← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 116

Sashe 107

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Gum yayi mata tamkar dutse,
ita kuwa sai surutai takeyi uwa aku,
ganin an gama labaran ne ya sashi,
miƙewa tare da kashe TV sannan ya nufi bedroom ɗinsa,
da sauri tabi bayanshi tana Magana, bai kulata ba, haka ya shiga bathroom,
ruwa ya watsa sannan yayi al'wala kana ya fito.
A bakin gado ya sameta tana zaune,
shi kuwa shirin bacci yayi kana yazo ya tsaya gefenta, da  hannu ya nuna mata hanyar fita alamun ta fice mishi daga ɗaki,
fuska a tsuke tace.
"Muyi maganar tukun!."
Fuska ya kuma tsukewa wanda saida taji gabanta ya ɗan faɗi, yayinda zuciyarta kuwa ta buga da ƙarfi,
hanyar fita ya kuma nuna mata,
da sauri tace.
"Dan Allah, dan darajar ma'aiki kayi haƙuri ka buɗi baki muyi magana."
Ido ya rumtse dan ya rigada ta haɗashi da Allah.
Itama sanin in dai ta haɗashi da Allah zai saurareta ne ya sata yin hakan.
cikin kaushin murya da haɗe fuska zuciya na tafasa murya a zafafe yace.
"Kije ki kwashi kayan da kika watsar ɗin ki maidasu ɗakinki ki ajiyesu yadda kika samesu."
da sauri tace.
"Dare yayi fa."
A kausashe yace.
"Baza kuma su kwana a waje ba."
Cikin sanyin jiki tace.
"To bari in ƙira Habu yazo ya kwashesu."
A ƙufule yace.
"Waya fito dasu?."
Kai ta juya tare da cewa.
"Ni ce."
Cikin bada umarni yace.
"To kije ki maidasu kizo muyi maganar."
Bata da zaɓi dan ta san kaɗan kenan daga halinshi dole taje a daren ta kwashi kayan,
ta maidasu cikin ɗakinta,
tana gamawa a gajiye ta koma ɗakin nashi,  a kwance ta sameshi cikin maida numfashi tace.
"Na maidasu. Ka tashi muyi maganar."
Kai ya jujjuya tare cikar haiba da isa da gidanshi yace.
"Maganar ai na gamata babu wani wanda zan aurawa ɗiyata Zaleeha sai Saifuddeen,  kuma babu wani mahaluƙin da ya isa  hanani sai ubangijin daya halicceni!."
Yana faɗin haka ya gyara kwanciyarshi tare da rufe ido alamun bacci zaiyi.

Cikin tsananin takaici haɗi da ƙunci tace.
"Ni kuwa Wallahi ƴata bazata auri gurgu kuma kurma ba, ɗiyata bazataje ta zama majinyaciya ina kallo da idona ba, sannan bazan taɓa bari takashe rayuwarta wajen kula da nakasasshe ƙaskantacce ba, Allah ya sauwaƙa ma, ni dai ajinina ban haifawa nakasashshe matar da zai aura ba ehe!!."
Tana gama faɗin haka ta juya ta fita a fusace.
Gyara kwanciya Baba Malam yayi tare da rufe idanunsa, sunayen Allah Kawai yake ambata acikin ransa.
***

Washe gari kuwa Zaleeha daga gidan hajja Inna ma'aikatarsu ta nufa, bayan ta gabatar da shirinta na mushaƙata kai tsaye gidansu kuma ta nufa.

