← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 116

Sashe 12

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Leda biyu ya kuma sarowa cikin sa'a kafinma ya isa wurinsu rabin ledane ya rage,
nan suka d'auka to ganin bai ishesu bane sai ya kuma komawa ya dauko leda biyu.
kai tsaye wurinsu ya nufa
nan suka k'ara guda uku.
sun bashi kud'inshi ya juya zai tafi kenan sai yaga wannan dottijon mai keke wanda suka tab'a had'u a shagonsu Hisham kusan tsawon sati d'aya daya gabata kenan,
still yauma kamar ranar dottijon ya kalleshi tare da mik'o mishi banduran leda guda hud'u irin kitika-kitikan ledojin da in an sayi koda katifan jarirai zai iya shiga ciki kai hatta gadon jariran zai iya shiga cikin ledan,
kana in zaka sai setin kayan sanyi dana abin goyo dasu rigunan yara dasu setin mayukansu da takalma duk leda d'aya zata iya d'aukansu dan irin manyan ledodi bak'ak'ennan ne,
sai kuma masu binsu sai masu zane bak'i da yellow nan,
cikin alamun gajiya dottijon yace.
"Yauwa yarona dan Allah mik'a musu."
da sauri ya ajiye botikin nashi kana ya amshi ledodin ya juya ya mik'awa Jabeer dake kusa dashi,
sai kuma ya kalli ogan nasu ganin yanayiwa dottijon mgna.
"Yauwa Baba bello ya a bamu ledodin na dubu hud'u dan na dubu ukun basa isanmu sabida yanzu iyayen yara sun fara sayayyan kayan sallan yaransu ga masu haihuwa nan nata zuwa ga yan mata da samari masu sayan kayan aure."
murmushi dottijon yayi kana yace.
"Masha Allah ai haka mukeso domin cini kinku shine namu,
domin sai kunyi ciniki da muyi tunda mu duk kasuwa abin mune k'arshen saya dole sai an gama sayyaya ake tuna sayan leda."
Jabber ne ya murmusa tare da cewa.
"Gashi kuma kasuwar taku da yawan al'barka take duk mai saida abu dole sai ya sai naku."
murmushi sukayi baki d'aya kana Alhaji Adamu ya mik'owa Saifuddeen 4k d'in sannan shi kuma ya mik'awa dottijon amsa yayi tare da sasu a aljihu sannan ya kalli Saifuddeen da kyau kana yace.
"Ngd matuk'a yarona Allah ya maka al'barka."
Amin Amin duk suka amsa harda Saifuddeen daya amsa a zuciya,
Jabeer kuwa cikin tsokana yace.
"Kai Baba bello wannan fa balarabene."
ba tare da mmkiba Dottijon yace.
"Yoh ai ba musu in akace hakanma."
Tahir ne dake gefe ya d'an bugi k'eyan Jabeer kana ya kalli Dottijon yace.
"K'aryafa yakeyi maka baba bello shi ba fulatanine kawai dai kurmane."
da sauri Baba bello ya kuma kallonsa cikin tausayawa yace.
"Allah sarki bawan Allah dama ance ko wani d'an adam tara yake bai cika gomba, wato kai kuma nan tawayar ka take."
sai ya kuma kalli Saifuddeen da kyau sai ya sauk'o bisa keken nashi.
hannunshi yasa ya jawo wuyan Saifuddeen yadda zai iya ganin tsakiyar kanshi ido ya zura mishi tsawon 38 minutes shi kuwa Saifuddeen shiru kawai yayi ya bashi kai d'in,
bayan ya gama dubawa yace.
"Masha Allah lallai kam wannan kan naka zai d'auki nauyin abu da yawa,
domin magergerar gashi tushe ukune a kanka wanda ba kowa Allah ke yiwa wannan halittarba."
shiru sukayi yayinda shi kuwa Dottijon ya kalli Alhaji Adamu tare da hawa kekenshi kana yace.
"Akwai al'khairi cikin yin mak'otaka dashi."
daga nan yaja kekenshi ya tafi,
shi kuwa Saifuddeen d'aukan botikinshi yayi tare da bin bayanshi,
yana ganinshi ya nufi shagon masu d'inka hijabannan da alamun suma a wurinshi suke sayan leda. Har zaibi bayanshi sai kuma yaga ana kiranshi a shagon alhaji ishaq haka yasa ya nufi can.
Pure water suka sassaya bayan sun bashi kud'in ya juyo kenan sai yaga Dottijon nan tuni ya bar wurin,
to sai kawai yaci ga da zageye da ruwan,
amman sai cinikin yayi d'ib tun bayan azahar ya d'aukosu amman har la'asar basu k'areba,
to saida aka kira sallan la'asarne sai kuma akayi ta saya ana al'wala nan ya samu wannan leda biyun suka k'are.
To koda aka idar da salla ya gaji sai ya koma layin shagon ba mishkila ya zauna ya zuba musu idanu yana ganin yadda aketa seye da sayarwa yana kallon yadda suke ink'anta awunsu.
Ya d'an jima a wurin sai biyar dai-dai ya mik'e a ranshi yake cewa.
"Uhmm Saif tashi kaje ko leda d'aya ka samu ka saida kafin magrib ai yafi zaman mutuwar jiki da zuciyan."
daga nan yaje ya k'aro leda d'aya,
to kuma lokacin rana tayi sanyi ba ciniki sosai,
ya jima yana yawo kafin ya samu aka sayi gwara shida na arba'in kenan daga nan yaita zagayawa,
tuni ya gaji dan yau kusan wuni yayi bisa sawunshi,
saida magrib ta gabatone akayi ta saya nan ya saida kab sai gwara d'aya da ya bari na al'walanshi. Bayan yayi alwalan ne ya bawa Jabeer botikin ya ajiye mishi a shagonsu,
sannan ya fito bakin gate d'in fita kasuwar yana lissafin bag nawa ya saida a cikin ranshi yace.
"Alhamdulillahi leda goma cib na saida, ya rabbil izzati kayiwa wannan kasuwa tawa al'barka ya Allah ka jib'anci lamurana ka fad'ad'amin hanyar samu in samu damar tallafawa k'annena marayuwa da mahaifiyata da yayata da marayun yaranta,
bayan anyi sallan magrib d'inne ya dawo inda Salisu zaizo ya sameshi yana ko zuwa Salisu na isa,
yauma kamar jiya shi dai fura da nono yasha shi kuwa Salisu ya sai nama yaci.
daga nan sukayi sallan isha kafin suka kama hanyar Dukku.

