Sashe 71
Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dawowarta daga wajen aiki kenan,
aɗan gajiye ta shigo cikin haɗaɗɗen ɗakin nata, jakar dake hannunta ta aje gefe tare da soma rage kayan jikinta, saida ta cire komai na jikinta sannan ta sanya wata kekyawar rigan wanka baby pink colour, dogon gashinta ta ɗaure da ribbom sannan ta wuce kai tsaye zuwa toilet, wanka tayi da sabulunta me daɗin ƙamshi kana ta ɗauro alwala, kasancewar ankusa ƙiran sallan Magriba, zama tayi agaban tangamemen dressing mirror'n ta wanda gabansa ke cike maƙil da kayan shafa masu kyau da tsada, body lotion ɗinta tashafa wanda gaba ɗaya sanyin ƙamshinsa ya game ɗakin, yanayin yanda takejin kanta agajiye yasanyata miƙewa tsaye, ahankali ta ƙarasa gaban drawer ɗinta wanda cikinsa ke shaƙe tam da kayan sawanta masu kyau da tsada, wanda ita kanta batasan iyaka yawan suturun sawanta ba, wata ƴar doguwar riga marar nauyi ta zaro wanda yake daga ɓangaren kayanta marassa nauyi, rigar irin mai taushin nanne wanda takebin jikin mutum ta lafe, da fararen stones aka ƙawata wuya da hannayen rigan, wanda hakan kuma ba ƙaramin ƙarawa rigan kyau yayi ba, sosai rigan ta amshi jikinta ta lafe, hakan yasa kyakkyawan body structure ɗinta bayyana, wanda da ace lafiyayyen Namiji zai gani to fa tabbas dasai ya rasa nutsuwarsa, jin anata ƙiraye ƙirayen sallan Magriba ne yasanyata zura wani dogon hijab ajikinta tare da shumfuɗa sallaya, koda ta idar da sallan magriba bata tashi akan sallayan ba har saida ta sallame sallan Isha, bayan ta tarin addu'ointa wanda mafi yawansu akan Saifuddeen ne, cikin sanyin jiki ta tashi daga kan sallayan tare da cire hijab ɗin ta ninkesa, kana tayi taku uku zuwa biyar ta isa bakin gadonta kwanciya tayi akan lallausan gadonda tare da jawo pillow ta matse a ƙirjinta, rumtse idanunta tayi da tsananin k'arfi tare da fesar da wani zazzafan numfashi me ɗan karen zafi yayinda takejin wasu zazzafan hawaye sun tsastsafo mata cikin jijiyoyin idanunta, cusa kanta tayi cikin hannayenta tanajin akowani bugu na zuciyarta da tunaninsa yake wanzuwa, ina yake!? a ina zan ganshi? wani hali yake ciki? sun kasheshi ko yana da rai? tana da buƙatar sanin waƴannan amsan fiye da komai ayanzu, gyara kwanciyarta tayi tare da buɗe idanunta, kan zanen pop'n dake mamaye saman ɗakin ta tsaida idanunta sun kad'a sunyi jazir cikin raunin murya take cewa.
"Ya Allah kasa ako ina yake yana cikin ƙoshin lafiya, in kuwa sun mishi rauni ya Allah ka bashi lfy!".
tafaɗi haka aɗan raunane, ahankali hawayen da suka cika idanunta suka samu daman gangarowa suka biyo ta gefen kumatunta, haƙiƙa zuciyarta cike take da son jin wani abu daga garesa, yayinda idanuwanta kuwa ke ɗokin sake ganinsa, tunaninsa ya matuƙar tsaya mata azuciya babu dare ba rana ko yaushe bata da sukuni bata fahimtar komai domin duk nazarinta da tunaninta a kanshi yake k'arewa,
sake muskutawa tayi ta gyara kwanciyarta akaro na biyu, kana ta lumshe idanunta da har yanzu suke ɗigan hawaye, da sauri ta buɗe idanunta tare da dafe ƙirjinta dake wani irin bugawa sakamakon tunowa datayi yanda
Yaran Dalla suka caka masa wuƙa abayansa, da ƙarfi ta rumtse idanunta tare da sakin kuka me cin zuciya cikin yanayi mai kama da sambatu tace.