A harabar gidan tayi kiciɓis  da ya Ahmad,
cikin shaƙuwarsu ta nufi inda yake, da alamun cewa shima yanzu shigowarsa cikin gidan.
hannunshi ta kamo tare da cewa.
"Ya Ahmad nayi kewarku kwana biyu bana nan ko kuyi cikiyata."
murmushi yayi tare da cewa.
"Muma munyi kewarki, kin san inata shirin tafiyarmu ne,
naso in wuce da Lubna amman Mamy tace wai in bar miki ita."
tsalle tayi cikin jin daɗi tace.
"Yessss! My mamy kai amman ko naji daɗi sosai!!."
Murmushi yayi tare da cewa.
"Ato ai dama amare yan jin daɗine."
Sam bata kawo komai a rantaba da jin furucinsa,
sai sakin hannunshi da tayi lokacin da sukazo dab da ƙofar Mama,  cikin alamun gajiya da kuma yunwa dake damunta tace.
"Yauwa Ya Ahmad bari inje inyi wanka sai inzo muyi hira,  ka cewa Aunty Lubna ta gasa min abin daɗi yunwa nakeji, please  ko roasted fish nema nasamu idan nazo."

"To." Kawai yace tare da juyawa yayi side ɗin Mamy.

Ita kuwa Zaleeha da sallama ta shiga,
da sauri ta kutsa kanta cikin parlour'n,  saboda hango Mamanta na zaune fuskar nan a kumbure alamun tsananin fushi,
da sauri ta durƙusa agabanta cikin tsoro tace.
"Lafiya kuwa Mama? Meya sameki? baki da lfy ne?." Duk tayi mata tambayar cikin kulawa, irin wacce ke tsakanin Ƴa da Uwa.

Cikin tsananin takaici Mama ta watsa mata harara tare da cewa.
"Ae naji ke har dariya ma kike ko? yayinda ni kika barni ina nan baƙin ciki da ɓacin ranki zasu haɗu su kasheni!."

Cikin zaro ido haɗi da tsoro tace.

"Na shiga uku Mama me nayi miki?."

A hasale Mama tace.
" kikamin ko kikayiwa kanki."
Sai kuma ta miƙe tsaye tare da watsawa Zaleeha wani  irin mugun kallo.
Sannan tayi cikin bedroom ɗinta, wanda idan  ba doleba, sam  bata son shigarsa, saboda idan taga wannan kayan ji takeyi kamar ta faɗi ta mutu, tsabar baƙincikin dake cika zuciyarta.

Da sauri Zaleeha ta bita,
a gaban Maman  ta tsaya, cikin raunin murya tace.
"Mama kiyi haƙuri in na miki laifine ki gaya min Wallahi bazan sakeba!."

Azafafe ta nuna mata tarin akwatunan wanda ita sam bata gansuba sai yanzu cikin kakkausan murya tace.
"Kinyi asara Zaleeha, Wallahi kinyiwa kanki sakiyar da ba ruwa, ki rasa wanda zaki zaɓa duk cikin masoyanki sai wannan banzan nakasasshen da baya ji baya magana, uwa uba kuma baya tafiya, ki zaɓeshi matsayin miji har zaki bashi dama ya turo iyayenshi su kawo tarkacensu harda su sadaki,
wato kin maidani shasha naje inata haushi ashema ban saniba kece kika amince mishi sai ɗazu Habu yake sanar min."
Mama fa bata tsagaita da masifaba bare tasan halin da Zaleeha ke ciki.
sai Zahira ne ta zaro ido da ƙarfi ganin yadda Zaleeha tasa hannu da tsananin ƙarfi ta kama kanta,
yayinda tuni kunnuwanta sun toshe tun lokacin da Mama tace mata an kawo sadakinta kuma wai ga kayan aurenta a gabanta,
sannan wai da yardarta uwa uba kuma wai da wancan ginannen taɓon ne da Allah ya ƙawatashi da kyan sura,
daga nan bata kuma jin zancen Mama ba, sai rumtse idanunta da tayi tare da  cilla wani irin gigitaccen ƙara mai tsananin ƙarfi, haɗe  da cewa.
"Ƙarya ne banice na turo shiba, bana sonshi! bazanyi aureba Wallahi, bazan zauna da kowaba sai wanda ya taimakeni!!." 
Sai ta kuma buɗe idanunta, wanda sukayi jazir ta kalli tarin akwatunan, wani irin gigitaccen ƙara ta saki wanda yasa,
Ahmad, Habu,Aunty Lubna da suka nufo parlour'n  maman tun ihunta da sukaji na  forko  ya sasu shigowa a guje,
suna shiga ita kuwa zaliha ta yanki jiki ta faɗi sumemmiya.

