← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 116

Sashe 38

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahmad da Mudassir kuwa har yau a gidan Adda Rahma suke,
ita kuwa Adda Rahma har yau Allah bai basu haihuwa da Ya Adnan d'intaba.
Warisu da Salisu kuwa suma yanzu an kusa bikinisu inda sun gina 'yan madaidaitan gida jensu a cikin unguwar Dubai cottars.

Ishaq kuwa shima yanzu ya fara taka k'asa,
tuni yayi gidan kanshi saidai har yanzu bai fara neman aureba,
yafi maida hankalinsu wa kula da k'ungiyarsu ta,
Joint national association of persons with disabilities,
(Jonapwd) gombe
state chapter. All the best!!! yayinda yanzu shi har ya samu muk'amin ciyaman a kungiyar,
Saifuddeen kuwa bai fiye zuwa ofishin nasuba sai dai yana matuk'ar bada taimako da dukiyar da Allah ya bashi ta sanadin nema da guminshi kusan akwai kason daya ware duk wata yakan saka a asusun k'ungiyar,
baya zuwa amman hannunshi na zuwa sai dai in zasuyi Mittin mai girma da mahimmanci to Ishaq na sashi zuwa bisa dolen-dole da zaran an gama mittin kuma zai tafi.

Ahmad kuwa soyayya yake zubawa Raliya sosai.

Yauma kamar kullum Hayatuddeen ya tasa Ummi da Saifudden da Rahma da tazo duba jikin Mamansu Ya Adnan a gaba,
fuska ya kwabe tare da tura baki cikin kalato hawayen dole yace.
"Dan Allah mu bar zancen auren Ya Ahmad da wannan yar cukului d'in shin nan."
bai kula Raliyya dake watsa mishi hararaba yaci gaba da cewa.
"Ni dai dan Allah ku rufa min asiri mu k'aura mu bar wannan gari na dukku wallahi ni dai na gaji da garin nan."
cikin irin son da iyaye ke yiwa 'yan autansu Ummi tace.
"Wai ni kam ku saurari autana d'innan mana yace muku ya gaji da dukku."
fuskarshi ya kuma kwab'ewa tare da cewa
"Ba waninnan Ummi ai duk kece kikak'i ki amince na san in kin cewa Hamma na mu k'aura dai zai yarda."
Rahma ce ta gyara zamanta cikin sanyin muryarta tace.
"Wallahi Allah ko Ummi nima ina son ku k'aura ku dawo cikin gombe kusa dani,
ku ganifa bani da kowa a can dan ma Allah yayi Mamansu Ishaq tanada kirki,
wlh ko Ya Adnan ma cewa yayi ya dai kamata ku dawo gombe ko dan karatun Raliya da Hayatuddeen,
dan cewa yayi ya kamata ace Raliya taci gaba da karatu ta samu koda N,C,E ne tunda sun nacewa juna ita da Ahmad kuma shi yace bai yi aure a gidan hayaba,
gashi kuma ya kasa k'arisa ginin gidanshi."
shi dai Saifuddeen ido ya zuba musu dan shi kanshi ya gaji da wannan zirga-zirgan kuma yana son faranta ran Hayatuddeen da Faruq,
shiru sukayi jin Faruq na cewa.
"Nima dai wlh na gaji da k'auyen nan yaseen ko mu k'aura mu koma gombe, ko kuma inbi Ya Adnan in koma gidansu."
cikin nitsuwa Ummi tace.
"To Saifuddeen ka jisu ko?."
Kai ya gyad'a mata alamun eh yaji,
cikin sanyi tace.
"To nima da kaina ina son mu koma cikin gombe ko dan tak'aitawa Saifuddeen zirga-zirgan da yakeyi kullum yana hanya tsakanin Gombe da dukku,
to sai dai haka kawai in na tuna mu k'auran sai inji zuciyata ta tsinke wani azabebben fargaba yazo ya rufeni shiyasa jikina ke mutuwa."
Da sauri Rahma tace.
"In sha Allah ba komai sai al'khairi kawai dai inaga fargaban rabuwa da inda kika saba ne shiyasa kikejin hakan."
kai Ummi ta jinjina dan kamar ta gamsu da mgnar Rahma,
cikin sanyi tace.
"To na amince Babana in dai kana son mu k'aura to na amince."
da sauri Saifuddeen ya kalli Hayatuddeen da Faruq da suka durk'usa gabanshi suna ta magiyar dan Allah yace shima ya amince."
kai ya gyad'a musu alamar to ya amince.
Ido suka zazzaro gaba d'ayansu dan ganin wani irin...!

