← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 137

Sashe 101

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amma Yah Ahmad duk matan da suke Kano ka rasa wa zaka so se Daughter Mechanic? Yar Talaka For heaven sake me take dashi? Sannan har Babanta ya zauna ya gaya maka wasu magana haka se kace ze baka Gold, duk ina Babes ɗin da suke nacin sonka? Ina su Najiba Shaka, Ina Khulsum Galadima yarinyar nan loves you dearly kuma dai duk abinda zaka nema gurin matar Aure tana dashi hankali har yayi mata yawa plus akwai zumunchi tsakaninku and if ba ita ba why not Zahidah Ab..."

'Jafar! Fatima nake so ba wata ba kuma a gurina tafi duk waɗannan da kake jerowa yanzun. What is wrong with her father been a Mechanic? Kanikanci ba sana'a bane? Talauci Fasadi ne? Karka shiga layin da bansanka akai ba kaima ka shiga sahun irin waɗanda suke kyamar wani Abokin Halitta saboda fifikon Arziƙi, idan na samu matsala daga kai i will loose hope dan nasan sauran ma babu me goyamun baya so please Jafar mu ajiye maganar Matsayi ko sana'ar Mahaifinta mu fuskanci ta yanda zan samu amincewar Alhaji akan maganar nan" Ahmad ya dakatar da Jafar.

Daga can ɓangaren Jafar ya fesar da iska daga bakinsa he can't believe simplicity irin na Yaya Ahmad har ya kaishi ga faɗawa soyayya da yar me gyaran Mota, Mechanic fa Yah Ilahi wace irin yarinya ce har haka da ta saka Ahmad ya manta waye shi ya manta gidan daya fito zece ita yake so?"

"Kayi shiru ko baka da abinda zaka faɗa mun?" Ahmad ya sake magana jin bece komai ba se sannan Jafar ɗin yace
"Gaskiya Yah Ahmad nidai idan shawara kake nema a gurina i will say just late that girl go, karka saka kanka matsala itama ka sakata. Iyakar problem ɗin gidanmu ya isa, kana kallon Maman Mu'allim ban sani ko yanzu ba amma sanda nake gida nasan rana daɗɗayane batayin kuka saboda abinda take gani a cikin gidan nan and sauƙinta ma is because Alhaji yana sonta I'm sure shiyasa takai yanzu a gidan nan.

Look at Anty Mardiyya ko cikin Co Inlaws ba kowanne taro take iya zuwa ba because of the humiliation she faced, haka kake so itama matarka ta tashi ana wareta kullum ana zaginta?"

"I'm different from Alhaji And Yaya Naziru, babu wanda ya isa ya wulaƙanta matar Aure na na ɗaga masa ƙafa suma su suka bada damar da ake raina matansu kuma ni ba zan zama irin su ba"

"Zakayita faɗa da yan uwanka kenan saboda matarka?"
"Bazanyi faɗa da kowa ba kuma bazan bayar da hanyar da kowa ze taka matata ba, look Jafar duk ba wannan ta saka na kiraka ba, I have already made my mind so no going back. Nayi magana da Momy ta saka mun Albarka akan maganar i wanted her to talk to Alhaji about it amma tace ba zatayi ba nina sameshi na masa magana kuma ni bansan ta inda zan fara ba, idan yace Aa bansan ta yaya zan roƙeshi ba shiyasa nake so kai kayi masa maganar Dan Allah" Ahmad ya faɗa cikin sigar roƙo.

