← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 116

Sashe 16

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan an gama warewa Baba Bello adadin da yake amsa kullum,
sai aka rubuta sunan Saifuddeen dasa hannun shi dana baba Bello kana akasa kud'in kayan da akabashi ganin yawan kayanne da yawan kud'in yasa Saifuddeen yiwa Dottijon alamun.
"Kayan basuyi yawaba kuwa?."
Murmushi Baba Bello yayi kana ya fara loda ledodin a k'aton kwalin dake bayan kekenshi,
saida ya loda kusan rabin ledodin kana ya hau kekenshi sannan ya kalli Saifuddeen cikin yin kasa da murya yace.
"Kada Ka damu ai zan had'aka da customers d'ina duka,
kaga duka-duka kayan dubu hamsin nake amsa dama,
nakan sa na ishirin da biyar,
in fita inje in rarraba in ya k'are inzo in kuma kwasar rabin.
Yanzu muje duk zamu rabashi sai mu dawo mu debi sauran."
cikin gamsuwa ya gyad'a kai kana yabi bayanshi.
tafiya kad'an suka isa shagon wani mai saida takalma bayan sun gaisa Dottijon nan ya d'ebo banduran leda takwai,
ya bawa Saifuddeen kana ya juyo ya kalli mai shagon tare da cewa.
"Alhaji bala ga Jikana ya fara kawo muku daga yau,
insha Allah kullum zaike kawo muku kamar yadda nakeyi daku sai in Allah ya kaimu bayan salla."
wanda aka kira da alhaji bala kuwa cikin kula ya irgo dubu 4 ya bawa Dottijon kana yace.
"To baba Bello Allah ya kaimu bayan sallan, Allah ya sadamu da al'khairi."
Amin Amin, yace kana suka shige shago na gaba nanma ya basu kaya suka bashi kud'i.
haka dai sukayi tayi har suka gama wanda suka kwason kana suka koma suka kwaso sauran kashi d'ayan.
Kai tsaye shagonsu Jabeer sukaje inda sukace a basu na dubu 5, nanfa Saifuddeen ya basu suka bashi kudin na jiya ya bawa baba bello,
Jabeer nata musu tsiya wai.
"Tab ku dai kam kun more dan ko bamu sayarba ku dai kun sayar."
dariya sukayi kana sukaci gaba dan inda sabo sun saba da shek'iyancin Jabeer.
daga nan suka zagaya har layin masu kayan kitchen nanma shagonsu Hisham suka saya,
sai kuma suka mik'e babban layi har kan shagunan ba miskila,
cikin sa'a suka sameshi shida kanshi bayan baba bello ya mishi bayanin Saifuddeen ya gamsu kana yace.
"To Baba Bello Allah ya taimaka mana,
yanzu ni daga gobe ya rink'a kawo min na 15k dan shaguna na babbar kasuwama za'a rink'a kai musu da na kasuwar mata da shagunan cikin unguwanni dan naku ledodinku suna da kyau, muna jin dad'insu."
shiko Saifuddeen murmushi yakeyi yana ganin darajar mutumin sabida duk inda yaranshi sukayi awu sai ya amshi kwanon awun ya kamfata ya zuba a ledan wanda aka gamawa awun,
yara sai godiya sukeyi.
daga nan suka ci gaba da rabawa har layin masu kayan kolliya.
Wasu na 5k wasu 4k wasu 3k wasuma na 1k wasu ma na 500 yayinda wasu 6k ko 7k kowa dai dai-dai cinikaiyarshi yake karb'a
Koda suka gama sai suka tafi can dilan nasu,
a hankali baba Bello yaja hannunshi suka d'an koma gefe,
kana ya fito da kudin da suka tattaro ya had'a kansu,
sannan ya irga inda ya samu kud'in dubu hamsin da shida ne da d'ari uku.
Gyara zama yayi kana ya ware dubu hamtsin sannan ya kira d'aya daga cikin yaran shagon ya bashi kudin ya irga,
sannan ya d'auko wani babban littafi yaja gud a kan sunan baba bellon tare da rubuta bama binshi ko asi,
sai bayan salla in ya dawo.
Sai kuma yasa sunan Saifuddeen k'asan na Baba bello tare da rubuta .
