Sashe 113
Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"What is Kalali? Because i know Badariyya, when ever she speak big big Hausa word she is up to no good" dukda yanda nake jina amma seda nayi dariyar maganarsa Yusuf yace
"Tana nufin you are a good match maker"
"Ehen" Sahid din ya sake fada da alamar be yadda da abinda ya fada ba amma se ya maida hankali kaina yana cewa
"He gave 100$"
"Kaji daɗi" Afeeya ta faɗa tana miƙewa saboda cikinta daya hautsina, tsallakesu tayi ta fita da sauri can gurin fanfo tana zuwa ta shiga sheƙa Amai masu wucewa suna binta da sannu. Kamar ta kunno ciwo tana gama aman marata ta riƙe ita da bata Mp se gashi ta gagara tashi tsaye daga gurin seda Badar tazo ta ɗagata.
"Muje Hostel kawai daman baki da lafiya amma kika fito?" ta faɗa suna tafiya a hankali. Yusuf ne ya kaisu har gaban Amina a motarsa kafin suje ta galabaita juye juye kawai take a cikin motar na azaba dakyar ta iya fita ai kuwa nan gurin Security ta kwanta tana kuka shaɓe shaɓe kamar wadda zata haihu, abinda bata sababa, bata taɓa experiencing ciwon Mara ba se lokacin shiyasa take jinsa wani sabon abu kamar zata maɗe.
aka daka saboda ciwo.
"Sannu Afeeya me yake damunta?" Anty Amina daya daga cikin matan security da mmsuke mutunchi dasu ta tambayi Badar,
"Inaga zazzaɓi ne" Badar ta bata amsa Afeeya ta nuna musu mararta da hannu, cikin tausayawa Anty Aminan tace
"Wayyo sannu, daure ku ƙara ciki se kisha ruwan zafi da pain relief, Allah ya kawo Afuwa"
"Kuje kuyi aure yara kun zauna kuna fama da ciwo" Ɗaya matar ta ɓaro maganar, Badar ta Anty Amina suka kamata ganin an fara taruwa akana kallonta wasu na cewa Aljanu takeyi. A common room suka ajiyeta ta kasa zama kan kujera se a ƙasa ta kwanta tana cigaba da murƙususu, ashe haka Matan suke ji amma ta ringa cewa Bafar raguwa idan tana ciwon Mara yau gashi Allah ya kamata itama kamar fa an hura mata wuta takeji a gurin wannan abu da akwai Azaba.
Ta fi awa a gurin kafin ciwon ya lafa mata lokacin har gashin kanta seda ya hargitse kamar wadda tayi naƙuda. A duddƙe ta ringa tafiya har sukaje ɗaki, duk wanda Badar ta gayawa abinda yake damunta se yayi dariya kafin ya mata sannu dan haka take musu. Sururat ta haɗa mata ruwa me zafi takai mun banɗaki kafin ta fito Badar ta haɗa mata shayi me kauri ta gyara mata gado, kamar wata sarauniya haka suke lelenta suna mata iskanci kuma, tasha Paracetamol ta kwanta bacci ya kwasheta wata Jalalar Mutumin ya sake diro mata a mafarki amma ba irin na daren jiya ba.
Na daɗe sosai tana bacci har gurin qarfe biyun rana kafin ta farka ta ji daɗin jikinta se abinda ba'a rasa ba. Kamar me ciki ta seda ta sakeyin Amai kafin tayi tsarki da ruwa me dumi sosai ta canza pad ta koma ɗaki tana tafiya salaf salaf kamar waddata fito daga Labour room.
"Abin nema ya samu" Ummi ta faɗa ta harareta kafin ta zauna kan Gadon Maman Minal tana cewa
"Tun jiya Ummi daga zuwa Lecture baki kwana a nan ba?"
"Bayan na fito daga lectures ne na hadu da Surayya shine kawai na bita City tunda yau banida lecture, yanzu ma motar bati na samu shiyasa na taho da wuri" Ummin ta bata amsa kan tabi Cousin ɗinta city gidan Antynta.
Afeeya ta kalleta badan ta yarda Zaria City tasan baze wuce yawonta na banza ta tafi ba. Ummi bataji ko kadan, ta santa tare sue a English da zasu shiga Level 3 ɗin nan ta bari ta koma Library science saboda rashin mayar da hankali ana nema a koreta, party da clubbing a Zaria babu inda bata sani ba yanzun a hakan ma ta rage ne zama dasu suna matseta dole ta rage wasu abubuwan da wuya ta fita ta kwana a waje duk yawonta zata dawo Hostel.
"Wlh gidan su Surayya naje idan ma baki yarda na kirata yanzu kiji da kunnenki" ta katsewa Afeeya shirun da tayi dason wanke kanta. Wayar Afeeya ta fara ringing akan gado ta ɗakkota tana cewa
"To me kikaji nace Ummi? Duk ma abinda mutum yayi ai dan kansa me kyau ko mara kyau zaka tarar da sakamakonka me sonka ne yake damuwa da abinda kakeyi har yake so ka hau hanyar daidai". Ahmad ne yake kiran kafin ta answer ta ktase se lokacin taga missed call daya mata kafin wannan kiran.
Wani kiran ya sake shigowa, ta ɗaga yana narke murya dan bata so wayar tayi nisa.
"Fatima kin tashi? Ya jikin?" Ya faɗa cikin kulawa, ta kwanta tana cewa
"Da sauƙi, ka kira aka ce ina bacci ne?"
