← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 116

Sashe 104

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Malam Ashiru ne ya amshi zancen da cewa.
"Alhamdulillah an tsaida ranar ɗaurin auren."
Cikin zumuɗi Hayatuddeen yace.
"Yaushe ne auren?."
murmushi bappa Ali yayi tare da cewa.
"Yau saura kwana ashirin da takwas yadda lissafi ya nuna."
Wani irin zabura Hayatuddeen yayi tare da sakin sauti,
sai kuma yasa hannu ya rufe bakinshi tare da komawa ya zauna ganin wani irin kallon da Saifuddeen ke mishi alamun ya nitsu.
Zumbura baki yayi tare da karkaɗa kai.
Shi kuwa Saifuddeen wani irin yalwataccen murmushi yayi a cikin zuciyarshi yana mai jin wani irin zazzafan farin ciki na ratsa mishi jiki jini jijiya harma da ɓargo,
a fakaice ya kalli Hayatuddeen tare da yin mganar zuciya.
"Hmmmm am so sorry Hayatuddeen, duk farin cikin da kakeji baka kai niba, da kunsan yadda nakeji tabbas da kunsha mamaki,.
lumshe idanunsa yayi tare da ci gaba da batun zuci.
"Badan kunya da nakasar da Allah ya minba da nashayar daku mamaki, Wallahi ina ɗagowa daga sujjadar godiya ga mahaliccina sai inyi ta tsalle ina kurma ihu da kururuwa duniya tasan cewa ban taba samun irin farin cikin dana samu a yau ba."
a hankali ya buɗe idanunshi ya kalli,
Ahmad da fuskarsa ba yabo ba fallasa inda yace.
"Masha Allah, Allah ya kaimu lokacin bisa rai da lafiya."
Amin Amin suka amsa baki ɗaya.
Shi kuwa Saifuddeen sai godiya yayi musu kana ya kalli Umminshi da yake hango abubuwa biyu a kwayar idanunta farin ciki da fargaba mai tattare da tsoro,
ita kuwa Ummi zallan farin ciki dake cikin kwayar idanun gudan jinin nata take hangowa hakane yasa kaso 50 cikin 100 na fargabanta ya gushe.
kauda idonta tayi daga gareshi ganin alamun yana son keɓewa da ita,
cikin kula ta miƙawa Hayayuddeen Key ɗin BQ ɗinsu tare da cewa.
"Tashi kaje ka buɗewa su bappa Ali masauƙinsu kazo ka kai musu abinci."
Amsa yayi ya fita kana suma su bappa Ali dake son hutawa sukabi bayanshi.

Goggo Dada da Aunty Mina kuwa ɗakin budurcin su Raihana suka shiga dan duk sun gaji,
Ahmad ma miƙewa yayi tare da kamo hannun Raliya yace.
"Ke mu tafi bacci nakeji."
cikin jin kunya ta miƙe tabi bayanshi,
shi kuwa Saifuddeen ko inda suke bai kuma kallo ba.
Kai tsaye side ɗinshi ya nufa.

Yana shiga ratsetsen parlour'n shi yayi wani irin sassanyan a jiyan zuciya,
tare da lumshe manyan idanunshi,
murza masarrafin wheelchair d'in nashi yayi tare zaro harshen sa ya karkad'a a rashi yace.
"Kaddararki ce aurena Zaleeha, insha Allah sai kin amsa sunan matar wanna gurgun kurma nakasasshe ginennen tabon nan zai shayar dake zallan ruwan madarar da zata tsastsafo daka gareshi,
sai kin zama inuwar ni'imata,
wannan ginennen tabon sai ya zautar da kwanyarki."
A hankali ya fara zare rigar jikinshi yanayi yana shiga bedroom ɗinshi,
cire kayan jikinshi yayi can ya rage dagashi sai boxer d'inshi mai zanen fari da ja,
Bathroom ya shige cikin tsananin shauk'i da farin cikin cin nasara yake komai da kuzarinshi.
yana cikin bathtube ɗin wankan shi ya kalli surarshi tare da lumshe ido kana ya fara zancen zuci.
"Am sorry Baby zakisha bulalar nan da kika tab'o lafiyarta tsawon shekaru talin bata tab'a tashi tsayeba bare ta harba saida kika tab'a sashinta,
kuma daga ranar duk sanda zuciyata ta tunaki sai ta harba,
wannan shine yak'inin gidanta a jikinki yake."
A hankali dai yayi wanka yana fitowa yayi shirin baccinsa.

