Sashe 74
Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau da ƙarfe uku na yamma jirginsu zai tashi hakan yasanya tun safe suka kammala shirya kayansu tsab inda zasu bar Hayatuddeen, dan kuwa zuwa yanzu jikin Saifuddeen sai dai ace Alhamdulillah. Hayatuddeen ne yaturo ƙofar ɗakin ya shigo hannunsa ɗauke da wasu manya manyan leda guda biyu, wanda jikinsu ke ɗauke da tambarin *Inorbit mall malad west Mumbai* kasancewar nan yaje yayi musu sayayyan ƴan abubuwan buƙatansu dangin kayan sawa da duk wasu abubuwan da baza'a rasa ba shida Saifuddeen.
Aje ledodin yayi akan gado yana me duban Dr Adnan da Ahmad wanda yake ƙoƙarin zuge jakan kayansa.
Murya asanyaye yace.
"Ya Adnan lokacin tashin naku yakusa ko?".
Murmushi Dr Adnan yayi tare da dafa shoulder ɗinsa cikin kulawa yace.
"Badai kuka zakamana ba". Ɗan murmushi yayi tare da son maida hawayenshi tare da cewa
"Sai kace ɗan ƙaramin yaro, kawai dai zanyi missing d'inku".
Dariya Ahmad da Adnan sukayi Ahmad ne yace.
"Ehem dakai ɗin babbane? sakalallen Ummi kawai! Ba gashi har idonka ya ciko da ruwan hawaye ba".
Dariya sukayi su dukansu kana suka nufi hanyar fita. Hayatuddeen ne ya riƙewa Dr Adnan jakansa, kana suka fice daga cikin ɗakin hotel ɗin.
Kaitsaye asibiti suka nufa don yin sallama da Saifuddeen.
Kamar koda yaushe kwance yake akan gadonsa yayinda kyawawan idanunsa ke rufe, ahankali Dr Adnan ya turo ƙofar ɗakin ya shigo kana su Ahmad suka biyo bayanshi, Jikin gadon ya ƙarasa tare da sanya hannunsa yaɗan taɓa Saifuddeen.
Ahankali ya ware idanunsa wanda samansu ke ɗauke da zara-zaran eye lashes da suka matuƙar ƙarawa fuskarsa kyau, ganin Dr Adnan ya sanyashi sakin tattausan murmushi, shima Dr Adnan ɗin murmushi yayi tare da cewa.
"Zamu wuce Saifuddeen lokacin tashin jirginmu yakusa."
Sai kuma ya d'an kalli sajenshi kana yaci gaba da cewa.
"Allah Ubangiji ya ƙara maka lafiya! Yasa nanda wata d'aya ka mik'e tsaye da k'afafunka".
still murmushi Saifuddeen yayi tare da jinjina kansa kana yayi masa alamar godiya.
Kallonsa ya maida kan Ahmad tare da miƙo masa hannu, hannunsa Ahmad ya kama idanunsa cike tab da ƙwallan tausayin abokinsa kuma d'an uwansa, ganin hawaye kwance a idanun Ahmad yasanya Saifuddeen girgiza kansa alaman kada ya bari hawayen idanunsa su zubo, da sauri Ahmad ya shanye hawayensa tare da juyawa da sauri yafita daga cikin ɗakin don bayajin zai iya jure tsayuwa agaban Saifuddeen batare daya zubda hawayensa ba.
Cikin dakiya Dr Adnan yayiwa Saifuddeen bankwana don shima hawayenne cike a idanunsa kawai dai shanyewa yake dan kada ya raunata zuciyar Hayatuddeen.
Tare da Hayatuddeen d'in suka fito kuma shi ya rakasu har airport saida yaga tashinsu sannan yadawo asibitin domin zuwa yanzu Hayatuddeen ya zama ɗan gari a india.
Nigeria k'asarmu ta gado.
Su Dr Adnan sun dawo gida cikin halin ƙoshin lafiya yayinda dawowarsu ya ɗan sanyaya zuƙatan masoyan Saifuddeen kasancewar sunji kyakkyawan labari daga garesu, inda hankalin Ummi ya ɗan daɗa kwanciya musamman da Dr Adnan da Ahmad suka shaida mata cewa ayanzu Saifuddeen har ɗan iya motsa jikinsa ya keyi, sannan kuma sauƙi yana samuwa sosai, inda kuma suka shaida musu cewa sun bar asibitin dake new delhi sun koma wanda ke garin Mumbai.
