← Book details Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 137

Sashe 59

Matar Mutum Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Binta ta kawo masa abin kari yau din jinta take kamar wadda akawa Bishara da Aljanna. Lantana ce tayi mata albishir din taga Zubaida a hanya da jaka sanda take tahowa ta gaji kenan ta tafi ba kuma zata dawo ba. Tana so ta zungureshi da maganar taji ko ya sani amma dai tayi shiru harya karya ya fito ta rakoshi ta ringa dariya qasa qasa ganin ya doshi dakin Zubaidan yana kwazara mata kira nan ma shiru bata amsa ba.
"Wai ina wannan yarinyar ta tafi?" Ya jefawa Binta tambayar ta watsa hannu tace
"Yo ka bani ajiyarta ne da zan san inda zataje?"
"Shikenan sena dawo" ya fada daga nan ya fice yana mamakin ina zataje dan sam be kawo gida ta tafi ba tunda ai bata san abinda takardar daya bata ta qunsa ba, haka ya dawo gida da yaqinin ze tarar da ita amma wayam bata nan, ya diririce, ta tabbata gidansu ta tafi kenan amma me yasa zata tafi to? Ya jefawa kansa tambayar rainin wayo.

Bayan Isha ya shirya tsaf ya cewa Binta zeje wata unguwa, gidansu Zubaidan ya tafi zuciyarsa ta ringa tuhumarsa me ze kaishi gidan amma hakan nan ya zungura kai yaje. Malam Hassan ya rasa ina ze sakashi saboda murna bayan sun gaisa ya tambayeshi Iyali yace
"Dazun Babarsu take cewa gobe In Allah ya kaimu zata leqa ta ganota kuwa jiki yayi nauyi har tana cewa ko zata dakkota tazo gida tunda haka akeyi a Al'ada haihuwar fari"

Cikinsa ya bada wani sauti quuuu, bata zo nan ba kenan? To ina yarinyar nan ta tafi kardai fa ta hefashi a masifa in duniya ta sake shiga ai da seta bari seta zo gidansu ta gayawa Mahaifinta komai sannan seta tafi amma yanzun ta ina ze fara yi masa bayanin shima nemanta yazo?

"Aa bafa abin dole bane idan baka so ta dawo gidan se tayi zamanta dan naga fuskarka ta canza daman matane da Al'ada kasansu basa wasa da ita" Mala Hassan ya katse masa tunani a zatonsa zancen dawowarta gida ne ya canza fuskar Audun besan Al'amarin yafi gaban haka ba. Tilas ya masa sallama a gurguje ya taho bayan ya ajiye masa na goro.

A gida ma rkicewa Binta yayi da tambayar ina zasu nemo Zubaida ina ta tafi?

"Ya wuce ta koma inda ta fito ne, wai kai meye ma naka na damuwa ina ka saketa duk ma inda zataje taje mana kana da matsala da ita ne?" Ta fada cikin jin haushin yanda yake ta safa da marwa cikin damuwa. Washe gari da farar safiya ya tafi gidan Yakubu ya ringa buga musu qofa kamar za'a tashi duniya Yakubun ya fito yana ganin shine ya shiga surfa masa fada shima yana tambayar ba'asin wannan bugu kamar ya masa sata. Daya masa bayanin abinda ya kawoshi qiris ya rage Yakubun yayi dariya amma ya kanne a ransa yayiwa Allah tasbihi wato tun ba'aje ko ina ba aiko ze gane kuskurensa domin baze fada masa tana gidan ba.

"Ni meye nawa a ciki yanzu Audu? Kashedi nawa kamun akan na fita daga sabgar gidanka? Ashe da nace kayi haquri ka bar maganar nan baka daddara ba to ka saketa ta bar maka gida meye kuma abin damuwa a ciki ko daman ka dauka zata zauna ne kuci gaba da ci mata mutunchi kuna aibatata kaida matarka?" Yakubun ya fada yana tsareshi da ido. Audu yaja tsaki yace

"Ni bance ta zauna ba amma data tashi tafiya ai seta tafi gidansu ko amma yanU naje jiya bata can yanzu me take so na gayawa mahaifinta idan suka zo ganinta basu sameta ba?"

"Se ka gaya musu ka saketa ita kuma tana tsoron ta tayarwa da mahaifinta hankali idan ta koma gida shine ta sake shiga duniya, ni dana san wannan shirmen ne ya kawoka wlh bazan bude qofata ba haka nan ina bacci na me dadi ka daga mun hankali da bugu. Ka tafi ka nemo yarinyar mutane dai kafin iyayenta su farga, kaga daman ba'a jima nayi wani case Mata ta bata Iyayenta sukace Mijin ne ya siyar da ita yayi kudin jini AAllah ya tsareka kaima kar suce kayi kudin jinin da ita daman an fiyi da masu ciki" yana gama fada masa hakan ya maida qofarsa ya rufe ya bar Audu cikin tashin hankalin daya ninka na farko akan maganar da yayi ta karshe.

