← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 137

Sashe 117

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Don't call me that again" ta faɗa jinyanda Afee daya kirata ya saka tsikar jikinta zuba,
Tanaji yayi wani mayaudarin murmushi yace
"*AFEEYAH* God i love the name, gaskiya Dadynki ya kyauta daya saka miki suna me daɗi da Ma'ana, idan munyi aure nima zaki haifarmun tawa Little Cute Afeeya like you ko?"

"Qit" takashe wayar,, koda wanda ta sani bata wannan zancen shirmen ballantana da stranger wanda bata san mutum bane ko Aljan. Seda ta kashe Data ta saka wayar a Silent kamar yanda takeyi idan zata kwanta kafin tayi addu'a ta rufe idonta amma bacci yace be san zance ba, dakyar da taimakon Allah ya saceata. Kwana tayi tana mafarkin mutumin wai suna tafiya akan Gajimaren suna tsinkar furen soyayya.

Da Asuba ta samu tsarki tayi wanka tana Azkar Ahmad ya kirata suka gaisa ya gaya mata yanzu ze tafi Kano.
"Da wurwuri haka?" Ta tambayeshi, tana ji yana warming mota yace
"Alhaji ne ya kirani zan takashi Hadeja Ɗaurin Aure kinga dole na tafi da wurwuri karna ɓata masa lokaci"
"Haka ne, Allah ya tsare hanya ya kaika lafiya" tayi masa Addu'a ya amsa da "Amin" kafin sukayi sallama ta kashe wayar ta juya da niyyar maida kai taui bacci aka sake kiranta.

"Jarabar duniya" ta furta a fili ganin me kiran da farar Asubar nan se kace wanda yake binta bashi ze fara kira wannan wane irin mutum ne mara lissafi ta shiga mita a ranta amma hakan besa taƙi amsa wayar ba dan harga Allah can ƙasan ranta har wani daɗi taji daya kira.

Cikin dakakkiyar muryarsa ta Maza irin wadda zakaji kamar har echo tke yi yayi mata sallama ta amsa tana jin wani sabon yanayi yana mamayarta.
"Jiya kika kashe waya kuma bayan nace bana so, kuma nayita kira baki amsa ba why?" ya faɗa a tausashe kamar bacci be gama sakin muryarsa ba hakan ya sa muryar tayi wani amo na daban me tsinka jini, numfashi taja ta fesar amma batace komai ba yaci gaba da magana yana cewa
"Bana so, don't you ever hang on me again gara ki gayamun ni na kashe wayana da kaina if you don't want to talk to me, raini ne wannan kuma bana so".

Ta shagala da sauraron Muryarsa se kuna ta zabura tace
"Wai kai a matsayinka nawa ne da zaka ringa kafa mun sharaɗi?"

"Ina son tsiwa, amma bana son rashin kunya, idan kika ci gaba sena fasa miki baki, then i will keep kissing it har se ciwon ya warke" ya bata amsa seta hangame baki ta kasa cewa komai, baccin da take tattalawa ya kama gabansa.
"Afeeyah, i hate it when someone hisses at me, karki sake" ya sake cewa

"Waye kai?" Ta samu kanta da tambaya dan wannan gadarar tasa ta shallake ta masu hankali kuma,
"I will call you by 10am, kina free?" Be bata amsar tata tambayar ba ya jefa mata tasa
Ta wurga ido kamar yana gabanta kafin tace
"No, i have class by that time"
"2pm?" Ya sake faɗa se ta karkace tace
"That will be my resting time"
"In the evening?" Be haƙura ba ya sake tambaya ba kai tsaye tace masa
"Kasan me, ina da lokaci amma ba naka bane so you better respect your self and stop calling me talk less of Bossing around kana wani gayawa mutum abunda zeyi da wanda ba zeyi ba"

"Idan na kira karki daga kinji" ya faɗa yanda kasan wani Baffanta kafin kuma tace wani abu ya kashe wayarsa ya barta da baki a gantale.

