← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 116

Sashe 61

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Malam Bashir Suleiman Dukku asalin haifeffen garin Dukku ne gaba da baya,
Malami ne wanda yakeda cikar haiba da kamala,
Su uku ne a wurin iyayensu babban yayansu Malam Umur sai shi Malam Bashir sai k'anwarsu Goggo Maryam wacce itace akayiwa mai suna da Maryam yayar Zaleeha,
Malam Umar yanada matashin hud'u reras Allah ya azirtashi da tarin yara sama da talatin,
Malam Umar mutum ne mai tsananin zafi da fad'a yanada tsananin kafiya shi kaifi d'aya ne in yace eh tofa eh dince har gaban abadan babu wanda ya isa ya karya mishi doka muddin ya kafa dokarshi,
mutun ne wanda in yayi gyaran murya koda kajin gidanshi suke nitsuwa,
Allah ya shirya mishi yaranshi yayinda Aminu shine babban d'anshi kuma shine ya gado zafin zuciyar Malam Umar da kafiyarsa kab,
sabanin Baba Malam shi kuma yanada tsananin nitsuwa da kauda kai da hak'uri ammanfa in aka k'ureshi yafi Malam Umar zafi da tsanani,
Mahaifinsu ya rasu, shiyasa suka k'auro suka dawo Gombe sun dawo gombe ba juyama Allah yayiwa Malam Umar rasuwa daga nan komai na kula da gidan ya dawo hannun Aminu da baba malam da Ahmad.
Goggo Maryam kuwa tana dukku gidan mijinta.

Hajia Aisha Mamy kenan itace matar Malam Bashir ta forko wacce sukayi auren lalle da lalle,
wacce Allah ya azurtasu da d'ansu Ahmad daga shi kuma bata sake samun haihuwaba.
Ahmad nada shekaru goma a duniya,
lokacin su Malam bashir suna shiga k'auyukan k'abilun gombe da kewaye suna da'awa,
kuma Alhamdulillahi kafurai sunata musulunta suna shiga addinin musulunci sosai,
a cikin hakane sukaje wani yanki kaltingo na k'abilun tangalu nan suka musuluntar da mutane da dama maza da mata a cikinsu akwai wacce ta musulunta da sunata Soro data musulunta ta zab'i a saka mata Halima,
sosai iyayen Halima suka tada hankalin kan musuluntar da tayi daga bisani sukayi mata barazar zasu kasheta,
ganin ta kafe ne kuma bata tsorita ba sai suka koreta,
to daga ranar tayi ta bibiyar malamai mata dasu Malam Bashir Sulaiman Dukku ke zuwa dasu yin da'awa,
dole suka d'auketa suka dawo da ita cikin Gombe suka ajiyeta cikin gidan da aka gina da isilamiya domin irinsu,
nan ta zauna tayi ta karatunta daga bisani akazo batun aure nan ta kafa ta tsare tace ita Malam Bashir takeso.
Allah yayi da rabo a tsakani cikin k'ank'anin lokaci Malam bashir ya sanarwa iyayenshi da matarshi Hajia Aisha duk sai suka bashi k'arfin guiwa dan dama ita Mamy tana buk'atan ya k'ara aure.
Nanfa akayi auren Baba Malam da Halima Mama kenan,
inda ya sai gida a ceceniya ya ajiyeta a nan sabida lokacin suna Dukku ya zama matanshi biyu,
in yazo Gombe ga Halima amarya in ya koma dukku ga Mamy uwar gida mace mai tarin hak'uri da tawakkali.
Zuwan Halima gidan keda wuya Allah ya azurtasu da haihuwa yau da gobe jibi da gata.
saida ta haifi 'yara shida Habu, Maryam, Zaleeha, Zakariyya, Ziyada , kana autarsu Zahira .
Zaleeha na yawan bin Baba Malam suje Dukku dan Mamy na matuk'ar sonta da kula da ita shiyass Zaleeha da Habu da Maryam sun zauna a Dukku sosai sun samu inƙantacciyar tarbiya a wurin Mamy kasan cewar haihuwar kunika Mama takeyi sai hakan ya zame mata kamar hutune da sauk'inta,
Mamy kuwa tasha wuyan yaran nan tamkar itace ta haifesu da cikinta dan ko Ahmad bata sha wuyan rainonshi ba kamarsu Habu Maryam Zaleeha kuma yaran suna masifar sonta hakan itama take matuƙar sonsu,
Zakariyya nada wata biyu ta samu cikin Ziyads,
so randa ta haifi Ziyada a ranar aka yaye Zakariyya daga nan Baba Malam ya d'auki Zakariyya ya kaiwa Innanshi,
lokacin babansu ma na raye daga nan Zakariyya ya zama tamkar d'ansu gata da sakalci dai na goyon kaka yana shanshi,
sai dai duk jikokinsu sunfi son Ahmad da Aminu sai Zakariyyan da Maryam .
Ziyada nada wata sha uku aka aihi Zahira auta
daga nan ita itama haihuwar ta tsaya taci gaba da rainon Zahira da Ziyada wacce takeda nitsuwa irinta Maryam,
daga baya ta kafa nacin a dawo mata da su Maryam shi kuwa baba malam yace takau bazai d'aukosu ba,
amman zai kawo mata Habu tunda ba d'a namiji a gabanta ko d'aya,
to fa shine mafarin fara gane halin Halima dama inkiyarsu ce Halima hali dubu babu na zab'e.

