Sashe 94
Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Naziru yaja hanci irin yanda masu zuƙar hoda sukeyi ya wani karkace yana hararar Zakariyya yace
"Kai ai kanka baya kawo wuta ne kwata kwata, kaji da Kuɗin mutane daka karba nasan sune matsalarka yanzu, zancen Gado kuma ai me sauƙi ne. Karka manta Yaya Tara ne a Ɗakin nan namu mu shida Maza a ciki munfi yan kowanne ɗaki yawa sannan mu muke da ruwa da tsaki a duk wasu sabgogin megidan nan, karka manta Kadarorin da uwar kuɗin kansu se abinda muka ga dama muka fito dashi za'a raba kuma ba wanda ya isa ya ɗaga mana yatsa"
"Wannan gaskiyane" Hajiya da tunda ya fara maganar batace komai ba ta faɗa tana gyara zama dakyau dan tafi jin dadin wannan Haɗi na Naziru.
"To idan suka haɗe mana kai fa? Kasan dai in suka haɗu sun nunka mu a yawa Mazansu da Matansu" Alhaji Zakariyya da yake jin shawarar Naziru bata kwanta masa ba ya sake faɗa, ta yaya za'ayi a zauna lissafin jiran Alhaji ya mutu? Cewa yayi yau ko gobe ze mutu?
"Kai kana bani ciwon kai wlh, a gidan nan kake zancen haɗin kai? Ko mu da muke Abokanan cin mushe muke cin dunduniyar junanmu ballantana kake maganar waɗanda a cikinsu akwai wanda suka fi shekara basu ga fuskar junansu ba, ni kana haɗuwa da Hussaini kuwa? Kasan zuwana Legos na ƙarshe kawai Mr Oniye ya ambato mun sunansa, wlh na manta a gidan nan munda wani Hussaini se lokacin wai yaron nan lasisin fitar da Mai ya taceshi yake nema bama ya siya a nan ba"
A tare Hajiya da Zakariyya suka zabura suna haɗa baki gurin cewa
"Hussainin?"
"Wlh fa, i was shocked irin kamar na faɗa tsakiyar transformer, kai nifa abun nan ma ya fara rikitamun lissafi ta yaya za'ayi ne mu mukeda kuɗi da iko from no where yaran nan su ringa fasowa suna mana over taking?" Nazirun ya sake faɗa, Zakariyya ya dunƙule hannaue yana kaɗa ƙafafu kamar mejin fitsari Hajiya kuwa kasa haɗiye kyashi, hassada da baƙin cikinta tayi kawai ta fashe da kuka tana cewa
"Nidai Binta ina ganin ta kaina a gidannan, na gama da Hadiza dakyar bangama da matsalar Aisha ba gata Zubaida tana neman ɓullo mun niko me nayiwa wani da wannan bala'u suke rikirkitomun haka wani bin wani?"
Haka taro ya watse dalilin wata sabuwa data bullo. (Ai daman duk wanda yace tukunyar wani ba zata tafasa ba to fa tasa ko ɗumi ba zatayi ba).
A bangaren Aminu Bechi tsohon AG kuwa cikin hukunci irin na ubangiji barinsa BECHI GROUPS ba'a ko cike sati ba yana zaune ya fara samun gayyata daga kamfanonin da suke hamayya da BECHI GROUPS din, wasu sun so jansa ne domin su samu damar da zasu karya BECHI GROUPS saboda sunsan dole yasan sirrinsu ciki da waje kuma korar sa da akayi tana iya saka yayi fushi ya nemi ɗaukar fansa a kansu sedai Aminunba haka yake ba, koda cewar beji daɗin abinda ya faru dashi ba kuma yana da wani Rauni daban a zuciyarsa gameda Chairman ɗin BECHI GROUPS wannan bazata saka ya ha'ince su ba domin karya Alhaji Audu daidai yake da karya kansa dan ko babu komai Uba yake a gurinsa shiyayi silar zuwansa duniya wanna ta saka ya karbi aiki a wani ƙaramin Kamfani dan be kai sauran da suke farautarsa ba,
Albashinsa be kai wanda ake biyansa a baya ba amma a hakanma ya godewa Allah tunda ya ishe shi yacigaba da biyan buƙatunsa na yau da kullum dan shi bashida burin ya tara kuɗi daman shiyasa tanadinsa ƙalilan ne, jin daɗi makura yana bawa Iyalansa a duk sanda dama ta zo kuma ya tabbatar ko be mutu ya bar musu komai ba wannan farin cikin da ya sanyasu sanda yana raue zasu ringa tunawa suna masa Add'u, abinda ya rasa daga nasa Mahaifin.
