← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 116

Sashe 85

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ɓangaren Zaliha kuwa kwana biyu kenan yau bataje aiki ba sakamakon ɗan jinyan da tayi, amma yanzu Alhamdulillah jikin nata yayi sauƙi sosai, yayinda kullum Aunty Lubna ke ƙara kwantar mata da hankali, hakanan yau tatashi tana mejin faɗuwar gaba yayinda takejin zuciyarta na tsinkewa akai akai haka dai ta kawar da duk wani abu da takeji ta shiga shirya kanta don zuwa gabatar da shirinta.

Fitowarsa daga wanka kenan lafiyayyar skin ɗinsa sai fidda daddaɗan ƙamshin tsadadden sabulun wankansa, zaune yake agaban mirror yana shafawa jikinsa mai, yana kammalawa ya shiga gyara ƙawataccen sajen dake kwance akan fuskarsa, wanda ta sauya gaba ɗaya kamanninsa na da, taƙarawa fuskarsa kyau da kwarjini. Wata dakakkiyar shadda me kyau da tsadan gaske wacce take da kalan skay blue ya sanya, sosai shaddar ta amshi jikinsa inda tayi bala'in da cewa da white skin ɗinsa, wata haɗaɗɗiyar hulan zanna bukar wacce jikinta ke ɗauke da ratsin sky blue yasanya, yayinda aƙafansa kuwa yasanya lafiyayyun takalma sau ciki ƙiran kamfanin bally suma kalar sky blue garesu hakan yasanya haɗuwar tasa ta ƙara bayyana, bakaɗan ba Saifuddeen yayi kyau yayinda kyakkyawan sajensa keta ƙyalli, tsadadden turarensa me daɗin ƙamshi ya fesa ajikinsa take ɗakin ya gauraye da ƙamshinsa, agogonsa ƙiran kamfanin rolex ya ɗaura akan tsintsiyar hannunsa na dama, wayarsa ƙirar iphone ya tura acikin aljihunsa tare da sarrafa kekensa ya nufi hanyar fita daga cikin ɗakin.
Daddaɗan ƙamshin turarensa shiya ja hankalin su Ummi da Hayatuddeen da kuma Raihana dake falon suka dawo da kallonsu garesa, "Wow Hamma Saifuddeen ka ganka kuwa? Wallahi Hamma na baka taɓa yin kyau irin na yau ba!!".
Hayatuddeen yafaɗa cikin santin kyawun da yaga hamman nasa yayi.
Murmushine ya bayyana akan fuskar Saifuddeen tare da duban Ummi cikin body language ɗinsa yayi mata alama akan wai maganan da Hayatuddeen yafaɗa gaskiya ne?
Dariya Ummi tayi tare da cewa.
"A kullum a koda yaushe kai kekyawa ne koda bakayi wonkaba bare kolliya.
to ya kake zato idan kayi kwalliya to sai kayi kyau tamkar balarabe.
kaga kenan sharrin Hayatuddeen ne kawai dama tuncan kai kyakkyawane!"
Dariya gaba ɗayansu suka sanya banda Saifuddeen wanda shidai saidai yayi murmushi.
Cikin yabawa da kyawun da yayi Raihana tace.
"Hammana wallahi kayi kyau sosai".
murmushi yayi mata tare da yi mata alama kan cewa ya gode, Hayatuddeen kuwa cikin azarɓaɓi ya ciro wayarsa hoto yashiga ɗaukan Hammannasa yana me cewa ya samu na sawa a status da kuma Instagram.
jin haka Raihana ta amshi wayar tare da yi musu hoto shida Ummi da Raliya data shigo yanzu. Sunyi kyau matuk'a duk suna murmushi Ummi ta d'an roggofo kanshi.

Cikin body language ɗinsa yayiwa Ummi bayanin inda zaije, fatan Alkhairi Ummi tayi masa tare da cewa.
"Adawo lafiya".

Har bakin mota Hayatuddeen ya raka hamman nasa yayinda da kansa ya sauƙa akan kujeransa ya shiga cikin tsaleliyar motarsa ƙiran mercedes benz, agidan baya ya zauna sannan Hayatuddeen ya sa mishi weelchair d'insa a but yayinda Sule driver ke tuƙasa...

