← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 137

Sashe 51

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*

*Muna da magunguna iri iri*

*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*

*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*

*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*

*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,

*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*

*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*

*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*

*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*

*Kutuntube mu ta wannan number 📞08129249549*
*📲07011401314*

Ta cika faranti da Kazar da tsire ta lullube da takarda sannan ta bude kayan Marmarin suma ta diba a Leda tana kallonsa tace
"Bari na kai mata". Da kai ya amsa mata ta dauka ta fita ya bita da kallo yana tuna lokutan baya a zamanin Amarcin Binta. Kullun ta Allah se sunci Gasashshiyar Kaza da tsire da wani damun fura me shegen dadi da yake siyo musu suci su biyu ko takardar Naman Bara'atu da Yaranta basa gani balle suji qamshi. A sannan ma yakan siyo hardasu amma indai ya fara shiga bangaren Binta dashi to ya zama haramiyarsu daga baya ma ya dena siyowa dasu ta cusa masa ra'ayin ai suna ci a Miya kuma sanda tana Amarya itama an mata dan haka yanzun lokacinta ne taci ita kadai shiyasa yanzun yayi amfani da maganarta ya siyo musu shida Zubaida kadai itace Amarya ai itama tana ci a Miya.

Zubaida kuwa a qofar dakin Binta ta tsaya ta rafka sallama, Bintan na zaune ta zabga Tagumi, abin duniya ya isheta taji sallama, bata dauka Zubaidan bace ta amsa harda bada izinin a shiga. Ta shiga tana qara wata qaramar sallamar ganin itace ya saka Binta zabura tana binta da kallo tundaga sama har qasa, dukda kyashi da hassadarta daya cika mata zuciya seda ta yabi kyan da shigarta tayi to ina ga Audu?

"Ke bakida hankali koM meya kawoki dakina? Da izinin ubanwa kika shogo?" Ta fada cikin hargowar data zame mata jiki, Zubaidan tayi murmushi tace
"Seda nayi sallama fa kika amsa kafin na shigo, kuma ba wani abu ya kawoni ba, kazar Amarci Mijinmu ya sake siyomun shine nace bazanci ni kadai na na raba na kawowa Dana" ta dangwarar mata da Farantin a qasa ta juya tana tafiyar yanga Binta tayi kukan kura ta kai mata cafka, a yanda ta cakumeta Allah ya dubeta kamar jifa sega Audu ya fado dakin badan haka ba ta tabbatar da tace seta ballata ta zuba a wilbaro tabbas abinda tayi niyya kenan.

"Baki da hankali Binta meye haka zaki kamata da dambe?" Ya fada yana janye Zubaida da zuciyarta ke buga tsalle daga hannunta. Bata dauka jarabar Matar nan takai haka ba, ita ko doguwar cacar baki ba iyawa tayi ba ina dmga yar bawa hammata iska kuma ace da wannan qansamemiyar basamudiyar ai wata rana murus zata kasheta idan akace suyi dambe.

"Dole kace bani da hankali mana wato kai ka aikota tazo tamun cinikinta Abinda aka saba ko? Ni zaka wulaqanta Audu da abinda zaka sakawa ubana kenan bayan duk halaccin da yayi maka a duniya? Karka manta mahaifina shi yayi maka rigar da har ka ringa yawo a gari ka kwaso wannan karuwar, to wlh bazan zauna baqin ciki ya kasheni ba tattarawa zanyi na bar maka gidan ka idan yaso ka auro irinta goma ka ajiye gara na koma gidanmu inda ake sona" tayi bal da farantin kazar da aka kai mata ta shige daki tana kuka wiwiwi, diri diri yayi ya rasa me zeyi, ya bita ne ko kuma su fita su bar mata dakin?

"Ka bita mana karfa ta jiwa kanta ciwo kamar watsi take da kaya" Zubaida ta fada jin Binta na zubar da kaya a qasa se ya tafi solo solo ya shiga dakin ita dai Zubaida ta juya ta fice har sannan jikinta be dawo daidai ba daga tsoron shan suburbuda a hannun Binta. Bata san ya suka qare ba dan har bacci ya fara fizgarta kafin ya shigo ransa duk babu dadi ganin haka yasa daman tayi shirin bacci a kwance take tana jiransa se kawai ta gyara kwanciya dakyau tayi baccinta shima ya gama abinda zeyi be nemeta na duk yanda yake cike da zumudin kebewarsu amma ya gagara yin komai, yanda Bintan ta ringa kuka tana fadin zata tafi kawai ta shiga duniya yana wulaqantata ne saboda yaga Dadynta ya goyi bayansa sanda ta koma gida ita kawai gara ta tafi koma inane tunda babu me qaunarta ya shiga tsakaninta da Iyayenta kuma yazo yana wulaqantata akan Matar daya hadu da ita daga baya tasan baya qaunarta tun sanda aka kashe mata Da amma be dauki matakin komai ba.

