← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 137

Sashe 71

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dan Allah ya kukaji abincin yau? Har wani dadi ya qara na daban saboda mun hadu Ahali gaba daya munci tare, gaskiya haka zamu ringayi daga yanzu saboda ni daman a gidanmu mun saba tare muke cin abinci gaba daya kaima ai ka sani" ta yi maganar tana kallon Audu se shima ya murmusa ya mayar mata da cewa
"Kwarai kuwa, ina fatan kuma wannan hadin kan ya dore"
"Nikam daga gurina babu wata matsala ai kamar yanda na gaya maka komai daya faru a baya ya wuce itama ina fatan ya zama haka a gurinta dukda har yanzu dai naga ta kasa sakewa se ta ringa darare jikinta kana kallo fa tunda muka zauna yanzu bayan gaisuwa babu abinda ta qara cewa ta barmu muna ta zuba kamar lalatattun Radiyo" Bintan ta soko Bara'atu wadda kanta ke qasa tana kallon lallen da tayi kwanaki biyu da suka wuce sanda ta karbi girki maganar Bintan kuma bata saka ta dago kota amsata ba saboda ita har yanzun ranta yaqi Aminta da wannan takun na Binta ba kuma taso ta saki jiki da ita ta sake shammatarta irin na wancan karon.

"Nikam matsalata dake kenan Bara'atu kin fiya qauyanci kiyi abu wani salo salo kamar mara jini a jiki tsakanin nida Bintan waye baqonki da ba zaki sake a cikinmu kiyi sabgoginki ba?" Audu ya fada yana gyara zama.

Seta daga kai ta kalle shi, kalmansa sun mata zafi dan har kwalla ce ta tarun mata a ido, bata da dauriyar zuciyar da zata jure cin mutunchi ko tozarci yanzu zata karaya ta fara kuka banda tsabar wukaqanci ita ze kalla yacewa Baqauya to ya suke shida itan? ai babu me gorantawa wani Asali dan tushensu daya koda yake shi daman be iya maganaba.

"Haba kai kuwa ya daga magana kuma zaka fara ce mata yar qauye? Koda yake kunfi kusa ai, Qauyawa biyu, yan Qauyen Bechi" Bintan ta zage su duk su biyun a wasance garan kuwa se ya hau dariya yana cewa shi ba baqauye bane ai baqauye wanda bashida wayewa kenan shi kuwa da yake fes ko haihuwar Birnin ba zasu gwada masa wayewa ba ai ita kuwa Bara'atu abun ya sake qular da ita amma ta hadiye bata ce komai ba sedai ta quduri niyyar yi masa maganar muddin suka kebe, zata gaya masa bata so, karya sake wulaqantata a gaban Kishiya (as if zata iya).

"Yanzu dai muyi abinda ya taramu dare yanayi" Audun ya dakatar da wasan ganin Bintan na nema ta wuce gona da iri a wasan nata ta fara tabosu tana cewa wai kaf garinsu banda Yakubu waye yayi Karatun zamani dan shi kansa bata yarda yayi sakandiran ba
"Ke kuwa nasan dakyar ma idan kin taba shiga Aji" ta sake takalo Bara'atu wanna yasa ya dakatar da ita danshi basa shiri da raini.

Bintan ce dai tayi magana akan tsarin da take ganin zasuyi, Me girki ita zata dafa abinci wa gida gaba daya, zasu hade girkin kenan sabanin da da kowa takeyin nata sauran Ayyukan gida kuma shara da wanke wanke wadda bata da girki tayi harda sharar dakunan junansu sedai idan da wani uzuri ko lalura to dayar na iya daukewa dayar aikinta tsarin Binta kenan.

Maganar sharar dakunan Junan tayiwa Bara'atu banbarakwai dukda take Baqauyiya mara Ilimin amma tasan ko a karkarar da suka fito Kishiya bata sharewa kishiya daki sedai idan da lalura ina laifin iya tsakar gida? Tana jira taji Audun yace wani abu akai amma shiru sema jaddada hakan yayi da yace sannan ya juya kanta wai yana tambayarta ya mata ko tana da magana? Taga to me zata ce musu? Ta ce be mata ba su samun abun magana daga shi har matar tasa kenan se kawai tayi shiru suka gama abinda zasuyi ta musu sallama ta wuce se bayan data koma dakinta kuma abin yayi ta damunta, Balaraba ta gaya mata karta ringa barin magana a ranta muddin akan abinda ze cutar da itane, koda za'a ce bata kyauta ba gara ta fada a gyara akan ta bar abin a cikinta ta cuci kanta da kanta to amma tana gudun tayi magana kuma su canza mata ma'ana saboda muddin bada zuciya daya Binta tayi wannan abin ba to tarko ta hada mata so take tace wani abu ta ruftata ciki, haka ta kwana tana saqe saqen me zatayi?