"Afee don do new catch" Sururat ta faɗa teasingly, takaicin daya cikata ya sa bata tanka mata ba tana jin Badar na cewa
"Tun jiya take wata waya kamar ta munafukai koma wanene yayi ta kansa wlh dan ina gani babu wanda ya isa yayiwa Ahmad over taking".

Kwanciya tayi cike da jin haushin kanta da biyewa mutumin har ya samu damar raina mata hankali.
"Amma ya haɗu, haka take son tsayayyen namiji, ta tabbayar da Ahmad ne sedai yayita lallaɓata yana cewa tayi haƙuri".

AHMAD
Ƙrfe Tara da mintina ya isa Kano dalilin Hold up daya samu a Kwanar Ɗangora wata babbar Mota ta faɗi a tsakiyar Titi wannan ya kawo cin koson ababen hawa a titin dan se zagaye suka ringayi suka kaucewa inda hanyar ta rufe ma. A Ƙofar Katafaren Get ɗin gidan Alhaji Audu Bechi ya tsaya yana danna Horn, Issa ya tsallako da gudu daga gidan dake kallon nasu inda suke zaune da sauran masu gadin gidajen layin ciki. girmamawa yake masa sannu da zuwa
"Yi sauri Issa, na makara Alhaji yana jirana" ya faɗa ganin Issan ya tsaya ɓata masa lokaci da gaisuwa da sannu da zuwa hakan yasa ya wangale masa Get ya shiga.

Cikin Rumfunan da aka tanada domin Ajiye mota yayi parking, motoci ne birjik a gurin yanda kasan kamfanin saidasu, cike da murna ma'aikatan dake kaikawo a Kantamemen compound ɗin suka nufeshi suna masa maraba, duk saurin da yake haka ya tsaya yana basu hannu, babu kyama balle nuna banbancin kasancewar Barorin gidansu ne su yake mu'amalantarsu wannan Ɗabi'a tasa ta karrama Ɗan Adam yasa yake da farin jini matuƙa gurin mutane.

Junaidu daya daga cikin masu kula da shara ya ɗaukar masa Ƙaramar Akwatin da kayansa suke ciki, har ya nufi bangarensu na Mazan gidan yayi burki ya juya zuwa ainihin cikin gidan.

Da sallama ya shiga tsakar gidan shiru babu kowa kai tsaye ya doshi Falon Momy, ya kai tsakiya ya tsinkayi muryar Hajiya a bayansa tana cewa
"Aa, su uban Bilki an dawo kenan?" (Baba Bilki tana kiransa Babanta saboda Tace Asalin sunan Tijjani Amadu ne dan haka da Babangida da Ahmad duk sunan Malam Babansu sukaci shine Hajiya ta samu idan iskancinta ya tashi take ce masa Uban Bilki) Jiya Ɗan uwanka yake cewa kace masa zaka daɗe a Habujan se gaka kuma da Sassafe lafiya dai ko?"

Birki yaci yana cije lebensa, ya tsani sunan nan data ke kiransa kuma a duk sanda tayi hakan tana nufin zagin Baba Bilki ne ta yuwu sunyi hatsaniya shine zata fake da haka ta zageta da alama kuma yau da ɓurɓushin mutunchi tunda har ta kira Jafar da Ɗan uwansa
Seda ya daidaita fuskarsa kafin ya waiwaya ya kalleta, babu yabo babu fallasa ya durƙusahar ƙasa kamar yanda yake gaida Mahaifiyarsa yace

"Hajiya Ina kwana?"
Tana ƙara matsowa ta amsa masa da lafiya tana sake maimaita tambayar dalilin dawowarsa da safiyar nan da be bata amsa ba. Ƙatuwar Robar hannunta ya kalla ya girgiza kai, Nama ne shaƙe a ciki yau Juma'a da alama tayi halin, zuwa take ta zaftare naman Abincin sadaka da akeyi duk ranar Juma'ar, tun suna yara haka Hajiyan takeyi ko ran girkinta ko ba nata ba se taje ta kwashe Naman kuma babu wanda ya isa yace dan me hatta kuwa da me bada kuɗin Naman wato Alhajin gidan.

