← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 116

Sashe 32

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kuwa Saifuddeen koda ya koma gida,
cikin nitsuwa yayiwa bappa Ali bayanin komai.
Cikin nisan nazari da zurfin tunani Ummi da Bappa Ali da Rahma suke karanta duk bayanin da ya musu,
tun randa ya fara kai kaya shagon Alhaji Kabiru da yadda yake sonshi da yadda ya samu su Alhaji Sani suna tattauna batun tallan sirri da company maggi ta kawo musu,
da yadda yaje ya sameshi da mgnar da yadda ya gaya mishi batun yawan kud'in sarin da ake buk'ata, ya kara musu da cewa ya gayawa Ishaq shi kuma zai gayawa Babansu, da Babban yayansu Barrister Rabi'u dan yasa mishi hannu a cikin lamarin ya tsaya mishi a matsayin lawyer inshi.
Ya kuma sanar musu cewar suma su Alhaji Kaburu sunce sai sunga iyayenshi sunji inda ya samu kud'in kafin su amince da batunshi.
Gyara zama Bappa Ali yayi tare da fuskarshi kana cikin sauk'e numfashi yace.
"To inaga dai mu barshi ya gwada mu gani, domin bahaushe yace matsoraci bashi zama gwani ko shi wanene,
mu bada yak'ini a kanshi tunda munada makama kuma ba da ka za'ayi abinba kamar yadda abokinshi ishaq ya bada shawara hakan za'ayi,
dan su kansu sun tsorita da batun yadda yace yanada kud'in shiyasa sukace sai sunga iyayenshi kinga alamun gsky kenan domin da 'yan damfarane ce mishi zasuyi kada ya gayawa kowa har uwa da uba in yana dasu kada ya gaya musu,
in kin amince ni dai na amince na kuma gamsu da kasuwancin."
Ya k'arishe mgnar yana kallon Ummi da Rahma jinjina kai Ummi tayi tare da cewa.
"Ba matsala Allah ya bashi sa'a ya sanya al'khairi da al'barka a cikin lamarin ni na amince."
sosai Saifuddeen yaji dad'in amincewarsu domin suna bada dukkan yardansu a kanshi tamkar bashida nakasar komai,
shi kuwa Bappa Ali cikin nitsuwa yaci gaba da cewa.
"Zan je in samu Malam Ashiru abokin ya Bello, in mishi bayanin komai sannan muje gomben mu samu Babansu Ishaq da shi barrister Rabi'un sannan muje wurinsu Alhaji Kabirun sai mu tattauna duk abinda ya dace."
cikin nitsuwa Rahma tace.
"Hakan yayi Allah ya shige mana gaba."
Amin Amin sukace baki d'aya sannan suka tashi daga taron nasu.

Washe gari tun da asuba bayan an fito masallaci Bappa Ali yasa Salisu ya kaishi gidan Malam Ashiru bayan sun gaisa ya mishi bayanin abinda ke tafe dashi kan batun Saifuddeen,
sosai suka tattauna a kai nan suka tsaida cewar gobe zasuje su samu su Alhaji Kabirun.

Salisu na dawowa suka d'auki hanyar gombe suna isa Saifuddeen ya rarraba ledanshi kana yaje shagonsu Alhaji Kabiru ya shaida mishi cewa gobe iyayenshi zasu zo cikin mutuntaka alhaji Kabirun yace to sai sun zo d'in.

Daga nan Saifuddeen ya wuce gidansu Ishaq yana shiga yayi kicibis dashi da a tsakar gidan,
a tare suka shiga parlour Babansu nan ya samu Ya Rabi'u ya iso, bayan sun gaisane suka tattauna lamarin nan ya sanar musu gobe ma su Bappa Ali zasu zo sundai ajiye zance sai goben.

