← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 116

Sashe 89

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

falon ya fito cikin kamala ya zauna gefen Ummi yayinda Raliya da Hayatuddeen ke gefe sunata hirar zasuyi kewar Raihana da itama gobe zata koma KD da mijinta.
nan suka d'anci gaba da hira, cikin hirar Ummi tace.
Raliya tare da cewa.
"Rana tayifa tashi ki shiga kitchen ki hada mana lunch kinga yau Hammanku wunin gida zaiyi yace yau lokacinsa namu ne."
dato ta amsa kwana ta mik'e ta shiga kitchen.
Raihana ce ta mik'e da sauri taje bakin k'ofar falon nasu jin ana d'an bubbugawa.
cikin fara'arta da sakin fuska ta kalli Mom d'in Amina tare da cewa.
"Sannu da zuwa shigo ciki."
cikin mmki ta kalli Amina dake bayan Mom da sauri ta k'ara matsawa ta basu hanya tare da cewa.
"La kamar na ganeki, ku ise."
murmushi sukayi baki d'aya kana suka kutsa kai cikin falon bakinsu d'auke da sallama.
Hayatuddeen ne ya mik'e da sauri tare d'an yin tsalle yayi gaban Amina tare da cewa.
"La likita bokan turai? Yaushe kika zo gombe? waya kwatanta miki gidanmu?."
Ummi ce ta mik'e cikin kamala take cewa Mom.
"Lale marhabin maraba lale ga wurin zama."
cikin sakin fuska Mom tace.
"Yauwa."
ita kuwa Ummi dak'uwa tayiwa Hayatuddeen tare da cewa.
"Kai auta me haka zaka tsareta da tambayoyi?."
kanshi ya fasha tare da nuna mata kujera kana yace.
"Kai naji dad'in zuwanki, zauna mana."
murmushi tayi tare d'an hararanshi k'asa-k'asa kana tace.
"Ba nace maka munyi fad'aba?."
dariya yayi sosai kana yace.
"Karki damu zan rarrasheki da dambun naman da Ummina tayimin."
Ummi kuwa cikin rashin saninsu ta gaisa da Mom.
kana ta juyo ta kalli Amina dake durk'ushe a k'asan carpet kusa da k'afafun Ummi tare da cewa.
"Ummi ina wuni."
cikin sakin fuska Ummi tace.
"Lafiya lau Alhamdulillahi."
kanta ta d'an d'ago ta kalli Saifuddeen dake can gefe kan weelchair d'inshi da system nashi bisa cinyarshi yana sarrafa cikin gwarewa, a hankali tace.
"Ya jikin Hamma Saifuddeen?."
zuba mata ido Ummi tayi tare da cewa.
"Alhamdulillahi jiki kam da sauk'i sosai."
a kunyace tace.
"Allah ya k'ara sauk'i ya bashi lfy rabbi ya sa yanada rabon sake takawa da sawunshi."
cikin wani irin tsananin jin dad'in addu'arta ga Saifuddeeen Ummi da yaranta duka suka amsa da. "Amin Amin Ameeen ya rabbil izzati".
cikin nitsuwa Ummi ta kalli Mom daketa kallon Saifuddeeen kana tace.
"Sai dai har yanzu ban ganeku ba?."
da sauri Hayatuddeen yace.
"Ummi baki gane Amina ba itacefa wanna nurse d'in dake kula da Hamma a Abuja kafin mu tafi Indian."
cikin mmki Ummi tace.
"Allah sarki Amina kai ngd ngd matuk'a Allah bar zumunci."
cikin tsananin jin dad'i Amina tace.
"Amin."
Raihana ce tayi sauri cewa.
"La wlh kuwa nima saida ka fad'a na tunata, yaudin tayi kyau da yawane shiyasa bamu ganeta ba."
dariya sukayi baki d'aya,
yayinda Raliya kuwa take ta kawo musu ababen sha dana motsa baki.
ita kuwa Ummi da kanta ta kalli Saifuddeen lokacin da Amina ta kallonshi.
tab'ashi tayi tare da nuna mishi Amina da mom sannan tace.
"Nurse d'inka ta Abuja ne da mamanta ko?."
ta k'arishe mgnar da kallon Amina alamun tambaya, cikin nitsuwa ta gyad'a kanta alamun eh.
shi kuwa Saifuddeen cikin d'an sassauta had'e fuskarsa ya gaida Mom tare da mata godiya duk cikin body language.
sosai Mom ke kallonshi,
shi kuwa kauda kanshi yayi daga kallonsu sam yak'i yarda ya kalli Amina.
shi kuwa Hayatuddeen sai jan Amina da hira yakeyi hakama Raihana.
Ummi kuwa da Mom hirar ciwon Saifuddeen suke d'an tabawa.
Raliya kuwa tuni ta koma kitchen.
Mom ce ta kalli Amina tare da cewa.
"Mu tafi ko Amina lokaci ya tafi."
cikin son bak'i Ummi tace.
"A a ai kwa tsaya kuci abinci."
da sauri Mom ta girgiza kai tare da cewa.
"A a kai Alhamdulillahi ai a k'oshe muke, jiya muka shigo gombe bikin yar k'awata a nan unguwartaku,
to shine fa Amina na zancen Saifuddeen sai aka samu wanda ta sanshi da gidan naku har ta kwatanta mana,
shinefa fir Amina tace sai munzo, ashe ba nisama layi biyu tsakani."
cikin jin dad'i Ummi tace aiko na gode matuk'a wlh naji dad'i.
Amman dai kuyi salla kafin ku fita tunda an kira sallan azahar."
sam Mom bata soba amman dole Ummi tasata suka shiga bedroom ta nuna mata k'ofar bathroom kana ta shimfid'a mata sallaya.
Hayatuddee kuwa kitchen yabi Raliya tare da cewa Amina.
"Bari inje in kawo miki abin dad'i."
murmushi tayi tare da kallon Raihana da ta nufi corridor d'in dasu Ummi suka shiga.
ido ta juya kudu da arewa gabas da yamma, ganin ba kowa a falon daga ita sai Saifuddeen da yaketa saurin ya k'arisa aikinsa ya shiga side d'inshi.
da sauri ta d'auki goran ruwan Faro ta garashi har zuwa gaban Saifuddeen d'in. Da sauri ya d'ago kanshi ya kalli ta inda yaga an turo goran,
fuska ya kuma had'ewa ganin ta zuba mishi sosai ya haɗe girar sama data ƙasa.
ita kuwa Amina, murmushi tayi tare da d'aga mishi gira kana tace.
"Eye kayi kyau, k'asar Indian ta amsheka ji yadda kayi wani fresh da kai kamar ba kaiba."
baki ta tura ganin ya k'ara had'e fuska a hankali taci gaba da cewa.
"Bafa zaginka nayiba kake wani had'emin kekyawar fuskarnan taka,
ko dai baka son in kalli wannan kekyawan sajen nakane."
dib yayi dan baya son yayi abinda zata gane yana gane abinda take fad'an.
ganin haka ita kuma ta lumshe ido kana ta bud'esu a kanshi a hankali tace.
"Wai kai baka gane mai sonka ne?
to in ma baka ganewa ni dai ina sonka, dan kana min kyau."
da sauri tasa tafin hannunta ta rufe ido dan ganin Raihana a tsaye a gefeta tanata dariya.
dai-dai lokacin Hayatuddeen da Raliya suka fito kitchen,
wanda suma suke dariya dan sunji mgnarta ta k'arshe inda take cewa dan kana min kyau.
wayyo ai ji tayi kamar ta nitse cikin k'asa ganin hakane Raliya ta jata suka tafi side d'inta inda acan tayi salla.
shi kuwa Saifuddeen baibi ta kansuba ya wuce side d'inshi.
Koda su Ummi sukayi salla suka fito ba yadda Ummi batayi akan suci abinci fir sukak'i,
dole Ummi ta hak'uri kana sukayi musu rakiya har bakin motarsu inda dama direbansu na nan yana jiransu.
saida suka tafi kafin su Ummi suka koma cikin gidan.

