Sashe 88
Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Harta kusa kai bakin motarta da sauri yasha gabanta, cikin yanayi naɗan mamaki taja baya, tana me ƙare masa kallo, murmushine ɗauke akan fuskar saurayin me suna Saleem, cikin da-ida-ita nutsuwarsa yace.
"Amincin Allah ya tabbata agareki yake wannan ma'abocian kyakkyawar halitta"
Idanunta taɗan juya tare da kafesa da ido.
Ɗan lumshe idanunsa yayi ganin yanda kwawawan idanunta ke yawo ajikinsa, cikin nutsuwa yace.
"Saleem Sa'ad Turaki,
fatan banyi laifiba dana tsaida ki, naga kamar sauri kike".
Baki ta taɓe tare da buɗe murfin motarta ta shige, ƙoƙarin rufe murfin motar take, Saleem yayi saurin riƙewa, cikin sanya fuskar tausayi yace.
"Nasan dacewa shawo kan kyakkyawar mace sarauniyar mata kamarki abune mai matuƙar wahala, amma please ko phone number ɗin kine ki bani hakan zai taimakamin sosai"
Hannunta tasanya taɗan dafe goshinta, cike da ƙosawa ta ɗago ta dubesa, shiɗinma kallonta yake wani murmushin k'eta tayi tare da bashi number Raveel kana ta gaya mishi sunanta,
murfin motarta ta rufe tare da data motar tatafi tabarshi tsaye awajen, murmushi ɗauke akan fuskarsa yabi motarta da kallo, harta ɓacewa ganinsa, cike da fatan sake ganinta anan gaba ya juya yakoma cikin havilla. Itakuwa Zaleeha tana tuƙi tanashan ice cream ɗinta, hakan kuwa sosai ya haifar mata da nutsuwa.
Ransa fari ƙal fuskarsa ɗauke da farin ciki yake sarrafa keken nasa har yakawo cikin falon, Ummi da Hayatuddeen ne zaune, carbi ne riƙe ahannun Ummi yayinda Hayatuddeen kuma ke zaune akan sofa, yana riƙe da plate ɗin dambun nama ahannunsa, ahankali ya turo keken nasa zuwa gaban Ummi dake zaune akan kujera, wanda ganinsa da tayi yasanyata sakin murmushi, ƙarasowa gab da ita yayi tare da ɗaura kansa akan kafaɗanta, cikin tsananin ƙaunar da takeyi masa tasanya hannu ta shafa lallausan gashin kansa tare da cewa.
"Da'alama wannan fitar taka al'khairi zata haifar mana don naga kafita cikin farin ciki, ka kuma dawo cikin farin ciki". Murmushine ya faɗaɗa akan fuskarsa tare da sake gyara zaman kansa dake kafaɗanta, shikaɗai yasan irin farin cikin da yake ciki ayau ɗin.
Hayatuddeen dake ta faman cin dambunsa yana jijjiga kai alaman daɗin dambun na ratsashi, dubansa ya kai ga Hammannsa cikin santin dambun nasa yace "Hamma nine fa auta kowa ya sani".
Hararansa Saifuddeen yayi cikin body language yayi masa alama da cewa.
"Idan kaine auta saime, shikenan sai kada Ummina tanuna min ƙauna?"
Dariya Hayatuddeen yayi tare da cewa.
"Ai dai ƙaunar dake tsakanina da Ummi na ta musammance, naɗan baka aronta ne naƴan wasu kwanaki"
Murmushi Ummi dake jinsu tayi, shiɗin ma Saifuddeen murmushi kawai yayi don ya fuskanci cewa dambun naman da Hayatuddeen ɗin ke cine yasasa santi. Dubansa Ummi tayi cike da kulawa tace.
"Akawoma abinci ne?".
Cikin body language ɗinsa yayi mata alama da bayanzu ba, ahankali ya tura kekensa inda ya nufi ɗakinsa don so yake yayi wanka kana yaɗan huta,
Shida kansa ya haɗawa kansa ruwan wanka acikin bathtube, inda yacika turaren wanka me daɗin ƙamshi aciki, kwanciya yayi luf acikin bathtube ɗin tare da lumshe idanunsa, ba'a iya jikinsa kaɗai yakejin sanyin ruwan ba har acikin zuciyarsa, wani irin ƙawataccen murmushine ya bayyana akan fuskarsa sakamakon tunowa da irin yanda take murguɗa masa baki dayayi, tausasan lips ɗinsa yaɗan ciza tare da sanya hannunsa ya riƙe dai- dai saitin heart ɗinsa, wani irin tarin soyayyarta ne yasake ɗarsuwa acikin ransa, sake gyara kwanciyarsa acikin bathtube ɗin yayi tare da sakin wani sabon murmushi, sannu ahankali yakejin sabon so da ƙaunarta na huda gaba ɗaya jijiyoyin dake jikinsa, aƙalla ya ɗauki kusan sama da 30 minute yana tunaninta yayinda wata irin ƙaƙƙarfan begenta ke neman zautar dashi, adaddafe haka yayi wanka, koda yafito daga cikin toilet ɗin wata brown ɗin jallabiya me kyau yasanya ajikinsa inda ya feshe jikinsa da daddaɗan turarensa mai sanya nutsuwa,
kwanciya yayi luf akan gadonsa tare da jawo laptop ɗinsa, ya kunna, kyakkyawan hoton fuskarsa ne ya bayyana akan screen na laptop ɗin, cikin nutsuwa yake danna laptop ɗin inda ya kasa aiwatar da komai gaba ɗaya tunanin kyakkyawar fuskarta da zazzaƙan muryarta ya hana masa sukuni.
ya dade haka daga bisani ya turawa Ahmad text.