Bakin gadonshi ya zauna tare da mik'e k'afafunshi sannan ya d'aura system d'inshi a kan cinyoyinshi bisa dukkan alamu,
aiki mai mahimmanci yakeyi, wanda kuma fuskarsa cike take da farin ciki,

Yana cikin haka yaga Umminshi ta shigo bisa dukkan alamu itama ta gama shirin baccinta,
ganinta ya sashi muskutawa ya ɗan bata wuri,
ganin haka ta zauna gefenshi,
cikin tsananin jin daɗi ya ture system ɗin kana ya matsota a hankali ya raba jikinta kanshi ya kontar a kafaɗunta,
ganin haka alamune na yana cikin tsantsar farin ciki, ko tarin gajiya,
sabida Saifuddeen baya da juriyar hawala ko kaɗan in dai Umminshi na kusa to tana gane rauninshi shiyasa baya ma boye mata.
hannunta tasa ta shafa kanshi,
sannan ta matso da system ɗin cikin rashin kwarewa tayi rubutu a hankali.
"Gajiya ne ko farin ciki?."
ganin abinda ta rubutane ya sashi lumshe ido tare narkewa jikinta a hankali ya rubuta mata.
"Daɗi farin ciki kwanciyar hankali salama da annashuwa, Ummi yau ina cikin farin cikin da ban taɓa jin irinsa ba."
ya ƙarishe rubutun yana kallonta dan sam bai iya mata ƙarya."
murmushi tayi tare da cewa.
"Allah ya cika rayuwar auren naku da farin ciki."
A saman lips inshi ya amsa da Amin.
Sai kuma tasa hannu bisa bedside ta ɗauko cup mai ɗauke da zazzafan tea mai ganyen Na'a-na'a, ta miƙa masa.
karɓa yayi tare da ɗan zuƙa a hankali,
idonshi ya lumshe dan jin ƙamshin da tea ɗin keyi.
Ita kuwa Ummi a hankali tace.
"Sai da safe ko."
Kai ya gyadɗa mata alamun "To."
tana fita ta wuce bedroom d'inta,
kwanciya tayi amman baccinta yak'i zuwa nazari sosai takeyi tana tsoron duk wani abu da zaizo ya cutar mata da ɗanta.

Hayatuddeen kuwa a d'akinshi yana konce yayi ɗai-ɗai yana shan dadɗan sanyin A.C kana yana chatting da yan uwa da abokan arziki inda yaketa sanar musu date ɗin auren Hammanshi.
musamman a dandalinshi na Instagram wanda yakeda mabiya sama da dubu 9 wanda kuma yawanci sabida pictures ɗin Saifuddeen ne da yake sawa, da kuma son jin ainihin waye shi,
tarin tambayoyin da ake mishi bazai iya amsarsu ba,
sabida da yawama a zatonsu Saifuddeen bazai iya aureba.

Ganin tambayoyin sun mishi yawane ya rufe datan Instagram yana niyar buɗe WhatsApp sai ga kiran Amina ya shigo wayarshi video call.
yana ɗagawa yayi dariya ganin yadda ta haɗe fuska,
A ƙufule tace.
"Dariya ma na baka kenan?."
Cikin dariyar yace.
"Hmmm to ni me nayi miki naga sai hararata kikeyi?."
ajiyan zuciya ta ɗanyi tare da cewa.
"Yau kwana biyar kenan ina kiranka baka ɗaga waya meyasa."
da sauri yace.
"Sabida nasan zakice in bawa Hamma Saifuddeen wayar,
kuma duk sanda kike kira baya kusa shiyasa bana ɗagawa."
baki ta ɗan taɓe tare da cewa.
"Ai dai yanzu kam yana gida ko?."
Miƙewa zaune yayi tare da cewa.
"To amman ya shiga fa."
Da sauri tace.
"Please karkace komai ka kai mishi wayar. Dan Allah karkace a a."
jin haka ya miƙe tsaye ya nufi ƙasa.