Washe gari kuwa koda su Bappa Ali da Baba Ashiru suka taho da babban yayansu Samisu yariman Dukku kenan kai tsaye gidansu ishaq suka wuce.
sosai suka samu tarba ta mutuntaka,
suka gaggaisa sannan sukayiwa juna k'arin bayani,
daga bisani suka sa ishaq yayiwa Saifuddeen text cewa sun isofa a ina zasu had'u dasu Alhaji Kabirun.
Yana ganin text d'in ya wuce shagon Alhaji Kabiru d'in ya gaya mishi cewar sun isofa,
cikin kula ya mik'e tare da cewa.
"To muje can gidansu abokin naka sai muyi musu jagora zuwa can gidan Alhaji Sanin."
cikin jin dad'in haka Saifuddeen ya gyad'a mishi kai sannan ya juya yabi bayan Alhaji Kabirun,
motarshi suka shiga kai tsaye suka isa gidansu ishaq sosai Alhaji Kabiru yayi mamaki ganin manyan mutane dan barrister Rabi'u sanannene hakama mahaifinshi baraden Gombe, ga kuma Yariman dukku ga kuma Malam Ashiru da Bappa Ali wanda da ka gansu kaga kamala irin ta malaman addinin musulumci.
bayan sun gaggaisa ne kuma suka mimmk'e suka nufi gidan Alhaji Sani wanda tuni Alhaji Kabiru ya mishi bayanin zuwansu a waya.

G.R.A suka nufa inda nanne anguwar gidan Alhaji Sanin yake,
suna isa mai gadi ya bud'e musu gate ganin tsaleliyar motar ya Rabi'u a gaba wanda Saifuddeen da Ishaq ke ciki a baya Yariman Dukku kuma yana gaba kusa da Barrister Rabi'un,
sai kuma motar Alhaji Kabiru wacce Malam Ashiru da Babba Ali ke ciki Babansu Ishaq kuma na gaba kusa da Alhaji Kabirun,
suna shiga harabar gidan sukayi parking,
suna firfitowa wanni d'an matashi wanda zai kai sa'an su Hayatuddeen ya iso gabansu cikin nitsuwa ya gaidasu,
kana ya kalli Alhaji Kabiru tare da cewa.
"Abba ku shigo ciki inji Daddy na."
shafa kanshi yayi tare da cewa.
"To Sulaiman." sai ya kuma juyawa ya kalli su Babba Ali tare da cewa.
"Bisimillanku mu shiga ciki."
to sukace kana suka biyo bayan yaron da aka kira da Sulaiman ,wanda yake rik'e da hannun Alhaji Kabiru yana cewa.
"Abba ina Isma'il baka zo min da shiba."
dai-dai lokacin kuma suka shiga cikin tamfatsetsen parlour yayinda Alhaji Kabiru yayi sallama tare da cewa Sulaiman.
"Isma'il baya nan ai sun tafi Yola shida Maminshi."
sai kuma yayi murmushi ganin Alhaji Sani ya nufi gaban Babansu Ishaq cikin mamaki yace.
"A a yau inada manyan bak'i kenan kaida kanka Baraden Gombe ai da kayi aike ka kiranima zan amsa kiran."
Sai ya kuma kalli su Bappa Ali dake cikin shiga ta kamala cikin sakin fuska yace.
"Marhabikun ku iso ku iso."
cikin kamala suka zazzauna shi kuwa Alhaji Sani cewa Sulaiman yayi.
"Sulaiman maza je ka kawo musu abin sha."
da sauri yaron ya juya ya fita ba jimawa ya dawo da wani babban tire cike da ababen sha mai sanyi,
sai ya kuma juya da sauri ya fita,
yayinda tuni su kuma suna gaggaisawa,
cikin nitsuwa Sulaiman ya kuma shigowa tare da tire cike da fruits ya ajiye bisa stol dake tsakiyansu,
sannan ya fara ajiye musu gorunan ruwan dana juice sai cup d'ad'd'aya a gabansu.
yayinda tuni su kuma suna tattauna abinda ya kawosu,
sosai Alhaji Sani ya d'auki abin da mahimmanci dan ganin manyan mutane suna cikin lamarin,
nan take yayi musu k'arin bayamin sannan suka bashi kud'in da dama sun taho dasu nan shaidu suka sa hannu,
Barrister Rabi'u da Barrister Salman yayan Saminu kenan Yariman dukku suka rattaba hannu ga manyan shaidu.
A nan take kuma sukayi mgnar hayan shagon da in kayan sun iso zai ajiyeshi.
ba tare da b'ata lokaci ba Alhaji Kabiru ya shaida musu akwai wani shago can k'arshan layinsu amman a luggune,
murmushi Babba Ali yayi tare da cemishi.
"Ba matsala nawane kud'in hayan."
Alhaji Sani ne ya d'an gyara zama tare da cewa.
"Shagunanshi ne ai, in kunaso ku biya kud'in wata shida in kuma kunga ba matsala ku biya kud'in shekara d'aya yadda dai kasuwa ta kama."
Barrister Rabi'u ne ya kalli Bappa da Saifuddeen tare da cewa.
"In dai da hali ku biya kud'in shekara d'aya."
da wannan shawarar bappa Ali ya biya kud'in shekara d'aya,
sannan Saifuddeen yasa hannu a cikin dukkan takardun da ya kamata na company maggi daga nan suka gama komai sannan suka sallami juna a mutunce suka tafi.