Gaba yayi yana ce mata
"Wlh Alhaji ne yayi mun kiran gaggawa zan rakashi Hadeja, yanzu ma sauri nakeyi nasan ya shirya ni yake jira". Ya lura da yanda murmushin kan fuskarta ya ɓace ɓat kamar ɗaukewar wutar Nepa hakan kuma nada nasabada jin cewar Alhaji ne ya kirashi.

Wucewa yayi ya barta nan a tsaye,
Da sallama ya shiga falon Mony wanda ya tarar da Ƙofar a buɗe, Momy na zaune a ƙasa tareda ƙanwarta Anty Maimuna da bata fi minti Goma sha biyar itama da shigowa Kanon ba daga Katsina inda take aure suna karyawa Ahmad ya shiga. Seda ya cire takalminsa sau ciki a baqin wajen kafin ya shiga yana sake nanata sallamarsa Momy da Anty Maimuna suka ɗago a tare kowacce fuskarta washe suna amsa masa ya zube a gabansu yana kallon Antyn nasa dake masa oyoyo kamar wani ɗan yaro yayi dariya yace
"Anty saukar yanzu ko nan kika kwana? Koda yake munyi waya da Momy dazun bata ce mun kina nan ba kenan yanzu kika zo".

"Zuwana " kenan Amadi ban daɗe ba, kayan lefe nazo haɗawa ƙnin Baban Sayyid nayi waya da shagon da zan siyi kayan basu fito ba shiyasa nayo nan na karya tukunna" ta bashi amsa seya ƙara washe baki yana gaisheta tareda tambayar Yaranta tace duk suna gida suna gaishesu kafin ya juya ya fuskanci Momy da murmushin kan fuskarta ya gagara gushewa saboda farin cikin ganinsa. Cikeda tsantsar ladabi ya gaisheta ta amsa tana tura masa plate din gabanta tace
"Nasan baka karya ba"
"Kai Momy, so kike Alhaji yamun faɗa kenan ƙarfe tara fa yace zamu tafi gashi yanzu goma ake magana" ya faɗa yana miƙewa tsaye, Momy ta goge hannunta da tissue tana cewa

"Dana ji shiru ma na zata har ka shigo kun tafi dan tun ɗazun dana kai masa abin kari naji kuna waya yace ka kusa gida da ai da Takwaran Alƙali zasu je ban san ya akayi tafiyar ta juyo kanka ba"

"Haba dai, kina da rai na taho daga wani gari na shigo har cikin gidan nan na fita ba tareda nazo na ganki kin saka mun Albarka ba ai ko bakida rai na shigo na kalli ɗakinki nayi miki Addu'a Momy" Ahmad ya faɗa, wani murmushi me nuna irin Alfaharin da Momyn keyi da kasancewar sa ɗanta tayi kafin ta miƙe tana cewa
"Ka hanzarta dan nasan yaji shigowarka karka ja yayi maka suruti" seya rusuna a gabanta yana cewa
"Zan fita"
"To Ɗan Albarka, Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya Allah kuma ya tsare ku daga sharrin ƙarfe" Momyn ta faɗa tana dafa kansa kamar ƙaramin yaro ya miƙe yana murmushi yacewa Anty Maimunan ya tafi itama tayi masa Addu'a kafin ya zura takalmin sa rabi ya fita da sauri jin agogo yana buga goma.

Anty Maimuna ta rakashi da murmushi kafin ta kalli Momy tace
"Allah kenan, idan ya baka dubu masu bata maka se ya baka ɗaya da ze wanke maka takaicin duka dubun nan. Yanzu ki gani har qofar dakin nan Salim yazo keda kika haifeshi baki isa ya leƙo yace ya kika tashi ba balleni baƙuwa zuwan yanzu kuma ba kunya ya karɓi abinci yayi tafiyarsa.
Chapter 117 · 0% Book details