka tab'a banbance makafin cikiba domin babu sanduna a hanunsu bare yan jagora kana suna cikin tsabtacecciyar shiga ta alfarma mafi akasarinsu sunfi kama da ma'aikata, kuramen ciki kuwa bazama ka tab'a zaton sunada wata nakasa a jikinsu ba, guragu kuwa sai dai ka gane da sawun wasunsu da suke a shanye wasu kuma da sanduna suke dan tokarawa gaba d'aya sun cika harabar asibitin kuma ba hayaniya bare sowa suna komansu cikin tsari da wayewa fiyema da masu ji da gani yayinda wasu ke ambaton.
"Ya Allah! kabaiwa d'an uwanmu Garkuwarmu lfy,
idan kacire manashi a cikinmu bamu san ya zamu k'are da rayuwaba dan munsan cewa zamu tagayyara mudawo abin kyama abin gudu acikin al'umma sunai mana kallon wasu hallitu na daban." makafin cikinsu nata fad'in. "ku kaimu inda yake?."

Mutane sukarika fitowa daga cikin asibitin, wad'anda suke gefe da asibitin wato mazauna gefen asibitin suma suka shisshigo,danganin taron mutanen dasuka shigo cikin asibitin.
Dan ganin abinda kefaruwa,jama'ar dasuka fito dan kallon mutanen sunsha mamakin jin kallama da ya kefita abakin wadanna nakasassun,sai ambaton Saifuddeen suke,
jama'a duk suka cika da alhinin jin sunan wanna bawan Allahn dasuke ammaba,to waye shi dahar wadanna mutanen zasu nuna damuwarsu da tashin hankalinsu akansa,lallai wanna mutumin komai akayi adaline,sosai a garesu domin wasuma sunyi zaton ko zanga-zangar lumana nakasassun keyi,
gurin ya kacame da hayaniyar mutane dake tambayar meke faruwa.
Hayatuddeen ne yamik'e tsaye da sauri yace.
"Ummi mutanen Hamma Saifuddeen ne sukazo dan naji sunata kiran sunansa bari naje wurinsu."
kai kawai Ummi ta'iya gyad'a masa alamar toh.

Hayatuddeen yafito farbajiyar asubitin suna ganinsa suka nufi inda yake suka zagayeshi,suna fadin.
"Ina Saifuddeenin d'inmu yake kanunama inda yake."
hannu sa yad'aga sama yana juyashi, tare da yin sauri ya isa gaban Ishaq cikin girmamawa yace.
"Ya ishaq barka da zuwa."
da sauri ishaq ya mik'o hannu ganin haka shima Hayatuddeen ya mik'o mishi hannu tare da cewa.
"Gani nan Ya ishaq."
da sauri ishaq yace.
"Yauwa Hayatuddeen ta ina Saifuddeen yake muje mu ganshi."
cikin d'an murmushi Hayatuddeen yace.
"Hmmm kai ishaq kullum lamarinka akwai k'arfin hali da iya ruggumar k'addara wai muje mu ganshi sai kace kana gani."
shima Ishaq murmushi k'arfin hali yayi tare da cewa.
"ai ba idone gani ba, ku masu idone kuke d'auka da ido kawai ake gani, mu kunnuwanmu ma tamkar idone kana da zuciyarmu da k'ok'wolwarmu, yayinda kuramenmu kuma idanunsu ne kunnuwansu, ba gashi yanzu koda bana ganinka nasan kana zubda hawaye daga sautin muryarka."
cikin sanyi Hayatuddeen yace.
"Ku kwantar hankalinku,
ku dakata dan Allah kuyi hakuri yanzu bazaku sami ganin saba dan yasamu yin bacci saidai zuwa anjima."
cikin gamsuwa sukace.
"To yajikin nasa?."
saida ya maida hawayensa dake kukarin zubo masa dagudun kada hankulansu yatashi,danyasan cewa basu kadai ahalinsa kebukatar Hamma Saifuddeen ba, hardasu wadanna nakasassun,dama wasunsu baki d'aya,.
"Da sauki". yace dasu atakaice,
dakyar shugabannin nasu suka samu suka lallab'asu sukatafi,sanna shikuma Hayatuddeen yayiwa su ishaq d'in iso zuwa ciki inda su Ummi suke.

Suna shiga Dr Adnan nafitowa,
kana Dr Arabi nabiye dashi su Ummi naganinsu sukamike tsaye suka k'araso inda suke,Ummi kallonsu take fuska kunshe da tanbayoyi
Dr Arabi yakalli Dr Adnan wanda keta noke-noke yayi masa alama da ido,
jiki asanyaye Dr Adnan ya mik'awa Ummi wata doguwa takarda fara yace.
"Ummi wanna takardar ta transfer ce zuwa Abuja,
naturaku asibitin kimiya dake birnin tarayya Abuja National hospital Abuja
,idan kun isa saikiba su wanna takardar
da sauri Ummi tace.
"Abuja! Kuma?."
kai ya gyad'a mata alamar eh,
a hankali tace.
"Lallai ciwon Saifuddeen babbane tunda har katuramu Abuja."
Kai Adnan ya girgiza dasauri,dan bazai iya fad'a mata akwai masala ba, yafiso sai sunje can d'in asanar musu.
tana karbar takardar yayi saurin juyawa dasauri dan gudun kada Ummi takuma jefo masa wat tanbayar,
yanafita yayi duk wani cuku-cukun dayadace natafiyarsu ba tareda bata lokaciba yakammala komai bank'arensu.
Ishaq kuwa takardar ya amsa kana suka juya tare da Raihana, kai tsaye Federal low cos suka nufa,
E passport d'in Ummi da Saifuddeen dana Hayatuddden yasa Raihana ta kawo mishi,
daga nan direban k'ungiyar tasu yaja suka wuce Airport, nan ya gama musu dukkan shirin tafiya hardashi d'in suka kuma yi sa'a akwai jirgin da zai tashi zuwa Abuja k'arfe biyun rana zai tashi.
Chapter 49 · 0% Book details