bayan shekaru kad'an babansu Malam Bashir ya rasu daga nan Malam Umar ya k'auro ya dawo cikin gombe a gidanshi daya gina a Fantami yaso ya d'auko inna amman sai tak'i a cewarta bata son tayi nesa da d'iyarta Goggo Dada,
lokacin kuwa tuni Ahmad baya k'asar yana k'asar Italy inda nan yayi karatunshi har ya zama cikekken pilot Aminu kuwa kuwa zama babban soja,
koda Baba malam ya sanarwa innansu cewa zai k'aura shima zai koma cikin gombe fir tak'i da kyar dai da sud'in goshi ya lallab'ata suka k'auro suka dawo gombe nan suka zauna a nan gidanshi na ceceniyan bayan shekaru kamar biyar lokacin tuni Ahmad ya taka k'asa yayi kud'i sosai,
Ahmad yana tsananin son mahaifinshi da k'annenshi baya son duk wani abu da zai tab'a mutuncin mahaifinshi yana tsananin tausayawa da son Mamynshi su Zaleeha kuwa jinsu yakeyi har cikin k'ok'on ranshi kusan shine yake musu komai na karatunsu.
To sanadin hakane Halima ke d'an ragarwa Mamy kisan mummuk'en da takeyi mata,
musamman da taga Ahmad ya sayi k'aton fili a New G. R. Aka tsantsara musu gida na gani na fad'a suka koma can kuma yana yiwa yaranta hidima.
Inna kuwa tace ita dai a barta a ceceniya ita da Zakariyyanta a kuma bata Ziyada acewar yanayin unguwar yana tuna mata k'auyensu badon Mama tasoba sai dan Dole Zoyada ta koma gaban fitinanniyar tsohuwar injita da faɗi.

Ana cikin haka Baba Malam ya had'a auren Aminu da Maryam dan lokacin Malam Umar ya rasu to yana son k'ulla igiyar zumunci tofa anan Halima ta fito da asalin halinta.
Gashi zuwa lokacin iyayenta duk suna ji da ita tunda yanzu tanada wadata sanadin Ahmad kuma tana kasuwanci in zataje garinsu zai bata kud'i ta musu ihsani.

Sosai taso ta zuga Maryam sai kuma tayi rashin sa'a Maryam rainon Mamy ce sai tabi umarnin mahaifinta.