Koda suka koma gida kuma Bappa Ali ya fito da sauran kud'insu na hayan filinsu da za'a kafa services ya nunawa Ummi dasu Saifuddeen dan cikinsune ya biya hayan shago,
nan kuma suka tsaida shawarar bappa Alin ya sari kayan abinci tunda dama sana'arsa ce aune-aune.
nan bappa Ali ya fara sari a duk kasuwannin da yake zuwa kamarsu.
Ngalda, bajoga, Nafad'a, Hashidu, dogon ruwa, kiri, Malam Sidi, Kurugu, kumo, Dad'in kowa D'ukul togo. Da dai sauransu.
kasan cewar lokacin Kaka'ace amfanin gona ya nuna so kayan abinci yana araha inda tuni masu kud'i keta sara suna boyewa da nufin sai yayi tsada su fitar to wannan dalilin yasa Bappa Ali fara sara da kekyawar niya dan taimakawa masu k'aramin k'arfi yayi aniyar zai canza salon wannan kasuwancin da ya sara ya ajiye in yayi tsada shi kuma ya fitar ya fara saidawa a farashi mai sauk'i.
to nanfa ya k'ara k'aimin bin kasuwannin k'auyuka yana sarar buhuhhunan su.
Masara, Dawa, Gero, Maiwa, Shinkafa, Rid'i, kalwa, Wake, Gyad'a, da dai sauran kayayyakin abinci,
cikin wata biyu duk ya gama sarin inda ya cika tsoffin d'akunan iyayensu duka biyu da buhunan kayan abincinshi.

Tuni Magginsu Saifuddeen kuma ya isa har an shirgesu a babban shagon da Saifuddeen d'in ya kama haya inda aka cikashi mak'il da katon d'in MAGGI mak'il kana aka ja shagon aka rufe, yayinnda shima burinshi irin na Bappanshi ne.
Ya kuma ci gaba da sana'o'insa da ya saba, yana kula da ahlinshi da ahlin Baba Bello,
yana kuma zura ribar shi a wani sabon asusunshi d'aya saya dan wancan asusun tuni ya cika a cewarsa sai ya cika asusu uku kafin ya bud'esu duka.

Bayan wata bakwai da saran Maggin kenan
Rayuwa taci gaba da gudana yau dad'i gobe akasin haka abu da dama ya faru.

Ana cikin haka rana tsaka Maggin da aka sani a hud'u goma sai gashi yayi gauron zabbi ya koma biyar ashirin kusan ninkin ba ninkin kenan,
yayinda yan kasuwa masu harkan magging da sun samu sun sara suketa farin ciki anata hidimar kasuwa anata hidima.
Chapter 32 · 0% Book details