Yanzu fa kake cewa ka shirya facing kowanne challenge amma kace ba zaka iya yiwa Alhaji Maganarta ba kaga kenan kaida kanka kasan maganar bame yuwuwa bace Alhaji baze karɓeta ba, kuma ni yanzu da kake so nayi masa magana idan nayi and it turns out Negative response nasan ni zaka ɗorawa laifi saboda na nuna maganar batayi mun ba, kayi haƙuri for the fist time bazan iya maka abinda kake so ba, kamar yanda Momy tace ka sameshi da kanka, Yah Ahmad is high time you stand for your self. Alhaji fa ba Dodo bane bare ka ce tsoronsa kake ji, go meet him ka gaya masa buƙatarka but it should be you and him alone, karka bari maganar nan ta fita asan wa kake nema,
Allah ya bada sa'a but i will pray you change your mind kafin ka sameshi because magana ta Allah banji yarinyar tayi mun ba" matsayar Jafar akan zancen Fatima kenan.

A karon farko Ahmad yayiwa wani mutum ƙarya, ya kasa samun Alhajinsu da maganar se kawai ya yanke komawa gidansu Fatima ya kuma tabbatarwa da Mahaifinta yayi magana da nasa Iyayen kuma sun yarje masa daya nemi auranta. A zuciyarsa ya tabbatar Allah baze bashi kunya ba tunda Aure yake so yayi ba wani mugun abu ba, kafin sanda zasu buƙaci ya turo ze san yanda zeyi da Alhaji, idan ma bashi ba Baba Alƙali ze kaiwa maganar Auransa kawai.

"Amma da akwai magana guda, Mamana Karatu takeyi, ta ƙare shekarar farko zasu shiga ta biyu yanzu suna hutu ne saura yan kwanaki su koma A can Jami'ar Zaria take Karatun" Malam Hafizu ya faɗa masa. Ahmad dake durƙushe yana faman sunne kai yace
"Babu komai Baffa, gidanmu gidan Karatu ne. Idan Allah ya nufa zamuyi aure Fatima tana cikin makaranta bbau damuwa zanyi duk abinda ya kamata gurin ganin bata takura ba ko Karatunta be samu matsala ba, sannan idan ta zaɓi har seta kammala kafin muyi Aure zan iya haƙuri na jira lokacin, fatana kawai na samu Amincewarta da taku"

"Allah ya shige mana gaba ya sa a ƙulla Alkhairi, bari na shiga ciki na turo maka ita" cewar Malam Hafizu daga nan ya shige gida.

Tun zuwan Ahmad na farko Malam ɗin ya sanarda ita daya wassafa mata kamaninsa ta ganeshi tunda ba sanin sunansa tayi ba. A lokacin ji tayi kamar tacewa Baffan nata ya sallameshi kawai yace ya mata Miji, tsakani da Allah be mata ba, kuma ita da wanne ido ma zata sake kallonsa bayan wancan abinda ya faru shi ma ya zeyi mata haka ya dawo? Dataji shiru be kirata a waya ba ta zata ya janza shawarane ashe shi me gaba ɗaya ya shirya mata biyowa ta hannun Baffa.

Tana jin yanda Baffan yake ta yabon Kamalarsa da hankalinsa sannan ya gayawa Umma yanda sukayi da abinda yace masa, Jiki a sanyaye ta fita, Dogon Hijabin datayi sallah dashi ne a jikinta, bata tsaya gyara fuska ba balle akai ga fesa turare ko sauran Al'adu da yammata sukeyi idan zasu fita hira haka ziƙau ɗinta ta fita abinka kuma da jiki kalar Madara a hakan ma tayi kyau abinta.

A cikin gida kuwa bayan fitar Fatima Umma tayi jugum kafin ta kalli Malam tace
"Ban tsammaci yaron nan ze dawo ba, Anya kuwa Malam ba'a yi ɗage da yawa ba? Ɗan gidan Alhaji Audu Bechi yazo neman Auran Afeeya, wannan fa ba irin Mijin Yayarsu bane idan ma ana maganar masu Arziƙi irinsu Alhaji Audu a ƙasar nan Sirikin Saudatu inaga ai ko gurin baze leƙa ba, gaskiya ni koda da sahalewar Iyayensa ba zanso wannan Auran ba, Malam kafa san irin zamanin da muke ciki yanda Aure ya zama ƙwarya tabi ƙwarya duk kuma wadda tayi kuskuren faɗawa gurbin da ba nata ba zata fusakanci ƙalubale"

