← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 116

Sashe 64

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Dai-dai lokacin kuma su Ahmad da Adnan suka shigo,
bayan duk sun gaisa sun tabayi ya mai jikine sannan Ahmad ya kalli Ummi cikin nitsuwa yace.
"In sha Allah jibi zamu tafi india,
kuma Alhamdulillahi kafinma muje bayanan zuwanmu ya shiga hannun doctors d'insu."
cikin sauk'e numfashi Ummi tace.
"To Allah ya kaimu lfy ya kuma bada sa'an aiki."
cikin son kontar mata da hankalin Dr Adnan yace.
"Yanzu Ummi keda Ishaq zaku koma gombe gobe."
da sauri Ummi tace.
"In koma Gombe kuma?." Cikin nitsuwa Ya Rabi'u ya gyad'a mata kai tare da cewa.
"Eh Ummi ba matsala ke da Ishaq ku koma gombe,
Ahmad da Hayatuddeen kuwa dasu za'a tafi,
tare da Dr Adnan kuma shima in yaje ba dad'ewa zaiba in yaga anyi aiki dai to zai dawo kiji labarin jikin Saifuddeen d'in kuma,
in ya dawo keda Ishaq da bappa Ali zakuje."
kai ta sunkuyar kana murya a sanyaye tace.
"Yanzu sai in zauna a tafi dashi har wata k'asa ta daban."
Ahmad ne ya d'an kalleta tare cewa.
"Ummi nida Hayatuddeen zamuyi duk abinda zakiyi mishi karki damu zamu kula dashi."
still dai kamar bata gamsuba ido ta zubawa Dr Batulu da ta dafa kafad'unta tare da cewa.
"Ummin Saifuddeen ki kwantar da hankalinki shi jinyan namiji saida namiji d'an uwanshi hakama mace saida macce yar uwarta,
kuma duk sanda kikeson zuwa zakije ki duboshi."
cikin gamsuwa tace.
"To ba komai Allah ya shige mana gaba."
Sai ta kuma juyawa ta kalli Saifuddeen da yake kallonta fuska cike da bege murya can k'asa tace.
"Allah ya baka lfy babana."
Amin Amin suka amsa baki d'aya,
shi kuwa Hayatuddeen wayarshi daketa ringing ya d'aga ganin Salisu ne ya sashi mik'awa Ummi.
"Barka da safiya Ummi."

"Barka dai Salisu ya kasuwa?."

"Lfy lau Alhamdulillahi, ya Saifuddeen da jikin?."

Cikin rawan murya tace.
"To Alhamdulillahi jiki sai dai ace da sauk'i.
Amman yanzuma fa shiri akeyi wai za'a fiddashi k'asar India."
sai ta kuma share hawayenta tare da ci gaba da cewa.
"Kuma sunce wai baza'a je daniba."

Cikin k'arfin hali Salisu yace.
"Ba komai Ummi in sha zai samu lfy ki kwantar da hankalin ki,
nima daga nan in na gama abinda nakeyi bazan dawo Nigeria ba zan wuce can india inga jikinshi kafin in dawo,
ki kwantar da hankalinki ai yanzu duniya a had'e wuri d'aya take."
sosai ya bata k'arfin guiwa sannan yace ta bawa Ahmad nan ta bashi suka gaisa.

Daga nan duk suka tafi dan ganin azahar tayi kuma doctor yace su fita su bashi wuri ya huta.

Koda suka koma gidan Ya Rabi'u,
sosai Aunty Mami tayi ta karfafawa Ummi zuciya har dai ta nitsu akan washe gari zasuyi sammako diraban ya Rabi'u zai maidasu Gombe kana ya taho dasu Rahma suma su ganshi kafin ya tafi.

Washe gari bayan an idar da sallan asuba Ayuba ya d'auki Ummi da Ishaq dan zasuyi sammako,
jin zasu biya asibiti ne yasa Hayatuddeen cewa to zai bisu a saukeshi a asibitin.

K'arfe bakwai dai-dai suka isa cikin d'akin da Saifudden yake.
Konce suka sameshi kamar ko yaushe yana tsabtace dan masu gyarashi na fita ne su kuma suka shigo.

Hannu ya mik'o ya kama na Ishaq tare da rubuta mishi text.
"Please Ishaq ga Ummi na dan Allah kake yawan zuwa gida kana kontar mata da hankalin,
kaga tare da Hayatuddeen zamu tafi,
Raihana kuma itama in sunzo kawai ta koma d'akinta kada tace zata koma gombe,
dan Saminu yace min shima ya kusa dawowa,
sannan akwai system na a motar Sule da k'aramar wayata,
duk a bawa su Raliya su kawo min su."
cikin nitsuwa Ishaq yace.
"In sha Allah ba damuwa nima da Ummin zamu zo ai mu dubaka,
ba matsala zasu zo maka dasu."