Kai tsaye Side ɗinshi ya nufa inda Ummi ta rufeshi ta baya dan haka a sauƙaƙe ya shiga parlourn,
a hankali yace.
"Ni dai duk in da akace nawane sai ya koma kamar tirken doki,
kalli yanzu parlour nan ko sarkin makka zai zauna a nan komai tsab-tsab sai ƙamshi tamkar da turare ake mishi mopping,
kalli can kuma sama yadda banzayen nan su Imran suka wancakalarmin da parlour haka aka barminshi kamar wani maraya,
to yaseen yau a nan zan kwana."
Ya k'arishe mgnar lokacin da yake shiga bedroom d'in.

Ita kuwa Amina sai dariya takeyi dan duk taji me yake faɗin.
Yana shiga kai tsaye ya nufi kan gadon inda ya hango Hamman nashi na zaune wayar ya miƙa mishi cikin zumbura baki ya haura kan gadon ya konta gefen ɗan uwan nashi tare da rufe idanunshi wai shi yayi bacci.
Murmushi Saifuddeen yayi tare da gyara mushi rufuwan da yayi dan yasan bazai iya jure kwana cikin sanyin dashi yake kwana ba,
sai ya kuma juyo ya kalli fuskar wayar tashi daya miƙa mishi,
da sauri ya rage idanun nashi ganin fuskar Amina ita kuwa,
girarta ɗaya ta ɗaga mishi alamun ya dai.
sai ta kuma kalleshi cikin lunshe ido tace.
"Ya jikin ka?." bata tsumayi amsaba dan tasan ba samu zatayi ba shiyasa taci gaba da cewa.
"In zo har garinku har gidanku in dubaka da jiki,
in dawo Amman ko ka kira kaji mun dawo lfy ko?."
a hankali ya zaro harshenshi ya lashi jajayan labbanshi hakan yasa suka ƙara fitar da sheƙi,
Lumshe idonshi yayi tare ds longoɓar da kanshi bisa kafaɗarshi tare da narke fuska, haka nan yaji wani guntun murmushi ya suɓuce mishi,
ido ta lumshe tare da cewa.
"Bakinka yana min kyau, gashin girarka mai kyau, idanunka masu  tarin   kyau,  sajenka yana min  kyau sosai Hamma, ina son komai naka surarka, yan uwanka, abokanka ina son duk wani abu naka,
bayan Ya Amir kaine mutun na forko da nake bege da so."
shiru yayi ya zuba mata idanu, yana karantar lafuzanta,
ita kuwa cikin zazzafar soyayyarshi dake sarƙe mata zuciya da ruhi tace.
"Ina sonka Hamma Saifuddeen zaka aureni?  Kayi haƙuri kunya nakeji bazan iya rubuta makaba, kuma inajin kunyan in gayawa Hayatuddeen, gashi kai kuma baka jina to ta yaya zan shaida maka soyayyata,
ina sonka ka zamo mijina uban ƴaƴana, ina addu'ar Allah ya azurtamu da samun yara masu kama da kai."
sai kuma ta kalleshi ganin ya tsareta da ido haka nan yake jin kalaman nata har cikin zuciyarsa,
to amman wai meyasa ita bata kunyan faɗi mishi wasu abin ne, ita kuwa ganin yayi shiru ya kuma rage girmam idanunshi ne ya sata cewa.
"Ka gaji ko? bacci kakeji ko?, naga idonka yayi limshi, bari in kashe wayar sai da safe."
Tana kaiwa nan ta katse kiran,
shi kuwa Saifudddeen dariya yayi a ranshi yace.
"Sokuwa kawai mai tunanin yara wato kina sona, hmmm ke dai faɗi gsky bani kike wani soba, kinada dai abinda kikeso daga gareni."
daga nan yayi ta aikinshi.
sai kusan ƙarfe ɗaya,
ya sauƙo ya shimfid'a sallaya kana yaje yayi al'wala sannan yazo yayi nafilfilinshi sai d'aya da rabi ya konta.

Washe gari ranar Jummu'a tun da safe su Zaleeha suka dawo,
daga gidan Hajja inna tayi wanka ta wuce Billiri dan hira da nakassusun wancan yankin wanda k'arfe biyar na yammacin ranar jumma'ar ne zata gabatar da shirin, tun randa ta had'u da Saifudden a Jonapwd, bata sake zuwa canba,
kuma tunda ta turawa ishaq text ɗin ban haƙuri bai kulataba itama bata sake bin ta kanshi ba,
shi kuwa Ishaq shida Saifuddeen bakinsu a had'e a cewarshi ita da kanshi zata nemeshi har mazauninshi...
Chapter 104 · 0% Book details