Sashe 75
Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
***
A Nigeria kuwa Yanzu Adda Rahama ta shiga watan haihuwanta, yanzu ma zaune take akan kujera yayinda ƙaton cikinta ya cika mata gaba, aje kofin tea ɗin dake hannunta tayi tare da kai dubanta ga Dr Adnan wanda ke gefenta yana me aiki a laptop ɗinsa, cikin kwantar da murya tace.
"Dan Allah Ya Adnan yaushe ne zanje naga Saifuddeen? koda yaushe idan nayi maka magana sai kace nayi haƙuri ba yanzu ba!".
taƙare maganar tana me langwaɓar da kanta gefe. Murmushi Dr Adnan yayi tare da dubanta cikin son kwantar mata da hankali yace.
"Kiyi haƙuri ba na hanaki zuwa bane, kinsan dai halin da kike ciki yanzuma haka kinsan kinshiga watan haihuwan ki haihuwa yau ko gobe, kiyi haƙuri idan kin haihu zamuje tare dukanmu!".
Sake shagwaɓe fuska tayi tare da cewa.
"Shikenan ai dai kullum haka kake cewa, Allah yasa na haihu lafiya ko sati bazan ƙara ba zanje na gansa!".
Dariya me kama da murmushi Dr Adnan yayi tare da kama hannunta ya shiga murzawa, cike da ƙaunar matar tashi yace.
"Karki damu zamuje ki ga ɗan ƙaninki".
Murmushi tayi tare da ɗaukan cup ɗin tea ɗinta tacigaba da sha kaɗan kaɗan.
Koda dare ya d'anyi nisa misalin ƙarfe 9 naƙuda ta tasowa Adda Rahama gadan gadan wanda har saida yakaisu ga zuwa asibiti, ƙarfe 10 dai-dai ta haifo kyakkyawan ɗanta na miji,me kama da ita sak, farin ciki awajen Dr Adnan ba a magana, nantake yashiga ƙiran mutane yana sanar musu, koda ya sanarwa mahaifiyarsa baƙaramin murna tayi ba, nan ya bugawa mutanen India yasanar dasu, daɗin dasu Ummi sukaji baya faɗuwa nan yabata waya suka gaisa, inda Saifuddeen kuwa ya ɗauki wayarsa ya tura mata saƙon murnar haihuwar da tayi lafiya tare dayin kyakkyawan addu'a ga yaron data haifa, koda takaranta saƙon sosai taji daɗi inda ta mayar masa da amsa tare da tambayar jikinsa.
Alhamdulillah kulawa ta musamman Adda Rahama ke samu daga wajen mijinta da mahaifiyarshi Dr Adnan inda yaɗau soyayya da tarairaya ya ɗaura ga yaronsu da suka haifa.
Ranan da ta cika kwana huɗu da haihuwa Raihana tazo daga Kaduna, sosai taji son yaron yana ratsata kyawun yaron ba, don idan ma idanunta ba ƙarya sukai mata ba har kamannin Hamma Saifuddeen ɗinsu ta hango akan fuskar yaron.
Ranan da tacika kwana 7 da haihuwa arananne aka sha shagalin suna wanda yasamu halartar ƴan uwa da abokan arziki, inda yaro yaci sunan SAIFUDDEEN. sosai bikin sunan ya ƙawatar don kuwa Dr Adnan ya buɗe bakin al'jihunsa inda ya gwadawa mai jego da ɗanta gata, anyi taron suna an watse lafiya sai- dai muce masha Allah, koda su Ummi sukaji sunan yaron Saifuddeen baƙaramin murna sukayi ba musamman Ummin nan tace ake kiranshi da Deen.
India.
Yau su Ummi suka cika sati a India kuma yau ne suketa shirye shiryen dawowa Nigeria, sosai kuma suka aminta da sauƙin da Saifuddeen ke samu don ayanzu su kansu sun samu nutsuwa a zuciyoyinsu, tsab suka gama shirya kayansu, inda suka wuce asibiti don yiwa Saifuddeen ban kwana, sam Saifuddeen baiso tafiyansu ba saboda zuwansu sosai ya ɗebe masa kewa musamman daya kasance kullum suna tare da abokinsa Ishaq, haka su Ummi sukayiwa Saifuddeen sallama bayan Ishaq ya basa maƙudan kuɗaɗen da Ƙungiyansu ta *Joint National Association Of Persons With Desabilities. (Jonapwd) Gombe state chapter. All the best!👍🏻* suka bada abasa kamar yanda suke bawa kowani member ɗinsu wanda ke cikin hali na rashin lafiya, sam Saifuddeen ƙin karɓa yayi shikuwa Ishaq rufe idanunsa yayi ya dage dole saida Saifuddeen ya amsa bisa sanya bakin Ummi.
Hayatuddeen ne ya rakasu airport inda suka hau jirgi daganan sai Nigeria.
Koda suka dawo agidan Adda Rahama suka sauƙa inda suka duba yaro, daganan Ummi ta wuce gidanta Ummun Ishaq ma ta wuce nata gidan...
Yau Jummu'a ta kasance ranar da Zaleeha ke gabatar da program nata mai taken babu nakasasshe sai rago.
Bayan ta gama gabatar da shirin natane ta shigo wurin masauk'i bakisu,
a hankali ta zauna akan wata baƙar kujera dake cikin office ɗinsu wanda ke cikin gidan radion vission FM.
