← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 137

Sashe 66

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza kai yayi cikin tsananin takaicin Audu ya miqe shima yace
"Banzo gurinka dan ka bani kudi ba kuma banyi maka abinda nayi shima saboda ka biyani ba nayi ne saboda Allah saboda kuma na daidaita rayuwarka tunda na fuskanci kai baka da alqibla ba kuma kasan ina kakw dosa ba. Abu daya da zance maka shine in har Allah yasa auranka da Bara'atu ya maidu kayi qoqari ka riqeta da kyau dan wlh muddin ka sake yarda Tuggu da makirci yacika ka rabu da ita se kayi nadamar hakan" yana gama fada masa ya fice daga Ofishinsa ya barshi nantsaye da kudi a hannu dan daman a sabon Kamfanin daya bude ya sameshi.

*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*

*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓

*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*

*Muna da magunguna iri iri*

*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*

*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*

*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*

*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,

*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*

*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*

*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*

*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*

*Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549*
*📲07011401314*

Karo na farko da jikinsa yayi sanyi akan bacin ran daya gani qarara kan fuskar Abokinsa koma yace Amininsa. Ya mayar da kudin Aljihu yabi bayan Hayatun da har ya fita farfajiyar gurin ya kwala maaa kira. Dalilin ma'aikata dake kai kawo a gurin ya tsaya, da yawansu duk Yan uwane da qannen Abokanan nasa ya kwaso daga Bechi ya basu aiki se kuma manyan ma'aikata wanda masu kwalayen makaranta ne ya dauka aikin su suke riqe da manyan muqamai a gurin.

"Mu koma ciki muyi magana" ya fada sanda ya cimmasa.
"Tsayuwar da kaga nayi anan ma Albarkacin wadan nan yaran kaci bazanso su gane cewar kowa kana da Baraka dashi ba" Hayatu ya bashi amsa. Audu ya bata fuska yace

"Wai wane irin abu ne wannan? Ni wai a wane kalar mutum kuka daukeni da duk abinda nayi kuskurene kowa ganin baikena yakeyi?"

"Ni kuma tsanina da kai ai magana ta qare Alhaji Audu, kayi haquri ma da katsalandan din da na maka bakina da bashida linzami ne ya kasa yin shiru, bari naje kaga Rana da daga zan iya rasa motar komawa gida" Hayatu ya fada daga nan yasa kai ya tafi ya bar Audu a tsaye a gurin. Jiki babu kwari ya koma Ofis ya zauna ya shiga Auna zamansa da Bara'atu da halayenta tareda na Bintan kamar yanda Hayatun ya shawarceshi.

Magana ta gaskiya ba tun yanzu ba yayi tunanin abubuwa da yawa da suka faru lokacin zaman Bintan da Bara'atu wanda ya fahimce su dalilin Auran Zubaida. Ya gasgata cewar A bayan idonsa Binta tana cusgunawa Bara'atu tayi amfani da yarintarta da wautarsa tayi wasa da hankalinsa abinda yasa ya fahimci hakan kuwa yanda ta kasa danne Kishinta akan Zubaida kuma har a gabansa bayyanawa takeyi shi kansa dalilin Auran Zubaidan ya fahimci halayenta da yawa da bata bayyana masa su ba a baya se yanzun kuma yaji rashin jin dadin yiwa Bara'atu uzuri a wancan lokacin har ya tsaya ya fahimci gaskiyar abinda yake faruwa ko ya bincika amma maganar mutuwar Zakariyya itace abinda ya gagara tsayar da matsaya akanta.

Magana ta Allah shida kansa ya zargi kansa daga baya da yanke danyan hukunci. Ya tuhumi kansa akan kasa bawa Bara'atun kariya koya shaideta saboda ai rainonsa ce, shine mutum na farko daya kamata ya gasgata duk abinda akace tayi ya san kuma tabbas bata da muguwar zuciyar da zata aikata kisan kai amma yanda Al'amura suka kasance a lokacin da yanayin zamansu hade da tasirin maganganun Binta ne suka juyar masa da hankali be kuma tashin gano hakan ba se bayan faruwar al'amarin daya wakana tsakaninsa da Zubaida inda qiri qiri Bintan tayi amfani da Duhun kansa ta ingizashi ruwa wannan ce tasa harya fara tunanin anya kuwa Lamarin Bara'atu ma babu lauje cikin Nadi kuwa?

To amma kuma seya tuna Idan sharri Binta tayi mata Ya Za'ayi yan uwanta harda Yaya Sakina su goya mata baya?

Gaskiya baya tsammatar ace gaba dayansu sun hada baki akan al'amari irin wannan tilas da akwai qamshin gaskiya a cikin maganar koda ba duka ba. Wannan abin ne har yasa yayarda ze maido da Bara'atun a ganinsa hakan ze wanke laifinsa a gurinta sannan ya daidaita tsakaninsa da yan uwansa qarfin guiwar sa kuma daya samu hadin kan Binta.