Ita kuwa Ummi cikin sanyi ta shafa kan Saifuddeen har zuwa goshinsa,
cikin sanyi tace.
"Babana zan tafi yanzu zamu koma gombe sunce ku kuma gobe zaku tafi india,."
sai ta kuma share hawayenta tare da ci gaba da cewa.
"Zan tafi badon na soba sai dai kada suce na raina musu ne,
Allah ya k'addara saduwarmu kan al'kairi Allah ya baka lfy babana Allah yasa da akwai sauran ganawa a tsaka ninmu,
Allah ya baka lfy."
da sauri ya jawo tafin hannunta ya mannashi bisa hab'arshi yana mai zubda wasu zazzafan hawaye wanda ganin hawayen mahaifiyar tashi ne yasa nashi zubowa.
Hayatuddeen kuwa hannu yasa yana share mata hawayenta,
dai-dai lokacin Nurse d'in nan Amina ta shigo,
gefensu can ta tsaya tare da kallon Ummi dake kuka cur-cur da hawaye,
da sauri ta sunkuyar da kanta dan itama idanunta sun cicciko da hawaye cikin danne rawan muryarta ta kalli Ummi tare da cewa.
"Kiyi hak'uri Mama ki daina kuka in sha Allah zai samu lfy."
kai ta gyad'a tare da kamo hannun Saifuddeen d'in tace.
"Allah ya baka lfy."
sai kuma tasa hannunta ta share hawayen fuskarshi dana Hayatuddeen kana ta juya da sauri ta fita.
jin motsin ta fitane yasa Ishaq yabi bayanta, kai tsaye inda Ayuba yayi parking suka nufa,
suna shiga yaja mota suka fita daga asibitin suka nufi kama hanyar gombe.

A cikin room d'in da Saifuddeen ke ciki kuwa Ummi na fita Hayatuddeen ya zauna kan kujerar data tashi,
ya kife kanshi gefen pillow Saifuddeen yana mai shesshek'an kuka a hankali,
shi kuwa Saifuddeen rumtse idanunshi yayi yayinda wasu hawayen ke zubo mishi, a hankali Amina ta matso kusa dasu cikin nitsuwa ta iso gabansu,
ido ta zubawa fuskarshi Hayatuddeen tana kallonshi tamkar Aminu k'aninta mai binta kusan komansu dai-dai da Aminunsu.
a hankali tasa hannu ta tallabo fuskarshi,
ido ya bud'e jin an d'ago kanshi,
kai ta jujjuya mishi alamun ya bar kuka,
sai ta kuma zaro hankicib d'inta dake cikin al'jihunta ta mik'a mishi,
hannu yasa ya k'arba sannan ya shinfid'eshi bisa fuskarshi,
ita kuwa Amina a hankali ta juyo kan Saifuddeen wanda idanshi ke lumshe hawayenshi na zubowa suna gangarowa har cikin kunnenshi kasan cewar konce yake a rigingine.

K'ara matsowa tayi gab dashi,
yayinda shi kuwa yake kallonta ta tsakankanin gashin idanunshi.
hannu tasa dai-dai bisa hab'arshi sai kuma tayi saurin janye hannun tare da zuba mishi idanu,
ganin idanshi a rufene yasa ta sake kai hannunta duka biyu a hab'arshi na gefen dama da hagu,
manyan yatsunta tasa can k'asa idanshi sannan tasa sauran yatsunta hud'un ta tare tsakanin hab'arshi da kunnenshi sai ta jawo manyan yatsun tannan a hankali tana koro hawaye suna gangarowa tsakiyar tafin hannunta.

Shi kuwa Saifuddeen wani irin razanennen bugu heart beat nashi yakeyi so fast,
shiru yayi tamkar baya numfashi,
hakan ya bata damar share mishi hawayen kab ta tarasu cikin tafin hannunta,
sai ta had'e hannunta wuri d'aya ta murza ruwan hawayen nashi tare da shafa hannun nata a fuskarta kamar mai shafa mai.

idonshi ya bud'e tare da tsareta dasu,
ita kuwa da sauri ta juya ta fuskanci Hayatuddeen,
sai kuma tayi saurin kauda kanta ganin Hayatuddeen yana d'aga mata girarshi tare da cewa.
"Kin yi sa'a kin samu tabarrakin hawayen hammana."
allura ta ciro ta had'a kana ta mishi allurar sannan tasa hannu zata b'allo mgnin ta bashi sai kuma ta tsaya jin Hayatuddeen na cewa.
"Kada ki b'are mgnin bazai sha abin hannunkiba in ba wonke hannunki kikayi ba."
ba tare da tace komaiba ta juya ta d'au goran ruwan dake gefenshi sannan ta d'an matso jikin window ta d'an bud'e window ta wonke hannunta sannan ta juyo tazo ta bashi mgnin sannan ta juya zata fita tare da cewa.
"Ka fito ka barshi yayi bacci."
jin haka Hayatuddeen yabi bayanta,
suna fita sukayi kicibis dasu Dr Adnan da Ahmad.
nan ya juya ya shiga dasu Ahmad d'in.

Sama-sama suka gaisa sannan suka fito suka tafi gida.

Shida dai-dai Ayuba ya iso dasu Rahma cikin asibitin kai tsaye ya musu jagora d'akin da Saifuddeen ke ciki.
Chapter 64 · 0% Book details