Sashe 79
Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Bata tsaya iya nan ba tazo da Turarukan ta na ban mamaki se wanda ya gwada ze bada labari, Kedai kada ki bari de wannan damar ta wuceki domin ta zabtare Farashin kayanta har zuwa kaso 50% discount! Kyaso wannan gara basa ta wuce ki kuwa Indai ba Bintan Audu kike ba* 🥴🥴
*A tuntubeta a WhatsApp:09086233009*
*Ko kiran waya a 08029988065*
*Siyan Nagari Maida kudi gida*
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*
*PAGE 30*
Se gurin sha biyu na dare suka samu sauqin Jamar da suka cika gidan maqil kamar wani sabon yinin biki akeyi,Binta na daki ita da Lantana da yau ta samu guri ga qugunta gana Binta akan Kujera tana bata shawarwari ita dai Binta jinta kawai take badanta fahimta ba, yanayin da take ciki yau din baze misaltu ba, Tashin hankali Kishiya biyu a rana daya. Bata iya runtsawa ba har gidan yayi shiru alamar kowa ya watse, maganganun habaici tasha su a waqe sedai wai yau ita Binta ta gagara yin gaba da gaba da mutanen da sukazo har gidanta suka takaleta da bala'i, yanda yan uwan Hadizan suka zo, dukda basu shigar mata ba waqe waqensu kadai ya sanar mata a shirye suke jira suke ta tanka musu su qaddamar mata dan haka ta kama kanta tana lissafin abinda zatawa Amaruar da zarar an watse domin ta rantse ba'ayi Macen da zata sha gabanta a gurin Audu ba, dole ta fita ta bar mata gida tun gabanin dayar da yake iqirari ta shigo.
Tana zaune tana gyangyadi Audu ya shigo, tayi firgigit ta miqe, Lantana dai tuni ta kwanta tana janna Rago taji Laushin Katifa ita ko tuna tana da Miji da yaya batayi ba ta baje a dakin Bintan.
"Bakuyi bacci ba ashe? Daman wasu kaya nazo dauka se gobe idan Allah ya kaimu zan shigo gidan" ya fada daga inda yake tsaye kafin kuma tace wani abu ya juya abinsa ya fice.
Washe gari ma haka gidan ya tashi da hayaniyar Ƙawayen Hadiza da suka kwana a gidan kamar wanda suka rako budurwa, tana jinsu suna cigaba da Habaice habaicen da suka fara jiya, gidanbe zama nasu ba se bayan la'asar zuwa sannan Yan Bechi sun tafi Ƙawayen Hadizan ma duk sun tafi gida ya rage Binta da Amaryarta dake can sama abinta. Audu be shigo ba se bayan sallar Isha'i, Niƙi Niƙi da ledoji yana daga labulenta ƙamshin gasassun Kaji dana Tsire suka ziyarci hancinta dan ita din ba daga nan ba gurin iya tantance ƙamshi. A tsaitsaye suka gaisa yace mata seda safe ya fita, data rasa abinyi se kawai ta dora hannaye a kai ta rushe da kuka.
Washe gari bayan data gama lallashinkanta ta kuma tsara yanda zata ci uban Amarya domin ance ba'a bori da sanyin jiki, Ƙarfe tara tayi wanla tsaf ta sheƙa kwalliya irin wadda ta manta rabon da tayita, ta kashe ɗauri ta fesa Turaren da Mama ta bata sanda zasu taho, fuskarta fes amma da za'a tona ƙasan ranta yafi gawayi duhu. Ta fito saɓe da Naziru, tana fitowa tayi kyakykyawan gani, Amarya Hadiza cikin nata salon gayun ta fito daga tsohon kitchen ɗinsu na tsakar gida hannunta dauke da Fulas na ruwan zafi da kuma na Abinci.
Cikin taku me kama da rausaya ta kama matakalar bene ta haye abinta kamar bata lura da tsayuwar Bintan ba. Binta ta bita da idanu tana jin tamkar ta shaƙota amma ta cije, seda ta daidaici Hadizan ta isa saman har yaci ace ta zauna kafin ta yunƙura zata bi bayanta sallamar Lantana ta sake dakatar da ita.
"Yawwa, riqemun shi" ta fada tana miƙa mata Naziru ya lafe amma haka ta yakiceshi ta bawa Lantana ya kuwa tsanyara kuka amma bata dakata ba ta haye saman tana fadin
"Shegen Yaro me dafar tsiya".
Seda ta saisaita kanta ta gwada takun da zata shiga dashi kafin ta tura ƙofar ta shiga kanta tsaye ta durfafi dakin baccin Audu. Hadiza na tsugunne tsakiyar falon tana gyara zaman abin karin data ajiye musu tana kuma dakon fitowar megidan dake ƙarasa shiryawa a ciki tajo an buɗe ƙofa ta daga kai taga Binta ce bata kalli sashen da take ba ta wuce kai tsaye abinta zata shigar mata ɗaki babu shiri ta daka tsalle kafin Binta ta kai ga ƙofar tuni ta cimmata ta tare mata gaba cikin yanayina babu yabo babu fallasa take faɗin "baiwar Allah daga ina?"
Binta ta kalleta sheƙeƙe kafin tayi tsaki tace
"Ban gane daga ina ba? Kanki daya kike mun wannan tambayar ko kuwa baki san ni wacece ba sannan baki san cewar nan ɗin dakin Mijina bane?"