Kai shi kansa ma ya sake qullewa kuma, Binta ta nuna tana son Bara'atu batayi kishi da ita ba ya auro Zubaida ta kusa haukace masa balahira babu kalar wadda be gani ba sannan yanzu kuma da kanta ta sake cewa ya maido da Bara'atu wai menene hakan ma tukunna?

Shine a birkice ko kuwa Binta ce bata da alqibla????
To duk yanda ake ciki madai ya himmatu ze maido Bara'atu, kuma kamar yanda aka saba inya nausa baya jin kira dan haka baya tsammatar akwai abinda zesa ya canza wannan qudurin.

Cikin satin ya shirya yaje Bechin, ya tara yan uwansa ya sanar dasu qudirinsa Yakubu da Baballiya ne kadai basa gurin se Hashimu da yace bashida lokacin saurar Soki burutsunsa ba kuma ze yarda dan da aka haifa a gabansa saboda yayi kudi ya zauna yana masa fadanci ba dan haka babu shi akayi zaman

Dukkaninsu sunyi matuqar farin ciki da Al'amarin kamar yanda ya tsammata ya san kuma Yakubu se yafi kowa jin dadin maganar har ya qagu yaga farin cikin da zeyi, ya bawa Yaya Baba kudaden daya ware matsayin na sadaki sannan ya sake ware wasu akan a bata tayi shirue shiryen da zatayi.

"Aa, wannan ai kai ya kamata ka bata hannu da hannu bamu ba" Yaya Baban ya fada masa amma ya dage akan su hada duka su kai saboda ya shiryawa ransa bazasu hadu ba harse an maida Auransu tukunna saboda gani yake zama ta rainashi idan yaje gurinta yanzu, amma idan yayi haka se abin yayi kamar yan uwansa ne ma suka tursasa dawowartata karma ta gane zumudinsa tazo tace zata rama abinda ya mata.

Dasu ka kai kudi kuwa ba'a tashi daga gun ba Mala Sadi yace a shafa fatiha kawai tunda ba sabon Aure bane, a karo na biyu Audu ya sake qullo Aure Binta bata sani ba se bayan daya koma ya fada mata maganar cikin Yaren da ya ke so ta fahimta a sannan cewar "Su Babangida zasu dawo nan da sati biyu".

Ta nuna jin dadi da murnarta a fili a zuciyarta kuwa dariyar mugunta takeyi tana shirya yanda zata kwarzabi rayuwarsu a ruwan sanyi kuma ba zata sake bari su koma Bechi ba balle Bara'atu taci Arziqinsa ta silarsu.

"Se a gyara musu dakin nan na tsakar gida ko, amma harda Abdullahi zasu dawo dukda dai ya nuna mun ni ba uwarsa bace tunda Bara'atu ta bar gidan nan ko hutu ne sake zuwar mana ba" Bintan ta fadi cikin kissa, Audu yayi murmushi yace

"Hardashi duk zasu dawo shi za'a gyara masa dakin tsakar gidan dai tunda yanzu ya zama saurayi su kuma su zauna dakin Mamarsu".
Bata kawo komai ba haka bata tambayeshi dawa zasu zauna ba to ina ruwanta?
Su zauna dakin su kadai ita bataqi ma wuta ta tashi cikin dare su qone ba kowa ya huta da lissafinsu.

Haka aka fara shirye shiryen gyaran tsohon dakin Bara'atu inda kuma Zubaida ta zauna, duk a salon kissa da kisisinar data qaro kwas yasa tayi shiru tana gani ana kankare kankare da liqe liqe har qofofi aka irin wanda aka canza na dakunanta da saman Audun babu jimawa sababbin shigowa na zamani se tayi tsammin ya canza ne saboda gidan duk yayi kala daya. Aka sake fente tsajar gida, ana ya saura kwana uku Bara'atu ta tare su Bilki da wasu yan uwan Bara'atu uku harda Hadiza qanwarta suka zo mata danki na neman magana.

Tarkacen kayan jere kadai suka taho dasu dan Audu ya fada musu ze saka mata Gado da Kujeru, Binta na daki tana baccin bayan Azahar suka iso Lantana da Mairo su na tsakar gida, Mairo na kai kawo tsakanin Kitchen da bakin famfo ita kuma Lantana tana daga jikin katanga inda Inuwa ta sauka tana zaro zance wanda duk gulma da tsegumin matan unguwa ne takeyiwa Mairon ita kuwa tafi ki mutu bata ce mata amma hakan be saka tayi shiru ba se zuba takeyi.
Chapter 66 · 0% Book details