← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 116

Sashe 10

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan sun isa shi Salisu yayi gidansu da machine d'in shi kuwa, Saifuddeen kai tsaye cikin gida ya nufa a tsakar gida ya samesu zaune,
gefen Umminshi ya zauna kasan cewar akwai wuta duk suna ganin juna,
da sauri Rahma ta kawo mishi abinci kana ta kunce bakin zaninta ta kunto 50 sannan ta kalli Hayatuddeen dake tsaye alamar zai fita ganin Saifuddeen dinne ya hanashi fita,
hamtsin d'in ta mik'a mishi tare da cewa.
"Ingo jeka gidansu Ya Adnan ka seyo mishi ruwan sanyi."
da sauri ya amsa tare ficewa.
Ummi kuwa cikin kula tace.
"Ya kasuwa?."
kai ya jinjina mata cikin son boye yanayin da yake wuni a cikin kasuwar.
Rahma kuwa ido ta zuba mishi tare da cewa.
"Saifuddeen gobema zakaje ne?."
da sauri ya gyad'a mata kai dan baya son su karaya.
Raihana kuwa cikin karya wuya tace.
"Hamma Saif me kake sayarwa ne to?."
ido ya zuba mata cikin rashin son yi musu k'arya ya girgiza mata kai alamar babu
da sauri Raliyya tace.
"To me kakeyi?."
sai ya kuma juyo ya kalli Ummi ba tare daya amsawa Raliyya ba,
cikin sanyi take ce mishi.
"To Babana me amfanin zuwan, kalli jiya da yau duk baka wuni damu ka tafi har Gombe kuma kaje ba wani abu kakeyi ba ai gwara ka hak'ura ko?."
murmushin k'arfin hali yayi kana ya fara rubutu a k'asa.
"Ummi wai har kin karaya ne? To ki aro jarumta ki yafa ai komai a hankali yake zuwa,
ai mai nema baya fushi, yoh su masu shagunan da kansu wata rana zasu bud'e ko asi basuyiba kuma haka bazaisa gobe su k'i zuwaba, kedai kiyi ta min addu'a in sha Allah, Allah bazai hanani abin yiba."
sai ya kuma kalli Rahma dasu Raihana yace.
"kuyi tamin addu'a in sha Allah dukkan tsanani tare yake da sauk'i."
cikin samun k'warin guiwa, sukayi mishi addu'a.

Bayan yaga sun saki Randi sunata hirane sai ya mik'e yad'auki bokiti ya debi ruwa a randa kana shiga d'anshi wanda da shida Nuruddeen ne,
farar jallabiyarshi ya d'auka da boxer inshi kana ya fito hannunshi rik'e da kondon wonkanshi ban d'aki ya nufa yaje ya shiga wonka.
Ya jima kafin ya fito daga cikin d'an madaidacin bayan gidan nasu da aka lailayeshi da fulo d'in siminti,
shaddan na can gefe kana wurin wonkan anyishi da mazaunin siminti da kuma inda zaka ajiye sawunka.

A hankali yake tafi bisa dukkan alamu baison kasa ya bud'e mishi sawune,
d'akin nashi ya shiga,
inda yake gyare tsab sai k'amshin turare yakeyi wanda ishaq ne ke saya musu tare,
ko ina a kimtse kodan babu tarkece sosaine,
leda carpet ne a malale a tsakiyar d'akin wanda sai Shek'i yakeyi alamun ya wadatu da tsabta sai katifarshi shimfid'e a gefe wanda yasha gyara sai pillows biyu a
gefen katifar.
can daga k'asa kuma wata yar madaidaciyar durowa ce,
inda gefe d'aya ya jera kayayyakinshi dake wonke a goge, sai d'aya side in kuma littafanshi ne a jere daga sama har k'asa kama dana boko na islamiya dana allonsu wanda wasu tun na kakansu ne, sai wani dogon madubi dake lik'e a jikin ginin daga sama har zuwa k'asa dan zaka iya kallon tsawonka duk ta cikin madubin
sai wani dan abun aje takalma kana sai fankar k'asa da kuma wani d'an k'aramin randar tabo da sai naso yakeyi alamun ruwan ciki da sanyi
sai butarshi a gefe kana can gefen durowar kuma sallayanshi ne ke shimfid'e.
Mai ya shafa sannan ya fito tsakar gidan tuni Hayatuddeen ya dawo har yayi bacci hakama su Faruq.

Gefen Umminshi ya zauna tare da tonk'oshe sawunshi abincin da Rahma ta ajiye mishi ya jawo,
bud'ewa yayi sai ya kuma yi murmushi ganin tuk'ek'k'en tuwan shinkafa da miyar busasshen zogale wanda yasha kifi, gyada, attaruhu, da albasa, wanda aka had'esu da kifi,
kana ga wake dasu kayan d'and'ano
miyar sai k'amshi take, Allah ya sani Saifuddeen nason miyar zogale shiyasa Umminshi ke yawan yin miyar in dai tanada halin yinta da yake miyar tanada cin kud'i.
ledan ruwa d'aya ya d'auka tare da b'ulawa kana ya wonke hannunshi ya fara ci,
ita kuwa Ummi ido ta zuba mishi tare da cewa.
"Yayanka Adnan yazo ya sallameni d'azu wai zai tafi karatu har Zaria."
kanshi ya d'an jinjina alamar Ayyah,
sai ya kuma yi mata alamun Allah ya kaishi lfy.
Amin Amin tace,
bayan ya d'an ci abincin ne ya wonke hannunshi Raihana ta kwashe kwanukan kana ta dawo sukaci gaba da hira.
Suna nan a zaune Bappa Ali da Aunty Nina ma suka shigo yi mishi barka da dawowa nan sukayi ta hira.

