← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 116

Sashe 48

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Hargida police d'in da aka had'ashi da Zaliha yakaita, abakin makeken gate d'in gidansu tatsaya,
kana yafita amotar tayimasa godiya yatari abin hawa yatafi,
dasauri tafita takoma gefen driver tunkan takarasa zama tadanna horn dan har'alokacin amatukar tsorace take,
da gudu maigadi yataho dan jin yadda aketa danna hon ba sassauci da sauri ya wangale mata get d'in,
da sauri ta kutsa hancin motarta cikin farfajiyar gidan nasu da gudu,
asakar farfajiyar gidan tayi parking tafito,
maigadi nakokarin rufe get
wata lafiyayyiyar mota mai azabar kyau da tsananin shek'i ta danno hancinta cikin gidan,
Zaliha kuwa har tajuya zata shige cikin gidan,
ganin shigowar motar yasata tsayuwa, yayinda gaba d'aya zuciyarta da tunaninta ke can wurin kelyawan mutumin daya taimaketan
har aka faka motar tana nazari asannu akabude marfin motar yazuro kafafunsa yafito,da murmushin sa yanufi inda Zaliha take,
itako kwabe fuska tayi tareda langwab'ar dakai gefe,
yakaraso inda take waro idanu yayi ganin galashin motarta afashe cikin mamaki
yace.
"Hatsari ki kayine Zaliha?." cikin muryar shagwaba ta tura baki tare da yarfa hannu tace.
Ya Ahmed ba y'an kalare bane na taddasu a hanyata ta dawowa sunata fad'a shine suka fasamin gilashin mota, badon a mota nikeba nima da sun fasa min kai."
takarasa maganar kamar zatayi kuka dan tausayin Saifuddeen da ta baro suna shirin kashewa,
dasauri Ya Ahmed d'in nata yace.
"Ina dai ke basu ji miki rauniba ko?."
kai tagyad'a masa tare da cewa.
"Amman dai ai sunyiwa motata illa ai."
cikin kula da shak'uwa yace. "To Alhamdulillahi da Allah yasa akan motace ba kan 'yar kekyawar k'anwata aka fasaba,
gobe ida Allah yakaimu zamuji kizabi motar da kikeso.
Amman fa mai sauk'in kud'i Hajia na sanki baki san zafin neman kud'iba sai son ayi ta kashesu ba sassauci."
bayanshi tabi tare da cewa.
"To Ya Ahmed duk yadda kace hakan za'ayi."
shi kuwa Ahmed motar tata ya d'an kalla tare da cewa.
"Wannan d'in za'a gyara sai a saida ta in cikata miki ki samu sabuwa koda wacce bata kai wannanba,
ki samu ta zuwa aiki."
tsalle tarikayi tareda rike hannunsa,
tana fad'in.
"Na gode Ya Ahmed Allah ya k'ara bud'i rabbi ya k'arawa Baba Malam daraja da lafiya da tsawon rai."
murmushi yayi cikin tsananin jin dad'in addu'arta ga mahaifin nasu ya rik'o hannunta suka shige cikin gida.
Wani babban parlour suka shiga wanda yake wadace da tsananin tsabta, wasu manyan kujerune na alfarma ke zagaye da fad'in parlour kana sai wani tattausan carpet mai tsananin taushi sai can gefen dama wasu manyan kanta guda biyu da suke cike da tarin Qura'anai da sauran littafai kama daga na addini dana boko harda su baibul wanda.
sai wani babban tv dake manne da jikin ginin, kana gefen hagu kuma dinning area wanda yasha gyara,
sai kuwa wata kujera dake tsakiyar parlour wacce tafi kama data sarakuna sai wani stoll na glass dake gaban kujerar.
wani dottijone mai tsananin kyau fari k'al k'al dashi yake zaune bisa kujerar nan ta tsakiyar parlour, bisa dukkan alamu alwala yayi yanzu, duk da anyi sallan isha koda yake hakan baya rasa nasaba da kasan cewarshi baya zama ba tare da alwala ba.
zaune yake kana ya mik'e k'afafunshi bisa stoll d'in hannun shi had'e wuri d'aya yana murzasu kana yana d'an karkad'a k'afafun nashi,
a hankali yake motsa labbanshi bisa dukkan alamu tasbihi yakeyi kasan cewa d'abi'arsa ce duk abinda yake bashi hanashi ambaton Allah.
can gefenshi kuwa wata kekyawar matace mai d'an ma dai-dai cin tsawo da jiki, bona ce ta jona jikin soket d'in wuta kana tasa wani turaren wuta mai dad'in k'amshi,
labulayen parlour ta sassake sabida yanayin hazo,
kana ta rage gudun fankan, sannan ta kashe A, C gaba d'aya.
cikin nitsuwa dottijon ya juyo ya kalli k'ofar parlour inda yaji muryar yaran nashi,
amsa musu sallamarsu yayi tare da basu izinin shiga.
a tare suka shigo gabanshi suka zauna cikin cikar tarbiya sukace.
"Barka da dare Baba malam."
cikin son yaran nashi yace.
"Allah ya muku Al'barka."
cikin tsananin jin dad'i Ahmed yace.
"Amin Amin Baba malam mun gode."
murmushi yayi dan yasan yadda Ahmed ke tsananin jin dad'i in ya mishi addu'a,
ita kuwa Zaliha cikin nitsuwa sanin a gaban Baba malam suke ta kalli Hajia Aisha mahaifiyar Ahmed kenan wacce suke kiranta da Mamy, cikin logob'ar da kai tace.
"Mamy yunwa nakeji."
cikin nitsuwarta ta matso inda suke kana tace.
"Ke kinada tsiya ne komai aka dafa kice bai mikiba, sai kije kitchen ki dafawa kanki dan ni dai tuwo nayi."
a hankali ta mik'a tare da cewa.
"Baba malam saida safe."
ido ya d'an juyo ya kalleta kana yace.
"Allah ya bamu Al'khairi kada ki konta bakiyi al'wala da adduba kada kiyita jin kid'e-kid'enan da kike sawa a gidan radionku."
cikin sanyi tace.
"Toh". kana ta juya ta fita.
Ahmed kuwa murmushi yayi sanin an d'aureta tunda an hanata shan kid'a,
nan sukayi ta hira da mahaifinshi da mahaifiyarshi,
ita kuwa Zaliha kai tsaye parlour Mamanta ta nufa,
gefen wata mata mai d'an k'iba da alamun rashin fara'a a fuskarta gefenta ta zauna da gani matar k'abilace ba hausa fulani bace sam bata da fara'a
cikin sauk'e numfashi tace.
"Mama barka da dare."
murya can k'asa a dak'ile tace.
"Sai yanzu kika dawo ko can d'akin uwar taki kika je."
konciyarta ta gyara bisa 2 str kana tace.
"Nida ya Ahmed ne kuma wurin Baba malam muke."
kai ta gyad'a kana tace.
"To tashi kije kici abinci Zulaihat ta muku awaran kuskus."
jin haka ta mik'e da sauri ta nufi dinning table, gefen washing hand baby ta nufa hannunta ta wonke sannan tazo ta zauna tanaci suna d'an hira da Mamansun.
Kad'an ta ci ta mik'e jiki a mace ta nufi d'akinta
tazo gab da bakin k'ofarsu Zaheera taji Zulaihat nata hayaniya alamun tana tarfawa Zaheera rashin kunya,
kai ta kauda ta wuce d'akinta dan bata cikin yanayin jin dad'i bare konciyar hankali.