Washe gari kuwa stab Saifuddeen ya shirya cikin shiga ta al'farma sai k'amshi yake zubawa cikin shirinshi na tafiya Dukku.
Yana ƙoƙarin ɗaukar wayarsa dake aje kan gado, yaji anturo ƙofar ɗakin anshigo, Ishaq ne yashigo bakinsa ɗauke da sallama yayinda shima yasha ado cikin yadin getzner me ruwan toka sosai shima yayi kyau.
Tamkar wanda ke gani ya lumshe idanunsa tare da faɗin.
"Kayi kyau sosai Saifuddeen!"
Murmushi Saifuddeen yayi yana me ƙoƙarin ɗaukar wayarsa don ya rubutawa Ishaq din saƙo, maganar Ishaq ta sake dakatar dashi inda yace.
"Bama sai ka sha wahala wajen rubutu ba nasan me zaka tambaya, cewa zakayi dawani idon nasan kayi kyau, bayan kuma nasha faɗa maka cewa masu ido abu ƙalilan zasu nunamin donni ma inaganin komai da zuciyata, zuciyata itace idanuna!"
Murmushi Saifuddeen yasakeyi aransa yana mejin ƙarin ƙaunar abokin nasa, cikin kulawa ya turawa Ishaq saƙo awayarsa kamar haka inda yace.
"Nikam nagaji da wannan surutun naka ni yanzu burina shine naganni a Dukku inda zan faɗi abun dake raina".
Ishaq na gama jin saƙon yasaki murmushi abayyane yace.
"Lallai Zaleeha tacika mai sa'a dahar ta iya sace zuciyar mutum ɗaya wanda yazama tamkar da dubu, jajirtaccen Namiji wanda samun irinsa keda matuƙar wahala"

