← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 116

Sashe 103

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sun gaisa ne tare da ɗan taɓa hira,
sai Bappa Ali ya ɗan gyara zamanshi tare da yin gyaran murya kana ya fito da damin kuɗi kimanin dubu ɗari cas,
daga cikin aljihun babbar rigarshi,
miƙa kuɗin yayi wa Malam Adam tare da cewa.
"To ga aiken ɗana Saifuddeen ga sadakinshi."
cikin sakin fuska Malam Adam ya karɓa tare da cewa.
"Masha Allah. Allah ya sanya al'khairi. Yasa ayi damu."
"Amin Amin." suka amsa baki ɗaya,
sai kuma suka kalli Dirankadi da yace.
"Tofa ɗalibin naka yace yanzu sauran a saka masa rana kawai."
Murmushi mai kama da dariya sukayi baki ɗayansu, sannan
Malam Adam ya kalli amininshi Baba malam da yaketa murmushin jin daɗi yace.
"To Malam Bashir me kace kan batun saka ranan?."
Kanshi ya ɗan rausayar ya kalli babban ɗanshi mafi soyuwa a zuciyarshi, kana kuma ɗansa mai tsananin biyayya da kare mutuncinsa,
sannan ya kalli ɗan ɗan uwanshi kuma surkinshi mai kare daraja da martabar ahalinshi wato Ameenu kenan, yace.
"To ga yayun Zaleeha nan mu basu dama muga irin dattakunsu mana."
da sauri Ahmad ya ɗago kanshi ya kalli mahaifin nashi sai kuma yayi sauri yayi ƙasa da kannasa tare da cewa.
"Baba malam in dai kuna raye ai mu bamu da bakin mgn, sai abunda kukace."
sosai Ahmad ke burge su Bappa Ali yanayin biyayyarsa tamkar Saifuddeen.
malam Adam ne ya ɗan kishin giɗa kana ya kalli Ahmad da Aminu yace.
"To Ahmad mu ɗin tabbata zamuyi ne?."
A hankali ya jujjuya kanshi yana mai jin tsoron randa zai rasa iyayenshi.
Shikuwa Malam Adam cigaba yayi da cewa.
"To kaga shiyasa muke jawoku a jiki dan mu nuna muku yadda ake aiwatar da komai na jagoranci,
a matsayinku na manya wanda dole wata rana kune a madadinmu,
yanzu dole zamu so muga yanayin dattakunku,  tunda dai kusan komai kuma kunga an kawo ko wani abu na al'ada kama daga gishiri da goro da lefe da kayan rufi, kana yanzu kuma kunga sun gabatar da abinda shariya ta zantar sun kuma buƙaci a saka ranar biki,
to yanzu dattakunku muke son gani,
kai Aminu kaine Babba kan Ahmad yaushe nene kakega za'ayi bikin?."
A hankali Ya Aminu ya ɗan rusunar da kanshi sai kuma ya kalli Ahmad,
kusan a tare suka haɗa baki wurin cewa.
"Ashirin da bakwai ga wata mai kamawa. Yayi ko?."
A hankali Baba malam ya fidda sassauƙan numfashi tare da cewa.
"Yayi kyau,  to Amman meyasa har wata ɗaya, baku shirya bane?."
Cikin nitsuwa Ahmad ya kalli mahaifin nashi tare da cewa.
"Eh to Baba malam mun shirya amman bamu gama shirin ba.
Nanda kwana biyar zan koma Abuja,
sannan inada zirga-zirga tsakanin ƙasashe da dama Dubai, India, US, Korea, Egypt. Yanzu dai in na fita zan ɗan kwana biyu kafin in karkato Nigeria, kuma inaso inyiwa Zaleeha kayan ɗaki mai kyau zan bata zabi kayan ƙasar da takeso,
zan gama saya mata komai a online sannan nasan cikin sati biyu jirgi zai iso dasu nan,
to shiyasa nake son ya kai wata ɗaya."
murmushi Dirankadi yayi tare da cewa.
"Yaran zamani ku dai kunfi yarda da kayayyakin ƙasashen turawa, sam kun Kasa tsayuwa ku inganta mana na ƙasarmu yadda zamuci gaba muma, yanzu jihar gombe wanne irin kayane babu?.
Duk fa arewacin ƙasarnan babu jihar da ta kai jihar Gombawa yawan kafintoci da ci gaban kafintoci. Babu irin samfurin kayan ƙasar waje da basa iya sarrafawa,yanzu konan cikin Sahaja Ventures kuka shiga ae akwai kaya masu kyau da inganci, wasu ma harsun ɗarawa kayan waje kyau."
Malam Ashiru ne ya amshi zancen da cewa.
"Ahmad wannan zirga-zirga duk na menene?."
Aminu ne ya ɗan kalleshi tare da cewa.
"Ai driver ne shiɗin shiyasa yana nan kamar farin wata yana ko ina."
Cikin mamaki Bappa Ali yace.
"Driver kuwa?."
Murmushi Malam Adam yayi tare da cewa.
"Eh shi pilot ne driver' n jirgin sama. Yana aiki da kamfanin Azman Air Land."
kai bappa Ali ya jinjina jin suna kamfanin ma aikatar Ahmad ɗin.
Nan dai suka gama tsara komai da shirya komai na bikin yadda ya dace,
an dai bar batun ɗaurin aure nan da wata ɗaya mai zuwa.