Daga nan kuma ta tsananta bak'in halinta

Yanzu su Zakariyya da Zahira da Ziyada ne suka rege suke karatu Habu da Maryam da Zaleeha duk har aiki sukeyi.
kab cikin yaran kuma Zahira ce munafukar da ta gado bak'in halin uwartasu da k'abilancin ta.
to kuma Zaleeha na shiri da Zahiran fiye da Ziyada dan ita Ziyada irin masu shiru-shiru d'innan ne sosai,
kasan cewar duk yaran da gefen babansu suke kama shiyasa sukayi kyau mai d'aukar hankali.
Shiyasa kuma Halima take jin kanta da yaran take nunawa Mamy rashin d'a'a dan ma yaran basu biye mata.

To yanzu kuwa Zaleeha ce kan ganiyar budurci tana shawaginta son ranta,
tana had'a gwara kan maza a cewarta sai ta duk mai nuna mata barazana da kuɗi ko wani matsayi baya ranta
duk kud'in na miji baya gabanta.
Tace ita soyayyar gsky zatayi duk wanda zata aura take kuma son ya mata tafi son miji jarumi mai tausayi da taumakon na ƙasa dashi kana har ranta tana son kekyawan miji bata son mummunan miji a ranta
Wannan kenan sune ahlin Zaleeha...
***
Ita kam Zaleeha sam bata wani damu da k'a'idar da aka bataba don ganin tsawon lokacin da aka bata takeyi kamar bazai zoba,
so bata wani damuba asalima duk damuwarta da tunaninta a kan son gano ina wanda ya taimaketan yake.

Bayan ta gama shirin baccinta ne,
tazo ta zauna bisa gadonta, ta ajiye system enta da wayarta a gefe,
da niyar had'e muryoyin wadanda tayi hira dasu yau a kaltingo,
kuma sai tayi shiru ta zuba fuskar System en idanu ko k'ibtawa batayi,
ta kai tsawon 5 minutes a haka kana taja dogon numfashi tare da lumshe ido cikin sanyin murya tace.
"Waya sani ma ko sun kasheshi ne?." sai kuma tayi maza ta girgiza kanta tare da cewa.
"Ya Allah ka kare minshi ka sake gaddara haɗuwata dashi."
sai kuma tace.
"To in ma yana raye ta ina zan ganoshi bare in mishi godiyar taimaka min da yayi,
ba abinda na sani a kanshi suna ko anguwa ko aiki ko dangi ko abakanshi bare in mik'a godiyata a gareshi koda a gidan radionmu,
ko menene sunanshi? ta yaya zanyi cekiyarshi ta ya zan ganoshi a faɗin duniyar nan?."
bud'e idanun tayi a hankali kana ta sharte hawayenta dan tabbas ta tuno lokacin da zata fito daga cikin sitadiyon d'in taga sun caka mishi wuk'a a bayanshi, da sauri ta kuma rumtse ido hawaye na zuba kana tace.
"Allah ya isan mishi, Allah zai saka mishi, mugayen banza azzalumai Allah zai saka mana."
sai ta kuma ture system en kana ta zame ta konta,
tana mai zubda hawaye a haka bacci ya saceta.

Dalla kuwa wani babban d'an kalarene wanda ya addabi birnin gombe da kewaye muddin yaga mace ko wacece ita inda ta mishi zaisa yaranshi su kamo mishi ita ya biya buk'atarsa da ita,
Dalla ya addabi garin gombe yayinda duk naci da k'ok'arin hukuma basu tab'a kamashi ba,
yana kuma da d'aurin gindin wani manya da suka medashi d'an bangar siyayasa shiyasa yake cin karensa babu babbaka babu wanda ya isa ya taka mishi birki.
To a yanzu dai babu 'yarinyar da yake cike da cikinta in ya kamata zaiyi mata Dalla-dalla sai Zaleeha,
sai dai shima a sashinsa ana shirin fitar dashi woje dan yana jinyar raunin da Saifuddeen ya ji mishi a gabanshi wanda yake sashi firgita dan gaba d'aya alamu suna nunawa kamar joystick d'inshi zata mace,
shiko fatanshi koda zata mace tayi hak'uri har sai ya rarake Zaleeha a cewarshi...

***
A nan Abuja kuwa
Chapter 61 · 0% Book details