Sashe 107
Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wayarta ta ɗauka take tayi blocking ta kumayi deleting number Ahmad, an gama chapter sa domin ba ayi wasu Ahali fa zasu wulaƙanta mata Baffanta ba kuma ko Ahmad ne Autan Maza sedai ta mutu batayi Aure ba.
MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*
*BOOK 2*
*PAGE 8*
Sosai Ahmad ya ɗauki fushi da Jafar akan abinda yayiwa Fatima, dukda shi Jafar ɗin ya sauke kai ya bashi haƙuri inda suka sake fafatota da yace se ya kira Fatima ya bata haƙuri ai ita yayiwa laifi nan fa Jafar ɗin yace muddin ba Momy bace bazeyi ba, sedai idan sanadin haka yasa Ahmad yace shi ba jininsa bane amma wlh baze bata haƙuri ba, da niyyar sati uku yazo Nigeria dalili wannan ɓarakar yasa kwana goma yayi a daddafe ya tafi kuma duk gida seda aka gane akwai matsala tsakanin Jay da Yah Ahmad ɗin nasa dan muddin yana gari duk inda zaka gansu tare suke amma wannan karon kowa sabgarsa yakeyi.
Momy ta tambayi kowannensu akan meya faru amma sukace mata babu komai, ta haɗasu tayi musu Nasiha akan karsu bari shaiɗan yayi tasiri a cikin zukatansu, su ɗin sun kasance abin misali cikin zuri'ar Audu Bechi karsu yarda seda girma ya fara zuwa kuma su kama wata hanya ta daban.
"Na san abu biyu shaiɗan yake saurin samun gakaba akan mutum ta dalilinsu, Mace da Kuɗi, karku bari ɗaya daga ciki ya haɗaku kuyi Ƙoƙari ku sasanta kanku" tace musu duk suka amsa mata da "In sha Allah" amma suna fita kowa ya kama gabansa.
Ahmad yanda ya kasa samun Fatima a waya shiya sake dugunzuma hankalinsa har yake ƙara tasirin fushin Jafar a zuciyarsa, Allah ya sani yana sonta, so me tsanani da yake jin tamkar idan be sameta ba ze iya rasa ransa. Daya kasa samun wayarta tilas ya shirya ya tafi Zaria abinda ya Ƙara tunzura Jafar shi kuma tsanar Fatiman ta ninku a zuciyarsa tunda har ta zama silar ruguza Alaƙar sa da Ahmad yayi rantsuwa ba zata shiga zuri'arsu ba domin Allah kaɗai yasan abinda zata haifar musu. Shirin komawa ya shigayi duk da kwanakin daya niyyata basu cika ba kawai gara ya tafi dan baze jure abinda Yah Ahmad yake masa akan Mace ba, Macen ma wadda bata kai matsayin ace Ahmad ɗin ya haukace haka akanta ba.
Har hasaso kamanninta yakeyi Ƙila wata baƙace mummuna da fuskarta kamar ta shafa Baƙin Man da Babanta yake ta'ammali dashi, kai Yarinyar nan ma dole asiri tayiwa Ahmad kuma tilas ya karyashi.
Hajiya kuwa ranta ƙal tamkar zata taka rawa data fahimci yanda abu yayi zafi tsakanin Jafar da Ahmad. Dubunta Hansin ta bawa Turai taje mata gun Malam akan ayiwa musu Farraƙu domin taga alamun Amadun yana neman yasa kwaɓarta tayi ruwa kuma aiki yaci. Duk wani buri da tanadi da take dashi akan Jafar in har yana tareda Ahmad ba zata samu cikar burinta ba Jafar kuma shine makamin ƙare danginta a yanzu. Tana da shiri da kuma tsarin ganin ya zama makwafin Alhaji. Da akwai matattarar sirrin Alhajin inda duk wani abu mai muhimmanci daya shafi rayuwarsa yake da wanda su suka sani harma da wanda basu sani ba takaddun Kadarorinsa na gida dana Ƙasashen waje duk a nan ya ajiyesu.
Wata Safe box ce a cikin Wardrobe ɗinsa ta kaya. Safe ce da akayita da wani irin matakan tsaro ta yanda duk tsiya da bala'i muddin ba wanda ya kulleta ba shi kaɗai ze iya buɗewa babu ta yanda za'ayi lalata tsaronta kuma ba zata fasu ba. Tasha ta saita Kemarar wayarta ta yanda zata ɗauko mata Ɗalamisan da Alhajin yake buɗe gurin dasu amma abu ya faskara kamar ma ba wani abu da yake dannawa se daga baya ta fahimci kwayar idonsa ce mabuɗin gurin, kenan babu ta yanda za'ayi ta buɗu indai ba shine da kansa ba.
Hankalinta yana Ƙololuwar tashi idan tayi tunanin yanzu ace ya faɗi ya mutu ta yaya zasu buɗe gurin su kwashe wasu abubuwan da bazasu so ace sun fito a rabon gado ba sedai ita da Yayanta su handame?
Da fari taso ta tattauna maganar da Zakariyya da Naziru taji ko suna da Mafita, sedai ta fasa hakan saboda ta sani a yanzu ita dasu shegen Sama ne uake dukan na ƙasa, kowanne ƙoƙarin ya gina kansa yakeyi idan kuma ya samu dama ya tattare komai shi kaɗai shoyasa ta fasa sakasu a cikin shirinta. Jafar kaɗai ta aminta da sakashi gaba akan cimma wannan ƙudurin nata, shi take so ya zama magajin Alhaji domin tayi ammanna duk cikin Yayansa babu wanda ya aminta dashi har zuwa yanzu ya sanar dashi ta yanda za'a buɗe ma'ajiyar bayan ransa.