Daman a Bechi ana rade radin qungiyar Asiri ya shiga yayi kudi farat daya da yawa sun qaryata cewar wai sirikinsa kuma ubangidansa ne ya buda masa yake samun kudi haka? Su kance shi din har nawa ya mallka da yake bawa Audun kudi haka? Zancen da akeyi yanzu rabi da kwatan Gonaki da filayen da suke a Bechi mallakinsa ne saboda duk wanda ya daga fili ko gona ze siyar da an tallata masa ze siya a farashi me daraja kuma shiyasa wasu ma haka nan suke siyar masa suje wani gurin su sake siya ragowar kudinsu susha shagali yanzu idan wannan magana taje Bechi ace matarsa ta bata da tsohon ciki la shakka cewa zasuyi yayi tsafi da ita kawai.

https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*PAGE 23*

Sati guda ya shude Audu na bulayin neman Zubaida sedai sama ko qasa babu ita babu kuma wanda ya ganta bare asan labarin inda tayi. Har Zariya sukaje da Bashir gidan daya dakkota suka tarar an tashi gidan ma gaba daya titi ya biyo ta kan hanyar haka suka juyo Kano babban abinda ya qara daga masa hankali ya bazama nemanta zuwan da Baba Zayya tayi akan taje duba Zubaidan Allah ya taimake shi yana gida ranar, daya rasa abin fada mata dole ya rangada mata qaryar Zubaidan tana Bechi, kuma daman yaso yaje ya sanar dasu tana can har se bayan ta haihu zata dawo Kano to Allah be nufa ba. Dake akwai yarda da Amana sam Baba Zayya bata kawo komai a ranta ba tunda ana hakan mace ta tafi garin su Miji haihuwa dan haka tayi musu sallama ta koma gida ta shaidawa Malam Hassan yanda akayi.

Wannan dalili ya qara zaburar da Audu ga neman Zubaidan, nadama mara amfani ta dirar masa biya hukuncin daya yanke ba tareda zurfin tunani ba. Haka ya ringa raba kudi wa malamai akan ayi masa Addu'a Allah ya bayyana Zubaidan ya kuma kareta a duk inda take. Cikin wannan yanayi Alhazai suka fara tashi, Binta taje gida tayi sallama da danginta ta dawo tana ta shirin tafiya sauke farali bacci ragagge takeyi saboda jiran ace su fito. Ita sam ta manta ma da wata Zubaida balle batun ba'a ganta ba, yanda Audun be cika nutsuwa ba a lokacin yasa ta tsahirta masa, ita kadai take ta shirinta tunda dai ya sallameta ya bata Guzuri me auki ita kam ya gama da ita se jiran ranar tashi kawai takeyi.

Acan gidan Yakubu kuwa hankali kwance Zubaida ke zamanta, tsakanin Balaraba da Yakubun ba zata tantance wanda yafi tattalinta ba. Duk wani abu da zata buqata suna mata haka nan basu barinta ta zauna shiru balle ta fada tunani ko wata damuwa a koda yaushe cikin hikima sukanyi mata nasiha akan rayuwa da qalubalen da yake tattare da ita. A dan taqin zaman ta fahimci banbance banbance masu tarin yawa da suke cikin rayuwar Haske data duhu ma'ana rayuwar da akeyinta cikin sani da wayewa ta Addini da kuma rayuwar Bidin bidima irin wadda tayi a baya ta koma dora yinta a gidan Audu.

Yakubun jajirtaccen Namiji ne wanda yake tsaye akan lamuransa dana iyalinsa. Ga daishi be tara dukiya tamkar dan uwansa ba amma rayuwar gidansa ta zamo abar sha'awa wadda duk me hankali idan aka bashi zabin kudi ko nutsuwa irin ta gidan Yakubun tabbas baze tsallaketa ba.

A kullum da Asuba seya dorawa matarsa da Yayansa karatu haka bayan sallar Isha'i idan sun zauna a maimakon hirarrakin banza na duniya sukan yi tasu hirar ne akan karatuttukan da sukayi. Ya tambayesu su tambayeshi, hatta da Qaramin dansu Tijjani me shekaru uku a sannan Alqur'ani ya fara zama a bakinsa, haka qananan Hadisai da ake dorawa Yayinsa yana tsinta har idan Yakubun yana tambayarsu sukayi kuskure Tijjanin da suke kira da Alhaji ze gyara musu ga wayewa ta boko turanci yafi hausa Nuna a bakinsu kodan inda suke zaune yaren da suka fi amfani dashi kenan? wannan abin ya matuqar birgeta ya kuma zaburar da ita kan cewar itama bata makara ba tana da damar da zata nemi ilimi tana kuma burin abinda zata haifa ya tashi cikin irin wannan rayuwar ta ilimi ba irin ta gidan ubansa ba.
Chapter 59 · 0% Book details