← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 116

Sashe 24

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Biyar dai-dai suka nufi dukku suna isa Dukku,
kamar kullum bayan sun gama komai ne sunje tabsir sun dawo ne ya fito da kayan yayi musu bayani sannan ya bawa Ahmad kayan tare da cewa yau Salisu ne zai maidashi da mashin,
Saminu kuwa nan yake ce musu.
"Yauwa ni nama manta ban gaya muku ba na saya mana takalma da huluna, wanda zamuyi fitan idi dashi dama d'inkin naso in yi mana to sai naga takalma da hulunan zaifi armashi."
sosai suka cika da farin ciki nan Salisu kuma yace.
"To ni kuma zan saya mana agogo masu kyau."
Ahmad ne ya kalli Saifuddeen da yake mishi bayanin wannan 10k d'innan ya sayi kayan d'inki dasu.
harara ya mishi tare da zaro kud'in dan dama ya taho dasu dan ya zargi hakan bashi kud'in yayi tare da cewa.
"Ingo amshesu inada kayan d'inki kai dai ba ka saya ba ka kuma bani to ba ruwanka da batun d'inki in naga dama in d'inka na iyayenane da abokaina da k'annena da yarana in naga dama ink'i dinka naka in d'inka na kowa.
Ga dai kud'inka nadai ci naman dubu d'aya a cikin kud'in jiya."
murmushi yayi tare da amsar kud'in ya sasu a aljihu.
daga nan Salisu yaje ya fidda machine inshi yazo ya maida Ahmad can Shabewa.

Tun daga ranan Ahmad ya fara d'inka nasu na maza.

Shi kuwa Saifuddeen washe gari da yaje kasuwa takalma ya sayawa su Rahma da Ummi dasu Hayatuddeen duk da saida yayi ciko da ribar omonshi na yau d'in.

Washe gari kuma da ya kuma zuwa yan kunne da sarka ya sassaya musu.

A takaice dai saida yayi kwana biyar baya ajiye ribarshi,
a cikin haka kuma ya kuma ya kuma sayan wani kayan yad'i shida ya bada d'inki cikin kasuwar kayan shida abokinshi Is'haqnshi.

tun randa akayi azumi ishirin da biyar ya gama hidiman dinkin salla da komai,

Daga nan kuma yaci gaba da zura kud'i a asusunshi.

Yau saba'an wota ishirin da bakwai kenan,
kuma yau yayi cinikin omo sosai,
k'arfe hud'u dai-dai ya shiga gidansu Is'haq,
Imran na ganinshi yayi sauri ya isa gareshi cikin murna yace.
"Hamma Saifuddeen gobe Ya Is'haq zai dawo yace min shi dai bazaiyi salla a Abuja ba."
kamo hannun Imran yayi wanda bazai wuce sa'an Hayatuddeen ba murmushi yayi tare da shafa kanshi sannan suka shiga parlour Baban Is'haq.
cikin fara'a yace.
"D'an halak kak'i ambato ko yanzu nake jajenka ka kwana biyu baka lek'oba ashe kana tafe."
kanshi ya d'an shafa tare da yin murmushi kana ya rusuna gaban Baba cikin body language suka gaisa har yake shaida mishi gobe Is'haq zai dawo,
sun jima suna hira daga bisani ya mik'e tare da cewa.
"Bari yaje yayi wonka."
daga nan ya fito parlour Mommy ya nufa step mom d'in Is'haq kenan bayan sun gaisa ne ta bashi key d'in d'akin Is'haq da woyarta dan tasan zasu gaisa da abokinshi.