Bayan sun isa wonka yayi ya canza kaya kana yazo yaci abinci,
sannan ya fita woje sugar ya seyo da madara da Lipton sai biredi d'aya.
kafin ya dawo duk sunyi bacci sai Ummi da Rahma.
Rahma ya mik'awa ledan kana ya zauna gefen Ummi data zuba mishi ido,
cikin kula tace.
"To kuma d'an dubu d'aya daka amsa d'inne zaka kasheshi a kanmu? buk'atunka zakayi dashi ba namuba ai dubu ukun nan zasuyi min sati ina cefene kullum d'aribiyar zata isheni cefenen dere da rana, tunda munada gari da shinkafa harda sauran taliya da mai da manja."
mik'e sawunshi yayi kana ya fara rubutu a k'asa yana bata lbrin ai ya fara sana'ar saida ruwa kuma Alhamdulillahi sana'ar tana gudu dan ya samu ribar 700 a wunin yau kawai.
Cikin tausayawa Ummi tace.
"To Babana ka dai nuna kai sana'ar tayi maka, amman ni tausayinka nikeji kaje kayita wuni a rana kana yawo da robar ruwa, amman Allah ya baka sa'a yanzu asusu zan saya zaka rink'a tara kudin in ka samu jari dai ka fara wata sana'ar kabar wannan."
cikin girmamawa da shak'uwa da tsantsar biyayya ya gyad'a mata kai tare da fara rubutu a k'asa yace.
"To Ummi na yadda kikeso haka za'ayi."
sai ya kuma kalli Hayatuddeen dake konce yayi pillow da cinyar Ummi ture kanshi yayi kad'an kana ya zame ya konta tare dasa kanshi gefen na Hayatuddeen da nufin wai zasuyi hira.
Amman ina tsananin gajiyar yawon daya wuni yanayi ne yasa tuni yayi bacci.
ganin baccin zai nisane yasa Rahma sa hannu ta d'an mari kumatunshi a hankali ya bud'e ido,
sai ya kuma kalli Ummi dake shafa suman kanshi da alamun bacci a idanunta.
cikin sanyi ya mik'e kana ya musu saida safe sannan ya kamo hannun Hayatuddeen da nufin suje d'akinshi su fara kwana tare amman sai k'ara mak'ale Ummi yakeyi hakan yasa ya barshi, yaje ya shiga kana suma suka shiga.