Wai to ina Zaleeha ne, mun dai san Mama da Zahira kan suna Doho,
Ziyada da Zakariyya kuma mun san su dama gidan Hajja inna suke da zama tsohuwa mai boris.

A gidan su Saifuddeen kuwa su Adda Rahma suna dawowa,
duk suka zauna parlour'n Ummi suna hirar mutunci da karramawar mutanen, Hajia Rabi ce ta kalli Ummi cikin nitsuwa tace.
"Na ɗan samu nitsuwa da naga gidansu yarinyar gidan mutunci ne, duk mutanen gidan sunada mutunci."
Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
"Masha Allah."
Aunty kubra ce tace,
"A gsky ba laifi sunada dattaku, sai godiya suketayi kamar kyauta muka basu kayan."
Hayatuddeen ne yayi dariya tare da cewa.
"Nan kuma wayo zamuyi musuba mu ɗauke musu ƴarsu kayan kuma gidanmu zai dawo da dalelliyar amaryar Hamma na."
Dariya sukayi baki ɗaya, Imran ne ya ɗan sosa ƙeya tare da cewa.
"Aunty Kubra zamu tafi fa."
cikin dariya tace.
"Yo to ku tafi mana."
Sulaiman ne ya ɗan zaro ido tare da cewa.
"To kuɗin namufa da aka bamu?."
da sauri suka juyo suka kalli Isma'il da yayi dariyar ras Kamar ba kurma ba.
Hajia Rabi ce tace.
"Ohoho ni Rabi'atu wlh wata rana kuɗi zaisa Isma'il ɗina yayi magana, ji shewar da yake jin ance kuɗin nasu ne."
Hayatuddeen ne ya kece da dariya tare da cewa.
"Yaseen kuwa Mom Isma'il in yaga kuɗi har harshenshi zakiga yana rawa."
Dariya yayi tare da kaucewa dukan da Isma'il ya kai mishi,
Ita kuwa Hajia Rabi kuɗin ta fidda cikin Jakarta irgasu tayi ganin dubu hamsin ne a rafar forko kuma duk girmansu ɗaya,
shiyasa suka gane cewa dubu ɗari uku ne suka basu tukuici,
wanda a al'adan gombawa in an kai kayan lefe anasa kuɗi a ƙasan turame,
in dubu goma akasa to dangin amarya zasu ƙaro wasu dubu goman su ɗaura kan goman dake ƙasan turame sai su bawa wanda suka kawo kayan wannan nasune tukuicinsu kenan so su yasu zasu raba,
in dubu biyar akasa to biyar ɗin dangin amarya zasu ƙara,
In 20k nema to dole zasu ƙara in 30k ne ko 50k Ko 80k 100k nema dole su ninka,
to su dama dubu ɗari suka saka a ƙasan turamen,
su kuwa madadin su ƙara dubu ɗarin sai suka ƙara dubu ɗari biyu,
shiyasa suka samu dubu ɗari uku.
Rafan dubu hamsin Hajia Rabi ta miƙawa Hayatuddeen tare da cewa.
"To gashi ku karɓi wannan."
Da sauri suka amsa tare da ɗaukan tiren da Adda Rahama ta cika musu pepper chicken dasu drinks akai, tace kuci abinci kafin ku raba kuɗin.
to sukace kana suka haura sama a parlour'n Hayatuddeen suka baje kolinsu,
Imran ne ya ɗauki kuɗin ya irga 10k ya bawa Sulaiman kana ya bawa Isma'il ma 10k shima ya ɗauki 10k kana ya bawa Hayatuddeen 10k, 40k kenan,
sai ya ɗago sauran 10k ɗin kuma yace.
"To wannan 10k ɗin kuma na Zakariyya ne.
kun san Zakari namu yaseen in mukaci kuɗin nan bamu bashi ba sai ya tsigemu.
dan baya nanne shiyasa bai samu zuwa ba."
dariya sukayi baki ɗaya,
Hayatuddeen ne ya figi lallausan tsokan cinyar kaza tare da taunawa ido ya lumshe jin harshenshi na motsi dan daɗi, buɗe idon yayi tare da cewa.
"Yanzu ma yamin text wai wlh mu ajiye mishi naman rabonshi."
dariya Suleiman yayi tare da cewa.
"Wai ina yaje ne?  Ni tun jiya bamuyi mgna da shiba?."
Hayatuddeen ne yayi gyatsa tare da cewa.
"Dad'in kowa sukaje da Hajja inna tamu, da wannan fitinenniyar yayar tashi wai sunje gidan ƙanin Hajja inna tamun sai gobe zasu dawo."
dariya sukayi ganin Isma'il fa baya tare dasu sai harraƙawa yakeyi.
Nan sukayi ta hirarsu irinta sabbin matasa masu jin da rawan kan gigin balaga.