Washe gari da sassafe Rahma ta hura wuta tayi d'umame kamar yadda suka saba,
da sauri ta d'auko pillet ganin Saifuddeen ya fito cikin shirin tafiya,
yau k'ananun kaya yasa wanda sukayi masifar yi mishi kyau blue Jeans ne a jikinshi sai bak'ar riga mai farin rubutu a jiki,
kanshi ba hula hakan ba k'aramin haskashi yayiba,
yana shiga d'akin Umminsu tana binshi a baya,
bisa kujerarta irin zauna kaci doya nan ne ya zauna,
ita kuwa Rahma mik'o mishi fillet d'in tayi kana ta jawo kolban man shanun da suke sawa in sunyi d'umame,
bud'ewa tayi tare da tsiyaya mishi kana ta mik'e ta koma kitchen robar dakekken yajin borkono ta d'auko sannan ta dawo barbad'a mishi tayi,
sannan ta d'auki kofi ta nufi d'akinshi ruwa ta d'ebo mishi a wannan randar tashi,
sannan ta kawo mishi tare da cewa.
"Kaci kafin ku tafi."
kai ya gyad'a mata kana ya kalli Umminshi dake shirya Hayatuddeen yanata zumbura baki, murmushi yayi tare da jawo hannun Hayatuddeen yana mishi tambaya irin tasu ta kurame ya tambayeshi me ya sashi fushin.
Bakin ya kuma turawa kana ya rab'a jikin Saifyddeen d'in tare da cewa.
"Hamma Saif ba Adda Rahma bace tayi d'umame kua tasan ni bana cin d'umame hakama Faruq da Adda Raliyya."
murmushi yayi kana ya jawoshi ya ajiyeshi gefenshi,
a hankali yasa cokalin da Rahma ta mik'i mishi ya gutsuri gayan kana ya dandalo miyar da taketa k'amshin man shanu,
bakin Hayatuddeen ya kai,
tura baki yayi tare kwabe fuska kana yace.
"Na k'os. "
bai k'arisa mgnar tashiba yayi shiru,
jin ya sa mishi loman a bakinshi, lumshe ido yayi tare da fara sarrafa abincin,
saida ya had'iye kana ya bud'e idanunshi tare da cewa.
"Dad'i wlh miyar tayi dad'i Faruq zo kaci."
Ummi kam da Raihana dake shirya Faruq tuni dariya sukeyi, shima Saifuddeen dariya yakeyi har saida dimples nashi suka lotse sosai kana fararen hak'oranshi suka baiyana manyan idanunshi ya lumshe tare daci gaba da basu abincin a baki,
aifa sukaci sukayi nak, sannan suka tafi makaranta,
ita kuwa Raihana da sauri ta fita tace.
"Adda Rahma ki samishi wani abincin su Faruq sun cinye wannan,
harda santinsu."
dariya sukayi kana Rahma ta samishi wani yana cikin cine Salisu ya shigo nan sukaci tare kafin suka fita suka tafi.

Yauma kamar kullum Saifuddeen wuni yayi yana yawo da bulayi a kasuwa,
sai da magrib tayi ya fito, kana yayi salla kafin Salisu yazo ya d'aukeshi yau ma fura da nono yasha da zasu tafi.

Haka dai Saifuddeen yayi ta fama yawo da wahala a cikin kasuwar Gombe har tsawon kwana bakwai,
to a ranan ne kuma Salisu ya basu balance ensu kamar yadda sukayi duk sati zaike basu dubu biyar.

Koda ya karbi kud'in Bappa Ali ya kaiwa su,
shi kuwa Bappa Ali k'in amsarsu yayi yace ya kaiwa Ummi kud'in zasu samu abinda zasuke sarrafa cefenen abincin.
da yake har yanzu sunada sauran abincin da baban Arabi ya kawo musu.

Shi kuwa Saifuddeen sai ya zare dubu biyu ya bawa bappan nashi, amman sam yak'i karb'a acewarsa ai da yanada hali shine ya kamata ya basu,
to dai ganin Saifuddeen ya b'ata rai ya sashi amsar 1k yasanya al'barka.
Shiko yaje ya bawa Ummi dubu uku sannan ya d'auki dubu d'aya.
Ummi kam sai sanya mishi al'barka takeyi.

Washe gari kamar kullum suka shirya suka tafi cikin. Gombe a inda ya saba sauk'eshi yau ma nan ya sauk'eshin, bayan Salisun ya tafi shi kuma Saifuddeen sai ya d'anyi tattaki zuwa bakin mashigar kasuwar, addu'a yayi kamar kullum kana ya shiga da k'afar dama,
yauma bakin shagunan yayi tabi har kusa k'arfe shad'aya lokacin rana ta tsala zafi ya fara,
sai ya nufi layin masu robobi,
yana zuwa shagon wani bayerbe sai ya tsaya,
bokatin kand'e tsirara ya saya wanda wasu ke cemai ganta sarai,
bayan sun gama ciniki cikin mgnar kurame ya bashi dubu d'ayannan,
kana bayerben ya bashi canjinshi,
daga nan ya nufi wani layin tafiya kad'an yayi sai gashi a wani babban shago da yake cike da d'ima-d'ima firiji masu tsawo da masu fad'i.
Chapter 10 · 0% Book details