Tana shiga ta cilla woyoyinta bisa gadonta kana ta zame ta durkusa a k'asa tare da kife k'irjinta bisa gadon pillow ta jawo tare da d'aurashin kanta a hankali ta rumtse idanunta sai kuma tayi saurin bud'esu da sauri sabida ganin tamkar yanzu ake sokawa Saifuddeen wuk'a a bayanshi kife kanta tayi cikin pillow ta saki wani irin zazzafan kuka mai sanyin sauti, ta jima tana kukan a hakan tayi baccin da baifi 45 minutes ba ta fara mafarki tana jujjuya kai da karfi ta saki ihu tare da cewa.
"Mu gudu kada su kasheka kazo mu gudu wayyo ya Ahmed sun kashe minshi."
sai ta kuma mik'e da sauri sabida farkawan da tayi,
kai ta kife bisa gadon tana wani irin kuka mai cike da tausayi da rauni,
sai ta kuma mik'ewa da sauri kai tsaye bathroom ta nufa al, wala tayi kana ta fito nafilfili tayi tayi wanda duk cikin sujjadanta shi take yiwa addu'a ranar da a haka ta kwana batayi bacciba wonkan da yake al'adar rayuwarta ma kafin tayi bacci amman yau bata Toshiba.
Chapter 48 · 0% Book details