A parlour kuwa Adda Rahma da Raliyya sam ƙin karɓan kuɗin sukayi.
Ummi ta kalli Hajia Rabi tace.
"Ku rabasu, ki ɗauki dubu hamsin Kubra hamsin sai Goggo Dada itama a bata hamsin Aunty Mina ku bata hamsin Sadiyan Salisu hamsin.
Su kuma Rahma da Raliya angon zaizo ya basu tukuicin."
Dariya sukayi duka ganin karamci da kima da dottakun Ummi sannan tasa Aunty Mina ta raba musu kayan ciye-ciyen da suka dawo dasu.

Ganin magriba ta karato yasa  duk suka miƙe suka sallami juna suka tafi.

Hakama abokan Hayatuddeen duk sun tafi.

Bayan an idar da sallan magriba ya Adnan ya shigo har parlour'n Ummi in da ya samu suna zaune gaba ɗayansu ga Aunty Mina da Goggo Dada,
cikin sakin fuska ya kalli Hayatuddeen tare da cewa.
"Eye ƙanin ango me ka samu hakane naga sai murna kakeyi?."
kai ya jinjina tare da cewa.
"Ji nake kamar dai na jawo bikin nan."
kafaɗanshi ya ɗan buga tare da cewa.
"kamar yau ne."
Sai ya kuma kalli su Ummi tare da cewa.
"To Ummi mu zamu wuce gida,
tun ɗazu Faroq keta kirana wai muyi sauri mu koma."
kai ta jinjina tare da cewa.
"To Allah ya kiyaye hanya."
"Amin Amin".
yace tare da miƙewa ya amshi Akih dake hannun Raliya,
sannan ya juya ga matar tasa tare da cewa.
"Rahma taso mu tafi ko."
to tace kana ta miƙe ta zari hijabinta tabi bayanshi.

Ƙarfe tara na dare dai-dai su bappa Ali suna parlour'n Ummi.
suna shiga da kamar 15 minutes Saifuddeen ya shigo bisa wani zazzafan wheelchair ɗinsa red colour da gani kasan sabone.
ganinshi ne yasa su murmusawa gaba ɗayansu,
Ahmad dake biye dashi a baya wanda shine daya maida Imran sai ya ɗaukoshi dan shi tunda yamma yana gidansu Ishaq .
Cikin girmamawa ya gaidasu,
kana shima Ahmad yazo ya zauna gefen kawun nashi tare yin gyaran murya yace.
"Kawu Ali kun jene?."

"Eh munje yanzu ma daga can muke?."

"Masha Allah, to ya batun saka ranan?."
Chapter 103 · 0% Book details