"Ya Allah Kasa ba mutuwa yayi ba, Ya Allah ko sau ɗayane ka ƙara nunamin shi, ya taimakeni alokacin danafi kowa buƙatar taimako, Ya Allah kasa yana cikin halin nutsuwa aduk inda yake ya Allah ka kaddara saduwa ta dashi koda godiya in mishi!!".
Da sauri ta d'ago kanta jin k'anwarta Zahira na cewa.
"Dan Allah Anty Zaleeha, ki bar irin wannan kukan, kici gaba da yimishi addu'a insha Allah addu'arki zata riskeshi."
cikin kuka ta kife kanta bisa cinyar k'anwar tata wacce ita kad'aine tasan da batun. Cikin kukan take cewa.
"Bai sanniba, bai tab'a ganinaba cikin taron maza dake wurin kab babu wanda ya kula da ni bare ya taimaka min dan tsoron Dalla da sukeyi,
sai shi d'aya ya zame min Garkuwata, kuma sun mishi illa gashi ban san ina zan sake ganinshi ba."
shafa kanta Zahira tayi tayi tare da kwantar mata da hankalin.
A haka tacigaba dayin kuka ƙasa-ƙasa tana me fidda shashsheƙa da haka har bacci ɓarawo ya ɗauketa.
***
A gidansu Saifuddeen kuwa.
Ummi ce zaune afalo tayi jigum yayinda tunanin ɗanta kuma farin cikinta Saifuddeen ke kwance acikin ranta, dare da rana bata da wani addu'a sai na nema masa lafiya awajen mai duka, Raliya ce da Adda Rahma da tazo musu tunda safe,
sune suka tafito daga cikin kitchine, hannun Adda Rahma ɗauke da goran ruwa me ɗan sanyi, jingina bayanta tayi da jikin ƙofar kitchine ɗin tare da kafe Ummin nasu da ido, wani irin tausayin kansune ke ƙara ɗarsuwa acikin ranta a kullum, haƙiƙa SAIFUDDEEEN shine komai nasu, Allah Ne gatansu amma Saifuddeen babban jigone agaresu wanda kuma shine gaba ɗaya farin cikinsu.
Raliya kuwa da sauri ta k'araso gefen Ummi ta zauna, ita kuwa Adda Rahma cikin sanyin jiki ta fara d'aga k'afafunda da suka kumbura sabida tsufan cikin jikinta da kyar take tafiya bisa dukkan alamu cikin ya cika wata bakwai ya shiga na takwas a hankali ta ƙaraso cikin falon tare da sanya hannu taɗan taɓa Ummi wanda tayi nisa acikin duniyar tunani.
Ummi kuwa jin sauƙan hannu akan kafaɗanta ne yasanyata ɗagowa da sauri ta kalli wanda ya dafatan, da fuska Raliya tayi arba wacce ta marairaice tuni idanunta sun tara k'walla.
A hankali ta kuma juya ganinta zuwaga Rahma wacce ta fara mgna cike da sanyin murya haɗi da tausayawa tace.
"Dan Allah Ummi kidaina sa kanki adamuwa, Ummi idan kika kasance acikin damuwa akullum natabbata Saifuddeen idan yasani bazai taɓa yafewa kansa ba,
Ummi kinfi kowa sanin Saifuddeen sam bayason damuwarki, dan Allah Ummi kidaina sanya kanki adamuwa Saifuddeen addu'a yake nema daga gareki damu baki d'aya , sannan Ummi kada kimanta addu'an uwa yana da matuƙar tasiri akan ƴaƴa, please ki tausaya mana ki dage da yi mishi addu'a!"
Wani irin dogon Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da ɗan rausayar da kanta gefe tana mai son maida hawayenta amman ina ta gaza tuni sun zubo mata bisa k'unshinta, haƙiƙa shiga damuwa yazame mata dole, tunda ɗanta mafi soyuwa agareta yana cikin wani irin mawuyacin yanayi a hankali tace.