"Munada kayan dubu hamsin a wurinshi."
sai ya kuma basu littafin sukasa hannu shima yasa hannu daga nan ya koma bakin aikinshi.
Su kuwa su Saifuddeen cikin nitsuwa Baba bello ya kalleshi tare da bashi 2k sannan yace.
"Kaga wannan ribanane na jiya,
ladan yawon da nasha yi cikin rana,
kuma kaima zaka iya samun haka a kullum koma fiye da hakan cikin duk kayan dubu goma ina samun ribar dubu d'aya da dari biyu,
wani lokacin in naga kasuwa bata gudu duk bandir din dubu goma sai inbi dubu d'aya rak kaga kenan duk fakitin dubu d'aya ina bin nera d'ari d'aya kacal ne,
kuma Alhamdulillahi a cinikin da nikeyi dubu hamsin kullum ina samun dubu shida ko biyar in na rage farashi na,
ta iya yiwuwa kai ka samu fiye da haka tunda kai yanzu ana hidiman cinikaiyan salla,
dole masu shaguna suna k'ara sayan leda,
kaga misali yanzu ba mishkila daga sayan na dubu 5 yanzu yace gobe na dubu 15 zaka kai mishi,
kaga Alhamdulillahi kasuwa ta fara a sa'a, dan haka kai gobe kayan dubu 60 zaka amsa,
yanzu zan gayawa shi Alhajin in dai ka buk'aci k'ari to ayi maka."
cikin jin dad'i da tsananin mamaki Saifuddeen yake kallonshi domin jin k'udurar ubangiji.
Mutun nawa ke raina kasuwar leda rashin sanin al'barkan dake cikinta ne yasa haka da yawa raina riba ke wahal da matasanmu da ganin sunfi k'arfin sana'a kaza sai kaza ko a a su sunyi karatu sunfii k'arfin talla a kasuwa sai zaman office.
cikin kurmanci yayiwa baba bello godiya tare fatan al'khairi.
Shi kuwa Baba bello 2k d'in ya kuma bashi tare da cewa.
"Amshi wannan ka sayawa Mamanka sugar ka kai mata taci al'barkacin sana'ata."
Da sauri ya girgiza kanshi alamun a a bazai amsaba ai ya gama mishi komai ma daya bashi aron sana'arshi ba tare daya mishi hasadan abinda zai samuba.
Shiko Dottijon cikin girma da isa yace.
"Bana son musu a tsakaninmu da mahaifinka ne ya baka zaka k'i amsane?
niko da ace Allah yasa inada d'a da na bashi ai bazaik'i amsaba sai daima yace in k'ara mishi dan haka maza karb'i kud'innan."
cikin tsananin ganin darajar Dottijon yasa hannu ya amshi 2k d'in kana ya mishi godiya.
Shi kuwa Baba bello,
ubangidan nasu yayiwa bayanin kan ba mmki Saifuddeen ya nemi k'arin leda.
cikin mutuntaka ogan nasu yace.
"Ba matsala aimu haka mukeso."
daga nan ya sallamesu, kana ya yafito Saifuddeen sannan ya hau kekenshi,
yana janta a hankali kana Saifuddeen na binshi a baya har sukaje bakin titi,
cikin kula ya bawa Saifuddeen hannu da sauri Saifuddeen ya bashi nashi hannun sai kuma ya zuba mishi ido jin ya rik'e mishi hannun cikin bada shawara yace.
"Ita sana'a bata yiwa mutun yawa,
kaga shi leda cikin awa uku duk zaka gama kaiwa kostomominka ka kuma tattara kud'i har ka biya kana ka zare ribarka.
To in dai ka gama da wuri to zakafa iya saida ruwanka d'in in kaga alamun zai saidu,
in kuma Kaga bazai saiduba tofa kada ka zauna banza ka samu sana'ar da zaka had'a dana ledan kafin bayan sallan ka komawa ruwan."
Cikin gamsuwa ya jinjina kai alamun in sha Allah hakan zaiyi.
shi kuwa Dottijon ya jima yana mishi nasiha da rik'o da amana da tattali,
sannan daga bisani sukayi sallama shi dottijon ya kama hanyar gidanshi kana shi kuma Saifuddeen ya koma cikin kasuwa ya d'auki bitikinshi ya kuma saran ruwa.
