Sashe 80
Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Audu kuwa fes suka karya da Amaryarsa suna raha da jin dadi ya mata sallama ya fice ba tareda yako leƙa ya gano halin da Binta take ciki ba. A haka yayiwa Hadiza kwana uku ya koma dakin Binta, a taƙin kwanakin nan kan Binta ta raina kanta domin duk wani tuggu da take jin ta iya Hadizan ta doketa ta shanye a kwana uku seda ta maodata abar tausayi a cikin gidan ta kankane komai ba ga me gidan ba hatta su Mairo se yanda tace dasu dukda daman Mairo bata da Matsala Lantana ce yar kwal uban kuma tun washe garin tarewar Hadizan ta saita mata zama data sakko da kwanuka Lantana na wanke wanake ta ajiye mata seta matsar dasu gefe bata wanke ba, bata kulata ba se da maigidan ya dawo har sannan kuma Lantana bata tafi ba taba daka dan yanzu ta zama ta hannun damar Binta da ita ake shawarta komai tunda basa haɗuwa da Turai suna zaune Audun ya shiga ya cewa Lantana ta fice masa daga gida an sallameta. Binta tayi tsugul zatayi magana ya yarfata yace idan ta sa baki se tabi Lantanar tunda gidansa ne akan me Matarsa zata sakata abu taƙiyi Lantana ta ringa tumami tana roƙon ayi haƙuri dakyar ya barta bayan yaja mata gargaɗi shikenan ta shiga taitayinta.
Kamar yanda Audu ya faɗi kwanan Juma'a na zagayowa Iyalan Gidan Sarkin Ƙaraye wanda suka samu rakiyar Ahalin gidan sarkin Kano dan can aka ajiye Amarya masu yi mata danki ne sukayi gaba suka dirarwa gidan Audu. Unguwa tacika maƙil ana ta kallon su masu busa Algaitu natayi. A cikin gida kuwa yai din ba Binta dake neman haukacewa ba su Turai na danneta hatta da Hadiza tasha jinin jikinta ganin wadda ake shirin kawo musu a matsayin ta ukun ta tabbatar wannan duk abinda suke taƙama dashi ta damesu ta shanye, abun da ta sakawa ranta kuma suka shawarta da Yayarta shine ta zauna lafiya da Amaryar, babu ruwanta da shirginta muddin ba ita ta sanyota ciki ba domin fada da saraki babu riba.
Se bayan Isha'i Amarya ta iso bisa da rakiyar Gimbiyoyin Kano da Ƙaraye da suka kawota. Dattijai ne na ƙwarai, dukda kasancewarsu sarakai sun san mutunci da darajar Dan Adam, sda suka shiga dakinBinta da kuma na Hadizan suka kai musu Amarya kamar yanda Al'adar Bahaushe take, kafin su iso Kano seda suka kaita Bechi gurin Dangin Audu suka kwana sannan suka dakko hanya washe garin suka iso Kano dan haka babu wanda yazo daga can.
Amarya na lullube cikin Alkyabba yar ubansu Ƙwarjinin matan da suka rakota yasa su Turai suka kasa iya daga ido dakyau su kalle su bare su gano ya Amaryar take, Binta dai tana kwance dan ta gagara zama abin dai ba'a cewa komai aka gama musayar gaisuwa da Miƙa Amana suka wuce dakin Hadiza.
"Dukda ban ga Amaryar dakyau ba gani nake yarinya ce ma babu wani abu da ze firgitaki akanta Binta" Turai ta faɗa bayan fitarsu. Binta tace
"Hmmm" kawai dan baki ya mutu.
An bar Amarya da kuyanginta guda biyu ragowar suka musu sallama suka wuce. Turai taso su leƙa Amarya tunda yan rakiyar sun tafi amma Zainab tace Aa, su bari sa dawo takanas su ganta kawai hakan sukawa Binta sallama suka tafi. Ranar Ango be kwana dakin Amarya ba, nan dakin tsakar gidan dai ya shige abinsa ya kwana. Washe gari kafin sha biyu Kuyangin Amarya suka ƙarasa mata gyare gyare sukayi mata sallama kamar yanda ta basu umarni su koma gidan sarki saboda Ango yace ayi masa uzuri base sun zauna ba da akwai masu taimaka musu da ayyuka har biyu anan gidan ya gayawa Yayanta Najibu kuma ya sanar da iyayensu suncr babu komai itama jiyan ya gaya mata shiyasa bayan sun kammala komai tace su wuce kawai.
Tun la'asar sakaliya Ango ya shige dakin Amarya wadda bata leƙo tsakar gida ba balle mutan gida su ganta. Hankalin Binta yayi ƙololuwar tashi da jin Al'amarin daya auku, kasa zama tayi ta tafi tagar dakin Amarya ta dasa kujera ason jin me zasu tattauna daya shiga daki tun yanzu tsabar zirgilli se gashi ta jiyo wa kanta abinda yafi ƙarfinta ta ringa kuka a tsakar gida jin Audu yana yiwa Amarya kyaututtuka cikin fitar hayyaci yace har gidan da suke ciki ya bata. Hadiza dake girki ta ringa wa Binta dariya kamar zata kife, faɗi take "Allah ya ƙara, a garin gulma da munafunci zaki jiyo abinda ze toshe miki dodon kunne ki dena ji gaba daya"
"Idan baki rufe mun baki ba senayi ƙasa ƙasa dake Hadiza" Bintan ta zaburo mata. Hadiza ta gyara tsayuwa ta dafe kwankwaso tace
"Idan baki fasa ba Binta, ai kin san karon mu dake wancan da nayi miki kadan ne wlh yau sace ki zanyi tas dan naga wannan luhu luhun jikin naki yasa kike neman masifar mutane"
"Zaki gane kurenki wlh dani kike magana" Binta ta maida mata tana shigewa daki dan ba hauka takeyi ba da zata sake gwabza dambe da Hadizan har yau bata gama jinyar ƙasusuwanta data tasamma karya mata ba.