Rayuwa taci gaba da tafiya, wanda yake binta a sannu tazo masa da sauƙi, wanda suka ɗauketa da girma tana cigaba da kwallo dasu bugu ta kowanne bangare har ana rasa na inda za'a tare se fatan ubangiji ya kawo sauƙi. A cikin shekara daya da wasu watanni ginin katafaren Shopping Mall ɗin Ahmad ya kammala. Gini ne akayi shi badai ya gini ba, tsari da taswirar gurin kaɗai ta isa ta sakaka ka shiga kayi siyayya ko badan kana ra'ayin hakan ba. An fitar da komai a tsare, bangare bangare daga na kayan Abinci na dafawa dana kwalama dangin su Alawa su Biscuit, kayan sakawa na manya da yara, kayan amfanin gida daga kan sumunti har zuwa ƙarshen abinda ake buƙata domingida ya amsa sunansa na gida da akwai a gurin, kai babu ce kawai Ahmad ne zuba a gurin ba, kuma wani abin jin dadi yanda ya faɗaɗa komai ya bawa Yan uwa da Abokanan Arziƙi damar shiga su saka hannun jari, bashida kuɗin da ze raya gurin shi kaɗai dan haka yayiwo gayya.
Yan uwansa na gidansu kaf babu wanda be samu akan maganar ba ya kuma tallata masa idan akwai abinda yake so ya zuba ya kawo amma kaɗan daga ciki suka amsa tayin. Takanas yaje har Bechi ya samu Alhaji Babannan wanda seya shekara biyar be taka ƙafarsa a gidansu ba seda babban dalili koda yake waɗanda suke cikin Kanon ma ba zuwa suke ba se su ɗin dai da iyayensu suke cikin gidan su kadai suke dabdalarsu idan kaga wani a cikin sauran tofa ba ƙaramin abu ya faru ba tunda Alhajin yayi musu Aure shikenan kowa ya sallami kansa.
Ahmad ya samu Alhaji Babannan akan zancen Shinkafa wadda yakeyinta sosai kuma yana jin yanda ake yabon irin da yake amfani dashi ana siyan shinkafar sosai dan kamfanunuwa ne suke kwasheta da yayi girbi dan hatta da BECHI RICE suna siyan shinkafar Babannan ɗin saboda ingancinta.
"Ina ganin Yaya me ze hana kaima ka samu Alhaji kuyi yarjejeniya kamar yanda mukayi dashi, a maimakon ka ringa siyar da shinkafar daka Noma ya gina mala kamfani ka ringa sarrafata da kanka ana packaging kai tsaye kana siyarwa zakafi ganin ribar abinda kakeyi sosai kaga se a ringa ajiyewa a gurinmu masu siyan ɗaɗɗaya yan sari kuma suzo kamfani gurinka" shawarar da Ahmad ɗin ya bashi kenan.
Alhaji Babannan ya murmusa kawai, shiɗin bashida yawan magana tamkar marigayiya Bara'atu amma kuma dafin da yake cikin zuciyarsa yasa maganganun bakinsa basu da daɗi sam.
"Kaine mara zuciya da har abin hannunsa ya tsole masa ido ka iya neman Alfarma a gurinsa, yanda beyimun abinda ya zama wajibi na haƙƙina akansa ba bana fatan Allah ya kawo wani abu da ze sakani neman Alfarma a hannunsa komai ƙanƙantarta, abinda nake samu ya isheni rufin Asiri a duniya dan haka ka tashi ka tafi" amsar da Ahmad ya dawo da ita kenan tana masa nauyi a cikin zuciya ya kuma kasa amayar da ita ga kowa domin shi ubangiji ya hore masa ƙarfin zuciyar iya sirri komai girmansa komai ƙanƙantarsa.