By
*GARKUWAR FULANI*
8/18/20, 7:51 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*NAKASA BA KASAWA BACE*

*PAGE 11*

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

~Dan Allah kuyi haƙuri masu cewa in rufe group bazan rufeba! Sabida inada dalilin barinshi a buɗe~

_Lale marhababikun masoyan littafin Nakasa ba kasawa bace ina maraba daku, turo katin mtn na 300 kacal ta wannan number! 09097853276. Ko ka/yimin transfee ta bank ac na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, pleess ku fahimceni ɗari uku nace kuma ga number da zaki turo tanan ko ac no ɗina_

_Dan Allah dan soyayyarmu da annabi kuji tsoron Allah ku dena tambayata tsoffin littatafaina, sai kuzo ku haɗani da Allah in ban kulakuba inji ba daɗi, dan Allah 🙏🏻 ku bari bana so! Pleees fans ɗin hukuncin Allah da suka saya wai yanzu basu dashi ku dena tambaya bana so😡ku tambaya a gruops ɗin Hukuncin Allah, bana son shegen takura da rashin tausayi ,fisabilillahi a wuni zan samu pc sama da 1000, masu sabon littafi da masu son tsoffi da ƴan gaisuwa da wasu ga tarin rashin fahimta nayi bayani inda za'a turo kuɗin da adadin da za'a turo amman sai kaji ana, Slm Aunty Aishs ta ina zan turo/ koko Garkuwa nawane kuɗin littafin koma kece Garkuwa en nace eh sai ace wai ,a a ƙarya kike ba kece Garkuwa ba, ko kuma wai Garkuwa nake nema, koko wai dan Allah turo min littatafai masu daɗi jifa kamar ni baiwarsu ce ƴan gab da kano kawai yaseen ku ba ƙanenne uwata bace da amsa muku zai zame min wajibi_