"Na samu matar aurefa yaro ka shirya shan biki."
Ahmad dake kwance bisa gado, yayi.da Raliya ke baccin gajiya a kan k'irjinshi.
dariya yayi tare rubuta mishi
"Eye-eye kace ka kusa shiga dausayin jin dad'in duniya yaro."
Tsaki ya tura mishi tare tura mishi nifa surkinka ne.
daga bisa ni dai yayiwa Ahmad d'an bayani,
sosai Ahmad yaji dad'i.
Washegari, yau tunsafe yatashi da wani irin ƙwarin guiwa nason mallakarta, wayarsa ya ɗauka ya turawa Ishaq text message inda yace shirya zuwa ƙarfe d'aya na gobe zai rakasa Dukku, koda Ishaq yaga saƙon abokin nasa murmushi kawai yayi don yasan kwanan zancen har acikin ransa kuma yaji daɗin hakan.
Zaune suke su dukansu akan dinning table suna break fast, surutun Hayatuddeen da Raliya ne ke tashi inda suke ta musu, Ummi dai jinsu kawai take yayinda Saifuddeen ya zaro wayarsa dake cikin aljihunsa, saƙon tafiyarsa Dukku ya rubuta kana ya miƙawa Ummi, amsan wayan Ummi tayi tare da karanta saƙon, ajiyar zuciya ta sauƙe tare da duban Saifuddeen ɗin da kyau, tabbas taji daɗin cewa da yayi zaije dukku'n saboda hakanma wani ƙarin karsashi ne dake nuna samun lafiyarsa, saidai kuma tayi mamaki don yau kwata kwata-kwata kwana biyar ne da dawowarsa Nigeria, sanin da tayi cewa koma mene zaije yi a Dukku'n tana da yaƙinin cewa al'khairi ne hakan yasa, tayi masa fatan zuwa lafiya da kuma dawowa lafiya, Hayatuddeen ne ya dubi hamman nasa jin Ummi nayi masa fatan alkhairi yace "Hamma tafiya zakayine?"
Kai Saifuddeen ya jinjina masa alamar eh tare dayi masa alaman.
"Ko zaka rakani?"
Baki Hayatuddeen ya washe tare da kaɗa kansa cikin sauri yace.
"Ƙafata ƙafarka ae Hammana!"
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"To ɗan sarkin son yawo tunda dai kanason yawo ae sai kabisa Dukku zashi".
Take Hayatuddeen ya kwaɓe fuska tare da girgiza kansa cikin halinsa na shagwaɓa yace.
"Dukku kuma? chab wallahi na haƙura dama wasa nake ba binsa zanyi ba".
Gaba ɗayansu suka sanya dariya don dama sunsan rashin sanin inda Saifuddeen ɗin yace zaije shiyasa cikin karaɗi yace zai bisa, suna kammala cin abincin, Saifuddeen ya wuce ɗakinsa, wanka ya ƙarayi inda ya shirya kansa cikin wata tsadaddiyar shadda Milk colour ɗinkin half jumper wanda taji coffee colour'n aiki a wuyanta, sosai shaddan ta sake fidda sihirtaccen kyaunsa, wata haɗaɗɗiyar hulan zanna bukar ya kafa akansa wanda gaba ɗayanta kalar coffee gareta saidai tana da ratsin milk colour ajikinta, hatta takalman dake ƙafansa kalan coffee garesu, inda farar fatarsa tafito tayi ɗas acikinsu, tsadadden agogo ya ɗaura ahannunsa inda ya feshe gaba ɗaya jikinsa da turare, masha Allah Saifuddeen baƙaramin kyau yayi ba, sai ayanzune ma nake lura da cewa ba kayanne sukeyi masa kyau ba shine keyiwa kayan kyau, don kuwa kowani irin kaya yasaka sai yayi musu kyau, haƙiƙa Allah mabuwayine ayayin daya tauye Saifuddeen da tawaya irin ta rashin jin magana da takawa da k'afaffunshi sai ya basa wani irin ɗanɗareren kyau haɗi da kwarjini yakuma sa ya zamto abunso azuƙatan mafi yawancin mutane, haƙiƙa kyawun Saifuddeen madubi ne wanda ko wacce cikakkiyar ƴa mace zataso fuskanta don ganin kanta acikin sa.