← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 137

Sashe 88

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya nuna Hafsatu da yatsa yana cewa
"Ashe abinda ake faɗa akanki gaskiya ne? Iskancin da aka ce kinayi dagaskene saboda kin shahara yanzu har cikin gidan ubanki kika kawo saurayi zakuyi iskanci?" Kai ta shiga girgiza masa tanaja baya domin Yakubu bashida daɗi, ba su ba uwar data haifeshi ma shakkarsa takeyi dan Lamarinsa me girma ne. Hajiya Binta ta dake tana hararar sa tace

"Kai bana son ɗiban Albarka, a gidan uwar masu faɗar aka ganta tana iskancin? Koda uban wani tayi a cikinsu da har suke bayar da shaida? Bakaji me nake faɗa bane? Ce mata nake fa ta saki jiki dashi ita ai gida huma ce duk samarin da kake gani suna zuwa suna tafiya ai ƙin basu fuska takeyi shi yake korarsu. Shifa wannan ɗin in gaya maka, Yaron Alhaji Mudi Tanko ne tsohon Senet piresiden kuma yanzu haka takarar gwamna yake a Garinsu, can kwanaki bana muku zancen sa ba har yazo sau ɗaya shine ya tafi be sake dawowa ba? Ai in gaya maka wannan shashashar yarinyar ce ta kusa kwafsa mana, wai fa ɗaukarta yayi sukaje Otal ya kama Ɗaki, daga cewa su shiga ciki shikenan ta gudo wai har da ce masa ita ba yar iska bace se kace yace mata wata tsiyar ze mata idan suka shiga. Shiko yayi fushi ya tafi, dakyar fa yanzu seda na baiwa Turai dubu ɗari ta kaiwa Malaminta akayi aiki akansa shine fa ya zo yanzu, faɗan da nake mata kenan kar a maimaita ta wnacan karon a samu a kamashi a hannu ya fito ayi zancen Auren nan masu yi mun dariya su sha kunya suji da ƙaryar sarauta suzo suga Arziƙi a inda yake dan duk na samu labarim gidansu ba ƙaramar wadaƙa ubansu yakeyi idan ya tashi Aurar da Yara ba".
Yanda take maganar hankali kwance tamkar me faɗar wani abin Arziƙi, Yakubu yayi sakato yana kallonta a ransa kuwa kokwanto yakeyi akan Hajiyar ce ta haifi Hafsatu ko kuwa Riƙonta takeyi?

Anya uwa zata yiwa yarta irin wannan huɗubar kuwa?
"Zatayi mana, mussamman uwa irin taku da take bautawa duniya da abinda yake cikinta" zuciyarsa ta bashi amsa. Seya ja numfashi ya furzar kafin ya zabura ya nufi ƙofa, cikin Hajiya ƙarama ya kaɗa, Hajiya kuwa yatsine fuska tayi tace

"Ke da Allah rabu dashi, ance masa bansan duk abinda sukeyi bane su? Duk fa haka suke lallatse yammatan suma suna basu kuɗi balle ke da Aurenki ma zeyi jeki abinki manta dashi kar kuma ko manta uar soyayyar nan da ake nunawa a fim irinta zaki masa kinji ki hargitsa masa tunani yayi maza maza ya turo azo ayi magana kar zancen Auran Aslamiyya ya riga naki tashi".

A saluɓe Hafsan ta fita duk karsashin da take dashi ya barta. A ƙofar fita daga ainahin cikin gidan taci karo da Ali Daya daga cikin Ma'aikatan gidan me kula da shuke shuke, da gudu ya taho badan ta matsa masa ba da tuni yayi tafiyar gari da ita.

