← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 116

Sashe 55

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gudu take tsulawa kamar mai tashi sama, a hankali take bin sautin wak'ar still kuma hawaye na kwaranya a fuskarta har yana d'iga bisa tudun brest d'inta,
fuskarta d'auke da murmushi daya tunzura hawayenta tace.
"Ina kake wanne hali kake ciki me sunanka?."
sai kuma tace.
"Allah ya isanmin bazan yafe musuba, Allah zai saka maka zai taimaka maka fiye da yadda ka taimaka min."
wayarta keta ringing tanaji tana gani bata kula kiranba,
sai yanzu da taji an cire waqar daga can vision d'in ta d'an ja tsaki tare da d'ago woyarta ganin Abdussalam ke kiranta d'an minister, wanda yaketa nacin binta tun last week da suka had'u , Duwa plaza
taje sayan burger,
tsaki ta kuma ja tare da cewa.
"Wannan wanne irin maye ne da baida zuciya, ko uwar me yakeso in mishi da bak'ar fuskarshi kamar an k'ona taya."
aje woyar tayi dai dai lokacin data isa, bakin gate din (Jonopwd) d'in.
tafiyar mai d'an tsawoce kafin ta isa gab da ofishin nasu, dan sai ka wuce farfajiyar court d'in, dake wurin,
ido ta d'an lumshe kana tace kai.
"Ya Habu ka cika naci dan kawai ka bani motarka kaketa nacin kirana kamar bazan dawo ba."
haka nan har yanzu hawayenta sunƙi tsayuwa
sai kuma ta amsa kiran tare da yin kasa da murya tace. "Ya Habu sai yanzu na dawo, kuma yanzu ma haka ina, jonapwd ne."
sai ta kuma bud'e marfin motar kana ta zuro kyawawan k'afafunta woje,
sannan ta kuma yi muryar shogoban da yanzu mai tushe takeyi dan cikin kwana biyun nan ta zama uwa wata lalatacciyar jiniya abi kaɗan tasa kukan da taketa son ɓoye,
to yanzunma hawayen takeyi tare da cewa.
"Kuma sai naje Vision dan gabatar da program na."
A can gefen Ahmad ne ya amshi wayar Habu kana ya kara a kunne tare da gyara zamanshi kana ya rusunar da kai ya kalli mahaifin nasu kana yace.
"Baba malam ke nemanki, yace maza in kiraki ki taho gida."
fitowa tayi daga cikin motar, idanu ta lumshe still hawaye na tsiyaya jin wani sassanyan iska dake ratsa dukkan abin halitta dake wurin, a hankali ta bud'e idanun nata kana ta zuwaba jerin bishiyoyi da tsirran da sukayiwa harabar wurin k'awanya,
a hankali ta fara taku ih zuwa cikin asalin harabar ofishin,
kana cikin fargaba tace.
"Dan Allah Ya Ahmad kace wayata bata shiga, nasan abinda Baba malam ke nemana dashi."
cikin nitsuwa da kamala Ahmad yace.
"Yana ma jinki dan ina gabanshi."
ido ta zazzaro tare da dafe k'irjinta cikin kad'uwa tace.
"Gani nan zuwa."
tana fad'in haka ta katse kiran kana ta k'arisa bakin k'ofar ta shiga danna door bell.
minti d'aya tsakani wani matashi yazo ya bud'e mata k'ofar,
kana ta kusa kai ta shiga wani corridor tafiya kad'an ta bulla cikin wani tamfatsetsen office wanda aka k'awatashi da ababen buk'atar dan adam,
wasu kujerenu ne masu kama da mazaunin lilo ke zagaye da wani babban table na bak'in gilashi wanda yaketa shek'i
kana sai fankoki kusan guda biyar da sukabi layin tsawon table d'in, sai wani babbab firij dake can gefe kana, sai wani d'imemen TV sannan sai na'urar AC gudu biyu da suke fuskantar juna,
sai kuma wasu k'ofofi d'aya k'ofar tana gab da k'ofar shigowa office d'in wanda bisa dukkan alamu bathroom ne,
sai gefen dama da k'ofofi guda uku ke jere bisa dukkan alamu office din shugabannin k'ungiyar ce,
kana gefen k'ofofin sai akayi wani dan steps guda biyar in ka haura wani d'an madaidaicin table ne na farin gilas mai ruwan garai-garai sai kujera d'aya rak a gaba kana sai d'aya a bayan table d'in sai tarin na'urai wanda sun kai bakwai.
sai gefen hagu nanma haka tsarin yake sai dai shi sai ka d'an ratsa cikin wani corridor mai d'an fad'i.

