Sashe 119
Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH*
*MUNA GABATAR MUKU DA UMMU-MAHEER COLLECTION Ita din dai kuka sani taku ta gargajiya da take kawo muku kayayyaki irin na yangayu daga kan ATAMFA, BUYERS BATIK, COTONOU BATIK, SWISS LACES, LAGOS LACES, MAYAFAI, KAYAN KWALLIYAR YARA DA SAURANSU. TA SAKE SHIRYOWA TSAF DA COLLECTION NA HIJABAI IRIN NA AFEEN JAYY FA AMMA BANA HAJJAJU BINTA GUMAMA BA*
*YI MAZA KU GARZAYO DOMIN KUYI SIYAYYAR KAYAN SALLARKU A GURINTA CIKIN RANGWAMEN FARASHI GA BIYAN BUQATA*
*DA AKWAI NORMAL HIJAB ME HANNU, MARA HANNU, POCKET HAND SE WANDA KIKA ZABA KALA KAWAI ZAKI BADA AYI MIKI AIKIN, JILBAB DINMU TAMKAR SAUKAKKE DAGA EGYPT, WANDA SUKA SIYA ZASU BAKI TABBACIN INGANCIN YADINMU. DA AKWAI NORMAL YARD, AKWAI LONDON CREP IYAKAR KUDINKI IYA SHAGALINKI*
TWO PIECES GOWN DA V HIJAB NA YARA DA MANYA HARDA MA ABUBUWAN DA BAN FADO BA ZAKI SAMUSU GURIN UMMU-MAHIR DA YARDAR ALLAH.
*SANQAMA MATA KIRA KO CHATTING AKAN 08142548705/07061838488 KO KUMA KIYI JOINING GROUP DINTA KAI TSAYE DOMIN SAMUN LATEST DESIGN AND AVAILABLE KAYA DA SUKE A QASA*
*MADALLAH DA MASU SO FISABILILLAHI IRIN NA AHMAD BECHI*
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*
*BOOK 2*
*PAGE 12*
"Rayuwa kenan, duk waɗannan da kaji muna magana dasu a sanda mukayi makaranta ƙyamatarmu sukeyi saboda su lokacin a gaban Iyayensu suke mu kuwa Almajiranci aka kawo mu Kano, naci da dagiya tasa muka Shiga Bokon amma yanzu dubi ka gani kowanne cikinsu so yakeyi yayi alaƙa damu, bakaga roƙon da Alhaji Mustapha ya ringayiwa Babanku Alƙali akan ya ɗaga tafiyarsa Umarah yaje masa ɗaurin aurannan ba, Allah kenan wato shiyasa duk yanda mutum yake karka rainashi dan baka san me ze zama a gaba ba, a lokacin suna ganin su yan gatane se gashi a yanzu da Yan Bokon cikin su da Yan Kasuwar babu wanda ya zarce nida Ɗan uwana" Alhajin ya faɗa cikin Alfaharin abun.
Murmushi Ahmad yayi, be tanka ba dan Alhajin yakanyi magana shi kaɗai wani sa'ilin, ya tabbatar idan so yakeyi ya bashi amsa kai tsaye ze ambato sunansa a cikin maganar, to mema zece masa shi?
Yana wannan tunani kuwa yaji Alhajin ya sake cewa
"Ya aikin Super market ɗin kuwa? Jiya Asiwaju ya kirani yana ta zuzuta gurin yace har yafi na Kano girma da tsari ko?"
"Ina ga dai kallon tsoro yayiwa gurin gaskiya amma befi rabin na nan Kano ba, kawai dai yanda aka fitar da taswirar ginin ne yasa ya ɗauki hankalinsa, an kusan kammala komai dan har an fara zuba kaya ma, yace so yakeyi a buɗe ranar Bikin haihuwar Yarsa, daman na bari sena dawo ne se muyi maganar" Ahmad din ya bashi amsa yana shafa kai domin ko Legos ɗin baje baniyyarsa daga Zariya idan ya dawo Kano seya bi jirgi. Ginin sabon Shopping Mall sukeyi wanda wani Aminin Alhajin Asiwaju Bayerabe Attajirine a birnin Ikkoh ganin yanda Bechi Mall ya samu karɓuwa a Kano yasa yace Ahmad yaje ze bada fili suyi haɗin guiwa ya sake gina Bechi Mall a Lagos ɗin gashi har an kusa kammala komai se abinda baza'a rasa bane ya rahe a gurin.