Ki kyautata zato ki kumayi Addu'a Allah ya zaɓa mata binda yafi zama Alkhairi, sannan ki tuna shi yaga Afeeya yace yana sonta bawai tura masa ita akayi ba, Nutsuwa da Kamalar yaron ta burgeni idan har Allah ya zaɓa matashi a matsayin miji zanyi mata murna kwarai dan daga ganinsa mutumin kirki ne" inji Baffa. Umma ta nisa tace

"Toh, Allah ya zaɓa mafi Alkhairi amma dai Alhaji Audu Bechi fa.."
"Ai kingama magana tunda kika miƙawa Allah zaɓi sedai mu zuba ido muci gaba da Addu'a kawai" Baffan ya sake tareta.

Seda Fatima tafi minti biyar tsaye a soro kafin ta hada courage ta fita, wata irin kunya da nauyin sake haɗa ido dashi takeji tasan yana ganinta wancan abun ne zero faɗo masa a rai, da dai taga babu sarki se Allah yasa ta fitan, Ahmad na jingine jikin katanga ta raɓe gefensa tana yar siririyar sallama kai a ƙasa tamkar wadda ya kama tana gulmarsa.

Murmushinsa me kyau yayi ya amsa mata sallamar kafin ya tsaya dakyau yana fuskantarta, har sannan kanta a ƙasa murya a sanyaye ta gaidashi
"Hajiya Fatima, se yanzu sarautar ta sakeki kenan har ina shirin na ƙaraso soron na taroki ai" ya faɗa cikin raha. Bata tanka ba haka nan bata ɗago kanta ba, ya waiwaya ya kalli Dakalin gurin kafin ya kalli mutanen da suke wucewa kamar an basu gadi duk wanda yazo seya zura musu ido sannan ya wuce se ya kalleta yace

"Mu zauna a nan ko mu tsaya cikin soron?"
"Bari na kawo maka abin zama" ta faɗa kafin ta juya cikin gidan ranta babu daɗi, shi gurin zama ma yake nema, ita data fita da niyyar su ƙarƙare kuma yana neman yaja maganar da tsayi.

Kujerun roba ta kawo guda biyu ta saka a Soron ta koma ta dauko pure water da Zobon da Ummansu take siyarwa ta haɗo masa da ƙaramin kofi dukda bata da tabbacin zesha. Seda ta aje komai kafin tace ya shigo, yana ta doka murmushi kamar sabon Ango ya zauna, kallonta kaɗai nishaɗi yake bashi musamman yanda take sunne kai yasan meye dalilinta naƙin haɗa ido dashi amma a ganinsa wannan ai ua wuce, banda abinta idan Allah yayi wata rana na jikinta ma ai wanke mata zeyi balle gurin da ta ɓata. A taƙaice yayi mata bayanin kansa da dalilinsa na zuwa gurinta.
"Kema se ki bani taƙaitaccen bayani akanki" ya faɗa yana ƙarewa fuskarta kallo.

Kyakykyawace Masha Allah komai na fuskarta ɗan daidai hasken fatarta kuma ya ƙara ƙawata kyan nata, tana da tsayi dan ko ze fita da kaɗan ne sannan ba ramammiya bace kuma bata da ƙiba, baze iya ƙiyasta shekarunta ba saboda suffarta irin wadda bata nuna shekaru ce, se kayi wa mutum kallon yaron idan kaji ainihin shekarunsa kuma kayi mamaki. Yanayin zubin jiki da fuskarta yafi kama dana Jajayen Buzayen Niger ko kuma Fulanin Mambila, sannan daga yanayin goshinta ya fahimci tana da kufar gashi, kuma irin me Laushin nan dan gashin goshin nata a kwance yake luf kamar na Jariri sabuwar haihuwa gashi baƙi siɗik.
Chapter 101 · 0% Book details