"Ina yimasa addu'a akullum akuma ko yaushe Rahma, sannan nakasa ɓoye damuwata akansa, ke uwace Rahma kinsan irin tsananin so da kuma ƙaunar dake tsakanin ɗa da uwa, wannan ƙaunar fiye da itace ke tsakanina da Saifuddeen, kuma kisani ko ban nuna damuwata afili ba to tana nan kwance acikin zuciyata tana cina!".
ta ƙare maganar murya araunane.
Hawaye ne suka cika idanun Raliya har suna kwaranyowa kan fuskarta yayinda itama Rahma ida nunta suka cicciko da hawaye,
tabbas idan harsu da suke ƙannansa suna tsananin jin ciwonsa ajikinsu, sannan kuma suna tsananin tausaya masa, basu da wani fata daya wuce samun sauƙinsa, to ya Ummi da take mahaifiyarsa zataji? ƙoƙarin maida hawayen da suka cika idanunta tasomayi tare da sadda kanta ƙasa murya asanyaye tace.
"Kiyi haƙuri Ummi In sha Allah Saifuddeen zai samu lafiya, zai warke yazama cikakken mai lafiya, Saifuddeen d'inmu shine jigo kuma farin cikin mu, In sha Allah ko dan wannan Allah zai dubemu ya bashi lafiya, don bamu kaɗai keda buƙatarsa ba mutane dayawa daga waje suna da buƙatarsa!".
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Allah Yasa!".
Da "Ameen".
Raliya ta amsa kana ta miƙe ta wuce ɗaki don duba Adam yaron Adda Rahma dake bacci koya tashi.
k'arfe biyar dai-dai na yamma Zaleeha ta shigo cikin gidan radio vision FM gombe. Driving takeyi cikin tsananin nitsuwa a hankali take tafiya,
yayinda take sa hannunta tana goge sirarun hawayen dake zubo mata time to time.
parking tayi kana ta fito kai tsaye d'akin watsa shirye-shiryen su ta nufa,
a bakin k'ofa tayi cikibis da Raveel wanda ya gama gabatar da shirinsa kenan ya fito da nufin zai kirata domin tazo ta gabatar da program d'inta.
Murmushi yayi tare cewa.
"Yar halas kink'i ambato yanzu nake kiranki a raina."
sam hankalinta da nitsuwarta basa jikinta bare ta kulashi ratsawa gefenshi tayi a bakin k'ofar shiga ta cire takalmanta masu d'an karen tsini,
kana ta zura silipas dake wurin sannan ta kutsa kai cikin d'akin.
Shi kuwa Raveel jingina yayi da jikin gini ya zuba mata idanu yana kallonta ko k'ebta idonshi bayayi koda ta shiga ta meda k'ofar ta rufe sai ya lik'a idanunshi kan takalmanta.
Ita kuwa Zaleeha tana shiga cikin d'akin watsa shirye-shiryen nasu wani azabebben bege da shauk'in son ganin fuskar da ta tab'a gani sau d'aya ya d'arsun mata a rai.
A hankalin ta zauna kan kujerar zaman nasu,
Kana ta ɗauki wannan ɗan abu da suke sawa a kai ta saka wanda yake isa har zuwa kan kunnensu ta jawo ta sank'ala.
Ji tayi zuciyarta na sarrafa gangar jikinta,
madadin ta gabatar da program nata mai taken Babu nakasshe sai rago,
kawai sai ta tsinci kanta dafuskantar na'urar tasu da kyau tare da zab'o wak'ar da take jijjiga sirrin zuciyarta.
can cikin gidan Radio kuwa cikin mmki managernsu ya kasa kunne a na'urorinsu na tantance abinda suke watsa jin sautin sassanyar wak'ar da Zaleeha ta sake, dan ya hango shiganta, da sauri ya kalli agogon dake fuskar wayarshi ganin ai lokacin gabatar da shirinta har ya shiga da 3 minute.
Da sauri ya jingina jikin kujerar jin ta d'an rage sautin wak'ar.
Yayinda mutanen cikin garin gombe da kewaye ke jinta dan shirinta yanada matuk'ar farin jini,
musamman a wurin nakasassu, wanda yanzu hakama duk inda nakasasshe yake yana jinta sanin lokacin nasune.