Haka ya kwanta ransa duk babu dadi sedai da Asubahi da yar dagwas ta kaishi gari me nisa tuni ya manta da wata Binta da Emotional blackmail dinta. Tana can ta saki baki tana jiran ya bugo Asubanci yaci gaba da rarrashinta dan jiyan Data gama surutai bandaki ta shiga ta kulle yayi yayi ta fito taqi tace ya fitar mata a daki in ba haka ba zata kwana a ciki sannan ya tafi to ta dauka daya dawo masallaci ko kafin ma ya fita se shiga ya dubata amma taji muqus har gari ya waye tarwai se Tara saura na safe suka fito da Amarya yayi shirin fita, tana zaune kan barander dakinta Lantana na share tsakar gidan suka fito ta zube tana gaishe su.

Kamar jiya yauma harda dan risinawar Zubaida ta mata ta gaidata, bata tanka ba ta zabga tsaki bata dai yi masifar data sababa shirun nata kuma se yaji babu dadi dan haka yacewa Zubaida yana zuwa.

Falon Bintan ya shiga ya tsaya a tunaninsa zata bi bayansa amma shiru, ya leqo ya mata magana nan ma ci kanka bata ce masa ba wannan ya hasalashi ta wulaqantashi gaban me aiki dan haka ya fice fuu ko Adawo lafiyar da Zubaida take masa be amsa ba.

"Zaki san ni ba sa'ar wasanki bace wlh yau se kin gane kurenki badai jiya ya ceceki ba? Yau naga ubanda ze kwaceki a hannuna" Binta ta fada tana miqewa bayan data tabbatar Audu ya fice daga gidan tabi bayan Zubaida data qarawa tafiyarta sauri jin abinda take fada, gudu ta saka ganin dagaske kamata take shirinyi tana fadawa daki ta turo qofa Binta ta saka hannu zata dannata ciki bisa tsautsayi ta datse mata yatsa da qarfi take ya fashe ya fara jini.

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*PAGE 20*

"Akan me zaki kulle qofa? Dukanki zatayi ko cizo da ze saka ki kulle qofa har ki hada da hannunta ki matse?" Audu ya fada cikin kaushi yana duban Zubaida dake durqushe gabansa kanta a Qasa Binta kuma na daga gefe tana yarfe hannu yatsanta data datse da qofa ya kumbura idanun nan sunyi fici fici da alamun tasha kuka ba kadan ba yau din. Audu na yin sallama Lantana da bata tafi ba ta zube a gabansa tana fada masa uwar dakin nata babu yanda take tana daki, hankali tashe ya doshi Dakota n nata can ya tarar da ita tayi zaman dirshan a qasa tana yarfe hannu tana kuka harda majina, shiri sukayi da Bintan akan hakan dukda dagaske take jin azabar ciwon yatsan amma tuggun da take so ta hada da faruwar hakan shi ya saka ta sake rakwarkwabewa ba iyakar zafin ciwon ba.

Daya tambayeta ya akayi taji ciwon take ta gaya masa Zubaida ce, akan ta bita daki su sulhunta kamar yanda ya roqeta jiya akan tayi haquri ta kwantar da hankalinta su zauna lafiya to bayan tafiyarsa tayi tunani akan hakan kuma taga ya kamata ace tayi shine yau taje dakinta da niyyar ta bata haquri akan abinda tayi mata jiya a maimakon ta saurareta se kawai ta hau zaginta tace ta fitar mata a daki, data tsaya ta dafa qofar shine ta hada harda hannuta ta datse shi kuma kamar fulawar da aka zubawa Yeast ya shiga kumbura ya tafi fuuu ya kira Zubaidan nan gaban Binta ya titsiyeta yana tambayarta ba'asin dalilin rufe qofa.

"Ni ba a sanina na bigeta ba kuskure ne" ta fada cikin sanyin murya, Binta ta zabura tace
"Wlh qarya takeyi tana sane ai Lantana na gurin ka tambayeta kaji"

"To a tambayi Lantanar mana in har zata fadi tsananinta da Allah ko ita ta san ba ina sane na bige miki hannu ba, sannan ni bani na nace ki shigar mun daki ba bare har ki saka hannunki qofa ta datse ki" Itama Zubaidan ta katseta
Chapter 51 · 0% Book details