Sashe 123
Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ji tayi kamar an watsa mata ruwan sanyi, kalamansa sun shigeta har tsajiyar zuciyarta wani yamm takeji a jikinta. Cikin nutsuwa irinta wanda ya san kan soyayya da yanda ze farauci zuciyar mace a karon farko ya ringa tsarata. Tayi shiru tana sauraronsa, tayi nisa cikin hakaito kamanninsa, se ta ringa ji kamar kafin haɗuwarsu a makaranta. Sana'arsa data sani a yanzu ta bata satar amsa tabbas tana ganin fuskarsa a wasu guraren kamar posters, jikin Baburan Adaidaita sahu da sauran gurare. Ta tuna Sani Abokin Yayanta Jay ake masa dalilin son da yakeyiwa Ɗan ƙwallo Jay, amma ya akayi bata ganeshi ba? Koda yake ba wai kallon Ball takeyi ba shima shahararsa ce da kuma yanda su Yah Malam kullum basu da aikinyi se magana akansa tasa ta riƙe sunansa da fuskarsa amma kuma data ganshi a fili ya canza mata.
Be rabu da ita ba seda ya tabbatar ya isa duk inda ya kamata a cikin zuciyarta kafin yace taje ta kwanta dare yayi. Be tambayeta komai akanta ba, ta ringa jin wani iri, ta sani surah da kyan fuskar da Allah yayi mata ne ya ruɗi Jay zuwa gareta idan har yasan ainihin ita wacece tabbas ze gujeta, Sanannen mutum a duniya kamarshi bazeyi tarayya da yar Talaka kamarta ba balle har suje ga batun aure.
Yanda ya ringa nanata mata Hajiyarsa tana sonsa ya tabbatar mata da Mama's boy ne, yace a gidansu sunfi su Talatin, daga kuma few things daya faɗa mata akan familynsa ta fahimci suma suna da ire iren matsalolin da da yawan Manyan gidajen masu hannu da shuni wanda suka tara Iyalai da yawa suke fuskanta, wasu har a social media zakaga suna raba hali. Yanda ta fahimta suna da matsala irin ta yan ubanci a gidansu, ta tuna Ahmad shima gidansu suna da yawa amma kuma bata taɓajin ya gaya mata wata ɓaraka a tsakaninsa da yan uwansa ba, sudai Allah ya taimakesu toh.
Kwana tayi tana juya maganarsa da yake ce mata
"Amma kinsan san dana ganki banyi zaton zanji kinyi hausa ba because you look Asian, da akwai wata girlfriend da nayi Zoya she is from Korea amma Dad ɗinta ne Korean mum ɗinta is Arab from Iran so she has that Iranian look and Korean skin, oh my God you need to see her, i have never seen someone as beautiful as she is se ke dana ganinki kunyi kama sosai wlh tsayi kawai zata fiki".
"Ikon Allah" ta fada a zuciyata bangare daya kuma haushin wai girlfriend ɗinsa da taji ya ce ya kamata har bata san sanda bakinta ya furta
"Oh saboda nayi kama da Ex Girlfriend ɗinka yasa ka kulani kenan?"
"Ko ɗaya, sanda nake tare da ita ma she was the one pushing the relationship and i supported her just because she was nice, Zoya was the most beautiful soul i have ever met in my life tana da kirki na ƙarshe ta so ni she really wanted to marry me kuma ko ni i lokacin idan da zanyi aure it will be her but unfortunately she lost her life in a plane crash ta tafi ganin Mamanta a Iran from London bata da lafiya tafiyan da bata dawo na kenan sukayi hatsari shekara biyu kenan and since then i remain single".
Ita da kanta ta yarda akwai mutanen da kirkinsu yake sakawa dole kayi mu'amala dasu kamar Ahmad, ta kwatanta a ranta ace shi ya mutu, irin yanda taji yasa tayi saurin kawar da tunanin daga raita
Washe gari dakyar ta iya tashi baccin da bata samu isashshe ba, sun daɗe suna magana da Jay a waya sannan data kwanta ta kasa bacci tayita bitar hirar da sukayi. Shida da rabi ta idar da sallah tana Azkar ya sake kiranta ta ɗaga fuskarta da murmushin da batasan ma tanayi ba suka gaisa.
"Zan fita ne nace bari na fara kiran Baby na naji ya ta tashi, or you are still in bed?" Ya faɗa salonsa dake kassarata. A shagwaɓe tace
"Aa na tashi nayi sallah Azkar nakeyi yanzu".
"Kinyi mana addu'a ko?" Ya tambayeta ta ɗaga kai kamar tana gabansa se ya sake cewa
"Zan fita Training ki kula da kanki i will call you when I'm back ok?"
"Allah ya kaimu" ta bashi amsa a sanyaye dan se taji bata so ya ajiye wayar. Be sake magana ba ya kashe tana ajiyeta kiran Ahmad ya shigo seda ta harari wayar kafin ta ansa.
AHMAD
Yana zaune a gefen gadonsa, shigowarsa kenan daga masallaci tun Asuba kwana yayi da tunaninta, tunda ya farka da Asubar yaso ya kirata amma ya daure ya bari gari yayi haske.
"Fatima, meya samu wayarki jiya taƙi shiga na kira yafi sau goma?" Ya faɗa bayan data ɗaga wayar. Muryarta a kumbure kamar me bacci alhalin haushine ya cikata tace
"Bacci nayi da wuri, kuma ban sani ba ta shiga DND se yanzun dana tashi na cire".