Be daddara ba ya samu Ali ɗan uwan Aminu, bayan aikin kamfani yana siyan gyada ya kai kamfani a fitar masa da Mai yayi packaging ya siyar, a cikin waɗanda suke uba daya banda Jafar da baya cikin lissafinsu Alin na da saukin Hali se Hassan su biyun daman yasan da wuya suƙi tayin nasa Alin ya yarda yayi murna sosaima har yake cewa daman ya gaji ya fara tunanin haƙura da harkar saboda yanda yake shan wahala da mutane idan suka karɓi kayan kafin kuɗinsa ya fito. Hassan kuwa Magunguna yace ze zuba a bangaren Pharmacy da aka ware yace kuma ze tuntuɓi Hussaininsa wanda ko Lambar wayarsa Ahmad ɗin yace baya samu zeyi masa magana ko kuɗine se su haɗa su buɗe Pharmacy ɗin.
"Amma Ahmad idan ban shiga abinda be shafeni ba da se nace me yasa kayi register Kamfaninka da BECHI AND SONS sannan kayi Naming Mall ɗinka BECHI SHOPPING MALL? why not AHMAD BECHI SHOPPING MALL If you must include the Bechi a cikin sunan? Ni kaina dana buɗe Clinic ɗina da BECHI HOSPITAL I'm regretting kuma ina shirye shiryen chanza masa suna soon" Dr Hassan ya faɗa, Ahmad ya ɗanyi shiru yana mamakin dalilin
wannan maganar lura da hakan yasa Dr Hassan yi masa ƙarin bayani yace
"Magana tazo mun cewar yan gidanku sun cewa duk mu gama wahalarmu a ƙarshe komai da muka tara ya zama nasu mun sauƙaƙa musu ma da mukayi naming property namu da na Alhaji, dukda ni nasan ko sarautar hauka suke taƙama da ita babu wanda ya isa yazo anywhere near my property yayi claiming cewar nasa ne saboda uban nasu ma besan sanda na gina abuna ba balle su" Dr Hassan ya faɗa cikin zafin rai.
"Kayi haƙuri Yaya ka tausasa kalaminka akansa ko babu komai mahaifinmu ne Allah kuma babu ruwansa da wani abu da yake tsakaninka dashi wannan kyautatawa da bayar da girman dole kayi masa" Ahmad ɗin ya tareshi cikin ɗar ɗar domin dama damarsa ya gani akan Alhaji Babannan da har ya iya yi masa togaciyar.
Ajiyar zuciya Dr ya sauke kafin yace
"Hakane, thaks for reminding me, amma kamar yanda nake gaya maka kai kana tsakiya, you still didn't own the property hundred percent, and you know that Man, he can be cunning, ina tsoron ya maka shigo shigo babu zurfi yayi ta kwace maka kuɗi daga ƙarshe ya barka da rigima da Yayansa ko kuwa ya baka papaers ɗin guri komai is in your name now?"
Ahmad ya girgiza kai a hankali alamar Aa, zuciyarsa naso ta kama zancen Dr Hassan sedai amintacciyar na jaddada masa babu yanda za'ayi Alhaji yayi haka, yama za'ayi hakan ta faru? Ya tabbatar suffar da suke ɗorawa Alhajin bashida ita haba da kuwa ya cika ƙarshen Azzalumi a duniya ace ya rasa wa ze damfara se Ɗan cikinsa kai wannan abin ko a labari be taɓa jin anyi irinsa bama. A sanyaye yace masa
"Bai bani papers ba amma komai da mukayi a rubuce ne akwai copy a gurina da Lawyer na shima haka, sannan Baba Alƙali ya sani, Baba Abdullahi ma ya sani Barr Aminu ma ya sani da Baba Musbahu duk suna cikin shaidu"