Tana shiga wannan mutumin daya bude mata k'ofar yace.
"Barka da zuwa Zalihan nakasassu."
murmushi tayi kana taja kujera ta zauna tare da cewa.
"Ya Ishaq fa baya nanne?."
ba tare data jira amsarshi ba taci gaba da cewa.
"Ya naji ma'aikatan naku shiru yau ba mutane?."
bisa kujerar gefenta ya zauna tare da cewa.
"Ishaq yana Abuja, mutanen mu kuma duk suna fad'ar jiha sunje kai gaisuwa ga mai martaba."
mik'ewa tayi taku biyu zuwa uku ta nufi gaban firij,
tsayawa ta yi jin abinda Sani ke fad'in.
"Ayyah kiyi hak'uri ban kawo miki abin shaba, sorry dawo ki zauna zan kawo miki."
cikin yanayin sabo dasu tace.
"Wai ku anya kuwa ku makafi ne? yanzu ya akayi kasan gaban firij na nufa?."
murmushi yayi tare da d'an kaikaice kunnenshi irin yadda makafi keyi kana yace.
"Motsinki da takun tafiyarki ne ya ganar dani inda kika nufa,
ke har yau kin kasa barin mmki kan lamarinmu, abinda baku saniba ku.
Mu nakasassun munada experience sama daku masu gadara da cikekkiyar halitta."
murmushi tayi bayan ta dawo ta zauna,
robar faron ta bud'a bayan ta sha kana tayi hamdala dan ta ɗanji tafasar da zuciyarta keyi ya ɗan ragu aje goran tayi sannan tace.
"Toh Ya Sani ni zan wuce tunda ciyaman bainan,
wata k'il sai next week, zan shigo, dama zan tattauna da sune a shirin da za'a haska a tasharmu na Farin Wata, dan yace min wannan karon da kurame zan tattauna, to gashi Malam Ishaq bai sanarmin bama a kan baya nan da ban zoba."
"To ba matsala, Allah ya kaimu lokacin, wannan karon kam hirar da kurame za'ayita?."
ya k'arishe mgnar cikin neman k'arin bayani tare da
mik'ewa yabi bayanta kana suka fito tare har gaban motarta,
sannan tace mishi.
"Eh shiyasa dole su sai a tasharmu ta TV za'ayi hira dasu. Yace min da wani babban abokinshi zamu zanta wanda shine Garkuwar asusunku, da nike ta cewa ku fasa ku bani in canza mota, kukak'i, saida kuka bari yan kalare suka fasa min glass, sannan Ya Ahmad na ya canzamin, kuma a kanku motata ke mutuwa kullum ina yawon binku da k'wak'ulo baiwarku."
dariya yayi sosai kana yace,
wannan asusun namune mu yamu."
itama murmushi tayi kana ta shiga mota sannan suka sallami Juna.
Daga nan ya koma ciki.
Ita kuma ta ja mota,
kai tsaye hanyar Vision fm Gombe ta nufa, sanin ana jiranta yasa take sharara gudu kamar babu gobe kana dama d'abirta ne bawa mota wuta,
tana isa harabar maikatar tasu tayi parking kana ta fito sauri-sauri gudu-gudu ta shiga cikin ainihin wurin kai tsaye d'akin tace murya ta nufa,
tana shiga tazo dai-dai masauk'in bakinsu,
taji abokin aikinta Rabeel na cewa.
"M.B. S Dukku, sai yanzu ne, ya mutanenki?."
bata kai ga amsa mishiba taji muryar d'aya daga cikin abokan aikin nata ta bayanta tana cewa.
"M.B Dukku, sai yanzu tun d'azu Abdulsalam da tawagarshi ke nan ya kasa ya tsare sai raba ido yake ta ina zaki fito bai saniba kina can cikin mutanen ki Nakasassu."
tsaki taja tare da cewa.