Yana shiga d'akin Is'haq wonka ya farayi sannan ya fito ya canza kayan inda tuni ya wonke wanda ya cire ya shanya.
gefen gadon Ishaq d'in ya zauna tare da fara rubuta mishi sak'o kamar haka.
"Assalamu alaikum, ya gida da Ramadan, Baba ya cemin gobe zaka dawo ko?."
jim kad'an sai ga amsa.
"Wa alaikissalam, nayi fushi da kai yau kwana nawa baka zo gidaba kullum sai na tambayi imran."
bai ida gama karanta amsarba wani sak'on ya kuma shigowa.
"Eh gobe zan dawo ya Rabi'u yayi mana d'inki komai iri d'aya yace wai ai mu tagwaye ne.
A gombe zamuyi salla ai ko?."
murmushi yayi tare da rubuta mishi.
"Allah ya dawo daku lfy ka cewa Ya Rabi'u ngd matuk'a Allah bar zumunci da k'auna, ina Ammi na nayi missing nata tare zaku dawo ai ko.
Hahhm Imran k'arya yakeyi ko last week nazo ai yanzuma hidimar kasuwane ke hanani zuwa yanzuma sauri nake zan tafi."
daga nan kuma ya mik'e ya fita,
har ya mik'a Mommy woyar sai kuma ta mik'o mishi tare da cewa mishi gafa wani sak'on yana amsa yaga abinda ke rubuce.
"Dole fa a gombe zaka zo muyi salla, naga kak'i ka bani amsar inda zakayi salla,
to kuma nasha gaya maka inaso mu kasance cikin ungiyar.
Joint national association of persons with disabilities,
(Jonapwd) gombe state chapter.
All the best!. domin k'ungiyace mai daraja da mahimmanci kungiyace mai zaburar da nakassasu domin su dogara da kansu ta hanyar yin rayuwa kamar ko wanne mai lafiya suna jan hankalin da nusar da nakassasu cewa itafa Nakasa ba kasawa bace, kuma babu nakasasshe sai rago,
suna gina zuk'atan duk nakasashen dake k'ark'ashinsu da nunin nakasar zuciya fa itace sahihiyar nakasa ba irin tamuba ta jiki,
so a sallan ya kamata muje garesu domin had'a hannu dasu."
da sauri ya rubuta mishi amsa da cewa.
"To ba matsala Allah ya kaimu na amince."
yana tura mishi amsar ya sallamesu ya tafi kuma har cikin ransa ya gamsu da shiga cikin sahun members d'in k'ungiyar dan yaga sunada kekyawar niya.

Koda ya koma kasuwa bai wani sake d'aukan Omo ba shagonsu Jabeer yaje suka d'an zauna suna hira dan mutane sun d'an tsagaita shigowa shine ya bawa yaran shagon damar d'an hutawa.

Ganin hud'u da rabi ta godata ne ya sashi mik'ewa tare da bawa Jabeer hannu,
musabaha sukayi sannan sukayi sallama.
Daga nan shagonsu Hisham yaje inda ya samu suma ba mutane da yawa ko dan yanzu kasuwarsu ta d'anyi k'asa sai 'yan tsirarun da suke zuwa sayan kulolin abincin salla.
kusan tare suka fito da Hisham inda yake tambayanshi.
"Gobema zaka zoko?."
kai ya gyad'a mishi alamun eh sannan ya nuna mishi yatsunshi biyu tare da mannasu a goshi alamun rannan salla ma zaizo amman ba kasuwa zai shigoba zaizo wurin best friend nashi."
cikin happy Hisham yace.
"To in kazo zaka isa gidanmu ko?."
ido ya d'an jujjuya kana ya mishi alamun.
"To ai ban san gidanku ba."
gane abinda ya ke nufine yasa Hisham cewa.
"Mu dai-dai ta lokacin da zaka zo sai inzo in sameka a bakin shagonmu sai mu tafi tare muje ka gaida Mom ena."
paper da biro ya zaro kana yace mishi.
"Jabeer ma yace dolefa wai sai naje gidansu wai Umminshi na son ganina so shi rubuta min address insu yayi, kaga kaima gwara kawai ka rubuta min address naku in sha Allah, in Allah ya nufa fa sai kaga nazo."
cikin gamsuwa Hisham ya rubuta mishi tare da cewa.
"In sha Allah, zama kazo."
dai-dai lokacin kuma suka isa bakin San HUSSAIN MALL inda nan Salisu zaizo d'aukan shi,
daga nan sukayi sallama da Hisham, shi kuwa Saifuddeen ya isa gefen masu fruits ya sassayi abinda ya sauk'ak'a, yana gamawa Salisu na zuwa daga nan suka tafi *Dukku d'iyam sad'i na kosam,* garin da ruwa yafi nono tsada, amman fa banda gidansu Saifuddeen dan su har rijiyoyi biyu ne a gidansu d'aya ruwan dad'i d'aya na zartsi, shiyasa duk 'yankin unguwarsu a gidansu ake zuwa d'iban ruwa, rijar dad'in ruwanshi sanyin ko yaushe ruwanshi k'alau ,na zartsin kuwa ko lokacin hutunrune in ka jawo ruwan sai ka sameshi da d'umi dai-dai yin wonka.