"Yawwa Hajiya kiyi sauri, ga Alhaji Yakubu can yana dukan baƙonki" ya faɗa yana haki. Ƙirji ta dafe tana zaro ido daga inda take kuma tana iya jiyo ihun kukan data tabbatar na Abba Tee ne da kuma hargowar Yakubu yana faɗin
"Daga yau ka sake zuwa wani gida ka yi iskanci da ƙanwar wasu". Da gudu ta juya ciki tana kuka tana kiran Hajiya. Binta nacan tana gyara zaman kofunan da za'a kaiwa Baƙon tana kwararaqa me aikinta Ashar akan wai bata goge su dakyau ba so take yace musu ƙazamai sega Hafsa na kuka jage jage, bata ko iya sauraronta gaba daya ba tayi waje cikin tashin hankali tana kiran Yakubu.

Yakubu kuwa dukan Ɗa da Uba yakeyiwa saurayin Hafsatu ya fasa masa baki da hanci ga hauri yana kai masa a ƙafafu yana kiran seya karya su yaga da wanda ze ringa yawon iskancin Hajiya ta iso ta cakumeshi tana zaginsa se kuma ta saka kuka tana cewa

"Shikenan kaima an taɓa ka, nidai yanda naga ka fito ido a jirkice daman kamar wanda iska ta shafa nasan da walakin, ni aka tozarta a gidan nan ko? Anga Asirin da akayiwa Yata yaƙici kullum sababbin Manema take samu shine aka biyo ta wannan hanyar ko? To wlh mu zuba mu gani, bana Boka bana Malam amma ko wanene ya taɓani seyaji a jikinsa" se kuka wiwiwiwi. Ma'aikatan gidan gaba daya sukayi dafifi suna kallon ikon Allah, Drama a gidan dai ba sabon abu bace ta safe daban ta rana daban ba kuma sa gundira da tirka tirkan gidan domin kullum sabon abu suke gani. Audu da hayaniyar ta fito dashi ya isa gurin cikin dakakkiyar murya yake tambayar abinda ya faru se sannan kuma Abba Tee ya samu ya miƙe ya nuna Yakubu yace zasu gamu seya san shiya taɓa, Yakubu ya zabura ze sake damƙarsa ya taka ya gurin motarsa da sauri ya shige yana cigaba da faɗin
"We shall meet in court, zaka san ni ka daka se ka gane baka da wayo".

Cikin tsawa Audu ya bawa ma'aikatan umarnin su watse kowa ya juya gurin aikinsa. Ya kalli Hajiya dake kuka har sannan Hafsatu ta runguketa itama tana kukan kafin ya mayar da hankalinsa kan Yakubu yana tambayarsa meya faru? Waye wancan ɗin kuma meya haɗa u harta kai ga duka? Kafin ya bashi sa Hajiya tayi zuruf tace

"Me kuwa ya haɗasu? Magautane sukayi masa turen Aljani haka kawai ya rufeshi da duka saurayin Hafsa ne fa, anga Allah ya fito mata da Miji na nunawa Sa'a shine aka bi yanda akayi shima aka koreshi kuma wlh ba'a taɓa banza ba ko wacece a cikin matanka tayi abin nan ta kwana da shirin zubin Adashi tayi ɗauka kuma dole, ka wuce kai kuma ka kwanta kana tsaye kana wa mutane muzurai ko Aljani ƙarƙuzu ne wlh sekaci ubanka sannan ka koma kan wadda ta aiko ka" ta faɗa tana aikawa da Yakubu wata harara me tafe da gargaɗi. Juyawar yayi kamar yanda tace ya fice daga gidan gaba ɗaya ita ma suka koma ciki da Hafsa dake kuka har sannan.

Alhaji Audu ya sauke ajiyar zuciya me ƙarfi yana kallon Ma'aikatan gidan da duk suka maida hankali kamar masuyin wani abun ya tabbatar kuma kunnuwa da hankulansu har sannan yana kansu, an gama na ɗazu ga wata an sakeyi kuma, idan ba'ayi sa'a ba kafin kwanciyar bacci se an kuma kafta wata Drama. A sanyaye ya ringa taku ya fita ya shiga Masallacin dake manne da gidan tunda Magriba ta kawo kai saura mintina kaɗan a kira. Carbi yake ja amma ya lula cikin tunanin daya aureshi, bashi da damar yayi shiru haka nan ko yayi tunanin abu me daɗi kullum se damuwa se ɓacin rai daga wannan se wannan.