Ta yarda da wannnan tsarin ko kuwa dai ta gwada sa'arta gurinnusar dashi rashin dacewar hakan? Bata son fitina ba kuma tason abinda ze sake janyo mata matsala da Binta ko Audu, a baya shiga dakinta na qasa da Minti biyar ya janyo har aka laqa mata sharrin kisan kai inaga yanzu taje shara?

A bangaren su Audu kuwa Bara'atun Binta ta gyara zama tana tsiyaya masa Zobo a kofi tace
"Se naga kamar Bara'atu bataji dadin maganar da akayi ba"
"Kinsan ta ai ita ba'a fiya gane ina ta dosa ba tunda kikaji bata ce komai ba hakan ya mata itama kenan" ya bata amsa bayan daya kurbi zobo. Ba haka taso ji ba dan haka ta sake kalailayewa tana cewa

"Uhm haka dai kace amma ni yanayin fuskarta na karanci kwata kwata maganar man bata zauna mata ba, idan lura kuma ai tunda kuka dawo daga Legas din nan tsumewarta tafi tada, kafin ku tafi ai tana dan sakin fuska idan mun zauna irin haka amma yanzu fa sedai tayita sunkuyar da kai tana irga yatsunta kodai har yanzu ta riqe abinda ya faru a baya ne a ranta?"

"To idan maganar abinda ya faru a baya ne ai ke ya kamata ki qullaceta ba ita ba tunda ke akayiwa laifi ko?" Cewar Audu, se tayi narai narai da fuska tace

"Nima dai hala na gani, nida aka cuta na dubi Allahmace na yafe amma kuma tazo tana so tayi zaman gaba dani idan fa ba a gabanka ba ko gaisawa bama yi bana so ina kawo maka maganarta ne kaga kamar wani abun nake so na hada shiyasa amma wlh sam duk yanda nake so na jata mu zauna lafiya taqi sakin jiki kayi mata magana in dai akan abinda ya faru take tunani dataqi sakewa dani wlh na yafe kuma na manta komai ta saki ranta mu zauna lafiya abinmu mu kama ka ram yanda ba zaka sake hango wata ba balle wannan karon ma ka sake kwaso mana Kara da kiyashi".

"Allah sarki Zubaida, aiko kin tunamun gobe idan Allah ya kaimu zanje na dubo su Hassan dukda dai nayi musu aike cikin satin nan amma gara naje na ganosu da kaina" Audu ya fada dan maganarta ta qarshe yasan da Zubaidan takeyi aiko abinda ya fada ya doketa har seda ta kware da Zobon da take sha ta ringa tuttula tari yana mata sannu dakyar ya lafa mata ido yayi jajir ta ringa maida nufashi zuciya na tafarfasa.

*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*

*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*❓

*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*

*Muna da magunguna iri iri*

*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*

*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*

*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*

*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,

*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*

*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*

*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*

*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*

*Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549*
*📲07011401314*

"Sannu bari na shiga ciki nayi wanka kafin ki gama" ya fada mata bayan da tarin ya lafa mata ya shige daki tabi bayansa da harara tamkar idanunta zasu zazzago. Tashi tayi ta hau tattare kwanuka ta sauka dasu zuciyarta fal da tunani, Wannan shi ake kira goma da Ashirin abu na nema ya hade mata biyu bata gama da wannan yar qauyen ba ya maido mata da zancen Zubaida ashe har aike yake musu yana kuma zuwa ya gansu?
Koda yake itace sakarya data manta da ita gaba daya matsalar Bara'atu tasha mata kai ta manta da batun tsinannun Tagwayen can data haifa to yanzu ita ina zata kama? Bara'atun zata bari ta koma kan Zubaida? Ko kuwa bari zatayi seta fatattaki Bara'atu sannan ta dira kan Zubaidar?

Tana hada abubuwan da zatayi amfani dasu a dakinsa take wannan lissafin a ranta, ta gama ta dauki ledar data zuba kayan, Nazirun na saman har yayi bacci Zakariyya kuma dasu Babangida zasu fita ya bisu yanzu da bata gama yanke yanda zatayi da Bara'atun ba tana bar mata yaron ya kwana da yan uwansa ranakun girkinta dan haka ta rufe qofarta ta koma Saman Audun tana ayyana matsalar Bara'atu zata fara kaudawa, zata bar Zubaidan tukunna dan tata me sauqi ce take ganin.
Chapter 71 · 0% Book details