"Ai tun daga plan daman da gani kasan ginin ze bada ma'ana, Allah ya sanya Albarka yasa a buɗe a sa'a. Maganar kayayyakin mu kuma idan kuna ka samu Idi kuyi yanda kuka saba".
"In sha Allah" Ahmad ya faɗa daga wannan seda suka sake shafe kusan minti talatin suna sharara gudu a titi kafin Alhajin ya sake cewa
"Ɗan uwanka fa? ya tafi ne ko yana nan har yanzu?"
"Aa ya wuce tun ranar Litinin, be kira waya bane?" ya faɗa yana satar kallon Alhajin. Shiru yayi harya fitar da ran ze amsa masa kafin yaji yace
"Kai kafi kowa kusanci dashi ka ringa masa faɗa kana nuna masa rayuwa shi yaro ne har yanzu baze gane abinda ake son nuna masa ba. Saboda nayi masa faɗa nasan uwarsa ce ta zugashi tace ya dena kirana ko? To ka jaddada masa wallahi, muddin na sake samun labari makamancin wanda ya faru sena a nan ze gane ni ba abokin wasansa bane, kuma daga ranar ya bar buga Ball".
"In sha Allah zan sanar masa, hakan ba zata sake faruwa ba" Ahmad ya amsa masa dan a yanda Alhajin yake magana ya hasala in kuma yace ze fahimtar da shi ya wanke Jafar daga laifin dayake zargin ya aikata yasan rufta kansa zeyi duk su hadu suyi laifi a gurinsa amma banda haka a bune a buɗe kawai dan shi Alhaji besan me duniya take ciki ba shiyasa ya ɗauki abin da zafi. Rape Allegation ai ya rigada ya zama ruwan dare akan Celebrities, Matan sun maida wannan harkar samun kuɗi a shekara Ɗaiɗaidaikun Manyan Celebrities ne suke tsallake sharrin Mata ba tareda kaji ance anyi ƙararsu akan sunyi Molesting wata ba abinda ya faru da Jafar kenan wata yarinya tayi Ƙoƙarin ɓata masa suna akan yayi Raping nata shi Alhaji har se bayan ma anyi case an gama yarinyar ta Ƙaryata kanta har kotu ta yanke mata hukunci kafin can ya gano tsohon labarin a Jarida.
Shine dalilin tattago Jafar yazo gida babu shiri, sunga Tijara daidai gwargwado wanda hakan yayiwa da yawa daga cikin Ahalin gidan daɗi dan Alhaji kulle ido yayi ya wanke Hajiya tass ita da ɗan gaban goshinta. Cewa tayi ita bataga laifi ba idan ma Jafar ya aikata abinda kace yayi, ubanwa ya kai yarinyar gurinsa?/ ko janta yayi ta ƙarfi? Basu suke bibiyarsa kamar jela yana yakice su ba banda ma rainin hankali Maza nawa ta buɗewa ƙafa se shi data raina take bibiya da sharri zatace ya mata Fyaɗe shine fa Alhaji ya zazzage mata tijara a tsakar gida yace ba zata saka yaje ya zubar masa da mutunchi a duniya ba. Abu ɗaya yasaka ya sassauta masa be tsaurara mataki akansa ba saboda sunan Bechi da be jona a sabgar ƙwallonsa ba, ba kowa nema ya san Ɗansa bane banda Close Family and Friends da yawa Muhammad Yayanta sukewa kallon Babansa dan dashi ake ganinsa ko Biography ɗinsa kayi searching it only shows Abdullahi Tijjani As his Father's name Nationality kuma Nigerian from Kano shikenan. Daƙyar Alƙali ya kashe maganar Jafar ya koma ashe Alhajin be haƙura ba.