"Haba nayi mamaki duk hankali na kuma ya tashi amma yanzu na samu nutsuwa tunda lafiya kike, ya school ɗin toh?" Ya faɗa har yana sauke ajiyar zuciya se kuma tausayinsa ya kamata wato So Jarabtace wanda Allah ya dorawa kaɗai yasan wahalarsa gashi itama idan batayi da gaske ba tana neman afkawa komar wanda ze wahalar da ita.
Ta miƙe tana ninke sallaya tace masa
"Lafiya lau nake, ya hanya? Kun koma Kano ko can kuka kwana?"
"A cikin Kano mukayi sallar Magriba ma" ya bata amsa ta haye gadonta tana cewa
"Masha Allah kunyi sauri gaskiya toh sannunka"
"Yawwa kema sannunki" daga nan suka ɗanyi shiru se ya sake cewa
"Bari na barki zaki koma bacci ko yau weekend nima cikin gidan zan shiga na gaida Momy se na dawo na kwanta an jima idan Allah ya kaimu zanje gurin Baffa kina da saƙo ne?"
"Aa, babu" ta bashi amsa se yace
"Toh shikenan ki kwanta we talk later"
"Bye" daga haka ta kashe wayar taja bargo dan bacci be isheta ba Badar ta fincike tana cewa
"Gidan uwar wa kika tafi jiya har sha biyu wayarki kuma bata shiga?"
"Not this early Badar bacci nakeji" Afeeyah ta faɗa tana sake jan bargon da taga zata takurata ta sakar mata ta janyo Hijabin data cire ta ƙudunduna duk kuma tsiyar Badar bata kula taba dan ita idan taso bacci babu abinda yake hanatayi dan mutum yaga dama ya dakko police band ya kaɗa baccinta zatayi sanin haka itama yasa ta barnta ta koma nata gadon tana cigaba da mita kafin tayi shiru tayi bacci. Se bayan Azahar da tayi wanka tana shiryawa ta lura da aika aikar da sauro yayi mata zaman da tayi a waje jiya jikinta yayi Jaa duk inda ya ciza ya tashi, Maman Minal tace
"Yauma cikin flowers kika je yin waya ko? Waini Afeeya wa kika samu da ba zakiyi magana dashi a ɗakin nan ba se kinje cikin sauro?"
"Bari na dawo ke kaɗai zan bawa labari Anty Zahra tunda mutane yanzu kowa boye sirrinsa yake" ta faɗa tana hararar Badar ta gefen ido, ta aje turaren hannunta da take fesawa ta kwaɓe
fuska tace
"Nasan idan kuka sani sena tsani kaina saboda tsokanarku duk na gama cika baki wlh So be kyauta mun ba wlh".
Suna class Jay ya kirata lokacin wayar na hannun Badar ta shiga Ig tana duba styles na ɗinkin da zasuyi da bikin Anty Yusra.
Ta miƙa mata wayar ta ɗaga ƙasa ƙasa tace masa
"I'm in class zan kiraka in mun fita" ta kashe.
"Waye kuma Jay kika samu?" Badar ta tambayeta bayan ta maida mata wayar, tayi fari da ido nace
"New catch, a big fish"
"Yaushe kika zama Money monger Afee?" Ta faɗa tana kallonta, Afeeyah ta zare ido tace
"Daga cewa Big Fish? To na janye ni ba abinda nake nufi kenan ba matsayinsa nake kwatanta miki, Professional footballer ne a Arsenal yake wasa ma"
Seta kalleta da sauri tace
"You mean JAY? No you must be kidding, Afeeyaj a ina ma ze ganki yana UK kina Nigeria? bama wannan ba JAY fa Afee, yes i know you are Beautiful, kin kai a soki but JAY noooo. A yanda nake jin labarinsa he can't date Nigerian girl Hausa for that matter. Shifa ko yammatan da ake ganinsa dasu se kin kallesu kin sake, irin models din nan ne da zakiga kamar su suka yi kansu sedai idan wani ne yake so ya yaudareki da sunansa dan ko a IG kika duba accounts masu sunansa sunfi dubu ma".
Kasaƙe tayi tana kallonta, koda ba laifinta bane gaskiya duk wanda tacewa JAY dai na Arsenal take waya dashi kallon batasan me take cewa ba zeyi mata amma dukda haka se tace mata
"Toh Badar ina shi Bahaushene me yasa za'ayi mamaki idan yaso Bahaushiya kuma lower class irina?"
"Yes Bahaushene Dan Kano nema aka ce amma abinda nake so ki duba shifa babban Celebrity ne, koda yake ke ba sabgar Ball kika sani ba amma da keda kanki idan aka ce miki shine sekin ƙaryata. Kamar fa kice min Messi ya kiraki ne ko Ronaldo".
Maganar Badar ɗin ta sakata tunani domin abinda ta faɗi yakan iya zama gaskiya tunda dai ita ba sanin wancan Jay na gaskiya tayi ba haka kuma wannan sau ɗaya ta ganshi sedai tabbas akwai kamanceceniya a tsakaninsu to amma menene ribarsa idan yayi mata ƙarya da sunan wanda ba shine ba?
"Dubo mun picture ɗinsa na gani indai shine zan gane" ta faɗawa Badar, seta kalleta kafin tayi dariya da alama cewar da tayi idan ta ganshi zata gane ne ya saka Badar dariyar.i
"Ashe kun haɗu face to face ma? ko hoto ya turo miki?" Tayi mata tambayar da sigar rainin hankaki ita kuma Innocently tace mata
"A school ɗin nan fa muka haɗu Badar ranar Monday da ace kina nan kema da kin ganshi na fito zan tafi class da safe ya tareni kuma shine wanda Sahid yace ya bawa number ranar da muna tare dake".