"Na damu dashi, in yayi ya haƙura ya bari d'an marasa zuciya kawai."
jin wani ya kuma kiranta yasa tace.
"Kai dan Allah ku barni in huta ni dai ba dama ku barmin suna ya huta, daga mai cemin Zalee sai me cemin B M Dukku sai masu cewa M,B,S Dukku irin Rabeel har Dukkun kawaima zai kirani,
sai yawan kiraye-kiraye kamar makaf.."
sai ta kuma yi shiru bata k'arisa ba.
su kuwa Dariya sukayi baki d'aya, kana Maigado tace.
"Yoh meyasa kikayi shiru? ki k'arisa mana ai mutanenki ne, ga kuma Rabeel d'an had'i kina fad'i zai yad'aki a shirin *Mu daku* ya sanar musu."
ɗan wani guntun murmushi tayi tare da cewa.
"Ai duk had'inshi bazai ci nasara a kanmuba dan sun san Zaleeha tasuce."
dariya suka kumayi dan Zaleeha ta kowace ita kowa natane tanada fara'a da farfar da jama'a kana ga kaud'i da rakad'i awani sashin kuma tanada tausayi da mutunci, kana tana da white blood tanada kwarjini, da shiga rai shiyasa duk inda ta shiga sai tauraronta ya haska sai yawan tsiwa. tsoro kuma tamkar farar kura. sai dai Raveel ya kula kwana biyun nan bata cikin haiyacinta da nitsuwarta.
Zaleeha fara ce k'al irin farin fulanin Dukku.
Wanda dukkan mazaunin gombe ko ince dukkan wanda yasan jamar Dukku yasa fulanine, kana fulanine da sukayiwa sauran tsashi na Gombawa zarrawa a fagen kyau ilimi wadata kiwo noma,
duk wanda yasa mahaifin Zaleeha Malam Bashir Sulaiman Dukku muddin yaga Zaleeha to tabbas zai san ita d'in jininshi ce, haka yasa take tsananin kama da Ya Ahmad d'inta duk da ubane ya had'asu,
Zaleeha kekyawace irin first class d'innan Kana babbar yarinyace yar gidan babban mutun mai daraja, wanda k'asarmu ke al'fahari dashi
sannan taurarinta na haskawa tutarta na kad'awa kasancewarta ga ilimi ga asali ga haiba ga kyau uwa uba ga kud'i, sannan ga kwarjini bugu da k'ari yanayin aikinta yasa ta zama so popular
ita ba doguwa bace kana ba gajeraba, irin dai tsaka-tsakin nance,
tanada jikinta dai-dai da shekarunta yar sumul da ita, tana shek'i tamkar tarwad'a, kana tana da asalin gashi na fulanin asali,
wanda babu surki gashinta har bisa kafad'unta bak'ine sitik kana yanada yauk'i da sulbi,
duniyar Gombawa da ma sauran inda aka santa sunanta na haskawa kasan cewarta maikaciyar gidan radio ne yasa muryarta ta sanu wa Al'ummar gari musamman matasa domin shirinta na mushaƙata yanada farin jini, kana fuskarta ta kasance sanenniya sabida aikinta daya shafi sashinsu na TV,
Duk na miji mai rai da lfy in yaga Zaleeha sai yayi sha'awar ta zama matarshi kana in kasan gidan data fito dole kayi sha'awar had'a zuriya dasu sabida ko ba komai ana zatawa damuna sanyi,
yayinda ita kuwa Zaleeha ta tarkace babin maza ta watsa a gefe, bana ce da ita ruwan idoba, to amman har yau mahaifinta da Ya Ahmad tare da Ya Aminu sun gaza gane dalilin daya hanata tsaida gwaninta, duk da gashi k'anwarta mai bin k'aninta Zakariyya ma ta kai aure hakama mai bin mai binta itama ta fara girma uwa uba tayi karatunta har ta d'an kwana biyu da fara aiki.
cikin Jerin masoyanta kuwa harda Manager d'insu duk da ya bar abin a ranshi ganin yadda wasuma ke neman shiga ta wurinshi kana ga abokin aikinta Raveel bar irinsu Abdussalam.
Chapter 55 · 0% Book details