Sashe 54
Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Tana isa gidan Maryam kaitsaye bedrrom ɗinta ta wuce,
Maryam dake zaune gaban mirror tana kwaliyya ganin Zaleehan ne ya sata juyowa da sauri sai kuma tayi shiru ganin ta zauna ta kife kanta bisa cinya tana kuka mai sanyin sauti,
da sauri ta dawo kusa da ita cikin kaɗuwa tace.
"Meya faru ? Meya saki kuka gaya min dan Allah hankalina ya tashi ,Baba malam ne ba lfy ko ya Ahmad."
kanta ta ɗan nago ta kalli yayar tata cikin kuka tace.
"Ya Aminu yana nanne?."
kai ta jujjuya mata tare da cewa.
"A a ya fita ya kai su Abdul makaranta, amman zai dawo yanzu."
jin haka ta miƙe ta koma bakin ƙofa, rufe ƙofar tayi tare da gyara labulen sannan ta dawo ta zauna cikin kuka ta bawa Maryam labarin tun daga shagala da kallon Saifuddeen da tayi har ta kai ga buge motar Dalla da binsu da sukayi da dukansu da Saiddeen yayi da kuma dukan da suma sukayi mishi.
Gaba ɗaya jikin Maryam rawa da tsuma yakeyi tuni itama hawayen take zubdawa murya na rawa tace.
"Shike nan mun shiga uku Zaleeha Dalla kuma, shike nan sun kashe yaron nan, to ke me kikayi a kai?."
wasu sabbin hawaye ne suka kwaranyo mata kana taci gaba cewa.
"Daga wurin ban dawo gidaba police station name wuce, naje na shigar da ƙara na faɗa musu komai, amman da yake basu da imani ƙasar nan ba'a bin gsky sai suka zagayeni a wurin babban cikin su yace min wai,
na kiyayi kai na na haɗiye wannan maganar kada na kuskura na bari wani yaji koda da wasane,
yace min wai yanzu dai yana ƙarƙashin kulawarsu in banbi umarninsu wallahi zasu kasheshi, kuma nima zasu bawa Dalla adireshina, kuma wai duk wanda yayi yunƙurin ɗaga zancen zasu kasheshi."
kuka sosai taci gaba dayi tare da cewa.
"Kuma sai da suka haɗoni da police ɗinsu guda ɗaya ya kawoni har ƙofar gidanmu, yace min.
Duk abinda zanyi suna bibiyata kada na yarda na kuskura na bar koda alama ɗaya da a gida za'a gane akwai wata matsalar har a kai ga tambayata, muddin nayi yunƙurin zuwa wani police station zasu sanarwa Dalla komai ya tura yaranshi su kasheshi." ɗan zagaitawa tayi tare da cigaba da cewa.
"Wallahi ni ba don raina ba sai dan tseratar da ranshi yasa naketa boye abun a cikin raina har kwana biyu, ina tsiron kada su kasheshi, gashi naje asibitoci da dama na bincika babushi babu dalilinshi, na koma bakin sitadiyon ɗin ya kai sau biyar to wa zan tambaya ,jiya wuni nayi ina yawo, kuma ko yau da safe sun kirani sun gargaɗeni wai bani yar jaridaba in na kuskura maganar nan ta fito to wallahi kasheshk zasuyima suga ta zancen sunce min motata ince ƴan kalarene suka fasamin amman kada in kira sunan Dalla.
Adda Maryam ya zanyi ina zan shiga in ganoshi ina zan saka raina da nasa mu tsira daga sharrin Dalla da yan sandda ya zanyi in bashi kariya koda rabin yadda ya bani kariya ne! bani da konciyar hankali da nitsuwa bana iya bacci bana iya cin abinci, duk da sun gargaɗeni kada fa na sake damuta ta baiyana."
wannan al'amarifa ya firgita tunanin Maryam ya girgizata itama tuni hawayen takeyi sabida rauninta yama fi na Zaleeha cikin tausayawa tace.