"No, dana kira baki ɗaga ba i called Badar ita ta gaya mun bakya jin dadi ta barki kina bacci i hope you are feeling better now? Kodai zakuje hospital ne kira Ilyas ya kaiku?" Ya sake tambayata a tausashe, a maimakon taji daɗin kulawar tasa ma haushi yake bata ya fiya sanyi da yawa ta muskuta tana cewa
"Nafa samu sauƙi kuma nasha magani, Ilyas na zata ya bar Zaria ai"
"No yana nan be samu sun canza masa din ba so kuma ma saura two months ya gama shiyasa ya haƙura" (cousin ɗinsa ne yaron sister Momy da yake Internship a Shika Asibiti).
"Ayya Allah ya bada sa'a, ya kake? Abujan? Yaushe zaka dawo?"
"Are you missing me?" Ya faɗa yana sakin murmushi najin daɗi yau Fatima ta tambayeshi wani abu daya shafeshi, kunya ta kamata tayi murmushin ita ma amma bata ce komai ba yaci gaba da cewa
"Se Thursday In sha Allah, kina zumuɗin ki ganni ne?"
"Uhm" kawai tace, cikin tsokana yace mata
"Da gobe fa zan taho, sena haɗu da wata yar farar Yarinya me irin zubinki, ita take so ta riƙeni na kasa tahowa".
Ba wani son sa take ba ba amma se da zuciyarta ta sosu da abinda ya faɗa kishi ya taso mata, a ƙufule tace
"Kace kayi budurwa yar Abuja yar gidan masu kuɗi" yanda tayi maganar ita kantaseda ta idar ta fahimci muryar da tayi amfani da ita tayi kauri da yawa ta kuma bayyana kishin daya taso mata ƙarara. Dariya sosai Ahmad yayi tayi shiru kunya da takaicin kanta suka rufeta, seda yayi me isarsa kafin yace
"Ashe dai Fatima na kishina haka? Gaskiya naji daɗi".
Bata sake ce masa komai ba ya gama surutansa tana ji ganin ta ƙi bashi amsa yasa ya canza akalar maganar da cewa
"Haka kawai Tuwo nake sha'awar ci da Miyar Kuka, kamar na tafi Kano yau ma nake ji"
"Ikon Allah Tuwo kuma ka rasa wacce miya seta kuka?" Ta faɗa cikin mamaki dan zata iya cewa a matasa dai shine mutum na farko data taɓajin yana son Miyar kuka, Yah Malam dinsu cewa yayi ganyen bishiyar Aljanu ne tsaɓar hatsabibanci irin na mata suka mayar dashi abinci shiyasa duk me yawan cinsa kwakwalwarsa toshewa take saboda sharri.
"Kuka dai da kika sani, ni ai idan kina so ki burgeni to ki bani abincin gargajiya amma fa with a touch of modernity bawai kuma ayi abu babu sha'awa ba, irinsu dambu, Akubus, Fate, Ɗanwake babu wanda bana ci kuma a kowanne lokaci zan iya ci be it safe, rana dare duk zan iya cinsu musamman idan an shiryashi ya dace da lokacin".
Kai ta ɗaga kamar yana ganinta tace
"Na gane"
"Yawwa idan ma baki iya ba se ki koya dan ni babu ruwana da wasu continental dishes da kika ganni shiyasa ma kikaga nake daidaitan se Umma ta sauke abincin dare nake zuwa gidanku dan ba Ƙaramin daɗin girkinta nake ji ba kuma na ci na Anty Sauda ma naji yayi kalar na Umma Allah yasa kema haka kika iya girki"
"Ina koya" ta bashi amsa a taƙaice tana janye wayar daga kunnenta, minti goma sha daya suna magana zan iya cewa basu taɓa kaiwa haka suna waya ba idan ma sunyi to befi sau a ƙirga ba. Kamar ya shiga ranta taji shima yana cewa
"This is our longest phone call so far, bari na shigar dashi a Diary yau ɗin ta shiga tarihi".
Ta yatsina fuska kamar yana ganinta kafin tayi magana cikin sauri taji yace
"Ki huta Fatima, i will call you later Jafar yana kiran ɗaya wayana".
Wani tuƙuƙin baƙin ciki ya taso mata dajin sunan wanda ya ambata. Ta tsani Jafar ɗin nan tsana me tsanani da bata san iyakarta ba. Bata ko amsa masa ba ta kashe wayar tqna jan mugun tsaki. Maman Minal da bataji shigowarta ba ta ce
"Lafiya kike tsaki haka?"
"Babu komai" ta bata amsa tana miƙewa saboda yunwa data faraji. Ta zuba taliyar data gani a tukunya ta hau ci ranta duk a dagule, ta kusan cinyewa Badar ta shigo da alama ta kwaso yunwa dan hannu kawai ta wanke ta dirarwa abincin da Afeeyan take ci seta tsame hannu ta bar mata dan daman ta ƙoshi gudun kar su mata masifar da suka saba idan ta rage abinci yasa take turawa daƙyar.
"Jibi tuwo zamuci a ɗakin nan" Maman Minal data idar da sallah ta faɗa, Afeeya ta kalleta, Badar tace
"Ai kuwa mun kwana biyu bamuyi tuwo ba. Bari rana ta lafa se muje cefane miyar me za'ayi?"
"Kamar Kuka naji kince ko Afee?" Ta jefawa Afeeyah tambayar, zare manyan idonunta tayi tana kallonta da rashin fahimta dan bata gane inda maganarta ta dosa ba, ita yaushe sukayi zancen tuwo?
Maman Minal Ta miƙe tana ninke sallaya tace
"Zancen tuwo naji sunayi da Ahmad shine naji sha'awarsa nima kinga se ta mana Jibi idan zezo"