Still yauma kamar jiya cikin ikon Allah ya saida leda goma kamar jiya.
Koda ya koma ya samu tuni Ummi ta sai asusu ta zura mishi d'aribar din jiya dan ya sai musu kayan tea na d'ari da biredin d'ari kana ya bata sauran d'aribar d'in duk cikin ribarshi 700 d'in jiyan,
kana jarinshi kuma na nan. To Alhamdulillahi yauma haka ya samu kamar na jiya,
toh sai ya bawa Ummi duka kud'in tasa 500 a asusu 200 kuma ta d'auka ta ajiye dan 'yan buk'atunsu irinsu omo ko kud'in break d'insu Hayatuddeen da Faruq
haka dai lokaci yaita shud'ewa.

Duk randa Salisu ya basu kud'in balance kuma zai bawa bappa Ali 1k kana ya damk'awa Ummi 4k d'in.

Alhamdulillahi rayuwafa ta fara juyawa kasuwa na tafiya tuni Saifuddeen ya saba da mutane da dama,
wani lokacin har leda 14 yake saidawa inda yake samun riba kusan 900,
sosai yayi abokai sa'anninshi manyan mutane kuma na son mgnanshi sabida yanada dad'in zama ga tsabta da girmama na gaba dashi.
Abu gaba-gaba yanzu harda robobin Faro, yake sara dasu Fanta, Coca-Cola, molt etc. Wanda yawanci matasa shi kan seya.

Yanzu ya saba da wahalar da yawon da ranar saidai ya d'anyi duhu farinshi ya disashe sabida rana da yake shiga.
Yana yawan had'uwa da Dottijon nan baba bello, mafi akasari shike mik'awa mutane leda su bashi kud'i ya bawa baba bello,
Alhamdulillahi yanzu littafi da biro yake yawo dasu a aljihu duk mgnar da kai mishi zai baka amsa,
wasu da dama dan suga rubutunshi suke son Magna dashi sabida Allah ya mishi baiwar iya rubutu in yayi tamkar na'urace tayi.
da yawa da Balarabe suke kiranshi wasu kuma suce Saifuddeen balarabe.

Azumi nata gaba towa dan yanzu baifi 8 days ya rage Ramadan ba,
Yayinda dukkan Al'ummar musulmai keta shirye-shiryen azumi.
kuma zuwa yanzu kusan tsawon kwana 46 da kafa asusun Saifuddeen.
To ga azumi yana zuwa gaba d'aya ya rasa sana'ar da zai kama dan yasan cikin azumi cinikin ruwa bazaiyi guduba tunda duk musulmai baki a rufe yake.
Yana dai ta nazarin abin yi amman har zuwa azumi saura kwana uku bai tsaida sana'ar da zaiba da fari yayi niyar ko zai koma saida dabino dasu kwakwane sai ya kuma ga sana'ar yawoce kuma ga azumi so yasan zai wahala,
a haka dai yau kam yayi niyar yin shawara da abokinshi Jabeer ko Hisham, duk da yaso ace da is'haq zai shawarar to is'haq kuma yanzu ya fi kwana 36 da tafiya Abuja wurin yayanshi Rabi'u kuma acan zaiyi azumi dan shida Ummarsu ne suka tafi,
dan bayan ya fara zuwa kasuwar da sati d'aya ne yaje gidansu Is'haq sai ya samu ranar sukayi sammakon tafiya Abuja.
Chapter 12 · 0% Book details