Adda Rahama kuwa ganin mijinta da jin labarin jikin ɗan uwanta yasanya hankalinta ya ƙara kwanciya don dama takusa shiga watan haihuwarta gab take da fita a wata na takwas.
Daren randa suka dawo bayan Ahmad ya gama kontarwa Ummi hankalin ganin dare ya tsala ne ya mik'e tare da kallon Raliya cikin sanyi da begen matarsa wata uku har an shiga na hud'u kenanfa.
"Tashi muje ki hada min ruwan wonka."
yace da ita,
kai ta rausayar tare da mik'ewa tabi bayanshi dan tabbas ta hango wutar begenta da sha'awarta a idanunshi.
Suna shiga bedroom nata yasa hannu ya jawota suka fad'a kan gado blanket ya jawo ya rufesu tare da cewa.
"Hak'uri nafa ya k'are ina gab da macewa in ban samu d'umin jikinki ba."
ido ta lumshe tare da shigewa jikinshi.
Hakama Ya Adnan sam ya kasa d'agawa Adda Rahma k'afa duk da tsohon cikinta.
Sati ɗaya da dawowan su Dr Adnan Ummi da Ishaq da kuma mahaifiyar Ishaq ɗin suka shirya tsab don zuwa India,
wata ranan Asabar da sanyin safiya jirginsu ya ɗaga zuwa India.
India.
Hayatuddeen ne zaune akusa da gadon Hamma Saifuddeen d'inshi wayarsa dake cikin aljihun wandonsa tasoma ƙara, ciro wayar yayi tare da duba sunan me ƙira "Zakari".
shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar, murmushi yayi dan tuno kullum sai Zakariyya yayi ta musu fasifar su dena yanke mishi suna suna medashi sunan wani abu da ban dariya yayi tare da amsa ƙiran kana ya kara akan kunnensa tare da cewa.
"Zakari namu ina kake ne?."
Zakariyya dake jingine da jikin motar Zaliha yanajin Hayatuddeen ya ɗaga wayan yaja tsaki tare da cewa.
"Yana cikin wondonka banzaye kawai, masu mgnar banza."
dariya sosai Hayatuddeen yayi kana yace.
"Yi hak'uri Ya'u namu."
tsakiya ya kuma ja kana yace.
"Gwara dai ba indiye ya akayi ne? Don katashi daga ba gombe ka koma ba indiye mai katon z!".
Dariya Hayatuddeen yayi tare da ɗan gyara zamansa kana yace.
"Amma Zakariyya baka da mutumci.
To Oho dai koma dai menene ina lafiya".
Dariya Zakariyya yayi tare da cewa.
"Masha Allah to yajikin Hamma Saifuddeen Ina fatan da sauƙi sosai ko?".
"Jiki Alhamdulillah da sauƙi sosai wlh,."
Masha Allah. Allah ya kara sauk'i."
"Amin Amin." yace cikin jin dad'i tare da ci gaba da cewa.
"Ya Nigeria?".
"Kai da kake ƙasar Indiyawa mene haɗinka dawani tambayar Nigeria?".
Zakariyya yafaɗa cikin tsokana.
"Ko madai mene ae Nigeria ƙasatace kuma nanne tushena abin al'fahari na."
"To Nigeria tana lfy."
Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
"Ina hajia Zaleeha masifaffiyar yar jarida?".
Hayatuddeen yatambaya cike da neman tsokana.
Dariya sosai Zakariyya yayi tare da cewa.
"Kana zancenta sai gata ta iso".
Duban Zuleeha Zakariyya yayi wacce tasha ado cikin wani tsadadden pink shadda me kyaun gaske, cikin rausayar dakai gefe yace.
"Adda Zaleeha Hayatuddeen ne please gashi ku gaisa".
Zaleeha wacce take ƙoƙarin buɗe murfin motarta kana ta tab'e baki ta amshi wayan batare da tayi masa musu ba dan tasan sai in zai tsokaneta yake ce mata Adda,
cikin zazzaƙan muryarta tace "Hello Hayatuddeen!".
Jin muryan Zaleeha yasanya Hayatuddeen sake gyara zama kana yace.
"Adda Zalees ina wuni ya aiki?".
Murmushi ta ɗanyi tare da cewa.
"Alhamdulillah ya mai jiki?"
"Jiki da sauƙi sosai" Hayatuddeen ya bata amsa.
"Allah yaƙara sauƙi".
tafaɗa tare da miƙowa Zakariyya wayarsa. Nan Hayatuddeen da zakariyya suka ɗan taɓa hira daga bisani sukayi sallama.