"Kin gayawa Baba Malam ne?."
kai ta jijjiga tare da cewa.
"A a ban gaya mishiba kin san Baba Malam muddin na gaya mishi zai tada zancen zai sa Ya Aminu cikin mgnar su kuma zasu iya kasheshi, ni kuma bana son su cutar dashi ina son rayuwarsa fiye da tawa sabida shi Garkuwane magarcine ya ahlinshi zasuji tunda ni da bai sani bama ya zamemin Garkuwa inaga ahlinshi." sai hawaye shar-shar na bin fuskarta a hankali taci gaba da mgna wai dan kar Ya Aminu ya dawo ya jisu.
"Amman dai na gayawa Baba Malam ɗin cewa akwai wani mara lfiya yana buƙatar addu'a,
yace kuma in sha Allah zai sashi a addu'a, Mama kuma dana gaya mata wai ita ni take jiyewa cewa tayi muddin na gayawa wani bata yafe ba,
ni kuma in ban gaya mikibs na damuwar zata iya fasa min zuciya."
cikin sanyi Maryam tace.
"Kinyi dai-dai karki gayawa kowa,
sabida bisa dukkan alamu yana asubiti kuma duk inda yake zasu sani, kinga muddin kika ɗaga mganar suna iya kasheshin,
gatan da zamuyi mishi itace addu'a domin annabi yace addu'a'u saiful muminin mu zama garkuwarshi da addu'o'i in sha Allah bazai basu damar cutar dashi ba, ki dena kuka ki yawaita mishi addu'a kuma kici gaba da zuwa asibitoci, ki kuma koma police station ɗin ki ce su gaya miki asubitin da suka kaishi."
sosai taji daɗin shawarwarin ƴar uwar tata haka anan tayi wonka ta shirya, ta fita daga nan fa tayi ta bin asibitoci duk da anata kiranta wurin aiki,
sai da tayi sallan azahar kafin ta tafi kaltingo domin yin hira da Nakasassun wannan yankin.
Tun k'arfe biyu na rana take cikin garin kaltingo, sai k'arfe hud'u na yamma ta gama tattara rahotanninta,
kana ta kamo hanyar gombe, tana gab da shiga cikin garin taji wayarta na suwa,
ido ta d'an lumshe kana ta bud'e su tare da meda hankalinta kan draving d'in da takeyi,
wanda sanyi A,C da k'amshi ya cika motar kana sautim wak'arnan ta. Soyayyar dake raina bazan sauya ra'ayiba, wacce akewa taken
*Da ƙauna ta biki jiki an komawa wada ƙanwa*
hannu tasa ta k'ara volume d'in gaba d'aya Kasan cewar a gidan radio ensu na vision FM Gombe aka saki wak'ar wanda nanne ma'aikatan da take aiki inda take gabatar da program d'in ta mai taken *Mushsƙata da kuma Babu nakasasshe sai rago* wanda take hira da nakassu dan jin yanayin da suke rayuwa.
Kamar yadda yanzuma aikin ne ya kaita kaltingo wata k'aramar hukumar jihar Gomben.
kai take d'an rausayawa tana bin sautin wak'ar,
tamkar itace ta raira wak'ar, still kuma idanunta zubda zazzafan hawayen da duk sanda ta tuno Saifuddeen sai ta zubdasu, wanda kusan hakan yabi jikinta a cikin kwana biyun nan tayi kukan da itama da kanta batams san adadinshi ba,
taje sitadiyon yafi k'afa takwas hakama taje asibitoci da dama dan ko zata samu lbrinshi,
ganin ba lbri yasa yau da safe taje police station d'in nan amman sai suka nuna basuma san da wannan zancen da take musuba,
kuma abun mmki da tsoro bata ga police officers d'in da ta samu a wannan ranarba ko guda ɗaya, shiyasa gaba ɗaya ta rasa tudun dafawa.