Tana gama shafa mai ta ɗauki tsadaddiyar hodan ta ta goga akan fuskarta, tana gama shafa hodan ta ɗauki black eye pencil ɗinta ta goga acikin manya manyan idanunta dake matuƙar gigita masu kallonsu, pink lipstick ta goga akan ƴan ƙananun laɓɓanta, yayinda tayi amfani da Mascara wajen miƙar da tulin eye lashes ɗinta, ita ba mace bace wanda take da yawan cika meckup akan fuskarta hakan yasa bata ƙara komai akan fuskarta ba bayan wannan ɗan kwallian da tayi.
Wani haɗaɗɗen lace wanda yaji dinkin riga da sket maroon colour wanda keda ratsin golding ash ta sanya, sosai kayan suka amshi jikinta inda sket ɗin ya bayyana haɗaɗɗiyar surar jikinta da kuma cikakkun hips ɗinta, parking dogon gashinta tayi atsakiyan kanta tare da zama akan stull ɗin mirror tashiga tsantsarawa kanta ɗaurin ɗan kwali, wani irin haɗaɗɗen ɗauri tayiwa kanta wanda yaƙara bayyana kyawun shigar nata, wata ƴar siririyar sarƙa golding ash ta sanya awuyanta tare da liƙa ɗan kunnensa me kamar manne akunnenta, wani takalmi me tsananin tsini da kyau wanda keda kalan lace ɗinta ta sanya aƙafafunta tare da ɗaukan wani vail shima maroon colour ta yafa ajikinta, baƙaramin kyau Zaleeha tayi ba ita kanta yau kyawunta ya ɗauki hankalinta, turarenta dake rikita maza ta fesa tare da ɗaukan haɗaɗɗiyar hand bag ɗinta me kalan kayanta ta riƙe ahannunta, wayarta tariƙe aɗayan hannun nata tare da car key ɗinta kana ta nufi hanyar fita daga cikin ɗakin, cikin nutsuwa take taku ƙwas-ƙwas hartakawo cikin falon mahaifiyartata, Mama dake zaune ta haɗe fuska tana ganin Zaleeha taji ranta ya sake, kallon Zaleehan tashigayi tana me godewa Allah daya bata wannan kyakkyawar yarinyar, lallai Zaleeha nada kyau irin nagaban kwatance, cikin nutsuwa Zaleeha tadubi Maman nata tare da cewa "Mama ni zanje (Jonapwd) saina dawo".
Tsuka Mama tayi tare da sake duban Zaleehan zata iya rantsuwa kyawun da Zaleeha tayi yau na dabanne amma abun haushin wai ba wajen wani hamshaƙin billionaire zataje ba wai gidan Nakasassu zata cike da ɓacin rai Mama tace.
"Yanzu akan zuwa wajen waƴancan Makafi da guragunne zaki wani caɓa ado kamar wata mezuwa gasan kyau na duniya?".
Baki Zaleeha taturo gaba tare da shagwaɓe fuska zatayi magana kenan Mama tace "Da halla ni ɓacemin da gani, ai dai indai wannan banzan aikin nakine kin kusa dainashi, don kuwa natabbata Abdussalam bazai bari kici gaba da wannan aikin ba don shi nasan awajensa aikinnan ƙasƙantacce ne".
Murmushi kawai Zaleeha tayi tare da sakai ta fice daga cikin falon, da kallo Maman nata ta bita aranta tana mejin wani sabon buri na ƙara ɗarsuwa acikin zuciyarta, don ayanzu tunaninta ya fara haurawa sama don kuwa har Abdussalam ɗinma tanaga Zaleeha ta zarce ajinsa.

Ita kuwa Zaleeha tana fita, tayi kicibis da Ya Habu,
cikin had'e fuska yace.
"Kina dai sane haramunne in mace baliga zata fita ta zabga irin wanna turaren naki mai shegen k'amshi, na hanaki yafi a k'irga amman da yake kunnen k'ashi gareki kink'i ki bari ko?."
ya k'arishe mgnar cikin zaro mata ido.
cikin yin rau-rau da ido tace.
"Ya Habu bazan sake ba."
kwaffa yayi kana ya wuce yayi cikin gida.
Motarta ta shige, maigadi na buɗe mata gate ɗin gidan ta cilla motarta kan titi. Cikin nutsuwa take murza steering motar tata yayinda daddaɗan ƙamshin turarenta ya cika gaba ɗaya motan.

Hancin motartane ta kunno kai cikin gidan nakasassun inda ta tsaida motar a parking lot, daga can wani babban falo kuwa nakasassune acike sun shirya tsab suna me jiran zuwanta.
Cikin nutsuwa take takunta ƙwas-ƙwas yayinda takun takalminta ke bada wani sauti, saura bai wuce taku biyu ta samu kanta acikin babban falon ba taji wani irin faɗuwar gaba ya rusketa, take taji wani irin iska na shiga jikinta, addu'a ɗauke abakinta ta sanya ƙafanta acikin falon, mutanen dake zaune da waƴanda ke gani da waƴanda basa gani tuni sun shaida da zuwanta saboda jin sallamarta da sukayi, waƴanda basaji kuwa hancinsu ne yasanar musu da zuwanta tahanyar shaƙan daddaɗan ƙamshinta, cikin mutumtawa haɗi da rashin ƙyama Zaleeha ta gaishe da kowannensu, Ishaq ne yashigo cikin falon fuskarsa ɗauke da murmushi yace "Sannunki da zuwa Hajiya Zaleeha!".
Murmushine yafaɗaɗa akan fuskar Zaleeha cike da kulawa tace.
"Yauwa Malam Ishaq ya fama da jama'a?".
Da. "Alhamdulillah ya amsa mata alokacin dayake ƙoƙarin zama akan kujera tare da gyara rik'on da yayiwa system d'inshi da wayarshi. Sosai ƙwazon Ishaq ke burgeta saboda yana aiwatar da komai nasa tamkar wanda yake gani.
Chapter 85 · 0% Book details