Sanye take da wata haɗaɗɗiyar doguwar rige me walwali yayinda tayi rollin kanta da mayafin rigar, sosai rigan ta bayyana tsananin kyawunta, wayarta ƙiran iphone 11 pro max ne riƙe ahannunta tana latsawa. Manager da shigowarsa offie ɗin kenan cak ya tsaya yana kallonta, sosai take burgesa komai nata abun so ne ga ɗa Namiji, haƙiƙa yasan Zaleeha dabance acikin mata.
Ahankali yatako zuwa inda take, Zaleeha da hankalinta gaba ɗaya ke kan wayarta ta ɗan ɗago kanta tare da dubansa, ganin Manager da kansa acikin office ɗin nasu yasanya ta sakin murmushin da ya sake bayyana kyawun fuskarta, cikin zazzaƙar muryarta tace.
"Barka da shigowa Manager!"
Murmushi Manager yayi tare da ɗan lumshe idanunsa, dan sosai yakejin wani abu na musamman a dangane da ita.
"Barkanki dai Sarauniya" Manager yafaɗa yana murmushi.
Aɗan mamakance ta kalleshi jin yaƙirata da sunan sarauniya.
"Sarauniya kuma manager?" tafaɗa tana me ƙoƙarin rataya hand bag ɗinta don dama lokacin tashinta yayi.
"Kin ma wuce haka Zaleeha, ke tamkar zara kike acikin dubbanin taurari! ko ince zinariya"
Yanzu kam sosai maganganun Manager ɗin yabata mamaki don baitaɓa mata irin waƴannan maganganun ba.
Murmushi kawai tayi tare da dubansa kamar zatace wani abu sai kuma taɗan raɓa ta gefensa zata wuce. Da sauri yaƙira sunanta, inda yace.
"Zaleeha!"
Jin yaƙira sunanta yasanya taɗan tsaya tare da juyowa ta fuskance sa.
Gyara tsayuwa yayi tare da zura hannayensa cikin al'jihun wandonsa cikin tausasa murya yace.
"Zaliha Ina sonki! Inada buri da fatan ki zamo matata uwar yarana na".
idanunta ta zazzaro da sauri sai kuma ta fara jan baya-baya ganin yana takowa zuwa gabanta,
da sauri ta rumtse idanunta ganin ogan nata kuma babban mutun ya durk'usa gabanta da guiwowinshi duka biyu,
hankalin ta ya kuma tashi jin yana cewa.
"Na dad'e ina adana soyayyarki a zuciya ta, ina sonki irin so mai kauda nitsuwar mutun, kece fatana ki zame min matata ta biyu, shine cikar burina.
Ina matuk'ar jin tsoro da fargabar kada na rasaki."
Wani azabebben ajiyan zuciya Zaheela taje tare da yin mgnar zuciya.
"Meyasa? Meyasa ne? mutane sukayi mata caaa a kanta, meyasa tun da can basu baiyana kansu gareta ba sai yanzu da Allah ya jarab ceta da son wanin namijin.
ido ta rumtse tare da bud'esu sannan tayi k'asa dai-dai gaban manager d'insu ta durkusa kamar yadda yayi cikin son yakice soyayyarta a zuciyarshi murya na rawa tace.
"Kai matsayin yayane a gareni, koda zan boyewa kowa kai dai bazan boye maka ba Ya Abubakar.
Zuciyata ta cika ta batse tana zubda tururin zazzafar soyayyar da nake mishi, ina gab da rasa lfyar zuciyata muddin ban sameshi ba, ya shigemin zuciya a lokacin da ni kaina ban Sabina, shine fatana, bani da mosoyi samadashi shine kad'ai mahaluk'in da zan iya mallakawa kaina,
shine abinda zuciyata keso. Tabbas da ka gabatarmin da kanka kafin had'uwata da shi to da na aminta da kai."
Idanu ya zuba mata yayinda yake gano wutar so da gskyar mgnarta cikin kwayar idanunta,
cikin tsananin kad'uwa yace.
"Waye ne shi?."
cikin zubda hawaye tace.
"Oho shine abinda nima nake son in sani."
ido ya firfitar cikin azama yace.
"Baki sanshi bane?."
Kai ta gyad'a mishi tare da yunk'urawa ta fita da sassarfa dan kukan dake taho mata.
wani mayataccen murmushi yayi tare da cewa.
"Wannan ai shirmenki ne, dama kin sanshi ya sankine dole in hak'ura amman yanzu dole in nace."
Ita kuwa tana fita ta nufi parking lot nasu,
tana isa wurin tayi kicibus da Abokin aikinta Raveel, ganin yadda take saurine yasashi saurin sa hannunshi ya kamo nata cikin tsareta da ido yace.
"A haka zakiyi draving so kike ki kashe kanki ni ki illatamin rayuwa ne?."
fuzge hannunta tayi tare da cewa.
"Ka sake min hannu."
cikin tsawa yace.
"Ank'i a sake d'in, ni da kika rik'e min zuciyata bance ki sakemin itaba sai ke dana rik'ewa hannu.
Na gaji da ganinki cikin damuwa, yanzu tsawon wata hud'u kenan na fahimci kina cikin matsala ki gaya min make damunki? meke faruwa da rayuwarki?."
tattaro sauran k'arfinta tayi ta fizge hannunta tare da wucewa ta shiga motarta ta figi motar da gudu ta nufi gidansu Bilku k'awarta da tasan sirrin soyayyar da take boyewa a ranta.