Haka Ango ya yiwa Amarya sati guda, rawar kan da ya ringayi ba Binta ba Hadiza kanta ranta ya sosu amma da yake ita tana da kissar zaman duniya seta shanye bata ko nuna a fuska ba wannan tasa Audun yake ta tata ya kuma hadata da Amarya a cewarsa ta zama ƙanwarta ta ringa kula da ita Binta kuwa data tayar masa da hauka fita yayi a sabgarta ta nemi shiga sabgar yar Amaryarsa da banda gaisuwa da murmushi babu abinda ke hadata da mutanen gidan nan ya nuna mata ya fita hauka.
"Wlh ko bisa kuskure naji hannunki ya taba jikinta se kin gane baki da hankali" ya faɗawa Binta sanda tayi niyyar marin Aisha lokacin daya hadasu su ukun.
Haka aka ci gaba dagurgura rayuwa, watanni uku Bi ta ta tayarwa da Audu zancen ya kamata a ɗebo yaran Bara'atu da Tagwayen Zubaida su dawo gida kodan saboda makaranta dan a yanzun ta dan rage abubuwa a ƙoƙarinta na son maido da darajarta data zube a idona Audun. Ya kuwa ji dadin maganar harya zanta da Hadiza da kuma Aisha. Hadiza tace zata riƙe su, zata karbe kayansu tunda daki daya ne da ita ba ze yuwu su ringa kwana can ba se su zauna nan dakin da Abdullahi yake amma Binta tayi tsallen Albarka tace ba'a isa ba. Ai ita ta tado da maganar a dakko su kuma ita ta zauna da uwarsu ita suka sani sannan itace babba a gidan dan haka ita zata riƙe Yaran. Daman ita Aisha yar kallo ce a tsakaninsu, idan ba an sako ta ba tafi ku mutu bata ce musu, seta wuni a daki in har ba ita take da girki ba shine zata fito Mairo tanayi tana kallo harta fara karban wasu abubuwan tana tayata dan a gida bata girki kusan yanzu ne ya kamata ace an fara sakata ire iren wadannan ayyukan se kuma Aure yayi mata sammako shi yasa koda suke rigimar waye ze riƙe yaran bata saka musu baki ba ƙarshe da Audun da kansa yace Binta ce zata riƙe yara haka kuwa akayi ya debo su suka dawo gidan, an musu nisa a makaranta wannan tasa aka sake maidasu baya Zakariyya ya wucesu se aka hadasu su biyar harda Naziru aka saka su.
Zama yaci gaba matayen uku suka samu ciki kusan lokaci daya, Binta bata lura da cewar sauran biyun duk sun samu ƙaruwa ba domin a duk sallar da zatayi se tayi addu'ar Allah yasa duk su kasance juya basa haihuwa ita kuma Allah yasa duk shekara tayita haihuwar Yara Maza ta cika gidan dasu tana ta kaɗifiri da iyayi wai ita me ciki bata san su biyun ma sun rigata samu ba se randa zataje Asibiti ta fito ta gansu duk su biyun kowa da shirin fita, bata ta Aisha domin tunda ta ganta tace wannan me sauƙi ce Hadiza ce a gabanta dan haka ita ta harara tana cewa
"Karma ki kuskura kice yau ma binmu zakiyi, ba zaki tashi fita ba se kinga zan fita da Mijina to se ki taka ƙafarki ko ki fita ki hau Bus"
"To ai yau ba ranar girkin ki bace balle ki nuna mun isa da iko, Miji kuma namu zakice dan bake kadai kike dashi ba" Hadiza ta maida mata. Aisha na gefe tana kallonsu bata ce uffan ba sema lafewa datayi jikin katanga tana kallonsu sega Audu ya fito
"Uhm Bismillahi zaku fara ba kudai se kace kajin hausa wlh baku da aiki se faɗa ce cacar baki Allah ya sawwaƙa muku" ya faɗa yana baza babbar riga. Binta ta tunzura dan ta tsani wannan wulaƙancin da yake mata a gabansu ya ringa nuna ita ba komai bace daidai suke da ita dan haka tace
"Idan ma fita zatayi ka gaya mata ko ta taka ƙafarta ko kuma ta nemi Bus dan ba zata bimu ba"
"Tunda motar takice?" Ya mayar mata ba tareda ya kalleta ba, ya juya kan Aisha ya dan saki fuska yace
"Bismillah, muje ko?"
"Kuje ina? Au itama fitar zatayi?"
"Kinga Binta idan baki zuwa ki koma ciki suma duk Asibitin zasuje". Tana cika tana batsewa suka fita wajen tayi wuf zata shige gaba Audu ya dakatar da ita da cewa
"Shiga baya, Aisha ce zata zauna gaba"
Hadiza ta kwashe da dariya Binta ta sake ƙuluwa ta lailayo Ashar ta watsa mata ita dai ta shige mota tana cigaba da dariyarta.