Da sauri Ahmad ya tarota ta faɗa jikinshi,
cikin rawan jiki murya a hargitse yake ɗan jijjigata tare da marin kumatunta yana faɗin.
"Zaleeha!  Zaleeha!! Ki tashi Zaleehaaa!!!."
Sai ya kuma kalli Zahira daketa kuka tana cewa.
"Shike nan ta mutu, tace muku bata son auren ba wanda take so ku barta ta jira wanda takeso anƙi gashi yanzu baƙin ciki zai kasheta.
Mama kuwa da sauri ta juya ta nufi falon Baba malam tana shiga tasa kuka tare da cewa.
"Shike nan baƙin ciki zai kashe min ƴata,
in ta mutu ai kowa ya huta sai a kaiwa shashashan musakin gawanta."

Shiru Baba malam yayi sai murmushin da yakeyi, Mamy kuwa da sauri ta miƙe zata nufi side ɗin Maman,
dan da fari da suka jiyo ihun Zaleeha sunyi zaton ko uwarce ke dukanta, shiyasa data yunƙura zata je Baba malam ya dakatar da ita.

A can ɗakin Mama kuwa a kiɗime Lubna ke cewa Ahmad.
"Hubby a sume take fa,  ko dai da gaske al'jani ne ya taima keta shine yau zasu baiyana kansu? Hubby mu kaita wurin Baba Malam!." Tafaɗi maganan cikin tsananin ruɗewa.

Yunƙurawa  Ahmad yayi da ita a jikinshi,  fita yayi da matsanancin sauri ya nufi parlour'n Baba Malam,
a bakin ƙofa sukayi karo da Mamy.
Cikin tsoro da firgitan ganin Zaleeha kamar gawa Mamy tace.
"Malam da gaske Zaleeha ba lfy."
Shi kuwa Ahmad a gaban mahaifin nasu ya direta tare da cewa.
"Baba malam al'janine fa a jikin Zaleeha da gaske danfa kawai taji batun auren ne yasa ta suma."
Habu ne yaja wani dogon tsaki tare da cewa.
"Ya Ahmad meyasa kake yarda wai Zaleeha iska gareta?."
Cikin tsawa yace da Habu.
"To in ban yarda tanada iskaba meya sumar da ita?
please Baba malam ayi mata ruƙiyya ko al'janin zaiyi magana."

Cikin takaici Habu ya juya gaban fridge ɗin dake gefenshi, buɗewa yayi tare da ɗaukan goran bottle water  mai ɗan karen sanyi,
kana ya juyo marfin gorar ya murɗa kana ya ziraro da bakin gorar dai-dai saitin fuskar Zaleeha ya fara tsula mata ruwan sanyin.
Wani irin wawan ajiyan zuciya taja, me ɗauke da azaban ƙarfi kana ta fizgo numfashinta da wani zazzafan kuka,
cikin kuka mai cin rai ƙuna da kuma tsananin tsoro take cewa.
"Bana sonshi Ya Ahmad ka gayawa Baba malam wallahi bana sonshi na tsaneshi!."
Sai ta kuma kamo hannun Ya Ahmad ɗinta da tuni ya fara zubda hawaye, cikin kuka taci gaba da cewa.
"Ya Ahmad ka gayawa Baba malam mana,
ka faɗa mishi cewa gurgu nefa haka kuma kurma ne, kace mishi bana sonshi na tsaneshi,
wallahi in aka aura min shi zan mutu wlh ya Ahmad mutuwa zanyi!!!." Taƙare maganar cikin wani irin kukan fitar hayyaci.
Chapter 107 · 0% Book details