"Ɗakin Mijinki fa? da alamu kece kanki yake da motsi a ciki shiyasa har kika gaza tantance a inda kike, to idan ma ada nan din Ɗakin Mijinki ne a yanzu ba nashi bane mallakina ne, sannan ko ace har yanzu yana mazaunin Ɗakinnasa bakida damar ko shiga tunda ina ciki, kwana nane dole ki jira harse randa na gama uzurina na fita kafin ki shoga ki shimfida naki mulkin" Hadiza ta mayar mata da martani cikin lafazin dake nuna daidai nake dake. Binta ta lafta mata harara tareda da jan dogon tsaki ta kauce mata ta kama mabuɗin ƙofar tana cewa
"Idan na shiga se ki fiddo ni waje isashshiya me ɗaki" bata ko gama rife bakinta ba kuwa Hadizan ya fizgota ta maidota bayaz Binta tayi taga taga zata fadi ta kama bango, data tabbatar ta daidaita a ƙasa ta shammaci Hadizan ta wats amata mari.
"Bantan uba, kika mareni? Wlh kin jangwalowa kanki masifa da bala'i se kin san ni kika mara" Hadizan ta fada a haukace kafin tayi ƙasa, Binta na jira taga ko ramawa zatayi se ji tayi ta wawashi ƙafafunta kafin tayi wani yunƙuri ta kaita ƙasa. Dambe ne rikica ya sarƙe tsakaninsu, Binta nada garin jiki haka kuma tana da ƙarfi amma naci da dakiyar zuciyar Hadizan tasa take neman cin galaba akan Bintan dan tunda ta fahinci ƙafafunta nan ne Rauninta su take riƙewa ta watsar da ita a ƙasa ta hayeta ta kila idan ta mirgine ita ma ta sakata a Osi ta daka haka suke ta birgima a falon sun yi watsa watsa dashi labulen ƙofar dakin kansa yayo ƙasa sun rikito da ƙarfen.
Audu na bandaki ya ringa jiyo kamar hayaniya kamar kuma ana dukan Bango, ya bude ƙofa ya leƙo da kunnensa dan son tantance daga ina hayaniyar take tashi idan ba gizo ba se yaji kanar daga Falo ne, ƙarar fashewar abu dayaji Tusss ta sakashi rarumar Kwangorinsa ya ɗaura din daya jikinsa duk kumfar da be gama ɗaurayewa ba ya fito yana goge ta fuskarsa, yana buɗe ƙofa ya tarar da dambaruwar da ake kwasa a falon, ƙarar dayaji kuma Talabijin dinsa suka rikito da ita ta fashe basu ma lura dashi ba, seda ya buga musu tsawar da ta saka dole suka shiga taitayinsu sannan kowa taja gefe tana sauke numfashi kamar Zakaru.
"Wane irin hauka da dabbanci kuke mun a gida? nan ɗin sansanin dambe ne ko yaya? ke Binta me ma ya kawoki nan ma da farko?" Audu ya faɗa cikin tsananin fushi yana kallon Binta dataji jiki dan gar bakinta ya fashe yana zubarda jini. Cikin kuka tace
"Bakaga abinda wannn mahaukaciyar daka auro a matsayin mata tayi mun ba se tambayata kakeyi meya kawoni dakin Mijina?"
"Wane ɗakin Mijin naki? Ai kinsan banida wani ɗaki a cikin gidan nan yanzu. Banda fitina da son tayar da zaune tsaye meya kawoki? ki maza ki bar nan gurin kuma wannan ya zama kado na ƙarshe da zaki sake tako ƙafarki zuwa saman nan muddin bame dakince ta baki dama ba, fice Malama" Audun ya sake mayar mata da bacin ran dayafi na farko, Binta ta kalleshi ta kalli Hadiza dake sakin murmushin cin nasara wani kuka me tafe da zallar baƙin ciki da takaici ya zo mata seta wuce tana yinsa wiwi dan tasan a yanda ransa yake a ɓacen nan idan ta tsaya zubar da mutunchin seyafi haka Hadiza ta bita da kallo.
"Ke kuma akan me zaki kamata da dambe?" ya maida dubansa ga Hadiza se tayi ƙasa da kanta kawai ba tareda tace komai ba, yayi tsaki ya juya yaba ce mata
"Ki Gyara gurin kuma ki samarmun wani abun da zanci tunda kun lalata wannan"
"Yanzun kuwa in sha Allahu" ta fada tana duƙawa ta fara tattare barnar da sukayi ranta ƙal da beyi mata faɗa kamar yanda yayiwa Bintan ba.
Binta kuwa seda taji kanta na barazanar fashewa kafin ta haƙura ta dena kuka. Fuska tayi luhu luhu ga kuka ga Kutufon data sha a hannun Hadiza. Har mamaki takeyi yanda Hadizan da take gani tafi ƙarfi ta lallasata tilas ta canza salo tunda dai a doke ita zata ji jiki to ita ma ta ƙarƙashin ƙasa zata bi mata kamar sauran ta hanyar tuggu da munafunci dan ta rantse ba zata zauna ba ɗayar ba zata shigo ta tarar da ita ba. Ta tafasa ruwa ta gargasa jikinta ta kwanta tana cigaba da ƙulle ƙulle a ranta.