Koda Jabeer ya ganshi yai ta mishi tsiya wai shine sana'a goma mgnin baccin safe.

Haka dai ranarma ya wuni saida kayan sanyinshi,
saida akayi sallan isha suka kama hanyar dukku wanda tuni anga wotan Ramadan,
gaba d'aya al'ummar annabi gobe za'a tashi da azumi.

Kamar yadda ko wanne gida ke shirin d'aukan azumi hakama gidansu Saifuddeen domin.
bayan yayi wonkane yaje ya samu Umminshi da Adda Rahma da Raihana,
nan ya gayawa Umminshi lamarin kasuwar sai dai bai gaya mata ribar da Dottijon nan ya gwada mishiba don baison ya fad'ad'a burinshi kan ribar gudun kada ya shigar da son zuciya.
Rahma ya kalla wacce ta kawo mishi abinci cikin sanyi tace.
"Yauwa Saifuddeen wannan k'awar Raliyya Salma sun zo d'azu tace wai in gaisheka in ka dawo."
ta k'arishe mgnar tana murmushi da son ganin fuskarshi dan tasan sam Saifuddeen baya shiri da Salma
Shi kuwa yi yayi kamar bai gantaba bare ya gane me take fad'i dama in baya son mgna da mutun haka yakeyi.
Ummi kuwa ido ta zuba musu tana murmushi,
abincin ya d'an tsakura kasancewar shi baida yawan cin abinci.
saida ya d'an gyara zamanshi kana ya kalli Hayatuddeen dake gefenshi tare da mishi tambayar azumi nawa zaiyi?."
cikin d'oki yace.
"30 zanyi ko d'aya bazan shaba."
dariya Ummi tayi jin Raliyya na cewa.
"Ko kuma ko d'aya bazakayi ba ko?."
cikin dariya Rahma tace.
"Ai kam saidai hakan."
shi kuwa Saifuddeen hannun Faruq yaja tare da cemishi shi kuwa nawa zaiyi.
yatsunshi uku na tsakiya ya d'aga alamun zaiyi uku da yake duk sun iya kurmanci.
Raihana kuma tana tsakiyar gida tanata kiciniyar tafasa tea da yin miyar asuba,
miyar dege-dege take musu dan Ummi dubu d'aya ta bada Hayatuddeen ya sayo musu hanta da jan nama,
tofa shine aka gyarashi tayi miyar ganyen albasa da yaji kayan miya dana d'an-d'an dan aji dad'in yin sahur.
koda ta gama tafasa tea d'in da tasa citta da kanumfari,
sai ta d'ura a filas kana miyar kuma ta barshi a tukunyar sai ta dorashi saman kanta sannan taja kitchen d'in ta rufe sai da asuban Rahma zata k'arisa aikin.
tana rufe kitchen d'in taje sukaci gaba da hira,
nan Saifuddeen ya bawa Ummi shawarar a hana Aunty Nina girki dan tana laulayin wani cikin,
to shiyasa yake son a hanata girki su had'a tukunyar,
sosai Ummi taji dad'in haka dan itama taso hakan sabida tasan Bappa Ali mutum ne mai kawaici tana sane cutar mijintane ya medasu basu da wasu yawan kadarori.
koda Saifuddeen ya tashi daga nan k'ofan Bappa Alin ya nufa inda ya samu Aunty Nina tana kiciniyar hura wuta a murhun gawayi yayinda shi kuma bappa Ali,
yake ruggume da Qur'an alamun zai fita masallaci.
nan ya gaya mishi shawarar da suka yanke shida Umminshi.
bawan Allah Bappa Ali sai yake jin kunyar wai shi ya kamata yaci dasu ya gaza sai kuma shima su ciyar dashi,
da fari kamar bazai yardaba to dole dai ya yarda dan Saifuddeen ya kafa ya tsare haka ya hak'uri,
sannan suka kama zance tafsir d'in da zasu fara gobe ya jaddawa Saifuddeen ya shirya dashi za'ake zuwa bayan sun gama mgnane ya fita wurin abokanshi.
Chapter 16 · 0% Book details