Wayar sa dake gaban Aljihu ta ɗauki Ƙara ya zarota, Alƙali Yakubu ne, miƙewa yayi ya fice daga cikin masallacin ya tsaya daga gefe lokacin wayar ta katse dan haka yabi bayan kiran. A taƙaice suka gaisa, Yakubun ya tambayeshi yanda Zaman su ya ƙare da matsaya akan zancen kuɗin.

"Mun rigada mun gama magana yayi rantsuwa akan bashi ya ɗauka ba kuma na yarda amma na sauke shi daga kujerar Takwaranka ze riƙe na lokacin kafin musan abinyi" Audun ya faɗa masa. Daga ɗaya ɓangaren Yakubu yace
"Idan har ka yarda dashi menene dalilin daya saka ka dakatar dashi daga aiki kuma?"

"Haka dokar take a rubuce, duk wanda aka kama da laifin cin hanci ko yiwa Kamfani zamba hukuncinsa korace sannan ze maido da duk abinda aka rasa, bamu baƙaci ya mayar da komai ba amma an dakatar dashi saboda idan banyi haka ba kamar na buɗe Ƙofa ne ga sauran kowa ze iya wasarere da dukiyar Kamfani saboda yasan babu matakin da za'a ɗauka akansa, kuma dalilin daya saka bamu buƙaci ya maido da kuɗin ba saboda Bincike ya tabbatar da basu shiga account ba, a rubuce ne kawai akwai su kuma idan aka tattara lissafi ya kamata ace suna ciki sedai am rasa ta inda suka maƙale".

Dariya jawabin Audun ya bawa Yakubu ya dara kafin yace
"Ai shikenan, tunda har ka gano da kanka inda matsalar take ina ganin babu laifin Aminu kamata yayi ka tattara shuwagabannin kowanne ɓangate su gabatar maka da lissafinsu da kansu sannan ka haɗa dashi wamda suka bashi daga nan za'a tantance me laifi da me gaskiya, most especially guraren da kuke generating kuɗi sosai Oil da sauran Mineral su ya kamata ka tsananta bincike akai na tabbata daga nan matsalar take" Yakubun ya bashi shawara daga nan suka ɗan tattauna wasu batutuwan kafin sukayi sallama dalilin sallah da aka kira.

A cikin gida kuwa a tsakar gida Hakiya ta kafa kujera tana zazzaga bala'i, daga Momy Har Anty babu wadda ta leƙo ballantana ta tanka mata daman da Baba Bilki tana nan ne itace zata kulata to tana gidan Sarki matarsa ta haihu ita take zauna mata. Har aka kira sallar Magriba batayi shiru ba bakinta har kumfa yake yawu na sarƙeta amma taƙi haƙura ita kanta Hajiya ƙaramar datayi iyakar yinta akan Hajiyar tayi shiru taƙi ɗaki ta shige tana cigaba da kukan Asarar da Yaya Yakubu ya janyo mata, ita ai bata ce masa zata biye ta zancen Hajiya ba domin da tana hawa layin data ke ɗorata da tuni ta daɗe da zama riƙaƙƙiyar karuwa a cikin gida domin abinda Hajiyar take nuna mata kullum shine tayi komai ba komai bane muddinba bude ƙafa zatayi ba. Ta rasa irin tunani da son zuciyar Hajiya, bata duba mutunchinta ko zunubin da zasu ɗauka da ita me aikatawar da ita data turata burinta kawai ta cafko musu Dan Attajiri wanda ya kere Mijim Anna dana Khadija da kuma saurayin da yake neman Aslamiyya tunda bata samu yanda take so akan Nazira data janyowa Nakasar data so ta hanata Auruwa daga ƙarshe Audun ya haɗata da wani Yaronsa babu laifi yana da abin hannunsa daidai Misali shima kuma yana sonta.
Chapter 88 · 0% Book details