Murmushi kawai Saifuddeen yayi inda ya danna madannin kekensa nan yafara tafiya, yana gaba Ishaq na biye dashi abaya haka suka fito daga cikin ɗakin, Ummi dake tsaye tana ganinsu ta saki murmushi cike da so da kuma tsananin tausayinsu tace.
"Har kun fito, amma dai kafun kutafi ai dai zaku tsaya kuci abinci, musamman ma kai Ishaq musamman na aje maka ragowar dambun nama don nasan kanaso"
Murmushi Ishaq yayi tare da cewa.
"Shiyasa nake sonki Ummi na, yanzu dai abani dambun natafi dashi sai naci acikin mota don naga wannan abokin nawa sauri yake kamar wanda zai tashi sama burinsa kawai shine ya gansa a Dukku"

Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"To bari kawo maka sai katafi dashi amma dai inkun dawo kabiyo tanan zanyi abincin dare harda kai!"
Murmushin jin daɗi Ishaq yayi inda yace.
"Insha Allah!"
Nan Ummi ta kawo masa dambun naman, har bakin mota ta rakasu inda tayi musu adawo lafiya, Hayatuddeen kuwa ɗan kalen baki hadda cewa Hamma Saifuddeen ɗin nasa wai yakawo masa tsaraba.

Ƙarfe Biyu daidai suka samu isowa cikin garin na Dukku, gari me ɗauke da tarin al'barka da shuke shuken tsirrai masu kyau da ƙawatarwa, agidan Baffa Ali suka sauƙa inda yacika da tsananin mamakin ganinsu da yayi don sam Saifuddeen baisanar masa cewa yana zuwa ba.
A falon Baffa Ali'n suka zauna inda Aunty Nina takawo musu ruwa tare daɗan abun motsa baki, gyara zama Baffa Ali yayi tare da duban Saifuddeen cikin kulawa yace "Kashammace ni Saifuddeen nida jibi nake shirin tahowa Gombe'n sai kuma gashi kazo batare da kasanar dani ba, ai da kafaɗamin kanada buƙatar ganina to tabbas da har gida zanzo nasameka".

Murmushi Saifuddeen yayi tare da duban Baffan nasa, saƙo ya rubuta awayarsa kamar haka, kana ya miƙawa Baffa Ali'n.
"Kagafarceni Baffa Ali, magana me mahimmanci ne ta kawoni, naƙi sanar dakai zuwana ne kuma saboda nasan idan kaji cewa zakayi nabari zaka zo".

Ɗan murmusawa Baffa Ali yayi bayan yagama karanta saƙon inda yace.
"Shikenan Saifuddeen ina sauraranka, tabbas nasan baƙaramar magana bace zata tasoka daga Gombe zuwa nan".

Ajiyar zuciya Saifuddeen yayi tare da sunkuyar da kansa ƙasa, Ishaq ne yaɗan gyara zamansa tare da yin gyaran murya cikin nutsuwa yace "Saifuddeen yaga mata kuma yana fatan aurenta wannan dalili shiyasa mukazo don musanar dakai, saboda yana da buƙatar anemamasa izinin fara zuwa zance daga wajen manyanta kamar yanda addini ya koyar!"
Chapter 89 · 0% Book details