So takeyi ta sake cusa Jafar ɗin jikin Alhaji ta fili data baɗini ta yanda ze Amince dashi ya damƙa wannan Amanar a hannunsa ya zama shine Magajinsa, ita kuma da wannan damar ta samu Jafar ɗin ya gama sanin komai game da Alhajin shikenan burinta ya cika domin se yanda tayi da Jafar ɗin da kuma dukiyar Alhaji sedai wannan muradi nata baze cika ba muddin Jafar yana tare da Ahmad, shi yasa bataji komai ba da Turai tace ta bada kuɗi zata je mata inda suka kai sunan Abba T saurayin Hajiya Ƙarama domin dukda dukan daya sha a hannun Yakubu be haƙura ba, ya dawo amma a can gidan Haj Turai sukeyin Hira ko kuma su fita yawo gari maganar da ake yanzu ma Bayan sallar Azumi yace Iyayensa zasu zo tambayar masa Auranta. Babu wanda ya san zancen a gidan kosu Naziru Hajiyar bata gayawa ba tace sedai aji komai katsahan tunda har a yayan cikinta akwai masuyiwa Hafsatun baƙin ciki.
Ahmad na Zaria Jafar ya tafi dan tarewa yayi a Hotel kullum haka ze je Samaru ya wuni a Faculty of Art yana bibiyar ta inda ze gamu da Fatima amma taƙi yarda su haɗu se ranar daya kwana uku ne ya samu nasarar ganinta sammako ya buga tun bakwai yaje ya zauna a bakin Class ɗin da zasuyi Lecture, a gurin wani Guy ya samu Time table ɗinsu bayan daya nuna masa hotonta ya tabbatar masa ya santa bata zuwa Class kwana biyu amma na goben ya tabbatar zata zo indai tana Makaranta dan Malamin baya wasa Individual Attendance yake ɗauka and is automatic carry over idan mutum yayi missing wannan tasa ya tafi da wuri, 8 zasu shiga amma 7 bata gama rufawa bama ya kafa ya tsare a bakin Ƙofa.
Yana tsaye a gurin suka zo ita da Badar da wasu yammata biyu, bata ganshi ba se Badar ce ta nuna mata shi tana cewa
"Kinga Ahmad"
"Ahmad?" Ta maimaita da mamaki tana kallon inda take nuna mata se gashi kuwa a tsaye ya zuba hannaye a Aljihu yana binta da kallo suna hada ido maganganun Jafar suka fara dawo mata tamkar a lokacin yake faɗarsu wannan tasa tayi saurin ɗauke kanta ta doshi class ɗin da sauri dan ba zata bari ya tareta ba amma kafin ta shiga yasha gabanta.
"Ka matsamun na wuce" ta faɗa ba tareda ta bari sun haɗa ido ba saboda yanayinsa da yake neman karya mata lago ya samu galaba akanta.
"Zan jiraki a waje ku gama" ya faɗa a sanyaye yanajin tamakar ya rungumeta saboda So, taja baya saboda kusancinsu yayi yawa tana cewa
"Karka jirani dan ko ka zauna bazan saurareka ba"
"Shikenan, zan shigo Ajin na roƙi Lecturer ya bani dama a gaban kowa nayi magana dake hakan ya miki?"
Yanda yayi maganar ta fahimci ze aikata abinda yake nufi dan haka tace
"Karka shigo, ka jirani a waje"
"Good girl" ya faɗa yana mata murmushin ƙarfin Hali, kansa ciwo yake masa be taɓa zaton haka so yake dagaske ba. Fatima ta wuce, Badar ta matso fuskarta ɗauke da fara'a, she is lively ko yaushe fuskarta a washe take kamar ta Ahmad ɗin muddin ba an tsokalota bane.
"Hi" ta faɗa tana waving masa,
"Hello Badar" ya mayar mata yana ɗaga mata hannun shima bakinta har kunne jin ya ambaci sunanta, ashe dai Fatima ta bashi labarinta.
"Karka damu, just give me your number, kaje ka samu comfortable guri ka zauna i will bring her to you damun gama Class" ta faɗa tana bashi wayanta. Ya karɓa ya shigar da Digits ɗinsa kafin ya mayar mata yace
"Nagode Badar, i will be in Shinkafi Elite, zan jiraku a can"
"Ayt, se munzo" ta sake ɗaga mishi hannu kafin ta shiga Ajin ta zauna kusada Fatima dake leƙensu ta window, duk a kan Idonta Badar ta bashi wayarta tana ganin yanda suke ta wani Murmushi duk seta tsargu. Badar batace mata komai ba har akayi Lecture aka gama suka fito, tana lura da yanda take satar kallon gurin da alama Ahmad yake nema amma bata ganshi ba A zuci Badar tace
"Munafuka kawai tana so tana kaiwa Kasuwa".
Suna tafe duk Fatima bata da laka, tunani takeyi ko ya tafi? ƙila ya haƙura da itan kawai tunda har ya karɓi number Badar.
A hanya Badar tace su biya ta Shinkafi su siya Chips tace ta ƙoshi amma Badar ta nace se sunje in yaso ta siya ita kaɗai.
"Kije can ki zauna kinga akwai layi kafin azo kanmu" ta nuna mata Table ɗin dake kusa dasu, Fatima tayi tsaki, can ƙarshe ta wuce seda ta zauna kafin ta lura da Ahmad ne a gurin. Zabura tayi zata miƙe ya dafe hannunta, karo na farko da hakan ta faru tsakaninsa da wata Mace da ba Muharramarsa ba. Cikin sauri ya saki hannun nata se kuma ya miƙe tsaye ganin tana shirin barin waje yace