Zabura da yayi tare zurma ihu mai cike da jin dad'i sai ya kuma zaro woyarshi dake cikin al'jihunshi samfarin infinix Hot 5 wanda a lokacin ita ake yayi, kid'i ya kunna tare da fara zabga rawa baji ba gani,
yayinda Faruq ma ke take mishi baya,
cikin yanayim fad'a Saifuddeen ya watsa mishi harara tare da mishi mgna cikin body language yace dashi.
"Irin godiyar da ya kamata ka yiwa Allah kenan bisa wannan ni'imar da yayi mana? rawa da ihu shine kaga ya dace?."
kai ya jujjuya mishi yana mai ci gaba da jujjuya k'ugunshi ganin haka yasa Saifuddeen yi mishi alamun cewa.
"To na fasa tunda hakane tunda bazaka nitsuba sai randa kayi hankali ka nitsu zamu k'auran."
da sauri ya nitsu tare fuskantar gabas kana ya gyara tsayuwarshi sannan yayi sujjadar godiya ga Allah,
yana d'agowa daga sujjadar ya fuskanci Hamma Saifuddeen d'in nashi cikin sanyi yace.
"Hamma Saifuddeen na nitsu dan Allah kada ka fasa kaji d'an uwana."
k'ara matsoshi yayi ganin bai kulashi ba sai ya kuma raunata fuskarshi sannan murya na rawa yace.
"Na tuba Abba."
cikin tausayin yaron Saifuddeen ya gyad'a kai dan duk sanda zai nuna mishi biyayya irin na d'a da uba to yakan ce dashi Abba.
tsalle yayi ganin Hamman nashi ya huce,
sai ya kuma lallatsa wayarshi sannan ya kara kunne jim kad'an aka d'aga.
Cikin tsananin jin dad'i yace.
"Hello Imran al'bishirinka."
A can d'aya sashin kuma cikin d'aga sauti da yanayin rawan kai da rigima irin na Hayatuddeen Imran k'anin Ishaq yace.
"Goro fari k'al ba dukke bani insha."
dariya Hayatuddeen yayi tare da cewa.
"Da kenan! yaseen yanzu Bagombe nake,
Hamma na da Ummi da Bappa Ali sun amince zamu k'auro."
wani wawan zabura imran yayi tare da zurma tsalle ya saki ihun da saida Ishaq dake gefenshi ya mik'e tsaye Mama kuwa dake bedroom ta fito parlour da gudu tana cewa.
"Innalillahi Imrana lfy kuwa meya sameka."
rawa yayi ya kuma juyawa sannan cikin karad'i yace.
"Su Hamma Saifuddeen zasu k'auro zasu dawo gombe,
yanzu Hayatuddeen yake gaya min."
sai ya kuma manna wayar a kunne tare da cewa.
"Hello Ba dukke kace wannan shekarar tamu ce lokacinmu ne kace birnin gombe zai amsa da rayuwar zafafan samari."
tsalle yayi tare da cilla woyar tashi jin Ishaq ya kama mishi kunne cikin yarfa hannu yake cewa.
"Wayyo Ya ishaq na tuba."
"K'arya kake baka tuba ba nasan ina sakeka zankaci gaba."
cewar Ishaq kenan Mama kuwa cikin farin cikin k'aurowar dasu Hayatuddeen zasuyi tacewa ishaq.
"Kai maza sakarmin kunnen d'an autana,
barshi yayi farin ciki,
nasan kaima d'in zakayi naka tsallen a side d'inka."
dariya sukayi baki d'aya kana suka zauna a parlour sukaci gaba da hirar,
mik'ewa Imran yayi ya d'auki wayarshi dake gefen Mama,
Suleiman ya kira wani abokinshi da suke yawan mgnar Hayatuddeen dashi ana d'aga woyar Sulaiman d'in yace.
"Hello Sulaiman."
da Sauri d'aya abokinsu mai suna Zakariyya wanda shine ya d'aga woyar Sulaiman d'in yace.
"Hege to ba Sulaiman bane Zakine."
dariya suka kece dashi baki d'ayansu sannan imran yace musu.
"Ba dukkenmu fa zasu k'auro zuwa nan cikin Gombe."
Sulaiman dake gefene yana jinsu yace.
"Yanzu Isma'il yamin text yake gaya min wai yaga Hayatuddeen ya fad'a a cikin what's app group d'inmu wai zasu dawo cikin gombe."
nanfa sukayi ta murnar dawowar da Hayatuddeen zai a kusa dasu dan sun saba sosai a media kuma duk sanda Hayatuddeen yazo gidan Adda Rahma to ranar dai su duka a gidanta suke wuni,
Imran, Hayatuddeen, Sulaiman, dan alhaji Sani, sai Isma'il d'an Alhaji Kabiru,
Sai Zakariyya wanda d'ane ga wani babban malamin da k'asarmu baki d'aya ke ji dashi,
kani kuma ga wani babban Pilot,
k'ani kuma ga wata shaharartiyar 'yar jaridar da taurarinta ke haska tutatar yayinda iska ke kad'a igiyar budurcinta kenta ya zama tamkar manuniya a gareta, *Zaleeha* sai kuma wasu sauran 'yan uwanshi...!

*****

Wata uku akayi anayiwa gidan duk kan gyare-gyaren daya kamata duk da dama gidan bashi da wani makusa yau aka gama komai na gyaran gidan.

Washe gari kuwa da Saifuddeen yazo shida Salisu a wata zazzafar motar da ys sarota a wannan satin.
kai tsaye gidan Adda Rahma suka nufa,
nan suka had'u baki d'aya,
Saifuddeen, Ishaq Salisu Ahmad, Warisu, Mudassir,
suka nufi federal law cos sukaje ganin gidan.
Chapter 38 · 0% Book details