Suna isa.
Kai tsaye ya kusa kai cikin gida,
a tsakar gida ya samu Ummi rik'e da botiki,
bisa dukkan alamu ta gama tuyan masa da k'osan dan duk ta sasu cikin manyan kulolin da cikin kayan Rahma suka fito dasu,
ga kuma tukunyar dama kunu yana bisa murhu amman ba ruwa a ciki,
daga can gefe kuma Raihana ce konce lib da alamun bata da lfy,
sai Rahma dake kitchen tana aikin girki,
Hayatuddeen ne da Faruq suka rugo a guje suka nufi inda yake tare da yi mishi oyoyo,
d'aga Faruq yayi sama cak ya ruggumeshi kana yasa hannunshi na dama yana shafa tsakiyar kan Hayatuddeen wanda tuni ya amshi ledan hannunshi,
Ummi kuwa ido ta zuba mishi sosai ya rame alamun rashin hutu k'arara a jikinshi.
gabanta ya iso tare da dire Faruq cikin fidda numfashi ya kalli botikin hannunta kana ya kalli tukunyar dake bisa murhu,
cikin body language yace mata.
"Baki sa ruwa ba."
kai ta jujjuya tare da lumshe ido sannan tace.
"Yanzu zan jawo ruwanma."
juyawa ya d'anyi gefen dama inda randunansu ke jere taku kad'an yayi ya isa inda randunan ke jere bubbud'esu yayi duk babu ruwa a ciki sai kad'an-kad'an ,
gaban Ummin ya dawo tare da mata alamun,
"Ya akayi ba ruwa a randunan me Raihana keyi da bazata ja ruwan ba tunda Raliyya bata nan Hayatuddeen kuma bazai iya dan rijiyoyin suna da d'an karen zurfi,
Rahma kuma na fama da aiki."
juyawa tayi a hankali ta nufi can gefen wata k'atuwar bishiyar maggoro da rijiyoyin ke k'asanta duk suna cikin inuwan bishiyar da sauri yabi bayanta,
suna isa ya zura gugar a cikin rijiyar dad'in, ita kuwa Ummi da sauri ta rik'e tare da cewa.
"Je ka huta zan ja ruwan ita Raihana yau tun da safe cikinta ke ciwo,
Rahma kuma jiya ta yanke a 'yar yatsarta garin yankan lemu."
da sauri ya jujjuya mata kai kana yaci gaba da zura gugan alamun shi zai ja ruwan.
Ita kuwa Ummi tausayinshi ne ya rufe mata zuciya da jiki tasan muddin in dai yana nan tofa baya tab'a yarda taja ruwa, to shi kuma in dai yaja ruwa sai hannunshi suyi jazir musamman yatsunshi da sai sunyi alamun d'ura ruwa, Ummi tafi kowa sani jikin Saifuddeen baya juran wahala yana tsoron wuya so amman sai yake b'oye musu hakan da jarumtar zuciyarshi da take tirsasa gangan jikinshi jajircewa koda ko zai wahala.
ido kawai ta zuba mishi ganin yadda yake jan ruwan da karsashi tamkar baya jin wahalan,
yana cika botikin yaje ya juye mata rabin a tukunyar rabin kuma ya juye a rand'a kana ya yafito Hayatuddeen tare da nuna mishi d'an k'aramin botiki alamun ya d'auko yazo suna kai ruwan rand'a,
da sauri Hayatuddeen ya mik'e tare da suran botikin.
daga nan sukaci gaba da d'iban ruwan in ya cika botikin shi sai ya cikawa Hayatuddeen sannan su d'auka a tare suje su juye a rand'a.
Ita kuwa Ummi tuni ta koma gindin murhunsu na wojen tanata hidiman dama kunun Rahma kuma na kitchen tana k'arisa aiyukanta.
Chapter 24 · 0% Book details