Sun isa Haɗeja Lafiya kai tsaye fadar sarkin Haɗeja sukayiwa tsinke inda a can za'a ɗaura auran. Alhaji Mustapha Babandede yayi matuƙar jin daɗin ganin Alhaji Alhaji Audu Bechi, suka riƙe hannun juna ana gaisawa yanda Alhajin ya sake da tsofaffin Abokanansa ana gaisawa cikin barkwanci ya bawa Ahmad mamaki, koda yake daman hakane, duk girma da wani matsayi da mutum ya kai a rayuqa idan ya shiga cikin waɗanda sukayi gwagwarmayar Karatu tare se kaga duk an koma yara ana tuna baya. To tare akaci daɗi aka sha wuya, lokacin da kowa be gama fahimtar tanadin da ubangiji ya masa a rayuwa ba.
Yakubu ya taɓasu labarin daya kai Alhajin taron Tsofaffin ɗalibai a ranar har rawa yayi, wai hana yin video akayi shiyasa be ɗakko musu ba abun ya basu mamaki suka ringa hakaito Alhaji yana rawa wane irin farin ciki ne haka ze sakashi ya taka se gashi yau Ahmad yaga makamancinsa a fuskarsa dan Dariyar da Alhajin yakeyi harda ƙyaƙyatawa abin ya tashin kansa ya kuma sake tabbatar da Abotar makaranta tana da wani ƙarfi da tasiri na daban sama da sauran Abota, an girma shekaru sun taru amma idan aka haɗu se a ringa ji kamar an koma bayane.
Se bayan da aka ɗaura auren a gurin Reception ya haɗu da yayayen Abokanan Alhajin waɗanda suka kawo iyayensu. Wasu ya sansu suna hulɗa wasu kuma ranar ya fara ganinsu, Basu bar Haɗeja ba se ƙarfe huɗu bayan sunyi sallar La'asar kafin kowa ya kama gabansa. A hanyar dawowa Alhaji ya ware yana masa labari irinsu "kaga wane? Lokacin da muna makaranta fa kaza da kaza amma yanzu kalli kaza ya faru" Ahmad ya lura Alhajin na cike da shauƙin ganin tsofaffin Abokanai shiyasa yau harya maidashi abokin hira.
"Ya kamata ku motsa ku fito da mata kuma tunda ƙannenku mata sun tsaya shiririta. Kasan ban fiya mayar da hankali gurin gayyato tsofaffin Abokanai na na ƙuruciya sabgar auren yayana ba amma ina ganin wannan karon har Gala Nigh zan shirya mana ta yanda zasu zo su kwana musha hira kafin ranar ɗaurin aure" Alhaji ya fada.
Ahmad ya shafa ƙeya da hannu ɗaya yana murmushi me kama da dariya, wato su Alhaji har Gala Night za'ayi lallai abin nayi ne, shi kuwa Alhaji yanayin nasa se yasa yayi zaton kunya yaji da yace su fito da Mata tunda yau a giya tara yake yan mutunchin na kusa se yace masa
"Toakwai ta a ƙasa kenan irin wannan murmushi da kake bugawa, Yar gidan wacece?"
"Ƙuuu" cikin Ahmad ya kaɗa, maganar tazo masa a bazata, ba tanan ya shirya tasota ba. Ya rigada ya gama tsara takan Baba Alƙali zebi shi ze kaiwa maganar auransa kai tsaye tunda dai shima Alhajin idan maganar ta tashi shi ze wakilta amma yanayin nasa neman auran yasa gara ya fara samunsa dan ya tayashi gyarota idanma matsala ta shirya afkuwa yanzu kuma Alhaji na nema ya titsiyeshi, be kuma san ya ze ɗauki maganar ba idan ya sanar masa da wadda yake nema musamman da yaji ya tambayeshi Yar wacece kenan yana tsammanin ze samo yar wani Attajiri ko ƙusar gomnati wanda yana faɗar sunansa ze gano wanenene?
"Kayi shiru, ko babu ne?" Alhaji ya sake faɗa yana kallonsa. Harda rage gudu Ahmad yayi kafin ya saci kallon Alhajin yaga shi yake kallo shima sannan ya haɗiye yawu yace
"Wata yarinya ce Fatima, a Marmara gidansu yake amma cikin lungune se anyi tafiya kamar za'a shiga Alfindiki, Mahaifinta Bakanikene yana gyaran mota da babur Amma kafin ma na fara zuwa gurinta seda nayi bincike wlh mutumin kirki ne kwarai da gaske haka ma ita yarinyar tana...."