Jirginsu Ummi na dira aƙasar ta india taji wani irin faɗuwar gaba ya rusketa, take taji wani irin fargaba, tsoronta ɗaya kartaje tasamu Saifuddeen ɗinta awani hali, Ummun Ishaq ne ta tara musu taxi inda kae tsaye suka faɗa masa inda zai kaisu sabida kwatancen dasu Dr Adnan suka musu, agaban katafaren asibitin mai taxi ɗin ya sauƙesu, batare da wani shan wahala ba suka isko ɗakin da Saifuddeen ke kwance.
Ɗaya daga cikin nurses ɗin dake kula dashi ne tayi musu jagora zuwa cikin ɗakin, kwance yake flat akan gado kamar wani wanda yake bacci.
Hayatuddeen dake zaune yana charting da Amina wayarsa ya ɗago da saurin jin muryar Umminsu, wani irin tsananin farinciki ne ya bayyana akan fuskan Hayatuddeen cike da tsananin kewarta ya mik'e da sauri ya ƙarasa gareta tare yana isa ya fad'a jikinta tare da cewa.
"Oyoyo Ummi na!".
Murmushi Ummi tayi tare da sanya hannu ta shafa kansa, cikin ƙaunar ɗannata tace "Na'am Autan Umminshi". dariya yayi tare da duban Umman Ishaq cikin girmamawa yagaida ta, fuska asake ta amsa masa gaisuwan tare da tambayarsa ya mai jiki.
"Da sauƙi, Umma ina Imran" ya bata amsa yana me duban Ishaq dake tsaye yana murmushi tamkar wanda yake kallon abun da sukeyi, ƙarasawa yayi ya kama duka hannayen Ishaq cikin son abokin hamman nashi yace "Ya Ishaq sannunku da zuwa".
murmushin dake kan fuskar Ishaq ne ya faɗaɗa hannunsa yasanya ya dafa kan Hayatuddeen cike da kulawa yace.
"Auntan Ummi Me jinya barkan ka dai, ya jikin Saifuddeen?!".
Ƴar dariya Hayatuddeen yayi cikin yanayin dayake ciki najin daɗin ganinsu da yayi yace.
"Jikin Hammana da sauƙi sosai Ya Ishaq, don zuwa yanzu yana ƙoƙarin yin wasu abubuwa da kansa".
cikin tsananin jin daɗi su dukansu sukace.
"Masha Allah- Allah yaƙara mishi lafiya".
Ummi ce taƙarasa jikin gadon da Saifuddeen ɗin ke kwance, idanu ta zuba masa tana mejin tausayi haɗi da ƙaunar ɗan nata na ratsa ko ina na jikinta.
Ahankali ya buɗe manya manyan idanunsa, tarwal ya sauƙe ganinsa akan fuskar mace mafi soyuwa agaresa wato UMMI'n sa, cikin tsananin farin cikin ganinta ya sanya hannuwansa ya kamo nata hannun.
Murmushine ya bayyana akan fuskar Ummi'n cikin jin daɗi tace.
"Ashe ma ba bacci kake ba"
Gane abun data faɗa yasanyashi kaɗa mata kai, tare dayi mata alaman cewa. "Koda ma bacci nake indai kece kika tsaya akusa dani dole za farka."
murmushi Ummi tayi dan tana tsananin gane body language , dai-dai lokacin Ishaq ya ƙaraso jikin gadon, tamkar wanda yake gani haka ya ɗaura hannayensa adai dai saitin zuciyar Saifuddeen cikin kulawa yace "Ko wani bai faɗamin ba yanda naji zuciyarka na harbawa nasan kana samun sauƙi".
murmushi Saifudden yayi tare da sakin hannun Ummi ya kamo na Ishaq ya riƙe cike da ƙaunar abokin nasa, mahaifiyar Ishaq ne taƙaraso tare da duban Saifuddeen cike da kulawa tace "Saifuddeen ya jikin naka?" dayake yana kallon fuskarta ne hakan yasanyashi gane me take nufi, kansa ya kaɗa mata tare da ɗan motsa laɓɓansa alaman da sauƙi, sosai su UMMI da Ishaq suka jima awajen Saifuddeen har dare kafun Hayatuddeen yayi musu rakiya inda zasu kama hotel, anan hotel ɗin Sahar International Mumbai suka sauƙa inda Ummi da Ummun Ishaq suka kama ɗaki ɗaya, shikuwa Ishaq nan ɗakin Hayatuddeen ya sauk'a, ganin sun samu masauƙi ne sun ci abinci yasanya Hayatuddeen komawa asibiti wajen Hamman sa...